Showing 111001 words to 114000 words out of 288773 words
Chapter 38 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt
numfashi kafun yaci gaba, "na kasance Ina yin rayuwata single a makaranta, ban tab'a kallon wata mace da fuskar soyayyah ba, duk da a raina ina da zab'in irin matar da nake son aure a rayuwata, amma duk da haka a lokacin ba abinda nasa gaba sai karatu, kwatsam ba tare da zato bare tsammani ba na had'u da wata yarinya, hak'ik'a ta kasance mace ta farko data fara d'aukar hankalina, tazo cif da irin matar da nake hasashen mallaka matsayin matar aure na,muka fara soyayyah da ita cikin aminci da aminta da juna, har mun gama tsara yadda zamu tafi da rayuwarmu bayan auren mu, Babu zato sai wani abu ya gindaya marar dad'i a tsakanin mu wanda ya zamo silar da bama tare a halin yanzu maganar da nake miki, sai dai akwai mafuta da yiwuwar zan sameta cikin sauk'i idan har na cika wani sharad'i a gurin mamana, sharad'in da zai kaini Isa ga b'arakar dake tsakanin mu na d'inke ta mu zauna tare har abada, sai dai bisa wani sharad'in shima,. Sai dai shi bana komai bane sai aure, tace dole sai nayi aure kafun ta amince da wancan sharad'in da zanbi izuwa ga cikar burina, anan sai naga munyi tarayyah kan abu guda, ke kina son kiyi aure koda na yini guda ne, ni kuma Ina son matar boge da zata taimaka mun na Isa ga cikar burina, shine na kawo mana maslahar aure me kama dana deal, nayi alk'awarin zan inganta rayuwarki ta yadda kaf mak'iyan ki sai sun dawo karkashin ki sun jingina da inuwar ki zasu huta, zaki samu cikakkiyar nutsuwa da damar zab'ar duk irin mijin daya dace dake bayan shekaru biyar a lokacin na tabbatar mun kaiga samun cikar burin mu, zaki ci gaba da karatun ki, sannan zan ni da kaina zan taimaka miki wajen ganin kin samu miji dai dai da ra'ayin ki, mai sonki so na gaskiya ba wanda wani guntun dalili zai sashi fasa auren kiba, amma yadda kika gani, zan baki kwana biyu kiyi tunani akai sai ki sanar dani hukuncin da kika yanke"......
Tunda ya fara magana take kallon shi tana sauraron shi da mugun mamaki har ya dire, wannan abu kamar a shirin firm? Ita a firm kawai tasan ana Contract marriage sai gashi yau abun yana shirin fad'owa kanta zahiri, tunani biyu tayi a lokacin taji tayi na'am da buk'atar shi ba tare da dogon tunani ko nazari ba, na farko matar Abba abubakar data lashi takobin bata Isa tayi aure kamar sauran mata ba, na biyu ummienta, ta d'aga hankalinta sosai akan y'ar hatsaniyar da aka fara samu cikin kwanakin nan, tana tunanin idan ummie taji mummunar labarin fasa aurenta da Imrana komai ma zai iya faruwa da ita, sai ta k'ara kallon khaleefa ta fara magana da karyayyiyar murya me cike da rauni, "ba sai kayi mun komai ba, na riga na jima da zama hopeless a rayuwa, a yanzu bani da burin daya huce na samu mafaka koda ta kwana biyu ce a gidan wanda zai amsa sunan mijina, muradina kawai duniya ta ga na tab'a aure koda sau d'aya ne a tarihi......". Sai ta tsaya tana sheshsheka kafun taci gaba, "na amince da auren ka,,,, na amince ba sai nayi tunani baaaa". Cikin jin dad'i da farin cikin da baisan kona meye ba ya k'araso gabanta kad'an yasa hankie yana share mata hawayen fuskarta, bata iya yin kwakkwaran motsi ba har ya goge mata fuskar ba tare da ya yadda hannun shi ya tab'a koda gefen fuskarta ba ya ajiye mata hankien a gefe. "Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shin kina ganin iyayen ki zasu yarda ki auri mutumin da bashi da cikakken asali". Wani irin kallon mamaki ta bishi dashi kafun ta sauke kanta k'asa cikin jin nauyin maganarshi, "Ni ban tab'a d'auka akwai wani abun nema ga iyaye a gurin mijin da zasu aurar wa da y'ar su wanda ya huce na kyakkyawar tarbiyya mai kyau abun koyi ga kowa ba, kuma nasan auntie tayi iya yinta wajen ganin duk kun samu haka kaida d'an uwanka..... Toh meye kake son fad'a bayan wannan". Girgiza kanshi kawai yayi a ranshi yana ganin kawai bata gane abinda yake nufi bane, duk da kalamanta na farko sun so yin tasiri a zuciyar shi ainun, amma sai ya bagarar saboda shi idon shi duka sun rufe, Saleema kawai yake gani sai tsanin da zai taka ya Isa gareta, burin shi d'aya ya kaiga dangin mahaifin shi ya samu abinda shima zaiyi alfahari dashi a cikin al'umma.
