Showing 279001 words to 282000 words out of 288773 words

Chapter 94 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

4798

alhamdulillah ta sameta lafiya lou ita da unborn babynta, sunyi hira ta hankali mai yawa da ita kafun ta tafi.
A ranar raihana ta kwana da kewar khaleefa da batasan zata yi ba da kuma tunanin hirar su da khausar. Ranar bacci sai b'arawo haka tayi ta juyi har k'arshen dare.

Washe gari dama tunda sassafe ta fara shiri don tasan khaleefa da wuri zai zo d'aukarta kamar yadda ya kawo ta.
Aikuwa tana zaune dasu ameena da suka samu labarin zuwanta suka zo sai ga aiken shi. Haka tana ji tana gani ta hak'ura da hira dasu saboda azalzalawar da ummie ta mata sukayi mata rakiya zata tafi, bayan sun d'aukar mata alk'awarin zuwa mata wuni guda.
Har motar da yazo ciki suka k'arasa suka gaisa suka k'arasa sallama ta shiga ciki su kuma suka juya.
"Ina kwana". Ta fad'a bayan ta d'auke kanta gefe. "Lafiya lou yasu ummie".
"Suna lafiyarsu". Ta bashi amsa.
Daga haka ba wanda ya sake ce da d'an uwan shi kanzil har suka k'arasa gida. Dama bata nufi part d'insu ba direct tayi saman b'angaren auntie. Tana shiga da suhaana ta fara had'uwa, ta kuwa daka tsalle ta rungumeta tana mata oyoyo. Itama sakin fuska tayi ta nuna farin cikin ganinta, bayan ta zauna suka gaisa dasu momma da auntie har suna tambayarta yadda ta baro mutanen gidan.
Ta jima a nan har saida kawaici da hak'urin khaleefa ya k'are ya shigo parlon yana tambayarta mukullin d'akin shi. Da mamaki ta tsaya tana kallon shi, ita da ta dawo gidan yau ina zatasan wani inda keyn d'akin shi yake? Toh da bata nan ina yake kwana?. Saita rasa abinda ma zata ce mishi a wannan gab'ar gashi gaban su momma yayi mata maganar, har momma na fad'in ko zata je ta duba mishi, auntie dama yi tayi kamar bata ji suba don tasan shegantaka ce ba wani mukulli, kuma dai ma yayi hak'uri don tafi hour uku gurin suhaana suna ta hira a wani sashe na parlon, tasan yayi kewar matarshi tunda tana ankare dashi kwanakin nan biyu gaba d'aya a dame yake, ita kuma bata son duk abinda za'a ga ta nuna son d'anta k'iri k'iri.
Dole ba don raihana ta so ba ta tashi ta musu sallama suka tafi. Tana shiga parlon khaleefa ya murza key, ta kalle shi ya d'aga mata kai, "keda futa kuma sai gobe tunda bakisan zuru ba".
B'ata fuska tayi ta zauna cikin d'aya daga kujerun parlon tana fad'in, "dama nasan ba wani mukulli don kawai ka raba nida cikin mutane ne".
"Kin fahimta dai dai kuwa". Ya fad'a shima yana zama opposite to her.
Sake k'ulewa tayi ta kwantar da kanta baya tayi banza dashi.
Shi kam murmushi yayi bayan sun d'auki lokaci shiru a haka kafun yace, "Wai ma kin daina kishin suhaanar ne da kika je gurinta kuna ta hira hadda jin haushi na rabo ki da ita.....".
Mik'ewa tayi zata bar gurin tace, "yaushe kuma ni nace maka ina kishi da ita?".
"Baki fad'a ba da bakin ki but your acting says". Shima ya fad'a yana mik'ewar.
D'akinta ta nufa direct shima ya mara mata baya. Tana ajiye gyalenta taji motsin shi a bayanta, tana juyowa ta ganshi dab da ita, zata ja baya yayi saurin rik'o ta, saita marairaice mishi tace, "what".
Hannunta ya d'ora a cikin shi, "cikina babu komai".
"Toh ni wanka nake son yi na kwanta kuma....".
Sai ya d'aga ta cid'ak, "anzo wajen yarinya nima dama wankan zanyi ai".
"Allah fa ba kayi datti ba, Ni nama fasa wankan....".
"Kin makara hajiya....". Daga nan bai bata damar furta ko kalma d'aya ba ya shige bathroom da ita, (na tafi zan dusa kai da Alk'alamina 😨 aka banko mun k'ofa a goshi🤣).

