Showing 6001 words to 9000 words out of 288773 words

Chapter 3 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

4711

gida. Interview akayi mata aka tabbatar da kwarewarta sannan aka sa mata ranar da zata zo a bata office.
Kamar wasa surayyah ta fara futa aiki 7-4 as a medical consultant doctor. Da albashinta mai kwari a wata, bata futa da twins gurin gwaggwo take barsu kafun halima tazo ta d'ora a lura dasu da abincin su, ita kuma tana dawowa aiki ta rungumi abunta suji d'umin jikinta, ta shayar dasu da abincinsu na hak'ik'a. Ta d'auki a k'alla wata uku tana futa aiki a napep kafun ta siya y'ar k'aramar mota irin ta mata don samun sauk'in kud'in transport da delay.
Sannu a hankali al'amuran surayyah suka soma yin nisa, yayinda a kullum safiyar Allah take sake ci gaba da samun rufin asiri, taci gaba da business tare da manyan mata y'an kasuwa a gurin aikinta, inda take saro kaya na mata, kama daga sitturu, mayukan shafa, cosmetics and deodorant, ga jeweleries. Tun tana iya business d'inta tsakaninta da ma'aikatan hospital d'in da take aiki har mutanen anguwar su da yawa suka fahimta suka soma k'ulla business da ita.
A halin yanzu ta daina tab'a kud'in da yake account d'inta sai albashinta kawai, ribar kasuwancin ta kuma ta soma adanawa future d'in y'ay'an ta.
Sannu a hankali gutsiri tsoma da k'ananun munafunce munafuncen y'an anguwarsu ya soma dawo musu ita da iya, Ashe suna ta yayatata wai bata da asali yaran ma basu da uba yanzu ta fake da aikin likita tana futa karuwanci, su kuma su iya sun mak'ale jiki suna taci daga haramun, a ranar surayyah taji wannan magana sam hankalinta bai tashi ba hasalima ba b'ata lokaci tasa k'afa tayi fatali da maganar.

