Showing 177001 words to 180000 words out of 288773 words
Chapter 60 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt
ya tabbatar mata yana jinta, aikuwa ta dinga sauke ajiyar zuciya a jejjere tana hamdala da Allah yasa bai mutu ba yana raye.
Janye jikinta tayi nesa dashi bayan ta d'auke hannunta daga kanshi ta kashe gas da yake aiki.
Tana nan dai tsaye kamar soja sai sannu take jera mishi lokaci bayan lokaci kuma tana share hawaye. Shi kuwa saida ya samu ciwon ya lafa mishi kad'an ya tashi zaune yana kallonta da idanun shi da suka dawo dishi dishi. "sannu ya kake jin jikin naka?". Bai iya amsa mata ba saboda wani mugun amai daya yink'uro mishi, ya mik'e da sauri don ya futa daga kitchen d'in sai dai taku d'aya ana biyu ya durk'ushe a gurin ya fara kelaya amai.
Gaba d'aya raihana ta rud'e ta rasa inda zata tsaida k'afarta sai jera mishi sannu take, ko daya gama ita ta bashi ruwa ya wanke fuskarshi da bakin shi tunda kayan jikin shi basu lalace ba, taja mishi stool ya zauna ita kuma ta fara wanke gurin, saida ta tsabtace gurin tass duk yana kallonta sannan tazo ta had'a mishi tea me kyau ta mik'a mishi, ya karb'a da kyar yana bin yatsun hannunta da kallo, bashi da wani zab'i a yau.
Saida ya rintse idonshi ya toshe hancin shi gudun kada yaji warin lallenta sannan ya fara sipping tea d'in kad'an kad'an, kafun ya gama kuma tayi sauri ta had'a mishi betroos, sweet potatoes, egg and mayosauce ta juya mishi sun gauraye guri guda ta ajiye mishi plate d'in a gaban shi.
Ya d'auka ba tare daya kalleta ba ya fara ci a nutse, yaci zai kai rabi ya maida plate d'in gefe.
Sai a lokacin hankalin raihana ya kwanta har ta tuna da yunwar cikinta itama, ta tsiyaya tea tasha, ta ci ragowar abincin daya rage tunda dama shi kenan ta dafa.
Abinda yasa ta matuk'ar baiwa khaleefa tausayi kenan, sau biyu tana nuna mishi sadaukarwa, yana sane a waccen ranar ma ba irin zagin da ba'a yi mata ba ta jure amma ana tab'a mahaifiyar shi ta maida raddi, gashi a yauma ta dafa abincinta don taci ganin shi a mawuyacin hali ta hak'ura daci har saida shi yaci ya rage, toh da bai rage ba kuma shikenan sai dai ta kwana da yunwa?, Anya kuwa akwai irin wannan yarinyar a zamanin nan? Toh ko Saleema dai iyakacin abinda zatayi mishi kenan.
Khaleefa bai tashi daga inda yake zaune ba har saida ta wanke kayan da tayi amfani dasu a lokacin, bata jin bacci sam cox abinci da shayin da tasha yasa idonta ya bushe, hakan yasa ta yanke shawarar goge k'urar data cika mata d'akin girkin.
Khaleefa yana zaune ya kasa tashi sai bin duk wani motsinta yake da kallo har ta gama, a nan ya sake tabbatar da tsabtarta kamar auntien shi.
Ita kuwa saida ta gama ta d'auki hanyar futa a kitchen d'in ta kalleshi tace, "Saida safe Allah ya k'ara lafiya".
A sanyaye ya amsa da, "ameen nagode".
Ba tace dashi komai ba ta huce, shi kuwa khaleefa shiru yayi yana nazarin wasu abubuwa masu girma tattare da ita, ya jima a gurin zaune kafun ya kashe wutar d'akin girkin ya futo, a parlour yayi kwanciyarshi don sam baijin komawa cikin d'akin shi.
*NIGERIA*
Amarya Saleema tana zaune a parlonta da safiyar washe garin kaita gidan mijinta, tayi kwalliyarta me kyau cikin riga da zani na wata atamfa blue tayi parking gashinta dokinta a k'eyarta tayi d'auri a saman shi.
Wayarta ce a hannunta tana yin chat da k'awayenta. A dai dai lokacin Imran ya futo shirye cikin shaddar shi dakakkiya, tak'aitaccen kallo yayi mata ya d'auki hanyar stairs zai sauka, ba tace mishi ba shima baice mata ba har ya futa.
Kai tsaye gidan auntien su ya nufa ya sameta tana aikin had'awa yara abun kari, a parlonta yayi zaman shi yana taya k'aramar k'anwarshi assignment kafun auntien ta futo ta ganshi, saita saki baki tana kallon shi da mamaki, "ango ne da wannan sammakon gidana?".