Khaleefa ya tambayeta sunanta da anguwar su, koda ta fad'i sunan saida yaji kamar ya tab'a jin sunan a gurin wani amma ya manta a ina ne, saida ta fad'i anguwar sannan ya tuna lallai yasan tane a gidan iya. Sunci gaba da zama jiran nurse don ta sallame su, kowa cikin su ya mama gaban shi musamman ma raihana da kiran Abba da ummie keta faman shigowa tana rejecting. Koda nurse ta dawo ta gansu tare suna magana jifa jifa mamaki tayi sosai, kenan sun shirya daga futar ta amsa kiran doctor?
Khaleefa tambayar ta yayi ko nawa ne bill d'in su na asibitin. Ta fad'a mishi Inda zaije ya biya, ya futa ita kuma ta dawo kusa da raihanan tana tambayar ta "ko zaki iya tafiya da k'afarta ?" Raihana tace, "watak'ila sai na gwada dai".
Koda ya dawo har ta sauko daga gadon, hakanan ta tattaka k'afar tayi sallama da nurse suka nufi hanyar futa tare kowa da abinda yake tunawa cikin ranshi.
(Nikam nace sun zo a bai bai, zasu koma a dai daiπ€π).
Har gurin motar shi suka je sai dai ta k'ek'asa k'asa tace ita sam ba zata shiga ba gwara ta hau napep,, shima bai damu ba ya nema mata napep ya biya kud'in bayan sunyi exchange phone number ta tafi. Saida ya jima tsaye a gurin tuni sun k'ule sannan ya iya tafiya wajen motarshi ya shiga, har yanzu baiga wani abu ba dai daiba a cikin abinda yake shirya jefa rayuwar shi a ciki wato yaudara, zai yaudari mahaifiyar shi abinda bai tab'a yiba tunda suka taso sai yau ta sanadin kace
*********. *********
Raihana kuwa har k'ofar gida me napep ya ajiye ta, ta futo tana d''ogasawa ta nufi cikin gidan su, lokacin tuni anyi magrib prayer, ummie da Abba suna shirin sake gwada no ta sai gata ta shigo bakinta d'auke da sallama, ummie ko lura da yanayin data shigo ma ba tayi ba ta zabga mata wani uban mari daya assasa mata ganin taurari ba tare data shirya ba. "Daga gidan uban wa kike a daren nan?".
