Showing 78001 words to 81000 words out of 288773 words
Chapter 27 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt
part d'in, shima matsakaicin parlour ne amma komai orange kalar da khaleefa yafi so, auntie tasa akayi gyara na musamman gab da dawowar nan tashi, bedroom biyu ne a ciki kowanne da bathroom. Zama yayi kan center table da yake tsakiya ya tambayi Ayman, wanne ne room d'ina a ciki? Da mamaki Ayman ya dube shi, ganin kamar bai fahimci abinda yake nufi ba saiya sake maimaita tambayar shi, dai dai lokacin ne kuma auntie ta shigo rik'e da tray na shayi ita da shaheeda, a dawowarta yanzu harta had'a shayin da zasu sha.
Mik'ewa khaleefa yayi ta ajiye trayn akan table d'in daya tashi, shi kuma Ayman cikin mamaki da jin abinda bai tab'a zato daga d'an uwan shi ba yazo gaban shi ya dafa kafad'ar shi, "na d'auka komai muna yin shi tare ne dama nida kai tun kafun tafiyarka karatu...., ka tuna yadda muke cin komai a plate guda mu kwana a muhalli d'aya? Mu saka Kaya iri d'aya....". Wani murmushin gefen baki khaleefa yayi ya girgiza mishi kae, ya cire hannun shi daga gefen kafad'ar shi yace, "ai wannan abu ne wanda ya dad'e da zama tarihi, tun daga ranar dana taka k'afata Germany na kwana biyu ba tare dana ganka ba, ba tare da munci abinci tare ko kwana tare ba na dad'a tabbatar da zan iya rayuwa ni kad'ai ko banji daga kowa ba....... Soo ka nuna mun wanne ne d'akin ka a ciki".
Yadda Ayman yayi surrender haka auntie da shaheeda dake tsaye bayanta. Babu musu ya nuna mishi nashi d'akin, sai ya nufi na kusa da wanda Ayman ya nuna a matsayin nashi zai murd'a handle ya shige, maganar Ayman ta dakatar dashi, "khaleefa idan na fahimce ka a dai dai, maganar ka tana nufin zaka iya rayuwarka kai kad'ai koda bana raye a duniyar nan ba tare da kaji kewata ko wani abu na daban ba.....". Bai k'arasa zancen ba Auntie ta d'auka, "ba Kai kad'ai ba Ayman hadda ni, yana nufin zai iya rayuwar shi shi kad'ai ko babu mua tare dashi.......".
_Comment and share_
24/03/23, 2:02 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page twenty two2️⃣2️⃣
Bai juyo ba ya bud'e k'ofar kawai ya shige, duk suka bishi da kallo har shaheeda da take tsaye bayan Auntie, yau ta tabbatar da abinda auntien take yawan fad'a akan khaleefan a duk lokacin da mammie tayi maganar halayenta, auntie takan ce khaleefa baud'ad'd'en mutum ne mai baud'ad'd'en ra'ayi da hali sab'anin na mutane.
Bayan d'aukar lokaci mai tsayi shiru, auntie ce ta ce da Ayman daya shiga damuwa, "ka d'auki duk wani abu da kasan nashi ne ka kai mishi ciki, kada ka sake ce dashi komai". Cikin ladab Ayman yace, "insha Allahu Auntie". Tace, "gud ga tea nan akwai snacks da nayi tun kafun mu tafi shaheeda zata kawo muku anjima kad'an,and please in shi bazai ciba kai nasan kana so kaci abinka". Girgiza mata kai yayi cikin sanyi "a'a Auntie ki barshi kawai naci abubuwa da yawan gidan iya am okay". Sai da tayi nazarin shi kad'an kafun su futa daga parlon ita da shaheeda, tana ganin Ayman ranshi ne ya b'aci kurum, kuma da zarar an d'au wani lokaci zai huce shi da kanshi don baya iya dogon fushi da kowa haka zuciyarshi take.
Shi kuwa khaleefa matsalar shi.......... Sai kawai taja ajiyar zuciya.