Murmushi yayi ba tare daya bata amsa ba ya fara gaisheta.
Ta amsa tana tambayar lafiyar Amarya, ya bata amsa da, "tana lafiyarta".
Ci gaba da taya baby assignment yayi ita kuma ta gama aikin had'awa sauran yaran breakfast ta had'a kansu har baby don suyi su karya taje ta ajiye su school gudun kada suyi late, Sam bata d'auka yau zai buk'aci abincinta ba tunda taga dai ai yanzu yana da aure ba irin da ba, shi kuwa Imran kusan abinda ya kawo shi kenan don haka sai baiyi kara ba ya tambayeta abincin. Saida ta gama zolayarshi Wai ta yaye shi sannan ta shiga kitchen ta had'o mishi a plate.
Ko daya gama breakfast shiya huce mata da yaran makaranta kamar yadda ya saba a duk lokacin daya je musu gidan da safe, ya raka su har harabar makarantar sannan ya huce kasuwa.
Saleema kuwa tana nan zaune hajiya tafeeda tasa aka turo mata da lafiyayyen abinci, taci ta k'oshi tabar kayan a nan dinning ko Imran zai dawo yaci ita kuma ta shige d'aki tayi kwanciyarta.
Hajiya tafeeda tun tana saka ran saukowar Saleema ta gaisheta har ta gaji, ragowar bak'i y'an biki da suka tashi tafiya suka ce zasu je suga amarya, bata hana suba sai dai har suka shiga suka gama sallamarsu a parlon bata kula suba tayi banza dasu saboda sunzo a lokacin da take waya da k'awayenta, haka suka gaji da zama suka tafi ba suga ko k'eyar amarya ba.
Ko da suka fad'awa hajiya tafeeda ba tace musu komai ba sai shiru da tayi tana tunanin ko bacci takeyi? Ko Kuma har yanzu dai jikin ne.
***********
A hankali ranaku suka dinga tafiya har gashi kusan sati da auren Imrana da Saleema amma ko sau d'aya hajiya tafeeda bata samu arzik'in gaisuwa a gurin shaheeda ba, tun tana kawo uzururruka a zuciyarta har ta daina, har yanzu bata fasa aika mata da abinci sau uku a yini ba, amma ko d'and'ane Imran bai tab'a yiba, a kullum safiya zai sauko ya gaishe ta a matsayinta na mahaifiyar shi, daga nan kuma yayi tafiyarshi gidan auntien su ya karya ya huce kasuwa don tunda yayi aure bai d'auki hutu ba, toh hutun mema zai zauna yayi, matar da ba ra'ayin shiba.
Idan suka tashi kasuwa yakan zauna tare da abokan shi a majalisa ko ya tafi gurin dad d'inshi ko kuma ya dawo gidan ya shige d'akin shi ya kwanta kafun lokacin bacci yayi ya shirya ya tafi d'akinta don bai tab'a raba makwanci da ita ba kamar yadda bai tab'a neman komai a gurinta ba.
Yauma kamar kullum ya dawo gidan wajen k'arfe tara na dare bayan ya biya gidan auntie ya cika cikin shi taf, tana zaune hamshak'iyar ta mik'e k'afarta kan doguwar kujera tana danne danne a waya, ya k'araso cikin parlon yana yi mata sallama, ta amsa tana yi mishi sannu da zuwa, baice mata komai ba ya ajiye mata ledar fruits a gefenta shi kuma ya shige d'akin shi.
Da kallo ta bishi har ya shige sannan ta dawo da idonta kan wayarta tana jan siririn tsaki, ba laifi shima guy nan ya had'u amma ba kamar khaleefa ba, banda wannan matar ta shigar musu hanci aida yanzu itace khaleefa ya aura ba raihana ba.
Da dare tana kwance bayan ta sauya kayan jikinta zuwa na bacci ta sake feshe jikinta da turarukan ta kwanciya tayi tana karanta addu'ar bacci a zuciyarta.
Tana jin shigowar Imran ta d'auke wuta kamar tayi bacci, shi kuwa yau yazo ne ya maida ita cikakkiyar matarshi don bashi da wani zab'i.
A gefen gadon ya zauna yana waya da wani abokin shi abokin kasuwancin shi da ya tafi Lagos a madadin shi, duk wayar akan abinda ya shafi harkar kasuwancin sune, ya jima suna tattaunawa kafun suyi sallama ya ajiye wayar, Saida yayi addu'o'in shi ya shafa sannan ya kwanta yana fuskantar bayanta, ya dad'e yana tunanin raihana a zuciyarshi kafun ya matsa jikinta yayi hugging d'inta tightly a k'irjin shi.