A daren ranar Ayman yana kwance da damuwar inda d'an uwan shi yayi tun yammacin yau har yanzu bai dawo ba, wayar shi ta fara ringing, koda ya duba Auntie ce take kiran, "kazo malam yazo har zai tafi". Abinda ta fad'a kenan a lokacin daya kara wayar a kunnen shi, ta katse kiran, sai ya yink'ura ya tashi ya taho parlon k'asa don malam baya tab'a hawa sama in yazo. Yana zaune kan kujera suna hira da auntie akan abinda ya shafe su su kad'ai, sai dai Ayman na shigowa suka bar zancen, shi kuwa bayan sun gaisa da malam abinda ya fara tambayar shi shine, "shin malam da gaske ne abinda naji cewa an fasa auren raihanatu?". Malam da mamakin shi yace, "Anya kuwa? A ina kaji wannan tatsuniyar ta k'anzon kurege kuma". Sai yayi shiru bai sake cewa komai ba, tunda raihana ta mishi massage d'innan ya tabbatar da gaske hakane an fasa d'in, don bata tab'a yi mishi k'arya ba, toh amma tunda malam basu sani ba shi bazai sake cewa komai a kai ba don ba zai yarda aji mutuwar sarki a bakin shiba. Daga Auntie har malam basu sake bi ta kan maganar Ayman d'in ba har suka gama hirar su yayi musu sallama ya tafi.
Yana tafiya khaleefa na shigowa, da kyar ya bawa Ayman da yake faman tambayar shi inda yaje tun d'azu hannu suka gaisa, ba tare daya bashi amsa ba yayi hucewar shi d'aki don yayi sallah da wanka ya sauya kayan jikin shi kuma ya kwanta
Ayman kam kasa hak'uri yayi da abinda raihana ta fad'a mishi har saida ya sake kiran malam bayan ya tabbatar zuwa lokacin ya koma gida, sake tambayar shi yayi, sai dai a wannan karon malam yana komawa yaji labarin a gurin mahaifin raihana yana neman shi za'a mayar wa su Imran kayan auren su daga bakin iya shima yaji wannan sak'on, saboda an k'ara samun matsala shi ma imrana yace ya fasa aurenta.
Ai bai jira ya gama jiba ya katse wayar cikin matuk'ar farin ciki ya daka tsalle tare da kaiwa iska naushi, ashe dai da rabon raihana zata zama tashi mallakin shi. Bai yi wata wata ba ya nufi d'akin auntie don ya fad'a mata abinda ya jima a cikin zuciyar shi.
Yau ko sallama sai bayan ya shiga parlon nata yayi, tana aikin had'a ordabur da zasuyi dinner dashi a daren ranar, futar mama haleema kenan shi kuma yana shigowa. Tunda ta d'aga ido ta kalleshi sau d'aya taga tsantsar farin ciki da annurin da yake kan fuskar shi tasan wani abu mai dad'i ne ya same shi.
K'asan k'afarta ya zauna cikin happy ya bud'e baki zaiyi magana khaleefa ya shigo, sai ya fasa fad'ar abinda yayi niyyah har sai d'an uwan shi ya zauna ya fad'a don shima ya taya shi murna, duk da yana jin tsoro da fad'uwar gaba, wanda ya ta'allak'a su da tsoron yadda y'an gidan su raihana zasu d'auki abun,, Shima a kusa da Ayman ya tankwashe k'afar shi, ya kalle shi suka had'a ido, take duk suka sakarma juna murmushi.
Auntie kallon khaleefa tayi shima, duk da yanayin fuskarshi bai sauya ba amma dukkan alamu sun nuna akwai magana a bakin shi shima, sai ta ajiye trayn hannunta gefe tace, "yau dai da alamu yarana suna tafe da wani labari me dad'i da suke son sanar dani?".
Murmushi Ayman yayi kanshi a k'asa, shi kuma khaleefa shafo sumar kanshi yayi yace, "eh Auntie nazo miki da maganar yarinyar nan sai dai a k'urarren lokaci, Soo nake a nema mun aurenta nan da gobe sai a d'aura auren nan da kwanaki biyar masu zuwa". Daga Auntie har Ayman basu san lokacin da suka kalle shiba, "wannan wace irin magana ce haka khaleefa? Aure ai ba'a tab'a yin shi haka da gaggawa, dole ana buk'atar a gabatar da wasu shirye shirye kafun aiwatar da neman auren har aje ga d'aurin auren". Shikam sake cewa yayi, "kada wannan ya dame ki auntie, basai kin wahalar da kanki akan komai ba, akwai y'an kud'ad'e na da nake zaton sun Isa ayi duk abinda ake buk'ata na tsare tsaren biki insha Allah, saboda aikin da mukayi na shekara d'aya cikin biyu na course d'in da mukayi duk biyan mu akayi, kuma kud'in suna nan a account d'ina ban tab'a amfani da ko 1 naira ba, Ni dai burina d'aya ki amince da abinda nazo dashi yanzu...... please auntie".