Khaleefa kuwa yana shiga d'akin bin komai yayi da kallo, babu komai a ciki sai uban girman d'aki fetal, zama yayi a k'asan gurin ya had'a kanshi da gwiwa yana ambaton sunan Allah, ya kasa had'iye damuwarshi shi, ji yake kamar yayi ta ihu a duk lokacin daya kalli fuskar auntie ya tuna ta samar dasu bata hanya me kyau ba, hanyar da duk wani musulmi me Imani yake kyamata wato *Zina*, wannan abu yasa yake misbehaving duk lokacin da zasu kasance tare, wannan kalma ta *shege* tana dukan ranshi tana cin zuciyarshi kwarai, musamman in ya tuna akan haka zai rasa Saleema, macen daya fiso bayan auntien shi a duk duniya, wayyoh Allah sai yaji kamar zaiyi hauka a garin nan don tashin hankali, rashin uba ba k'aramin gararanba rayuwar mutum take fad'awa ba, bana rashin abinci da abin sha ko sauran buk'atun rayuwa ba, a'a rashin baya jigo majingina kuma garkuwa a tare dasu, tabbas uba gata ne ga kowanne yaro musamman a wannan zamanin da muke ciki.
D'ago kanshi yayi jin an bud'e k'ofar d'akin shi, Ayman ne ya tattaro duk wani abun da yasan zai buk'ata ya kawo mishi, suka dubi juna lokaci d'aya kowa ya d'auke kanshi gefe, haka Ayman yayi ta shiga yana kawo mishi abun amfanin shi na yau da kullum, ya kai na bathroom ya ajiye mishi, ya dawo ya shimfid'a mishi carpet ya ajiye mishi praying mat a kai.
"Thanks" khaleefa ya fad'a mishi a lokacin da zai fuce daga d'akin. Uhm! Kawai shima Ayman ya fad'a yayi hucewar shi.
Ko bayan ya futo wanka shiryawa yayi cikin kayan bacci farare k'al ya nemu guri gefe d'aya ya zauna ya kunna wayarshi, so yake yaji daga Ahmad ta hanyar watsapp sai dai koda ya duba shiru, sai no Saleema da aka ajiye mishi sak'o, yana bud'ewa yaga voice note uku sai rubutu a k'asa inda tace, "I'm really Sorry it's not my fault, try to understand me khaleefa.....". Tsaki yaja me tsayi a fili har zeyi playing voice d'in nata sai kuma ya fasa gudun kada ya sake jin wani abun b'acin ran ko sare gwiwa da zai sake jefa shi cikin tashin hankali da damuwa. Tuni ya sanya su a delete ya sauke layin ya kakkarya shi. A fili yayi magana kamar wani yana sauraron shi, "daga yanzu har zuwa lokacin da zaki zamo tawa baza ki sake ji daga gareni ba, nayi alk'awari saina shayar dake ruwan mamaki Saleema.
_(nikam nace ayyah khaleefa rashin sani yafi dare duhu)_
Asalin abinda ya faru a Germany. 👇
Saleema ta kasa jurar rashin khaleefa, ta shiga tashin hankali data tabbatar da yabar Germany ba tare da yaji wani abu daga gare ta ko ya neme taba, k'awarta Amna ta tabbatar mata da cewa khaleefa yana nufin ya barta ne har abada, ai dama ta shaide shi akan zuciya in yabar abu ya barshi kenan fintinkau baya sake waiwayen shi Hakan yasa a washe garin ranar ta kasa nutsuwa har saida tayi mishi voice na kwantar da hankali da K'arfafa gwiwa, ta fad'a mishi mahaifinta zai iya saukowa saboda albarkacin soyayyar da yake mata, na biyu yayi k'ok'ari ya samu ko mutum d'aya ne daga dangin mahaifin shi suzo ayi maganar aurenta, daga k'arshe ta nemi yafiyarshi ta fad'a mishi kuskurenta akan karyewa da zuciyarta tayi da farko, yanzu kuma data fahimci ba zata iya rayuwa ba tare dashi ba saita bawa kanta kwarin gwiwa shima take k'ok'arin bashi.