Wani irin rass! rass!! shaheeda taji a lokacin data jita gaba d'aya a jikin shi karo na farko a tarihin rayuwarta.
Shi kuwa a nutse ya dinga aika mata da sak'onnin shi, ba tayi yink'urin hana shiba saida taga ya fara hargitse mata kamar ba shine yake tafiyar da ita gently ba, take maganar da sukayi da k'awarta feena ranar da tazo ta dawo mata a rai, tsoro da firgici suka shige ta aikuwa ta mik'e da sauri taja duvet tana jifan shi da wani irin kallo duk jikinta ba inda baya rawa.
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page fifty 5️⃣0️⃣
Dafe kanshi yayi da duka hannuwan shi, ita kuwa ido rufe cikin maseefa take cewa, "futa! Ka futar mun daga d'aki Imran tun kafun nayi maka rashin mutumci a cikin daren nan, dama wannan ne dalilin da yasa kake shigo mun d'aki kullum dare? Toh wallahi tunda wuri ka kama kanka don ba zaka tab'a samun abinda kake so daga gare niba.....".
Yadda ta rufe Ido tana fad'in duk maganar da tazo bakinta sai kawai Imran ya saki baki yana kallonta. Duk da maganar da takeyi ta k'ona mishi rai amma ko a zuci baiji zai iya kulata ko ya bata amsa a lokacin ba.
Jiki a sanyaye ya sauka daga gadon yaja jikin shi ya futa zuciyarshi na k'una, wai shi wannan yarinyar take zagi da fad'awa duk abinda yazo bakinta kamar wani sa'anta.
Shaheeda kuwa saida ta murzawa d'akinta key ta tabbatar ta tsira sannan ta koma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. A daren ranar kasa hak'uri tayi saida ta turawa feena k'awarta text, "Wai me yasa kika sani nasha wannan maganin? Kuma sai yaushe zai daina aiki a jikina". Tana tura sak'on ta ajiye wayar ta kwanta don tasan ba samun refly zatayi a wannan lokaci da dare ya fara nisa ba.
Ranar haka shaheeda ta dinga bacci ko sallar asubah bata iya tashi ba har saida gari yayi haske. Cikin baccinta taji kamar ana buga wani abu tsakiyar kanta.
Aikuwa ta tashi a razane, saida ta nutsu sannan ta gane k'ofarta ake bugawa haka, ta tashi a hankali ta nufi k'ofar tana tunanin wanda yake mata wannan bugun tashi ka mutun da safiyar Allah.
Tana bud'ewa idanunta suka fara tozali dashi, yana tsaye da shirin futa kasuwa, saida gabanta ya fad'i da tsorata da ta ganshi donta d'auka sake dawowa yayi, hakan yasa ta fara k'ok'arin maida murfin zata rufe, Imran cikin sabon b'acin rai ya tura ta daga ita har k'ofar ya shiga cikin d'akin yana mata wani mugun kallon gargad'i.
A lokacin ba abinda take sai zare ido da muzurai, Saida Imran ya gama mata kallon k'ask'anci up and down sannan ya huce ta ya shiga ya d'auki wayarshi inda ya barta jiya.
Tana nan tsaye rakub'e da murfi tana sauke numfashi yazo zai huce, har ya futa ya tuna da wani abu sai ya dawo, ya auna ta daga sama har k'asa ya tab'e baki, "meye sunan kima?".
Cikin yaba rainin hankalin shi shaheeda baki na rawa tace, "shaheeda".
K'ara tab'e bakin yayi ya kalli gefe guda yace, "hajiya shaheeda ke yanzu a tunanin ki saboda me na aure ki?". Shiru tayi kanta a k'asa ta kasa amsa mishi, "tambayarki nake kinyi shiru kina jina". Girgiza mishi kai tayi a d'arare tace, "nima ban sani ba".
"Gud! Daga yau zan fad'a miki idan kina zaton na aure kine don wani abu ki daina, ni na aure kine saboda mahaifiyata ba wai don soyayyah ko wani abu daban ba, sannan kamar yadda ban musa mata maganar auren ki ba, bazan yi yink'urin cutar dake ko shiga hak'k'in kiba, wannan yana daga dalilin da yasa kike ganin sassauci a tare dani, sannan shine dalilin da yasa na nemi hak'k'ina dake kanki a daren jiya ba wai don kin isa mace, ko kina da wani abu da yaja hankalina ba, in aka d'auke kyaun fuska baki da wani abu da zakiyi tak'ama dashi, kada ki manta akwai millions of mata marassa aure a garin nan, kuma a cikin su zan iya samun wanda suka fiki komai a yau ba sai gobe ba,,,,, Soo ki kama kanki niba irin mazajen da za'a ciwa mutumci akan k'aramin abu bane Ina fatan kin fahimta?".