Gaba d'aya khaleefa ya gama kullewa auntie da Ayman kai sai suka tsaya suna kallon shi kurum suna jujjuya zancen shi da mamaki, Ayman ne ganin bil hak'k'i da gaske abinda yake nufi kenan yace, "Toh wai a ina ma ka had'u da ita, sannan wacece ita wannan yarinya.....?".
Khaleefa Saida yayi d'an jimm kafun can ya nisa yace, "sunanta raihana salees Abdallah, gidan su yana nan kusa da gidan iya ba tazara sosai.......". Ai bai kai k'arshe ba Ayman daya shiga wani mugun tashin hankali ya mik'e tsaye babu shiri Yana kallon shi had'e da nuna shi da yatsa, cikin rawar baki da d'aga murya yake fad'in, "bazai yiwu ba,,,,, raihana ba zata tab'a auren kaba,,,,, saboda ita d'in ba matar ka baceee,,,, ya Isa haka..... Wasan ya Isa haka don Allah,,,,, har abada raihana ba zata tab'a auren wani namiji ba saboda ni ne nan...........".
_Nikam πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ d'ora hannu nayi aka Ina kallon su har bansan lokacin da Alk'alamina ya fad'i k'asa ba_
_Da wannan nake sanar daku cewa zanje hutun sati d'aya insha Allah zaku ci gaba da jina next week Friday in na dawo,,,,, ku huta lafiyaβοΈ_
_comment and share_
24/03/23, 2:05β―pm - Merhreeyaertou βπ»βπ»: *JARUMAR UWA*π§
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page thirty two3οΈβ£2οΈβ£
Ganin duk sun zuba mishi ido kallo yana Shirin komawa kanshi sai ya soma ambaton sunan Allah a cikin ranshi ya koma ya zauna a inda ya tashi ya dafa kafad'ar khaleefa, "don Allah khaleefa kada ka saka kanka a matsala.... Raihana fa duk mun shaida bikinta saura kwanaki k'alilan da Imran taya yanzu kuma zakace kai zaka aureta?". Khaleefa kallon shi kawai yake yana tunanin abinda ya d'aga mishi hankali daga maganar zai auri raihana lokaci d'aya har ya birkice mishi haka, "Ayman akwai wani abu ne?". Ayman daya rasa abinda zaice ma sai kawai yayi shiru yana kallon shi da tarin zarge zarge a cikin ranshi, yayinda zuciyarshi take tsananta bugu, khaleefa ya lalata mishi duk wani burget d'inshi! Ya gama jefa shi cikin garari, yana ganin raihana kamar itace hasken da zata yaye mishi duhun daya cika zuciyarshi,,, sai gashi khaleefa ya mishi shigar sauri ya kawo maganar wa auntie..... Sai kawai ya tallabe hannun shi a k'afar shi da gwiwar hannun shi, ya zabga uban tagumi yana ambaton sunayen Allah a cikin zuciyar shi don ya kawo mishi d'auki da sassauci da gaggawa.
Auntie kanta zuba musu ido tayi tana musu kallon tuhuma, barin ma khaleefa, ko a wasa, ko a mafarki bata tab'a zaton zai zo mata da irin wannan maganar ba, a yau da Ayman ne yayi mata wannan maganar ba zatayi mamaki ba, don tasan dole biri zaiyi kama da mutum, shak'uwar dake tsakanin su a kowanne lokaci zata iya rikid'ewa ta dawo soyayyah mai tsanani, musamman a lokaci irin wannan.
