Showing 183001 words to 186000 words out of 288773 words
Chapter 62 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt
mata a gefen kunci, "love you wife".
"Nima haka". Ta k'arasa fad'a tana sake shigar da kanta jikin shi.
Raihana da take zaune tana opposite d'insu tuni ta mik'e ta shige kitchen don kawo musu ruwa tea, tunda dai ta fahimci khaleefa bay kawo musu ko ruwa ba.
Shima khaleefa mik'ewa yayi don ya basu guri da kyau, kasancewarshi mutum ba mai son yawan takura ga kowa ba.
Tray biyu ta had'a, na farko ruwa, na buyu shayi.
Ruwan ta fara kawowa bayan ta rabka uwar sallama tun kafun ta k'araso gurin, duk don susan da zuwanta su gyara daga yadda suke manne da juna, madadin haka sai sake shigewa jikin shi da yasmine take kamar wadda za'a sace.
Ita dai ta ajiye musu ruwan ta sake kawo musu na tea.
"Thanks raihana".
Yasmine ta fad'a tana tsiyaya ruwa a cup, don ita dai batasan ana shan tea kowanne lokaci bayan lokacin breakfast ba.
Ganin Ahmad ya tsiyaya a k'aramin cup ya kai bakin shi sai itama taji tana son shan tea d'in.
Ta tsiyaya kamar yadda taga yayi ta kai bakinta. Sai gashi ta shanye shi tass hadda k'arawa.
A lokacin khaleefa ya dawo cikin parlon.... Shima kamar dai raihanan, yadda ya barsu haka ya dawo ya same su, sai yaja k'aramin tsaki a ranshi ya k'arasa ciki ya zauna. A lokacin yasmine ke aikin zuba santin raihana ta iya dafa tea, Ahmad nata mata dariya, raihana kam murmushi tayi ba tace komai ba.
Shi kuwa khaleefa d'auke kanshi yayi don baiga wani abun burgewa a iya dafa shayin nata ba.
Hira suka ci gaba dayi jifa jifa har zuwa lokacin da aka kira sallar magrib suka tafi don sauke farali.
Suma sallar suka tashi zasuyi. Raihana har d'akin barcinta ta yiwa yasmine jagora, Saida ta lumshe idonta ta bud'e tana shak'ar daddad'an k'amshin turaren daya manne da d'akin tana bin komai da kallo, yadda d'akin barcin ya tsaru sai abun ya burgeta har ta magantu a zuciyarta, "gata dai a haka kamar bagidajiya amma komai tana yinshi da nutsuwa da aji kuma a waye".
Yasmine bata sake raina kanta ba saida suka idar da sallah ta tafi kitchen don had'a musu abinda zasu ci ta bita.
Tana aikin suna hirar su ita da yasmine jefi jefi har ta kammala ta shirya musu shi a dinning.
Y'ar hirar da sukayi ta fahimtar da ita wacece raihanan cikin sauk'i, anan ta gane ba wayewa ce bata dashi ba, kawai tana da nutsuwa da sauk'in rawar kai irin na y'an matan wannan zamanin, gata da aji sai dai ta cika miskilanci kamar mijin nata.
Koda suka zo cin abinci raihana d'aukar nata tayi tunda khaleefa bacin abincinta yake ba ta bar musu dinning d'in.
Aikuwa suka dinga ci suna santi daga miji har matar aka rasa gwani. Ita dai komai sukayi sai dai tayi murmushi.
Khaleefa da yake zaune cikin parlon kuwa ya cika b'am, haushin su Ahmad da wannan magananniyar matar tashi me rawar kai da k'afar nan mak'il a zuciyarshi, sun zauna ko kunya basa ji tana yaba kwarewar wata sai kace ita ba mace ba, ita kuma sai wani murmushi take. "mattss!". Yaja tsaki a fili a ranshi yana fad'in, ko meye ma abun burgewa don wasu can sun yaba girkinta ba mijinta da suke tare ba, mtssss!". Ya k'arashe da Jan wani tsakin.
Duk da ba kusa dashi take ba amma taji tsakin shi sarai, bata damu ba tunda ba wani abu tayi mishi ba.
Ranar basu bar gidan ba sai dare, raihana ta rakasu tana musu godiya da alk'awarin zuwa musu bada jimawa ba itama.
Tana aikin gyaran parlon inda bak'inta suka ci abinci khaleefa ya futo rik'e da Mukullin gidan zai futa.
"Allah ya kiyaye hanya". Ta fad'a bayan ta d'auke kanta ga barin kallon shi.
