Showing 144001 words to 147000 words out of 288773 words
Chapter 49 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt
Auntie da mama haleema keyi mata, ita dai nata sauraron su, Ayman kuwa maida kanshi yayi ya langwab'ar yana Allah Allah khaleefa ya dawo ya bar musu d'akin.
Khaleefa bai zoba sai wajen tara da y'an mintuna.
Lokacin tuni mama haleema ta tafi saboda yaranta da mamanta suna buk'atar ganinta suma, Auntie ma ta shiga d'akinta ta futo, daga ita sai Ayman, itama jira take auntie ta dawo ta mata sallama ta tafi saboda idonta daya cika fal da bacci.
Futowar Auntie yayi dai dai da shigowar khaleefa, su biyu kawai suka kalle shi, ya sauya kayan jikin shi da wad'an da yafi ganewa wato riga da wandon jeans.
"Yauwa khaleefa Ayman yana taso kazo ka taimaka mishi zuwa d'akin shi, ga raihanatu nan ma ta fara gyangyadi kazo ku huce haka".
Hucewa yayi ya taimakawa Ayman ya mik'e, rik'e dashi suka fara tafiya a hankali har suka isa parlon su, Ahmad da yake duniyar waya da yasmin a lokacin ya mik'e ya taimaka mishi suka k'arasa har cikin bedroom d'inshi ya zaunar dashi gefen gado.
Khaleefa yana tsaye gefe guda hannun shi hard'e a k'irji yayi crossing legs yana kallon shi.
Ahmad a mute yasa wayarshi ya dubi khaleefa, "Wai ba munyi sallama dakai ba ya kuma ka dawo?, ko akwai abinda kake jira ne".
Da sauri Ayman ya kwanta ya sake rufe idon shi ruf, shi kuma khaleefa yaja k'afar shi ya futa bayan ya musu sallama. Raihana tana zaune a inda ya barta sai wasa take da k'asan hijabinta, auntie kuma tana waya ya sake shigowa d'akin,
Daga tsaye ya tsaya har ta kammala wayar ta kalli raihana, "daughter nasan kin gaji ko? Ga nan khaleefa yazo ai zaku tafi, oya kuje Allah ya huta gajiya".
A nutse ta tashi tace "auntie saida safe". Auntie tace, "Allah ya bamu alkhairy".
Khaleefa shiya fara futa sannan itama tabi bayan shi.
Babu wanda yace da d'an uwan shi ci kanka har suka bud'e k'ofar parlon suka shiga da sallama, khaleefa zama yayi kan kujera yana jira yaga d'akin data d'auka, ba b'ata lokaci kuwa tayi d'akinta ta rufo k'ofa, mik'ewa yayi bayan ya kashe hasken gurin ya nufi wanda yake tsakiya, had'ad'd'en d'akin bacci me d'auke da gado na alfarma komai milk, sai ya tsaya yana bin d'akin da kallo, Anya kuwa raihana ba wannan ne d'akinta ba? Tunda shi yasan bai shirya d'akin baccin shi a side d'in ba, ba don Ahmad da auntie sun takura mishi ba da a part d'insu zai ci gaba da zama har zuwa lokacin da zasu tafi.
*Bayan wasu kwanaki*
Tuni Ayman ya watstsake tangarau sai abinda ba'a rasa ba, amma a hakan ya shirya komawa bakin aiki yau saboda zaman gidan ya ishe shi, Ahmad ma ya tafi tun bayan kwanaki biyu da biki, amma fa bayan ya dunk'uli gudun mawa mai tsoka ya ajiyewa khaleefa. Auntie kam har yanzu tana cikin hutun biki data d'auka, mutane da yawa sunzo mata Allah sanya alkhairy, wasu ma har da abin arzik'in su kwatankwacin yadda take kyautata musu.
A kullum safiyar Allah kafun raihana su tashi bacci tasa ma'aikatan gidan y'an mata sun k'alk'ale musu part d'insu, sannan lafiyayyen kayan breakfast data shirya da kanta da hannunta su biyo baya. Haka da rana da dare duk ita take musu girki mai kyau ta aika musu.