Khaleefa koda ya d'aga ido ya kalleta yaga ta rik'e hab'a tana kallon shi marairaice mata yayi, "please Auntie yarinyar kirki ce kada kice baki amince ba.....".
Sai ta dogare hannunta a k'asa tana ci gaba da kallon shi tace, "Ni kuwa zan fad'a maka haka,,,, yarinyar daka tafi kusan shekara goma ka barmu tare da ita,,, kaga kuwa sai dai ma ni na baka labarinta,, yanzu kaje kawai zamuyi magana da malam zuwa safiya zan neme ka".
A hankali ya tashi yayi musu sallama ya futa, amma fa zuciyarshi sai kai komo take akan yadda Ayman ya d'auki maganar,,,, har yanzu ya kasa fahimtar abinda yasa yanayin Ayman d'in sauyawa lokaci d'aya daga cewa zai auri raihana, koda yake bari su gama tattaunawa da Auntie dole a yau sai yayi mishi bayanin komai.
Auntie Kam ko bayan futar khaleefa saukowa k'asa tayi ta zauna kusa da Ayman ta dafa kafad'ar shi tace, "Ayman akwai wani abu da yake faruwa ba dai dai ba? Shin meye ma'anar khaleefa ta auren raihana.... Don ni na tabbata ba soyayyah suke ba.... Yaushe ma ya santa tukun mutumin da kullum yana nad'e a cikin gida.....".
Ajiyar zuciya me k'arfi ya sauke a b'oye, ya sake daidaita kanshi da nutsuwarshi ya k'ak'alo murmushi mai kama da kuka yace, "toh ni kaina Auntie ban sani ba,,, amma tunda kika ji shida kanshi har yace zai aureta, to Ina ganin yana sonta ne, don in baya sonta bazai tab'a cewa zai aure taba, haka nasan khaleefa....".
Nazarin kalaman shi tayi sosai kafun ta sake jefa mishi wata tambayar, "Toh kai dama ba sonta kake ba tuntuni....?". Baisan lokacin da idon shi ya tara ruwan hawaye ba, amma dai ya daure da kyar ya had'iye su tare da wani abu mai d'aci daya tsaya mishi a mak'oshi. "mutumcine kawai da gaisuwar mutumci amma ba wani abu mai kama da soyayyah a tsakanin mu,,,,". Ganin zata k'ara mishi wata tambayar sai ya mik'e tsaye,,,, "Auntie ya kamata naje na kwanta dare ya fara yi....". Itama mik'ewa tsayen tayi tace, "bamu gama magana da kai ba Ayman... So nake nasan dalilin da yasa da khaleefa yayi magana da farko ka so ka k'alubalance shi.... Idan baka sonta me yasa yanayin ka zai sauya farat d'aya? Sannan me yasa khaleefa zaice ze aureta??".
Wata irin jarumta yasa a wannan karon ya juyo yana fuskantar ta, "har abada.... Babu wani abu mai kama da wanda kike zato tsakanina da yayana, saboda khaleefa a shirye yake daya sadaukar mun da duk wani abu dana nuna Ina Soo a rayuwa... Nima kuma haka, dukkan mu muna da kyakkyawar alak'a da kusanci da juna.... Sannan ni ban tab'a son raihanatu ba.... Da Ina sonta da ban amince da soyayyar Nur da aurenta baaaa... Sannan abinda kika gani a tare dani ba komai bane illa tsorooo!! Tsoron yadda iyayen raihana zasu karb'i maganar khaleefa..... Shin ko zasu iya bada auren y'ar su ga wanda bashi da asali me kyau, ake zaton ma shefe ne???"
Sai yayi shiru har na wasu dak'ik'u kafun ya sake cewa,,,, "Auntie idan har k'awar ki aminiyar ki da kuka d'auki shekaru tare, tafi kowa sanin ki ciki da bai, lokacin muna yara har muna zaton ku y'an uwane zata hana d'anki auren y'arta,,,,, taya kike tunanin wani can a gefe zai baki.....".
Jikinta a