Ko amsa ta baiyi ba tsabar takaicinta daya cika mishi zuciya, ba don kada ya kwana da yunwa ya samu matsala ba da ba abinda zai futar dashi galantoyin neman abinci da wannan daren, ada kafun Ahmad yayi aure tare suke yawon, yanzu kuma da yayi aure shi kad'ai ya bari yana gararamba, zuwa yanzu yasan d'ai d'ai daga masu gidan abinci da basu sanshi ba a garin Berlin, kuma duk ta silar wannan banzan lallen da yak'i futa a k'afarta kamar tisashi ake kullum.
(Yoh toh ai tisashin ake kamar karatu😂😂)
____________*****
Washe garin ranar ya sameta da safe a kitchen tana aikin had'a breakfast, bai shiga ba ya tsaya daga bakin k'ofar yana kallonta da shigar tata ta yau, karo na farko daya tab'a ganinta ba zumbud'ed'en gyale da hijjab, koda yake wannan d'in ma,,,,, amma dai laba'asa tunda straight skirt ne da riga me dogon hannu, sai gyale siriri data yafa shi ya rabu gida biyu yabi ta kowacce kusurwar hannunta, saboda santsin gyalen daya zame sai ya futar da gaban gashinta ma'abocin kyau da santsi yana haske idon duk mai kallon shi. Kamar kullum fuskarta babu komai zai lip balm da kwalli data zirara.
Aikinta take tana voice call dasu al'ameen, rabi duk hirar suce ta shirme da rigingimun su da baya k'arewa a kullum safiya, ita dai tana sauraron su tana dariya wani abun kuma in taji ta tsawatar. A dai dai lokacin da hibba ke kawo k'arar al'ameen ya sake kwace mata socks har yana dariya wai tunda auntie raihana tayi musu nisa bata nan zaiga me bata wani, "ai zaki kawo mun wata ko auntie raihana tunda ban kula shiba kuma ummie tace ba kiyi nesa damu ba tunda muna iya waya dake ko?".
Murmushi tayi a wannan karon bayan ta murd'e gas data gama girki tace, "rabu dashi hibbah zansa a kawo miki socks masu kyau da idan ya gani saiya kusa kuka". Cikin farin ciki yarinyar ta daka tsalle, "yeee! Ai dai auntie nace ke ni kad'ai ko?".
"Eh mana ke dai kawai duk abinda aka saki ki dinga yi, shima Yaya al'ameen ko me zaiyi kar ki kula sa, Ni kuma insha Allah na dawo tsarabar ki sai tafi ta kowa yawa".
Cikin farin ciki hibba ta sake daka tsallen murna har ummie data futo zata shige d'akinta na warning kada a fasa mata waya. Ita dai raihana tayi dariya don tayi kewarsu ba kad'an ba.
Shi kanshi khaleefa da yake bayan su abun ya k'ayatar dashi, kuma har lokacin duk abun nan da yake faruwa bata ganshi ba, tsayuwar mutum daf da ita yasa ta saurin d'agowa ta zuba mishi idanunta lokaci d'aya kuma taja jikinta baya, wayar hannunta ya zare ya tsura ma screen d'in ido yana ci gaba da sauraron hibba da take ta bata labarin abubuwan da sukayi da bata nan kashi daban daban.
Murmushi yayi ya kira sunanta idanun shi akan raihana "hibbatullah!" Daga can shiru yarinyar tayi don bata gane shiba.
"kun manta dani sai auntien ku kad'ai kuke kira".
Al'ameen ne ya fara gano shi ya rad'awa hibba, sai suka hau rige rigen gaishe shi. Ya amsa yana tambayar lafiyar kowa.
Sunci gaba da magana dashi idon shi akan screen d'in wayar yana kwashe no's d'in a kwakwalwar shi.
Yadda yaran suka sake dashi suna magana abun har mamaki yaba raihana, sai kace sun shekara da sanin shi.
Saida ya ajiye wayar yake fad'a mata abinda ya shigo dashi, "ki shirya anjima kad'an Ahmad zai zo ku futa".
Kacal abinda ya fad'a ya juya salin alin ya fuce hankalin shi kwance, da kallo ta bishi a ranta tana mamakin wane irin mutum ne wannan, Ina kuma zata shirya taje da abokinn shi?
Bata dame bata amsa shiyasa itama saita d'auki wayarta da abincinta ta futo a kitchen d'in.
Cikin satin Ahmad ya yiwa raihana duk abinda ya dace na shirin shiga makaranta, tunda shine a k'asa bai koma aiki daga hutun biki ba. Alhamdulillah ta samu addmision inda zata karanci BSc nursing kamar yadda khaleefa ya gani a rubuce jikin kwalin diploma da tayi a kano.