@@@@@@@

Surayyah taci gaba da rayuwarta salamun daga ita da yaranta sai su iya da halima kafun Allah ya had'a ta da k'awa ta gari sameera. Sameera sun had'u da surayyah wata rana a asibitin da take aiki, lokacin twins d'inta nada shekara biyu a duniya don ta yaye su tuni, ta shigo antinatal ward zata had'u da wani likita abokin aikinta, har ta huce ta gurin sai kuma ta dawo da baya sakamakon jin maseefar da nurses biyu keyi kamar zasu ba hammata iska.
Da farko ta d'auka fad'a suke, sai dai ko data nutsu saita fahimta duk wannan hayaniyar suna yine ga wata kwayar mutum guda da take zaune gefe tana faman share hawaye, ga yara biyu a gefenta duk ba gyara, ita kanta matar wujiga wujiga da ita zani daban mayafi daban kallabi daban, gata yarinyar mace kyakkyawa kuma.
Cikin bin ba'asi surayyah tace da nurses d'in, "haba mana zulaiha ya zaku saka mace a gaba kuna zagi don kawai tazo neman taimakon ku akan yadda zata haife abinda yake cikinta".
Sassauta murya zulaiha tayi tace, "Allah doctor surayyah matar ce da abun haushi, duk lokacin da tazo awo sai mun rubuta mata maganin da zai k'ara mata lafiya ita da babyn ta bayan wanda gwamnati tasa a basu kyauta, amma kinganta dai ko ba zata tab'a siya ba, y'an kayan vitamins and protein bata ci, shi kanshi zuwa awon sai ta had'a sati uku bata zo ba, sai yanzu da zazzab'i ya kamata ta d'ebo jiki rab'e rab'e ta taho mana nan".
Cike da tausayawa surayyah tace, "ayyah aiba haka zaku yi mata ba, da farko ma duk wannan maganar ba'a zo kanta ba tukun, kamata yayi ku jata gefe ku tambaye ta kuda ita bawai ku tozartata gaban mata y'an uwanta ba, kuji meye matsalar ta kuda ita inta taimako ce kutaimaketa y'ar uwar kuce fa mace, haba zulaiha". Duk shiru sukayi kafun surayyah ta sake tambaya, "yanzu taga likitan ko kuma bata gani ba?".
"We are sorry doctor insha Allah zamu kiyaye, eh taga ni magani za'a bata ta tafi sai take fad'a mana wai ashe ko kud'in motar komawa bata dashi ga zazzab'i ya sake taso mata ba zata iya tafiya a k'afa ba.......".
Da sauri ta d'aga ma zulaiha hannu, "ya Isa nurse na fahimta".
Dubanta ta mayar ga matar da take durk'ushe tana sake fashewa da sabon kuka. "yi hak'uri baiwar Allah inba damuwa na ganki minti uku mana a office d'ina".
Cikin jin dad'in ganin y'ar gayun likitar da bata fi tsarar age d'inta ba ta nuna tausayawa a gareta tace, "toh".
"Am nurse zulaiha raka ta office d'ina".
Da toh itama ta amsa mata.
Ko bayan ta gama uzurinta ta koma office ta iske matar zaune k'asan tiles duk ta had'a zufa tamkar ba sanyin AC a office d'in yaran suna ta mata kukan yunwa"
"A'a d'an samari da y'ar budurwa ya akayi kuma?". Surayyah ta fad'a tana tsugunnawa daf dasu, d'aya daya d'an fi wayo da alama shine babbah yace, "abinci".
"Au kukan na abinci ne kenan toh bari Ina zuwa?".
Kayan karin ta da iya kesa a biyo ta dashi kullum ta d'auko ta zuba musu abincin mai yawa a plate, tayi amfani da dispenser ta had'a musu tea shap shap, ta zuba musu madara ta kai musu saman carpet. "ga abinci malama amma ku koma kan carpet, kada kiji komai ki saki jikinki dani baiwar Allah".
Ba musu taja yaran suka soma cin abincin bayan tayi mata godiya, ita kuwa d'auke hankalinta tayi daga kansu don basu damar da zasu ci abincin su ba d'ar d'ar.
Saida Suka kammala matar ta gyara mata gurin sannan surayyah ta koma gareta ta fara jefa mata tambayoyi akan abinda yasa bata kiyaye dokar likita don lafiyar jikinta data babyn ta, kuka ta sanya har Saida tayi ta bata baki sannan tayi shiru, labarinta ta soma bata don haka kurum surayyah taji matashiyar y'ar gayun likitar ta kwanta mata a rai.
"Ni dai sunana sameera, haifaffiyar garin Kano, nayi makaranta tun daga primary har zuwa secondary, haka ta b'angaren alkur-ani na sauke hizfi sittin, nayi aure da shekara hud'u yanzun, bayan shekara guda na haifi haydar ga shi shine babbah, bayan wata shekara da wata ukun na sake haifa mishi k'anwa gata itace asiya, itama watan ta bakwai na samu wani cikin wanda shine yake jikina yanzun ina wata na takwas da satittika. Toh da farkon auren mu mijina yana yi mun komai dai dai k'arfin shi, sai dai Ina haihuwar farko ya sauya, ba wadataccen abinci, ba kud'in cefane, bare a kaiga sutturar kirki ta sawa, wulak'anci yake mun iri iri, wani lokacin kona yi fushin zuciya zan tafi gidan mu saina hak'ura saboda yace duk ranar dana bar gidan shi tona tabbata na ajiye mishi duka yaran shi tunda ba dasu nazo ba, yanzu haka Ina zaune ne saboda su, saboda idan na tafi bansan wacce kalar matar zai auro ta rik'e su ba gashi har gobe bai sauya hali ba......". Ta k'arasa maganar tana fashewa da kuka, hankie surayyah ta bata don ta tausaya mata matuk'a har saida hawaye suka cika idonta, wani lokacin k'addarar mata duk iri d'aya ce, matsala ce akan *AURE* sai dai ita kash tata tasha banban. Sai ta lumshe idonta a hankali ta tashi daga gabanta ta koma kan kujera ta zauna, ta bata damar ta gama kukan ta ko taji sauk'in rad'ad'in dake cikin zuciyarta, sai bayan tayi shiru don kanta sannan surayyah ta sake dawowa gabanta ta zauna tace, "ke kuma bakya sana'ar komai don ki rufawa kanki asiri?".
Sameera tace, "Toh ai duk wata sana'a bata yiwuwa saida jari, ni kuma da nake ta abinda zanci.....".
Jinjina Kai surayyah tayi tace, "haka ne kam, tabbas malama sameera labarin ki mai tab'a zuciya ne, sannan yadda kika yadda dani har kika bani labarin ki duk da a yau kika fara ganina, toh nima naci alwashin zan taimaka miki da abinda zaki fi k'arfin komai keda yaran ki harma shi mijin naki tunda zuciyar shi ta mutu, sai dai dole zamu ajiye komai har zuwa lokacin da zaki rabu da wannan cikin na jikin ki".
Ita dai sameera jinta kawae take, don a lokacin tana ganin kamar ta gama k'are mata bata da wani sauran hope a rayuwa. A ranar bata sallami sameera ba har saida kud'i masu gwab'i ta bata catin ta da phone no tace don Allah data haifu tayi k'ok'arin sanar da ita.
Koda ta dawo gida bata b'oye ma iya da halima komai ba, su kansu sun tausayawa matar kuma sunji dad'i da irin taimakon ta da tayi, koba komai Allah mad'aukakin sarki yace "waman sutra muslimun, sutrahullahu yaumal k'iyamati"
"Duk wanda ya suturta musulmi zai suturtashi ranar alk'iyama".
Kwana ashirin da biyu cif sameera ta haihu a nan asibitin sai dai yaron bai zo da rai ba, a wayar mahaifiyarta ta kira surayyah take fad'a mata a lokacin da ta cika kwana hud'u da haihuwa. Surayyah saboda yanayin aiki bata samu damar zuwa ba sai weekend. Ta tafi kuwa da abubuwa masu yawa, kama daga wasu cikin kayan sawarta har zuwa kan kayan abinci dana shayi, su biyu sukaje sai twins. Aikuwa sameera da yayarta sukayi ala ragab da yaran, don sun bala'in burgesu.
Bayan tayi musu ta'aziyya da ya me jiki bata jima sosai ba suka tafi ita da halima bayan sameera ta sa yayyanta sunyi mata godiyar tarin alkhairan ta gare su ita da yaranta.
Toh tun daga lokacin huld'a mai k'arfi ta shiga tsakanin su, surayyah bilhak'k'i take taimakon rayuwar sameera, har sun soma business tuni bayan anyi yarjejeniya da mijinta da mahaifiyar ta sun amince.
Allah mai had'a mutum da mutum, kafun shekara ta kewayo sameera ta samu rufin asiri ta kama k'asa har tana rabawa mutane kaya sari. Yanzu komai zata yima kanta ta yima yara, tuni ta shirya planning haihuwa sai nan da shekara biyar ta samu abinda zata kula da masu zuwa sosai, yanzun yaronta babbah da k'anin shi har sun soma zuwa private school daga nursery kuma suka fara.


