Showing 156001 words to 159000 words out of 288773 words

Chapter 53 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

4788

gaisa dashi su futa kamar yadda ummie ta musu umarni.
Duka cikin ladab suka gaishe shi, ya amsa yana tambayar sunan kowanne d'aya a cikin su, "al'ameen! Hibba! Sai ke kuma jidderh abi?". Khaleefa ya tambayi jidderh da take zaune gefen shi don ita ta rattaba mishi sunan kowa.
Su al'ameen da muhibba sun tashi zasu futa khaleefa ya hana su, dole suka koma suka zauna suna satar kallon raihana da batasan ma suna yiba, kacokan hankalinta yana kan khaleefa tana mamakin yadda yake ta jan su jidderh da surutu,,,,, ashe ya iya magana da yara haka? Amma bai iya da manya ba? Ko kuma sune yake yiwa magana a tsaitsaye ba russunawa oho mishi?
Futowar ummie ce ta katse kowa daga abinda yake yi, babban gyale ta rufo har kanta, daga wajen k'ofar d'akinta ta tsugunna, shima sake russunawa yayi yana gaishe ta. Ta amsa a gurguje ta tashi ta koma d'akinta.
Kamar jira yake su gama gaisawa ya tattara shima ya mik'e ya bawa su al'ameen kud'i yace ma raihana bari ya jirata a waje.
Yana shirin futa Abba yana shirin shigowa, sai ya durk'usa a nan shima suka gaisa ya k'arasa futa shi kuma Abba ya k'arasa shigowa.
Har d'akin shi raihana taje ta gaishe shi, ya amsa cikin jin dad'in ganinta da sauyawar da tayi, duk da ba k'iba ko fari tayi ba amma ta samu nutsuwa da ganin yanayinta.
Ta jima suna hira har ta karb'i takardunta na makaranta da suke gurin Abban amma koda wasa bata fad'a musu batun tafiyar ta da khaleefa Germany ba.
Ko data dawo gurin ummie naseeha mai ratsa jiki ta k'ara yi mata mai had'e da jan kunne, tayi shiru tana sauraron ummien har ta gama.

K'ara rashewa tayi tana ta hira da k'annenta kamar a gidan zata kwana bayan taci abinci, ganin bata da niyyar tafiya sai ummie ta tambayeta, "Wai yaushe zai dawo ku tafi? Ko kuma anan zaki kwana?".
"A'a yana k'ofar gida nice ban tashi tafiya ba har yanzu ummie......".
Saroro ummie tayi tana kallonta da mamaki kafun tace, "raihana mijin naki kika shanya a k'ofar gida kamar wani yaron ki ko drivern ki?, Yanzu fa na gama yi miki naseeha ashe aikin banza nayi tabi ta bayan kunne".
Raihana shiru tayi a ranta tana tunanin shiya sani,,,,, da ya kawota tun da wuri kamar yadda auntie taso ai data sake kamar kowa a gidan su yadda ya kamata.
"Maza kije ku tattara ku tafi". Ta tsinci muryar ummie a kunnenta tana fad'a cikin bada umarni. Mik'ewa tayi ummie ta bata duk abinda zata bata ta tattara ta har wajen k'ofar parlon tana yi mata sallama da addu'a, "ki gaida gida ki gaishe da doctor surayyah, mun gode da ziyara mijin kima kiyi mana godiya a gurin shi..... Su hibba sunga sak'o Allah ya k'ara rufa asiri".
Cikin muryar shagwob'a tace, "ummie kora ta kuke yi....".
Ummie tace, "ehh tafi gidan ki tunda dai nan ba gidan ki bane".
Y'ar k'aramar dariya tayi tace, "Allah ummie zan iya fasa tafiya ma....".
Ummie tace, "toh fasa mana kiga in zaki samu gurin bacci a nan...".
Dariya tayi, ummien ma tayi murmushi.
"Ummie zanyi kewarku" raihana ta fad'a kamar tayi kuka.
Ummie tace, "muma zamuyi kewarki muna kan yi ma,,,, maza ki gaida mutanen gidan".
Murmushi raihana tayi daga haka sukayi sallama ta futa.
Yana zaune cikin mota ya kwantar da seat yana kallon k'ofar gidan su, lokaci bayan lokaci kuma yakan ja dogon tsaki,,, kafun ta futo kuwa ya cika yayi fam kamar zai fashe.
Kallo d'aya raihana ta mishi ta d'auke kanta a lokacin data shiga cikin motar.
Yaa jima kafun ya tashi motar yayi reverse ya fara gangarawa gidan iya.
Wannan karon tare suka futo, ya d'auko ledar tsarabar su, yana gaba tana bin bayan shi suka shiga cikin gidan.
Malam yana kishingid'e kan madaidaicin carpet a tsakar gidan, gefen shi radion shice yana sauraron taskar labarai. Ganin su ya sashi mik'ewa zaune had'e da fad'ad'a fara'ar fuskar shi yana musu lale marhaba.
A kusa dashi khaleefa ya zauna, raihana kuma ta zauna d'an nesa da inda yake tana gaishe shi. Malam ya amsa mata cikin sakin fuska har yana zolayarta "wannan tafiya ta dare ince ko anan zaku kwana....?".
Murmushi tayi had'e da gyad'a mishi kai, malam yace, "yauwa koda naji".
Sai a lokacin suka gaisa da khaleefa shima.