Shi kuwa khaleefa a rashin sani ya goge duka muhimman sak'onnin.
(Nikam nace rashin fahimta, tuntub'e dad'in gushi......)
★★★★
Kamar yadda yake bisa al'adar khaleefa sallar subh bata tab'a huce shi haka yauma ya tashi da wuri, ya fad'a bathroom ya d'auro alwala ya sauya kayan jikinshi zuwa jallabiyyah brown colour. Kusan tare suka futo da Ayman lokacin da aka tada sallah. Take Ayman ya shanye komai ya k'irk'iro murmushi akan fuskarshi ya mik'a mishi hannu, shima hannun ya bashi sukayi musabiha sannan suka d'auki hanyar masjid a tare. Ko bayan da aka idar da sallah ma tare suka dawo khaleefa yana sake k'arewa gidan kallo, suna tafe kan stairs ya kasa hak'uri yace, "yanzu wannan gidan auntie ita da waye zasu zauna a ciki haka?". Cikin jin dad'i Ayman ya kalle shi don bai d'auka wannan sabon khaleefan zai sake yi mishi wata magana ba, sai yace, "tun jiya kake maganar nan, toh ai babu laifi muna aure zakaga mun cika mata gidan taffff!". Murmushi khaleefa yayi a zuciyar shi yana tausayin k'anin nashi, da baisan abinda shi ya sani game dasu ba, ko waye zai bashi aure babu uba da dangin shi?
A nan parlour suka zauna su duka, Ayman ya danna switch haske ya gauraye ko'ina, khaleefa ya fara lazimin shi shi kuma ya kwanta ba jimawa ya koma baccin shi. Sai da gari yayi haske sosai sannan khaleefa ya shiga d'akin daya zab'ar wa kanshi, ya sake gyara ko'ina ya had'a ruwa a heater ya shiga wanka.
Bayan ya futo ya shirya cikin d'aya daga shaddojin da mahaifin Ahmad ya basu, ya tsaya jikin windown d'akin yana kallon yadda wasu yara matasa maza guda biyu ke faman share harabar gidan da k'alk'ale shi. Wasu tunanika ya fad'a, lokaci guda ya fara tuno komai daki daki tun daga tasowar su a gidan iya. Yana nan tsaye goye da hannun shi a baya yaji ana knocking k'ofar shi, daga yadda yake ya bada izinin shigowa, wata yarinya ta danno kanta ciki zata shigo hannunta rik'e da mopper da long broom. "wait!" Ya fad'a da fuska ba annuri, saita dakata tana kallon shi, "me zakiyi a nan?". Cikin firgici da ganin yadda ya tamke fuska shaidar baya son wargi tace, "amm ehh dama nice nake gyara wannan b'angaren". Khaleefa cikin sake d'aure fuska yace, "toh ki futa ni bana buk'ata". Saita juya kurum ta futa tana tunanin ko me ya samu Ayman yau? Taga kullum ita take gyaran b'angaren bai tab'a cewa don me ba sai yau, sai tayi fucewarta dama ta gama gyara parlon ne zata gyara d'akin daba kowa sannan taje ta gyara mishi nashi, tunda yace baya so kuma falillahil hamdu ya sauk'ak'a mata aikinta ma.
Ayman kuwa bayan ya gama baccin shi da gari yayi haske sosai tashi yayi ya shige ciki, yayi wanka ya shirya cikin yadi golden colour, so yake ya gama da wuri Cox akwai d'aurin auren wani abokin aikin su da yake son halarta wanda za'ayi k'arfe goma na safe. Lokacin daya futo har zai shiga d'akin khaleefa sai kuma yayi tunanin maybe ya koma bacci a lokacin, ga abun mamaki yarinyar nan ta gyara parlon su tayi gaba ba tare data jira in ya futo ta shiga ta gyara mishi nashi d'akin ba.