A wannan rana raihana ta sake tabbatar da gaskiyar abinda yake k'asan zuciyar khaleefa, soyayyah yake nuna mata madararta mara algus, da wannan damar yayi amfani ya warware mata komai dangane da Ayman da suhaana, a k'arshe ya samu nasarar daidaita su yanzu alhamdulillah har sun fahimci juna ma. Raihana taji dad'i ta nuna farin cikinta da taya Ayman murnar yadda ya samu mace mai nagarta kamar suhaana. Murmushi khaleefa yayi da yaga yadda take ta farin ciki a lokacin yace, "kishi da jin haushin khaleefa ya k'are ko?".
Sai ta rufe fuskarta tana b'oye fuskarta a hannun shi na dama.
Murmushi mai kyau yayi yana kallonta da jin sabuwar k'aunarta a zuciyarshi, sai yaja ajiyar zuciya ya d'ora hannun shi saman gashinta ma'abocin santsi da d'aukar ido ya kira sunanta carmly, bata amsa ba ta dai d'ago ta kalle shi, shima yana kallonta yace, "Ina sonki Raihanatu, Ina k'aunar ki sosai, Allah yasa kema kina Sona haka?".
Mik'ewa tayi zaune a lokacin tana kallon shi tace, "toh ni wacece ma da zan yarda nayi asarar classy guy kamar ka khaleefa?".
Cike da jin dad'i ya rik'o hannunta yayi kissing, "I much love you, keta musamman ce ko a cikin mata dubu samun irin ki sai an tona, shiyasa nake matuk'ar godiya ga Allah subhanahu wata'ala daya mallaka mun ke matsayin matata da zata zamo uwar y'ay'ana bada jimawa ba, Ina fatan kin karb'e ni matsayin abokin rayuwar ki har abada....".
Hannunta ta zame a hankali ta shige jikin shi ta d'ora hannunshi saitin zuciyarta, "zuciyata tana bugawa da gudu saboda soyayyarka, idan akace so ana nufin yarda, aminci, sadaukarwa da komai daya shiga cikin zamantakewar yau da gobe tsakanin ma'aurata, raihana is yours khaleefa sai yadda kaso zakayi da ita.....". Tana rufe bakinta ya sauke nashi ciki yana kissing d'inta tun daga zuciyarshi.
Haka suka wuni cikin farin ciki da faranta ran juna, da dare ma shiryawa sukayi suka bar gidan, sosai khaleefa ya nutsa da ita cikin gari suna shawagi kamar wasu tsuntsaye kafun at last yayi burki a wani hadadden gallery, bai bata damar d'aukar komai ba sai shi daya jida mata wasu shed'anun expensive classy English wears. Ita kunya ma taji da suka dawo gida ya titsiyeta tana gwada mishi kowanne d'aya a jikinta, tamkar dama don ita akayi kayan haka suka zauna mata cif a jikinta. Tun kafun aje da nisa ta fahimci kalar mijin da Allah ya bata, yana son soyayyah, tattali da kulawa cikin kaya masu d'aukar hankali, shiyasa ta fara yak'i da yakice duk wani nauyin shi don ta zamo irin yadda yake so sai su zauna lafiya.

****Washe gari suka tashi da shirin tafiya garin tofa su duka gidan, sunsha tafiya sun kuma k'aru da abubuwa masu yawa, sunga tushen familyn Abban su, an karb'e su hannu bibbiyu an kuma taya Suraj murnar samun surayya a karo na biyu (don su sun d'auka b'ata tayi a haka kuma aka barsu) kwanan su biyu suka dawo da tarin alkhairin wad'annan mutane masu karamci.

***** Tsakanin suraj da surayyah kuwa har yanzu basu samu zama yadda zasu fahimci juna ba, bata jin zafin shi ko k'ank'ani cikin ranta, tun lokacin data fahimci irin rayuwar da yayi bayan tafiyarta ta sake saduda da amincewa soyayyar shi gareta mara algus ce.
Shi kuwa ta b'angaren suraj ganinta matsayin matar shi kad'ai ya gama mishi komai, ko a yanzu Allah ya d'auki ranshi zai tafi cikin farin ciki salaamun, shiyasa shareshin da take baya wani damun shi, tunda ya fahimci da b'urb'ushin soyayyarshi a zuciyarta ya bata ratar lokaci taja zarenta yadda ranta yake so, yana nan yana wani b'oyayyen shiri cikin zuciyarshi na bayan fage da zarar komai ya kammala sun samu keb'ewa da juna zata tabbatar Soyayyah bata tsufa komai shekarunta.