Turus! Iya ta tsaya ganin bak'in da bata saka ran zuwan suba a wannan tsohon dare. Saita k'araso a hankali ta ajiye damammiyar furar malam data sa mishi a firinji wai ta d'anyi sanyi.
"Wad'an nan kuma daga ina ni jikar Indo cikin uban daren nan".
Murmushi raihana tayi, khaleefa kuma ya d'auke kanshi kamar baiji ta ba.
Maficin gefen malam ta kwandalo mishi a keya, "kana jina ina magana kayi shiru....".
Khaleefa ya dafe k'eyar shi inda maficin ya sauka yana fad'in, "ouch! toh nikam me zance miki iyaaa? Zuwa fa mukayi mu gaishe ki keda malam".
"Kuka zo gaishe ni ko kuka zo kwana a gidana?".
Kusan su duka murmushi sukayi saboda yadda iya tayi maganar cikin ban dariya.
Sun gaisa da ita itama, kafun khaleefa ya ajiye musu ledar daya shigo musu da ita gaban su.
Duk sukayi godiya. Sun jima kad'an iya hadda jan raihana d'akinta suka had'u da harira suka yita hira.
Khaleefa kuwa shiru yayi a gaban malam, abinda ya alamtawa malam akwai magana a bakin shi, sai ya fuskance shi da kyau yace, "khaleefa kamar akwai abinda kake son fad'a?".
Khaleefa ya kalli malam, sannan ya sauke kanshi k'asa yace, "Eh Ina son naji ko ka tuntub'i Auntie da maganar nan da mukayi dakai farkon dawowata?".
Murmushi malam yayi irin nasu na manya yace, "kad'an k'ara mana lokaci, maganar tana buk'atar nutsuwa".
Khaleefa yayi shiru yana wani nazari a cikin zuciyar shi kafun ya sake cewa, "na kusa komawa Germany fa! sai dai ba damuwa zanci gaba da sauraron ka". Malam yace, "Masha Allah! Surayyah ta fad'a mun waccen ranar da tazo,,, fatan Allah yayi jagora ya bada dukkan nasara...".
Khaleefa yace, "ameen". Sunci gaba da tattaunawa akan aikin da abinda ya shafe shi, tare suka sha furar da iya ta kawowa malam, kafun iya ta fargar dasu dare da ya fara nisa. Yana duba lokaci kiran auntie yana shigowa, sai ya d'aga ya kara wayar a kunnen shi "da gaske baku dawo ba?". Ta tambaye shi kai tsaye.
Khaleefa yace, "eh! Amma yanzun nan zamu taho".
Da sauri auntie tace, "cikin daren nan kake nufin zaka taho da yarinyar mutane,,,, idan kai ka saba wasa da rayuwarka toh ita bata saba ba, ku kwana a nan da safe kawai sai ku taho".
Khaleefa zaiyi magana auntie tace, "bani malam d'in".
Sai ya mik'awa malam wayar yana tunanin yadda zasu kwana a gidan bayan basu zo da shirin kwana ba. Tayi magana ta mintuna da malam kafun suyi sallama malam ya bashi wayar shi.
Iya da take gefe tace, "Magaji idan ba zaka kwana ba, ba dole zaka iya tafiyarka amma kai kad'ai, don raihana tayi bacci a parlour tuni".
Malam yace, "ai bazai yiwu ya tafi kuma ya barta a nan ba,,,, zasu kwana tare saboda shima akwai lazimin da zan bashi yayi cikin dare".
Iya tace, " zai iya kuwa? Nasan Magaji da bacci fa" malam yace, "banda neman rigima dai,,, khaleefa ne fa ba Ayman d'in da kika saba yiwa tsiyar ba tohh".
Sai a lokacin khaleefa yayi murmushi. Iya kuma ta tashi ta tafi tana dariya.
D'akinta ta gyarawa raihana ta bata sabuwar rigar bacci dal a ledarta fara, ta had'a mata ruwa me zafi tayi wanka ta futo ta shirya cikin kayan. Ta nad'e a lafiyayyen gadon iya sai bacci.
Shima khaleefa alwala ya d'auro, malam ya fad'a mishi yadda zaiyi komai daki daki, d'akin da aka sauki raihana iya ta mishi jagora da sallayah sabuwa.
Saida yabi komai na d'akin da kallo, d'akinta a gyare kamar a yada tuwo k'asa aci. Dama indai ana maganar tsabta iya k'arshe ce.
Kusan kwana yayi yana sallah da addu'o'in da malam ya bashi. Tun raihana na farkawa cikin dare ta ganshi har baccin ta yayi nisan data daina farkawa ma.