Auntie kuwa yau da kanta ta shiga kitchen don ta had'a irin breakfast d'in da tasan khaleefa yafi so don yaji dad'i a ranshi in ya futo. _(Allah sarki uwa)_ koda haleema tazo ta tarar da ita kane kane tana aiki a kitchen dariya tayi tace, "kice yau kin tuna da girkin mutanen k'asar Sudan". Tana dariyar itama tace, "sannun ki da zuwa mama haleema kin cika alk'awari yau gaki kinzo da wuri". "Ai dole uwar d'akina, a jiya fa muka dawo cikin dare". Surayyah tace, "Kai baki ji tsoro ba". Haleema tace, "toh ya zamu yi abune daya kama mu dolee, da zamu taho kuwa baki ga uban kukan data dinga yi ba ni dai na baro mata k'aramar k'anwarta nayi tahowa ta". Surayyah cike da tausayawa tace, "ayyah Allah sarki mufeeda bata ji ance aure yak'in mata ba". Haleema tace, "aikuwa kam, bamu gaisa bama Ina kwana fatan kun dawo lafiya". Surayyah tayi murmushi tace, "lafiya Lou alhamdulillah!". Haleema tace, "Masha Allah ya y'an biyu fatan an kammala karatu cikin nasara". Surayyah tace, "shima yana lafiyar shi Lou, kinsan tare muka taho yana ciki yana bacci".
"Allah sarki bari na k'arasa aikin kije ki huta haka". Haleema ta fad'a tana Shirin matsawa kusa, dakatar da ita surayyah tayi tace, "ki barshi mama haleema yau da kaina nake son yin girkin nan saboda dawowar khaleefa kinsan shi ba'a iya mishi".
Haleema tace, "haka dai kuke yawan fad'a". Surayyah tace, "humm! Baki ji akace Kaya da Yani sai uwar d'iya ba..... Kema don kin manta shine.".
Dariya haleema ta sake yi tace, "toh ni da nake cewa ma zan taimaka miki nasan yadda ake had'a girkin ne?". Auntie tace, "zaki iya mana ai ba wahala". "Anya kuwa wannan girki na y'an gayu ai sai ku". Surayyah tayi d'an dariya again.
Sunci gaba da hirar su tana girkinta har zuwa lokacin da Ayman ya futo, bayan ya dudduba ko'ina bai ganta ba, k'amshin abinci da yaji shine yasa ya taho kitchen don ya tambayi haleema ko ta futa ne. Sai kuma ya sameta a kitchen d'in. Su kuwa duk kallonshi sukayi, ya russuna suka gaisa da mama haleema, tana ta zolayar shi ai dole yau yayi late tunda yayan shi ya dawo kuma, shi dai yanata mata murmushi baice komai ba.
Itama Auntien gaishe ta yayi, sannan ya d'ora da complain d'inshi, "auntie ke kika hana yarinyar nan ta share mun d'akina yau?". Saita tsaya tana nazarin shi, "bata gayara muku part d'in bane?". Ayman yace, "iya parlor ba". Ta corridor kitchen ta lek'a ta kwalawa yarinyar kira sannan ta dawo, ba jimawa kuwa sai gata tazo ta russuna kan gwiwowinta a gaban auntien, "me yasa yau baki gyara wa Ayman d'akin shiba" kallon shi tayi sai kuma ta maida kallonta ga auntien, "kiyi hak'uri hajiya shi yace mun na barshi baya buk'ata" da sauri ya kalleta yace, "Ni kuma? Yaushe kenan" ita kanta yarinyar saida ta kalle shi sai kuma ta shiga rud'ani, d'azu aiba wannan kayan ne a jikin shiba, auntie kuwa a take ta d'ago bakin zaren tace, "a Ina ya ganki kukayi haka dashi?". Nan ta fad'awa auntie duk yadda sukayi da khaleefa, daga ita har Ayman shiru sukayi auntie ta girgiza kai kafun ta fad'a mata, "twin d'inshi ne baya son hayaniya sam, inda kika same shi nan ne d'akin shi, Soo take note saiki kiyaye baya son hayaniya ko a shiga shirgin shi, yanzun in kin shiga ainahin bedroom d'in Ayman zaki gyara ba ruwan ki dashi"