Zuwa yanzu khaleefa ya had'a kayan shi da duk wani abun amfanin shi zuwa sabon muhallin daya sauya, bai sauya daga baud'ad'd'en khaleefa da suka sani ba har yanzu, sai dai yakan yi k'ok'arin danne zuciyarshi wajen ganin ya zauna da kowa lafiya a gidan.
Tsakanin raihana da auntie zama suka d'auka mai kyau mai cike da girmamawa da mutuntawa irin na surukan da suka san ciwon kansu. A kullum raihana zata je ta gaisheta har tana riga khaleefa ma zuwa, kasancewar gidan ba wani aiki ne dasu ba bare tace zata taimaka, rabin nasu ma an sauk'ak'e musu sai ya zamana suna gama gaisawa take komawa tayi wanka ta shirya ta karya kumallo, k'afarta ta warke sosai tuni tana iya takata ba d'ingishi.
Wani lokacin bak'i sukan kawo musu ziyara daga y'an uwan ummie ko masu makwabtaka dasu wani lokacin kuma ta yini ita d'aya, a irin wannan lokacin take kwantawa ta huta, tunda tazo gidan ko ruwan tea bata tab'a tafasawa ba, yini ake kawo musu shayi ita da bak'inta, abinci da rana ko sunkai su goma za'a kawo wanda zai ishe su suci su k'oshi, haka da dare ma.
Raihana tun washe gari ta tattara fiye da rabin kayan snacks na cikin gara da aka kawo mata dana abinci ta baiwa mama haleema aka kai part d'in auntie, da farko Auntien fad'a tayi tayi kuma ta k'i karb'a amma daga baya da raihana ta mata bayani yadda zata fahimta saita amsa ta d'ibarwa su iya da duk wanda ya kamata ta bashi.
Ba zata ce suna zaman lafiya da khaleefa ba, ba kuma zata ce suna fad'a ba, saboda kowa harkar gaban shi yake ba ruwan wani da wani, in suka had'u Ina yini ko Ina kwana ta raba.
Yauma tun safe data lek'a suka gaisa da auntie ta dawo ta sake kwanciya bata tashi ba har sai wajen k'arfe sha d'aya da yunwar cikinta ta takura mata, sanye take da doguwar rigar material ta yane kanta da wadataccen gyale, hannunta rik'e da wayarta ta futo ta isa inda ake ajiye musu abincin su, ruwan tea ta soma tsiyaya ta d'umama cikinta dashi sannan ta d'auki gasashshen bread ta fara ci a nutse, daga yawan abincin ta fahimci yau khaleefa bai ciba kwata kwata.
Bata damu ba ta gama abinda take yi ta koma d'akinta, sake gyara d'akin tayi da kyau sannan ta zauna tana duba wasu daga cikin kayan lefenta, saboda auntie tace ta d'ebo wasu ta bawa khaleefa a d'inka mata.
Yawan kayan ba k'aramin tsoratata yayi ba har ta kasa yin abinda tayi niyyah ta tsaya kawai tana kallon su. Wannan uban kaya duk ita da waye zasu saka su? Anya ba mistake akayi aka had'o mata da wad'an da ba nata ba? Toh amma waye a gidan su zaiyi aure nan kusa da za'a ce lefen tane ko lefen shine aka kawo mata.
Duk da haka bataji zuciyarta ta nutsu ba saida ta kira ummie, bayan sun gaisa take tambayarta "ummie duk wannan kayan na waye?" Ummie daga can b'angaren murmushi tayi tace, "na kine raihana wani abu ne".
Zaro ido tayi kamar tana gaban ummien tace, "ummie ai sunyi yawa".
"Tom saiki fad'awa doctor surayyah da mijin ki su rage miki su tunda su suka kawo su haka".
Rufe bakinta tayi tace, "Kae! ai bazan iya fad'a musu haka ba".