Da asubah ita ta fara farkawa, ta ganshi a zaune kan sallaya ya jingina da gefen gadon yana bacci.
Karo na farko data tab'a tsayawa ta kalleshi, yana kama da Ayman irin kama ta sak da sak d'in nan, sai dai yafi Ayman haske sosai da murd'ewar jiki, komai nashi me sanyin kyau ne in aka d'aukewa baud'ewa da izzar maseefa fal ranshi.
Hucewa tayi bayan ta gama yi mishi kallon k'urilla, a bathroom d'in ta d'auro alwala, tana futowa ta ganshi a zaune kan gadon ya had'a kanshi da gwiwa.
Bata bi ta kanshi ba ta shimfid'a sallaya ta gabatar da raka'atainil fajr. Ko data idar bata tashi ba ta d'ora da addu'o'in ta har zuwa lokacin da aka kira sallar asubah, tana jin shi ya d'aura alwala ya futa ita kuma ta tada tata sallar.
Kafun khaleefa ya dawo ta gyara d'akin duk da ba wani datti yayi sosai ba, ta maida kayan jikinta na asali da hijabinta, ta zauna can k'arshen gadon tana laziminta, a haka khaleefa ya dawo ya same ta. "barka da safiya" raihana ta fad'a bayan ta d'ame zuciyarta don cika umarnin auntie. "lafiya" ya amsa mata kamar kullum.
Wayoyin shi ya d'auka da mukullin motarshi yace, "zamu tafi yanzu ko zaki taho anjima". Mik'ewa tayi itama ta d'auki wayarta.
Ita ta fara futowa sannan shi, har k'asa ta durk'usa ta gaishe dasu iya da harira da take aikin had'a abin karin kumallo.
Suka amsa iya na d'orawa da tambayarta, "ba dai har zaku tafi ba?". Khaleefa da yake bayanta yace, "eh iya tafiya zamuyi". Iya tace, "haba magaji ai ka bari rana ta futo ko?". Durk'usawa yayi ya gaishe su d'aya bayan d'aya. Suka amsa da sakin fuska. Ya tambayi ko malam ya dawo zaiyi mishi sallama, iya ta fad'a mishi malam bai dawo ba,,, watak'ila shida shigowa ma sai rana tayi haske.
Ba don iya taso ba sukayi mata sallama suka tafi.

*****Malam yana zaune yana cin abinci iya na gefen shi, labarin tafiyar khaleefa Germany yake yi mata da ranar da zasu tafi d'in. Iya da mamaki take tambayar shi, "Amma khaleefa ba dai zurfin ciki ba, kasan Allah bai fad'a mun ba, koda yake zamu gidan nida harira kwanan nan zan had'u dashi ai".
Malam ya jinjina kai yace, "shin wai ko kinsan yaran nan basa son junan su kuwa?".
Da mamaki iya tace, "wad'an ne yaran kenan malam?".
Malam yana sake jinjina al'amarin yace, "Abdallah da raihana nake magana a kai".
Iya shiru tayi kafun can malam ya sake cewa, "Ina tunanin akwai abinda yake shirin faruwa tsakanin uwa da yaranta, lallai wani abu mai girma yana tunkaro surayyah".
Rausayar da kai iya tayi, don inda sabo ta saba da irin wannan maganganun na malam, har yanzu ta kasa fahimtar abinda yake tunkakar surayyah da malam yake magana a kai, gashi kota tambaya baya wani tsayawa ya mata cikakken bayanin da zata fahimta.
Sai ta mik'e tana fad'in, "toh Allah ya iyakan ce mata".
Malam ma yace, "ameen" a lokacin da yake gyara hannun rigar shi zai fara cin abinci.