Kusan tare da yasmine akayi komai don itace y'ar rakiya. Haka raihana ta dinga shiga tsakanin ma'auratan a komai yasmine ta dinga nanewa mijinta kamar wata chewing gum, tun raihana tana kunyarsu har ta daina don ta fahimci ita yasmine ma ko a jikinta bata d'aukar hakan a matsayin komai.
Koda Ahmad ya kammala komai khaleefa ya samu da dare ya warware mishi duk yadda akayi.
Ranar da zata fara shiga makaranta k'arfe tara zasu shiga lectures amma ko kafun lokacin tuni ta shirya tsab cikin doguwar riga me mayafi irinta matan Sudan. Jakarta da wayarta rik'e a hannunta tana zaune a parlon, saboda zumud'i ba abinda ta iya ci sai tea da tasha funjali biyu.
A shiryen shi ya futo tsab cikin kayan da suka dace da jikin shi, waya ce sak'ale a kunnen shi hannun shi rik'e da LC jakarshi rataye a gefen kafad'ar shi.
Yana rufe k'ofa idon shi ya fad'a kanta, kallonta yayi na adadin wasu sakanni yana ci gaba da amsa wayar har ya gama.
Saida ta russuna ta gaishe shi, ya amsa mata kamar kullum. Sake kallonta yayi yana nazarin wani abu cikin ranshi, lallai yarinyar nan tayi kama da wadda ta karanci halayyar d'an Adam, duk wani abu daya yink'ura zai sata tayi sai yaga tayi. Yanzun ma ya d'an jinkirta futa ne saboda ita, yasan ba lallai ta iya kai kanta makarantar ta dawo da kanta ba, tunda bata san sunan anguwar da take zaune ba bare inda zata samu motar haya ta shiga.
Ajiyar zuciya ya sauke yace, "zamu iya tafiya yanzu?".
Gyad'a mishi kai tayi ta tattaro duk abun buk'atar ta ta nufi hanyar futa a gidan.
Shiya tsaya ya rufe gidan ya k'araso inda take suka fara tafiya a gefen titin anguwar. Shiya tare musu motar haya suka shiga har zuwa makarantar, ya sallame su suka futo yaci gaba da mata jagora har ciki.
A wani keb'antaccen guri da babu yawaitar mutane ya barta, ta zauna tana jin dad'in yau matsayin ranarta ta farko a makaranta. Wasu nau'in kud'i ya d'ebo a aljihu ya ajiye mata saman cinyarta da mukullin gidanta, "Nottingham Ln, ocean pines, MD 21811, ki rik'e wannan address d'in in an tashi shi zai maida ki gida,,,,, ranar ki ta farko a makaranta, fatan alkhairy".
Yana gama fad'a ko sauraron komai bai tsaya yiba yayi gaba abunshi, da kallo ta bishi har yayi nisan daya b'acewa idanunta.
Saita rubuta address d'in a wayarta tare da sauke ajiyar zuciya.
Sun shiga lecture da misalin k'arfe tara dot, ko kad'an bata sha wahalar gano yadda komai yake a cikin makarantar ba saboda kwata kwata bata da duhun kai.
A ranar komai bai mata wahala ba don anyi musu karatun ne da harshen turanci sab'anin tunanin ta. (Abinda raihana bata sani ba, dama makarantar kusan international student sunfi yawa a ciki)
Da address d'in da khaleefa ya bata tayi amfani ta koma gidanta.
Koda ta koma a k'alilan na lokaci tayi duk abinda ya dace, ciki hadda wanka da girki ta turare gidanta tsab kafun wani lokaci k'amshi ya gauraye ko'ina.
Ranar khaleefa bai dawo da wuri ba, ita Kuma bata bar parlon ba ta zauna dakon shigowar shi tana d'an duba littattafanta.
Tana nan har ya dawo ya murza key ya shigo, kallo d'aya da raihana ta mishi ta fahimci a matuk'ar gajiye yake.
Shi kuwa saida ya shak'i daddad'an k'amshin turaren ta ya lumshe idon shi wata nutsuwa na saukar mishi, gajiyar daya kwaso na sake sauka a duk gabban jikin shi tana nuk'urk'usar su, k'arasawa yayi cikin parlon ya zauna ba don komai ba sai don saboda wannan tsumammen k'amshi daya cika ko'ina banda d'akin shi.
"Sannu da zuwa". Ta fad'a da tattausar murya. Bai iya amsa taba sai kanshi daya kwantar baya yana lumshe ido.
Ruwa ta kawo mishi mai sanyi da mara sanyi a tray ta ajiye k'asan k'afar shi.
"Mai sanyi?". Ta tambaya da kulawa.