"Toh tunda ba zaki iya yi musu magana ba nima saiki daina tambayata".
Shiru tayi tana sake kallon yawan kayan kafun ta sake cewa, "toh kuma ummie ba za'a iya rabawa mutane ba? Sai kuma ku d'auka wasu a ciki?".
"In banda ke raihana ina kika tab'a ganin an rabar da lefe, na dai rabawa k'awayen ki kayan kwalliya sai Inna dana d'aukar wa atamfa itama saboda gudun matsala tunda ana su khausar ma duk saida na bata atamfofi".
Raihana tace, "toh ummaa fa? Ita ba'a d'aukar mata ba?".
Ummie tace, "a'a ita ummaa bata da matsala, ko an bata ba lallai ta karb'a ba".
D'an jimm raihana ta sakeyi kafun tace, "shikenan ummie sai anjima ace dasu hibba bana gaishe su tunda sun kasa zuwa mun har yau".
Ummie dariya tayi tace, "ba ruwana ni kam bana bada sak'o irin wannan". Daga haka ta kashe wayarta tana murmushi, in banda ma raihana ina ake d'ibar lefe a rarrarabar aje a samu matsala da dangin miji, ita kam ko ba za'a samu matsalar bama ba zata iya tab'a kayan nan ba tunda ga da sunan wadda aka siya.
Kusan kala bakwai ta futar, atamfa leshi da wani shegen material.
Kwaso kayan tayi ta nufi b'angaren saman Auntie.
*****Sameera kuwa tun a waccen ranar da suka baro asibiti bata yi burki a ko'ina ba sai gidan hajiya tafeeda. A lokacin tana shirin gama abinda takeyi taje gidan sameeran, yanayin su data kalla kad'ai tasan lallai ba lafiya ba, saita zauna tana tambayarsu, "lafiya kuwa k'awata na ganki haka?". Girgiza mata kai sameera tayi ta warware mata duk yadda sukayi da surayyah a yau, tab'e baki hajiya tafeeda tayi bayan gama sauraron duk bayanan bakin sameera, "kinga abinda nake fad'a miki kullum ko? Dama ke kika d'auki surayyah wata mutuniyar arzik'i har kike shirin bata aurin y'ar ki, Amma Allah na tuba astagfirullah surayyah har mutum ce......". Da sauri Mamie ta d'aga mata hannu, "ai kinji matsalar ki tafeeda, bansan me surayyah tayi miki ba da yasa bakya iya fad'ar alkhairy a kanta sai sharri,,,,, Ni yanzu abinda ya kawo ni shine, zuwa nayi ba dama kina son had'a Imran da shaheeda aure ba? Toh don Allah ki fasa da shaheedan ga nuriyyah nan mu had'a auren da ita madadin y'ar uwarta,,,,,, shiru hajiya tafeeda tayi tana tunanin yadda zata karb'i Nur d'in don ita tun farko ba ita taso ba shaheeda take so, itace irin zubin surukar da take fatan samu don ta fudda ita kunya cikin k'awaye".
*Bayan wasu kwanaki*
******Tsaye take gaban mirrow ta tsurawa kanta ido tana kallo wai dole saita gano muninta kota inda ta gaza, a lokacin tana sanye da riga iya gwiwa kamar gown sai dogon wando tight daya kwanta a jikinta yabi fatar k'afarta ya lafe. Sai riga marar nauyi white data d'an kamata kad'an daga sama, ta bud'e daga k'asa.
Sallamar Nur ta sata sauƙe k'ak'k'arfar ajiyar zuciya tare da lumshe idonta, kan drower mirrown nuriyyah ta zauna ta fashe da kuka mai ban tausayi, a tsanake ta juyo duk da yadda zuciyarta ta tsinke da jin sautin kukan Nur d'in.
Zuba mata ido tayi ba tare da tace komai ba tana kallon yadda take risgar kuka.