_Comment and share_
24/03/23, 1:58 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page three3️⃣


Rayuwa taci gaba da cud'a musu, yayinda surayyah har kullum take ci gaba yakice maganar mutane.
A lokacin da su khaleefa suka cika shekara shida a duniya, lokacin tuni sun shiga primary da islamiyya, yaran Masha Allah sai San barka, ga wayo ga farin jini kowa son su yake kama daga malaman makaranta da mutanen gari, ranar wata asabar surayyah tana zaune kan carpet d'in dake malale a parlon iya tana taya iya d'aurin gyad'a, yayinda take ta zolayar halima da take basu labarin takaicin wai wani bazawari na sonta, ita ta dage baza tayi aure ba bayan da k'uruciyarta, yayinda ita kuma uwar d'akinta ta dage lallai zata iya yin aurenta ai ba haramun bane (haleema kenan).
A lokacin ta tura su khaleefa lesson na French language, tunda weekend basa zuwa kowacce makaranta, sai dai bayan minti k'alilan da futar su saiga yaran sun dawo sarkin zuciya ne gaba k'anin shi na biye dashi a baya fuskar nan murtuk kamar zaiyi kuka
"Ya aka dawo kuma mazajen iya". Iya keyin wannan maganar tana duban su.
Zama khaleefa yayi opposite d'in surayyah yana ta faman kumbura fuska, dama ita surayyah sam bata nemi jin ta bakin shiba, cox tasan he will never say anything at that moment da zuciyar shi take up and down. "Ayman ya akayi?". Ta tambayi Ayman on a serious way da harshen Arab.
Satar kallon khaleefan yayi sannan yace, "Auntie ba wani yaro ne na gidan su abulkhair ba kullum in ya ganmu zamu makaranta sai ya dinga ce mana wai 'shegu'".
Wani irin Damm k'irjin doctor surayyah ya buga, wannan shine karo na biyu ko uku da yaron yana jifan yaranta da wannan mummunar kalma, bata san kuma ya zata guje ma k'addararorinta ba, dole akwai gurinda yaron ya tsinci wannan magana, bata san dalilin da yasa yaran hausawa suke wasa da kalmomi irin wad'an nan marassa dad'in furtawa ba.
Murmushin ta k'ak'alo mai ciwo duk da nufin b'oye damuwarta, shoulder khaleefa ta dafa don shine mai damuwa, "haba khaleefa na, me yasa zaka damu don ya k'irk'iro sharrin shi ya lik'a maka don ya b'ata maka rai kawai, ka daina damuwa kaji babana?"