*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*


_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page forty four4️⃣4️⃣


Da yamma raihana tana tsaye a kitchen d'inta tana kallon kayan kitchen d'in da bata tab'a amfani da komai a cikin suba, saboda auntie data haramta mata aikata hakan, a cewarta akwai inda ake buk'atar girkinta fiye da nan gidan. Yanzun ma sanye take da doguwar rigar atamfa, sai dai ko kalar atamfar ba'a gani saboda yadda hijabin ya sauka kamar zai rufe tafin k'afarta.
Ajiyar zuciya ta sauke ta futo a hankali ta zauna cikin parlon, tana daga nan taji dawowar Auntie, sai da ta bari aka d'auki wasu mintuna ta tabbatar ta nutsu ta huce gajiyar aiki data d'auko sannan ta tashi ta nufi saman.
Sai dai kamar tare suke da khaleefa tana zama ko gama gaisawa ba suyi ba shima ya shigo.
Saida suka gaisa auntie ta fara tambayar shi yadda sukayi da iyayen raihana jiya.
Khaleefa yayi k'asa da kanshi yace, "ita zaki tambaya auntie".
Kama hab'a auntie tayi tana kallon shi, cikin had'e rai da harshen Arab tace, "khaleefa dama munyi haka da kai? Toh wallahi ka kama hanya anjima da dare kaje kayi musu bayani da kanka tun kafun naja layi tsakanin ka da Germany kowa ya huta...".
Baice mata komai ba, har ta gama maganarta ta tashi ta bar musu gurin, raihana ma mik'ewa tayi ta futa, ta rasa abinda yake had'a khaleefa da auntie rigima,,, Koda bata ji abinda auntie ta fad'a ba tasan fad'a ne takeyi akan wani abu daya yi mata ba dai dai ba, abinda bata tab'a ji ko gani sunyi da Ayman ba, magana d'aya ce take had'a su ta raba su, amma khaleefa saita b'ata rai yake yin abu komai muhimmancin shi.

A daren ranar ba don yana so ba ya shirya ya koma gidan su raihana, Abba ya yiwa maganar tafiyar, a take kuwa ya nuna amincewar shi, "tunda matar kace mu meye namu a ciki khaleefa! Ka d'auketa ku kewaye duniya ma". Ya d'ora da mishi addu'o'in fatan alkhairy da samun nasara.
Sun rabu yau ma bayan khaleefa ya gaisa dasu hibba ya basu tsarabar biscuits, sukayi godiya suka bashi sak'on ya gaishe musu da Aunty raihana". Yace zai fad'a mata, ya musu sallama ya tafi.
Yau ko gidan iya bai tsaya ba, sai number haeydar daya kira ya tambaye shi ko yana gida.
A k'ofar gidan su yayi parking ya fad'a mishi ya k'araso, koda haeydar ya futo yaso su shiga daga cikin gidan ya gaisa dasu mammie, sai dai khaleefa ya nuna mishi yana sauri ne sai ko in ya sake dawowa. Suka gaisa a gurguje ya huce gida.

Rayuwa taci gaba da tafiyar musu lafiya kamar yadda suka fara, suna zaune cikin mutumci da mutunta juna, tsakanin raihana da khaleefa suna gudanar da rayuwarsu ba takurawa ko tsawwalawa ga juna.
Khausar da Salma sunzo mata yini, taji dad'i kuwa suka yini suna hirar su ta zumunci, har Salma na mata albishir da cikin khausar,,, taji dad'i ta taya ta murna sosai, ko kafun ta tafi saida ta raka su gurin auntie da yamma suka gaisa da ita, khausar aka fara d'auka sannan Salma ma mijinta yazo suka tafi daga baya.
Har suka gama yinin su suka tafi basu ga khaleefa da idon suba, saboda ranar ya tashi baya jin dad'in jikina shi kusan wuni yayi a kwance cikin d'akin shi.

Shirye shiryen tafiyar su Germany ya kammala, auntie ta had'awa raihana turaruka kala kala, ta adana mata su yadda ba zasu fashe ko su zube cikin kaya ba. Ta sake k'ara mata wasu itace na hawa dasu dilke da yadda zata had'a ragowar kayan gyaran jikin kamar yadda ta koya mata, sai dai ta umarceta da kar ta fara amfani da komai inba turaren wuta na d'aki dana jikinta ba har zuwa lokacin da zata cika wani adadin lokaci, in lokacin yayi kuma ita da kanta zata fad'a mata.
Sam raihana bata gane kan karatun Auntie ba, kuma bata takura kanta lallai saita gane d'in ba.

@@@@@@ Cikin satikan da suka biyo baya aka tsaida maganar auren shaheeda da Imran, basu sa da yawa ba don bazai huce nan da watanni biyu masu zuwa ba.
Farin ciki a gurin hajiya tafeeda ba'a magana, sai yanzu taji hankalinta ya kwanta d'anta zai auri irin matar da take so, gashi yanzu Imran ko musu baya yi mata akan komai, ranar data tura shi ganin shaheeda ma uban shopping d'in da ya mata, saida tayi ta saka mishi albarka bata shirya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login