Bata tambayeta ba'asi ba har tayi mai isarta ta fara bata labarin abinda yake faruwa, "kinsan Allah na tsani kaina na tsani wannan rayuwar da nake ciki a halin yanzu, me yasa mamie take son lallai sai taga bayan rayuwar mu sai kace ba ita ta haife muba?, Da farko ta raba ni da Yaya Ayman yanzu kuma tana son lallai saita had'a ni da wanda sam bana ra'ayin shi shima bece yana sona ba......". Sai a lokacin shaheeda ta dafa kafad'arta tasa hannu tana share mata hawaye da tafin hannunta, "kiyi hak'uri Nur kowanne mutum da kike gani da k'addarar shi a rayuwa, sannan wani abun sam ba alkhairy bane a rayuwar mu muke nacewa a kan son shi, watak'ila Ayman ba shine mijin ki ba shiyasa komai yake shirin zuwa k'arshe a tsakanin ku cikin lokaci k'alilan,,,,,," shiru ta sakeyi kafun taci gaba da maganarta, "waye shi wanda ake son a had'a kun?".
Nur dakatawa tayi da kukan da take kad'an tace, "Imran ne d'an hajiya tafeeda....".
Wani irin murmushi shaheeda tayi a ranta tana k'issima yadda zata juya al'amarin izuwa ga mafarin shi, lallai ya kamata hajiya tafeeda ta girba abinda ta shuka na izgilanci da shiga hususiyyar ubangiji ko yayane. Saita sake gyaraa zama tace da Nur, "to ke meyasa ba zaki amince ba, ko kin fison kiyi bawan ba k'anin, ga rashin Ayman ga rashin mutum kamar Imran".
Cikin muryar kuka yanzun ma tace, "kinsan fa waye Yaya Ayman, haka zalika kinsan wanene Imran tunda ai da dake ake son had'a shi auren,,,, ko k'afar Ayman Imran bai kama ba a hali da d'abi'u masu kyau na rayuwa, kuma fa shi bawai yana Sona bane, meyasa ma zan auri tsohon saurayin raihana da maman su ta shiga ta futa ta raba su ba tare da tayi mata laifin komai ba, shine ni kike tunanin in na aure shi zata bari mu zauna lafiya,,, wallahi bazan aure shiba yaya ko zan rasa raina sai dai duk abinda za'ayi mun ayi amma wallahi bazan aure shiba....".
Ta k'arashe fad'a tana sake fashewa da wani sabon kukan. Rungume ta shaheeda tayi tsam a k'irji atana rarrashi da fad'a mata dad'ad'an kalaman da zasu kwantar mata da hankali, cikin hikima da dabara kuma ta dinga zugata kan karta amince ta yadda ta rasa masoyinta Ayman, don ba zata samu kamar shiba a wannan duniyar. Shaheeda ta nuna mata cewa zata goya mata baya ta tsaya mata da iya k'arfinta har ta kaiga cimma burinta na auren masoyinta Ayman.
*******Yana zaune a office d'inshi ya had'a kanshi da table, sanye yake da suit black colour ya sakaye k'afar shi cikin cover shoe samfurin.... Biro ne a hannun shi na dama da wata bugaggiyar takarda da alama zaiyi signing ne.
Da sallama kaamil ya turo k'ofar office d'in ya shigo, baiji sallamar ba har ya k'araso gaban table d'in dake gaban shi yaja kujera ya zauna. Da farko ya d'auka bacci yake yi amma daga baya saiya gane idon shi biyu kawai yayi zurfi a duniyar tunani ne.
Buga table d'in yayi kad'an da hannun shi, abinda yasa Ayman yayi firgigit ya d'ago kanshi had'e da dafe kan da hannun shi d'aya tare da lumshe ido a lokaci guda.
"Kamar baka da lafiya Ayman? Ko har yanzu jikin ne? Ai dama kayi saurin dawowa bakin aikin bayan hutun kama bai k'are ba har yanzu". Kaamil ne yayi wannan maganar da tarin kulawa.
Bud'e idon shi da suka sauya launi yayi ya maida hannun shi kan takardar yayi signing ya turawa kaamil ita gaban shi.