Zama yayi sosai k'amshin turaren jikinta na kaiwa k'ofofin hancin shi marfaki, girgiza mata kai yayi.
Ta tsiyaya ruwan da sauri don rage kusancin da sukayi ta bashi.
Ya karb'a ya kai bakin shi nan da nan ya shanye ya sake mik'o mata kofun, har ta koma mazauninta ta sake dawowa ta tsiyaya mishi wani, ya k'ara shanyewa, ta k'ara mishi ya sake shanyewa, zata dad'a mishi na hud'u ya d'aga mata hannu ya d'auki duka gorar ya bulbule a bakin shi.
Kallon shi kawai raihana take a zuciyarta tana tunanin shi kuwa wacce irin k'ishin ruwa ya kwaso haka!
Had'a ido da sukayi dashi yasa tayi saurin maida kanta k'asa, shima d'auke kanshi yayi kamar yadda tayi.
Ita kuwa had'e komai tayi guri guda ta durk'usa kan k'afafunta ta fara mishi godiya, "Na gode Allah ya saka da mafificin alkhairy, ya baka abinda kake so duniya da laheera".
Kamar wanda aka watsawa ruwan sanyi haka yaji tasirin addu'ar ta a cikin jikin shi, addu'ar data mishi Allah ya mallaka mishi abinda yake so nan duniya dai dai yake da tace Allah ya bashi Saleema tunda itace abinda yake so fiye da komai a duniya in aka d'auke mutum biyu, abinda yake so a laheera kuwa abu ne da kowanne musulmi yake fata da burin samu wato jannatul firdaus, sai dai shi da k'arin haka, don yana son Saleema ta kasance matarshi har a can ma.
Tattausan murmushi yayi bayan had'a addu'arta da tunanin shi waje guda yace, "na gode da addu'a, amma na cika alk'awari nane kamar yadda kema kika cika naki tun a Nigeria".
Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta har zuwa wani lokaci data gama jin zama inuwa guda dashi ta had'a kayanta zata tafi, daga bayan shi ta sake russunawa, "bazan fasa godiya ba don ka zamo silar dana jini gab da cikar muradaina a yau,,,, BSc nursing shine burina na tun k'uruciya,,,, nagode Allah ya faranta maka kaima kamar yadda ka faranta mun".
Tana gama addu'ar ta juya zata tafi saboda hawaye daya cika idonta, har ta fara tafiya maganarshi ta sata tsayawa cak ba tare data juyo ba.
"A watannin baya, nayi neesa da wani abu mai matuk'ar muhimmanci gare ni har na fara fidda ran samun shi gaba d'aya, sai dai a yanzu ta sanadiyyarki na jini kusa dashi saboda kusanci har muna iya jiyo numfashin juna..... *Saleema* itace farin cikin rayuwata, kiyi mun addu'a Allah ya bani ita".
Maganar a bazata ta zowa raihana, shi yasa ta kasa duk wani motsi tana son tabbarwa kanta wai khaleefa ne yake maganar wata mace da gaske gareta.
_nayi typing mai yawa zan muku update Monday a rashin sani naje na share shi gaba d'aya saida na sake rubuta wani yanzun🤦♀️🤦♀️ saboda rashin lokaci nayi muku shi in briefly_
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page fifty two5️⃣2️⃣
Murmushi ta sake yi ta juyo rungume da tulin littattafanta tace, "toh Allah ya baka Saleema".
Kamar ya tashi ya d'ora ta a kanshi ya kewaya Germany da ita haka yaji a lokacin, baya jin a duniya akwai abinda za'ayi mishi a lokacin da zaifi wannan addu'ar ta raihana mishi dad'i. Har ta shige d'akinta bai iya d'auke idon shi a kanta ba, nutsuwarta, kamewarta, ladabinta da tarbiyyarta duk basu tab'a sa ta burgeshi kamar wannan addu'ar ta yau ba. A yau ya fara zana sunanta cikin b'angaren manyan masoyan shi daya yiwa aji na musamman a wani yanki dake cikin zuciyar shi.
★★★★
Rayuwarsu tana tafiya a sannu a sannu bada gaggawa ba, raihana sosai ta maida hankalinta akan karatun ta da yafi d'aukar hankalinta a yanzun, shi kuma khaleefa kan aikin shi da binciken shi ta k'ark'ashin k'asa, duk da suna rayuwa a gida d'aya basu fiya had'uwa ba sai irin weekend da baya futa aiki in ya gaji da zama cikin d'akin shi ya futo parlon, bai fiya futa kowanne gidan cin abinci ba a irin wad'annan ranakun, mafi yawan lokuta raihana tana kaucewa yake shiga kitchen ya jagwolgwola abinda zaici da kanshi, da