Da kyar ta iya gyad'a kai, yasa kai ya futa daga d'akin ita kuma ta durk'ushe a gurin tana kuka, wato tunda take a rayuwarta wani mutum bai tab'a ci mata mutumci irin yadda Imran ya mata ba a yau, wato itace yake nufin bata da suffa irinta mata saboda kawai bai samu abinda yake so daga gareta ba? Mik'ewa tayi taje gaban mirrow tana sake k'arewa kanta kallo wai ko zata ga gaskiyar abinda yake fad'a.
Ta jima a gaban mirrown tana kuka da tunane tunanen zuci kafun ta share hawayenta, ta wanzar da murmushi saman fuskarta. Ta lashi takobin saita nunawa Imran ita d'in ta huce yadda yake zaton ta, sai yazo har inda take ya rok'e ta akan ta soshi. (🤔 Shaheeda kina son lasar takobi da wuri)
Yauma kamar kullum tayi wanka tayi kwalliyarta cikin k'ananun kaya da suka zauna a jikinta, tana zaune tana tunanin abinda ya hana a kawo mata abincin kari har gashi lokaci yaja, ga ko masu aikin da ake turo mata ma yau basu zoba tun d'azu sai zuba ido take yi.
Ganin tana tunkarar yini guda ba ko d'aya daga abinda aka sabar mata da shi a gidan sai ta tashi da kanta ta nemawa kanta abinda zata ci, ko data gama cika cikinta aikin ma da kanta tayi.
Washe gari ma haka ce ta kasance, wata washe garin ma haka, tun shaheeda na kid'aya har kwana ki suka yita tafiya ba y'an aiki bare abincin da ake kawo mata. Gashi abinda tayi ranar da aka kawota yasa mammie ta hana su Nur da duk wani makusancin ta zuwa gidan, sai k'awayenta da suke d'an zo mata time to time suma sai in an tashi lectures da wuri ne.
Gaba d'aya shaheeda ta shiga damuwa a rayuwar gidan, tun ranar da suka samu sab'anin nan da Imran bai sake ko kallon inda take ba, d'akin nata ma ya daina zuwa. Ga a satin nan take son komawa makaranta don k'awayenta sun fad'a mata gab suke da fara exams, ta kira mammie a waya ta fad'a mata tace ita ba huruminta bane mijinta zata fad'awa tunda yasan da maganar karatun tun farko.
Shiru shaheeda tayi tana tunanin ta yadda zata iya tunkarar Imran da zancen komawa makaranta, ita da ko gaisuwa bata had'a su.
Sosai ta shiga damuwa cikin satin, sau uku tana zuwa hanyar d'akin shi tana komawa, ta rasa ta yadda zata iya je mishi da maganar.
A k'arshe dai saita hak'ura ta koma d'akinta ta d'auko wayarta ta kira feena k'awarta ta rok'e ta don Allah tazo gidanta akwai shawarar da zasuyi, hak'uri ta bata don ita inba ranar makaranta ba bata samun damar futa ko nan da harabar gidan su.
Haka shaheeda dai ta hak'ura har sai nan da kwana biyu inta futo makarantar.
Aikuwa kafun kwana biyu shaheeda duk ta k'osa, ranar da feena zata zo ko abincin safe bata iya dafawa ba bare taci.
Feena kamar yadda ta mata alk'awari ta futo da wuri a gida kafun lokacin shigarsu lectures. Direct gidan shaheedan tayi ta parking motar ta a k'ofar gidan ta shiga.
A lokacin shaheeda tana tsaye a balcony ta k'osa da zaman jiran zuwan feena ta fara kiranta a waya kenan sai kuma gata ta shigo.
"Kina da damuwa k'awata". Ta fad'a bayan ta zare farin glashin idonta, ajiyar zuciya shaheeda ta sauke tana kallonta kamar tayi kuka tace, "ai kece feena kin kasa fahimtar a halin da nake".
"Toh kin fad'a mun halin da kiken ne? Naga cewa kikayi kawai kina nema na". Feena ta kai k'arshen zancen tana zama kan d'aya daga kujerun parlon.
Itama shaheedan kusa da ita ta zauna ta rik'o hannunta da damuwa tace, "kwana na uku a gidan nan bana iya bacci sai b'arawo, feena na rasa ta yadda zan tunkari Imran da maganar komawata makaranta".
Dariya feena ta kyalkyale mata