D'auka yayi yana dubawa, ya mayar da ita cikin kundinta ya sake tsayar da idanun shi kan Ayman da yayi relax kan kujera still idon shi a rufe.
"Engineer Ina ganin ka tafi gida haka ka huta nasan zakaji sauk'in abinda yake damun ka, and please kar ka dawo har sai ka warke".
Hankie yasa ya share zufar fuskarshi sannan ya tsaida hankalin shi kan kaamil yace, "kaamil ba zaka gane ba, zamana a nan zanfi samun nutsuwa da kwanciyar hankali akan zama inuwa d'aya da ita Ina kallonta da jin duk wani motsinta a cikin jinina yana gudu,,,,,, kaamil bansan ya zanyi na cire ta daga zuciyata ba,,,,, Ina ganin sonta shine zai zamo ajalina don a yanzun ta tsere mun tserewa irinta har abada....".
Cikin matuk'ar tausayin shi kaamil yace, "matsalar soyayyah ce kenan? Tana raye ita masoyiyar taka kota mutu? Don naji kana ta tsere maka".
Girgiza mishi kai yayi ya sake bud'e bakin shi daya mishi nauyi da kyar yace, "bata mutu ba".
Kaamil yace, "toh ai da sauk'i,,, tasan kana sonta?".
Sake girgiza mishi kai yayi yana yak'i da ruwan hawayen shi da suke gudu wajen ganin sun fallasa kansu ga kaamil.
Dukan table d'in kaamil yayi da k'arfi yace, "no wonder! gaskiya mana kake son kashe kanka a banza, ai kai kaso ka wahalar da kanka Ayman, ka tab'a ganin inda aka dinga dakon son mutum ba tare da an sanar dashi ba,,,, how do you expect she know all that you are feeling....".
"Ba zaka gane ba kaamil ta riga ta gama fin k'arfina zuwa yanzu saboda zata kasance k'ark'ashin shak'ik'ik'ina..... Khaleefana, y'an biyuna......". Ayman yayi wannan maganar kamar me yin fad'a da wani irin tune, sai a lokacin hawayen shi suka samu damar futowa.
Shikam kaamil shiru yayi na adadin wasu mintuna kafun ya mik'e tsaye yayi tattaki zuwa gaban Ayman ya tsaya, "tabbas tafi k'arfin ka kamar yadda ka fad'a nima na yarda, sai dai ka amayar mata da abinda yake cikin zuciyar ka, ba don ka jawo hankalinta zuwa gareka ba, a'a sai don kaji sauk'i da sassauci a cikin zuciyar ka, ajiye soyayyarta daga kai sai kanka shine yake cin ranka yake hanaka sukuni, amma da zarar taji zaka nemi rabin damuwar ka rasa insha Allah.....".
Daga kallon da yake mishi ya gane sam Ayman bai fahimci abinda yake nufi ba, ba kuma zaiyi ba,,,, sai dai fa shi yana ganin hakan shine kad'ai maslaha, da zarar ya futar kuma zai samu nutsuwar zuciya, in Allah ya taimake shi har ya fara mantawa da ita da babin wata soyayyar ta gaba d'aya.
A d'arare ta shigo parlon duk da bata ji alamu ko motsin wani a ciki ba, har yanzu sanye take da kayanta na d'azu har gyalen, sai dai rungume da tulin kayan data d'auko za'a kai d'inki kamar yadda auntie ta bata umarni.
A d'aya daga kujerun parlon ta zauna ta ajiye kayan gefe tana kallon wani tabkeken hoton su da sukayi su uku, Ayman da khaleefa a gefen auntie, ta rungumo su jikinta gaba d'aya ta sasu a tsakiya tana dariya.
Sunyi maseefar kyau a hoton, kuma hoton an yi shine tun kafun tafiyar khaleefa karatu Germany. Hankalinta da tunaninta sun tafi gaba d'aya wajen kallon hoton shiyasa har bataji shigowar shi parlon da sallamar da