Da "toh" ta amsawa auntie ta mik'e ta fuce. Shima Ayman futa yayi ya koma parlon auntien ya zauna, alk'a'idar tunanin shi dai ya koma, yanzu dai yasan bai huce kwanaki k'alilan a d'aura auren raihanatu ba, da zai iya ya kamata ya biya ta gidan su in ya dawo d'aurin auren nan yau su gaisa, sai dai sam baya jin hakan, ba zai iya jurar ganinta tana shirin zama matar wani ba, k'ara mishi damuwa kawai zatayi a banza, gashi itama dama kwana biyu ta futa harkar shi, sai text massage d'inta daya gani cikin satin nan tana tambayar fatan yana lafiya, ko refly mashi baiyi ba, wata zuciyar ce tace dashi, to kai da kake abokinta meye ma naka na shiga damuwa da tashin hankali akan aurenta,yadda raihana tasha wahalar nan da matsalolin data dinga fuskanta a maganar aurenta ai kamata yayi ma kafi kowa murna da taya ta farin ciki matsayin babban abokinta na kusa, sai gashi kana nema ka wulla kanka cikin jerin y'an bak'in ciki da hassada da Sam basa son ci gabanta. sai daya kai k'arshen tunanin shi sannan ya sauke doguwar ajiyar zuciya, Shi tunda yake bai tab'a jin yana bak'in ciki da kishin alaqarta da wani kamar wannan lokacin ba, ya kasa fahimtar abinda hakan ke nufi.
Yana nan zaune haleema ta fara jera kwanukan abincin da suka dafa saman dinning, motsinta ne ya farkar dashi daga mafarkin ido zaune daya fara tafiya, yana mik'ewa wayar shi tana fara ring, sai ya koma ya zauna, ganin Nur ce sai yayi rejecting kiran shi ya kirata, gaisawa suka k'ara yi ta tambayi lafiyar shi da Allah ya k'ara huce gajiya. Sunci gaba da wayarsu irinta masoya har auntie tazo ta shige shi, d'akin da shaheeda take ta shiga ba jimawa kuma ta futo shaheeda na bin bayanta.
Sallama Ayman yayi da Nur a waya ya mik'e tsaye da murmushi saman fuskarshi suka gaisa da shaheeda. Sanye take da doguwar rigar material ta yane kanta da k'aramin gyale kalar kayan, d'aya daga sababbin d'inke d'inken auntie ne ta bata tunda bada shirin kwana tazo musu gidan ba. "Wai d'an uwan ka bai tashi ba Ayman" ta tambaye shi da harshen Arab. Ayman yayi y'ar mik'a yace, "shi zan je na duba yanzun". Yana gama maganar shi ya nufi hanyar part d'insu, futowar shi kenan Ayman ya shigo, "na d'auka har yanzu bacci kake". Yamutsa fuska yayi kad'an yace, "ai tunda nayi sallah ni ban koma bacci ba".
Ayman yace, "ai ni bansan sai zuwa yaushe zaka fahimci martabar bacci ba kai kam koda yake Auntie ce tace na duba ka ta gama shirya table". "okay dama zanje bamu gaisa da ita ba". Tare suka jera har babban parlon sama, ita da shaheeda ne zaune kan dinning ko hira suke shaheeda dai tana ta faman dariya tana rufe baki. A gaban auntie ya d'an russuna yace, "barka da safiya auntie". Tana kallon shi tace, "barkanka dai khaleefa fatan ka tashi lafiya" Ciki ciki yace, "Ina lafiya alhamdulillah" jan kujerar kusa da Ayman yayi ya zauna, shaheeda ce ta gaishe shi, sama sama ya amsa ba tare daya kalli inda take ba.
Auntie ce tayi saving d'insu da abinda tasan kowannen su yafi ci wajen karin Kumallo, as she expect khaleefa yaci abincin da yawa kafun ya tashi ya koma inda ya futo.
Ayman kuwa koda ya gama zama yayi kan d'aya daga kujerun parlon yana ya dubo no haedar saboda guy d'in d'an anguwar sune. Sun tattauna inda zasu had'u su tafi tare kafun ya mik'e,
Sallama ya yiwa Auntie ya koma