Har yanzu fuskarshi a d'aure take ya d'ago ya dubi mahaifiyar tashi yace, "Auntie Sam wannan baiyi kama da sharri ba, saboda idan sharri ne ai bazai ci gaba da fad'a kullum kullum ba, har fa cewa yayi idan da gaske muna da uban mu nuna musu shi su gani, wai ance tunda kika zo anguwar nan ke kad'ai aka ganki ba'a san asalinki ba, don Allah Auntie ki kaimu gurin mahaifin mu muma mu ganshi har mu nuna musu su daina ce mana shegu plsss Auntie".
Shiru tayi tana jinjina maganar yaron, kamar ana karanta mishi zance haka yake zaro shi, sai data sauke ajiyar zuciya mai tsayi sannan ta sake fuskantar shi, "har sau nawa zanci gaba da fad'a muku mahaifin ku ya rasu khaleefa?".
Kwantar da kanshi yayi jikin Auntien yace, "I'm sorry mum amma ba yadda zaki sa ya dawo duniya ya fad'a musu shine baban mu sai ya tafi, in suka ganshi nasan ai zasu daina ce mana shegu". Duka a gurin babu wanda baiji tausayin su ya tsirga mishi ba, lallai su d'in abin tausayi ne, rayuwa babu cikakken asali abun tutiya jigo kuma alfaharin kowanne d'a lallai akwai wahala musamman cikin al'ummar mu da basa iya ganin zarau sai sun tsinka. Lallaba su surayyah tayi da kyar suka tafi ita kuma ta fuskanci iya, "iya Ina ganin ya kamata na taka ma yaron nan burki ta wajen iyayen shi, kinga yana son ya Samar mun da sabuwar matsala tsakanina da yarana".
Nan take iya tayi na'am don lallai yana da kyau a yiwa rufkar hanci.
Ita da halima suka tafi bisa jagorancin halima don ita tasan y'an anguwar sosai. Da sallama ta shiga suka gaisa da uwar yaron da kishiyarta, kafun ta fad'a musu ummul'a'ba'isin zuwanta, take matar ta k'aryata a cewarta sam yaronta bazai aikata hakan ba, tun surayyah na fahimtar da ita har ranta yayi zafi tace tunda ta k'aryata in bai fasa ba toh tabbas zata hukuntashi da kanta. Nan fa mata tace aka tab'a mata d'a ba zata kyale ba, tunda ai ba k'arya yaron yayi ba shegun ne kuma duk anguwa ansan basu da uba. Nan fa akayita d'auki ba dad'i tun suna yin abun su biyu har kishiyarta ta shiga, halima dai tana ta basu hak'uri.
Sam surayyah bata iya fad'i in fad'a ba, haka bata San yadda ake tashin hankali ba sai ranar. Anyi rigima ta gaske wadda saida ta dangane da police, y'an sandan da surayyah ta kira suka kulle matar su kuma mutanen anguwa Suka yiwa surayyah caaa, sosai al'amura suka baddale duk anguwa ta rud'e.
Malam shine ya tausasa surayyah data kwana batayi bacci ba tana kuka da takaici gami da yin kaico ga rayuwarta.
Dole at de end ta hak'ura aka saki matar saboda shigar malam da mai anguwa zancen, sai dai fa an kafa mugun sharad'i akan duk wanda ya kuma sheganta mata yara d'auri ne da tara mai yawa, sannan ba batun yafiya. Malam yayi signing mai anguwa yayi sign, surayyah tayi matar ma tayi.
Toh kusan sai ince tun daga wannan lokacin surayyah bata sake samun nutsuwa ba duk da a anguwar wani bai k'ara aibata yaran ba. Sai daifa sun taso da abun a ransu more especially khaleefa da yake da rik'e abu, wasu halayen nashi suna kamanceceniya dana Suraj duk da bai tab'a ganin shiba bai taso a daman shiba balle har ace ko zama tare dashi ne, a waccan ranar iya ta bata shawarar ta nemo mahaifin su muddin hakan zai yiwu, sai dai ta fad'a ma iya ko ta tunkari Suraj yanzu sake b'ata mata rai zaiyi don bazai tab'a karb'ar yaran ba, don haka take ganin a barsu kawai a yadda suka d'auka cewa mahaifin su ya mutu har gaban abadan.
Ko khaleefa daya dameta da labari akan mahaifinsu taka mishi burki tayi, ta kuma sa ya alk'awarta mata shida tambayarta waccen maganar har abada. Kalaz aka rufe babin su gaba d'aya.


@@@@@@@@@


Rayuwa taci gaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa gami da wadata, tuni surayyah ta siya wani fili makimanci a irin sababbin anguwannin da ake yankawa inda ake futar mata da tsarin gida mai kyau da tsari na zamani sama da k'asa.
A lokacin da aka kammala ginin yaran suna 18 years, sun kammala secondary school zasuyi bikin saukar alkur-ani mai girma nan da two months.
Tuntuni take son tashi sai dai ta fi son suyi bikin saukar su a nan gidan iya inda kowa yafi sanin su kafun ta sauya muhalli. Tana office ranar da yamma tana shirin tashi saiga khaleefa ya shigo kamar an wullo shi, "abbana Kaine tafe da yammacin nan?"
"Eh auntie na d'auka ma kin tafi har Ina addu'a".
Komawa tayi ta zauna tace, "ban tafi ba amma Ina shiri Ina Ayman da iya". Zama yayi kan kujerar da take opposite tata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login