Bayan kwana d'aya da dawowarsu kamar yadda khaleefa ya alk'awari ya kai raihana gidan kakanninta biyu da kanshi. Suka gaishe dasu da zasu tafi ya cika su fal da alkhairy kamar wancen lokacin.
Suna tafe a mota raihana tana tunanin sauyawar kakarta inno, gaba d'aya kamar sauyo ta akayi ba wannan hargagin da maseefar, itace hadda sakin mata fuska yau, koda yake watak'ila hakan yana da alak'a da rashin lafiyar da tayi.
Khaleefa da yake nazarinta tunda suka taho, kallonta yayi na wasu y'an sakanni sannan ya fara maganarshi da fad'in, "haka rayuwar duniya
take, in kayi hak'uri a sannu a sannu gaskiya take fallashe kanta ga kowa, ki daina mamakin sauyawarta, raihana duk wani mak'iyin ki zuwa yanzu kin mishi nisan da sai dai ya d'aga kai ya hango k'urar ki, ba kuma da kud'i ba amma da abinda kud'i baya bayarwa wato kwanciyar hankali da nutsuwa, alhamdulillah na cika alk'awarin dana d'aukar wa raina....". Ya k'are maganar da murmushi yana jifanta da kallon tsantsar so da k'auna. Murmushi tayi tasa hannu tana share hawayenta, "tabbas ban manta ba ka cika duk alk'awarin daka d'auka da wanda ma baka d'auka ba, a lokacin da nima zan d'aukar maka nawa alk'awarin, insha Allah ni raihanatu salees zan kasance mace ta kwarai ga mijina kuma bazan tab'a juya mishi baya ba komai tsananin da zai shiga a rayuwa, zamu gudu tare mu tsira tare mu shiga aljanna tare insha Allahu".
Khaleefa lumshe idanun shi yayi, ya gangara gefen titi yayi parking motarshi ya rik'e duka hannuwanta biyu "I love you, I love you soo much raihana, zamu kasance tare har k'arshen numfashin mu it's my word".
Janye hannuwanta tayi ta d'ora d'aya saman nashi tana kallon cikin kwayar idon shi. "you know what?". Ya tambayeta, ta girgiza mishi kai.
"Some promises are always unbroken, some memories are always unwritten". Sai ya d'ora hannunta saitin zuciyarshi, "feel the magic of the true relation, and you will realize that true feelings are always unspoken, you are the end of discussion raihana, without you my life will become useless......".
Lumshe idanunta tayi ta bud'e cikin tsananin farin ciki a lokacin da taji kalamanshi suna sauka har cikin k'arshen zuciyarta, a hankali ta matsa dab dashi ta sumbaci kuncin shi hagu da dama, zata kauce ya rik'o ta tsam ya nuna mata lips d'inshi, marairaice mishi tayi, "muna hanya fa....".
"Shhh! End what you start ko na gudu dake inda ba idon wanda kike kunya....". Da sauri tasa hannu ta rufe mishi idanu sannan ta mishi light kiss ta koma mazauninta da sauri ta maze kamar ba ita tayi abinda tayi ba, khaleefa yayi dariya ganin yadda tayi yace, "I like dis your innocent face...".
Murmushi tayi ta rufe fuskarta da tafin hannunta, "Ni dai muje please".
Yayi murmushi ya tashi motar suka bar gurin.......

_kuyi hak'uri ina sane daku ma fans, shiyasa nake ta bakin k'ok'arina wajen ganin na rufe muku labarin nan kafun Ramadan insha Allah, godiya da jinjinar ban girma gare ku masoyan asali😍_
*Ina mik'a sak'on taaziyyata ga maryam sulaiman (ummu elmustapha) bisa ga rashi da sukayi na d'an uwa cikin wannan satin, Ina fatan Allah ya jikan shi ya gafarta mishi, yasa ya huta*



_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page seventy nine7️⃣9️⃣


_Second to the last🤗_


Satin su d'aya da y'an kwana ki a garin Kano suka tattara suka huce garin Abuja, tare da iya da malam da Suraj ya takura su lallai sai sunzo sunga muhallin shi.

Babban shagali aka sakeyi na murnar gani da taryar surayyah, wanda ma basu tab'a saninta ba sai a hoto sun ganta ido da ido, sai kuma yaran gidan suka hau santin ganinta a zahiri, ashe duk yadda suke kallon kyanta da gayunta a hoto, zahiri tafi haka. Ita kam mamaki tayi da ganin yadda zuri'ar Abdallah tofa ta cika ta tumbatsa, Fatima dama kuka ta dinga yi tana neman yafiyarta bisa ga yadda suka yarda da k'ullin Aysha har suka bada goyon baya aka tozarta ta.
Surayyah bata rik'e kowa a ranta ba, ta yafe musu duka ta kuma nemi itama dasu yafe mata, a nan suka dinga yabon kyawawan halayenta da fad'in, su me tayi musu, ai su wallahi ba wani abu da zata nemi yafiyarsu a kai.
Washe garin ranar suka shirya tafiya gidan sauban, kusan su duka wanda suka zo garin Abuja daga Kano har iya da malam.
Kasancewar ranar weekend sai abun yazo a dai dai don tabbas sauban baya futa ko'ina weekend hutawa yake a gida, kowa yasan wannan tsarin shine da baya sauyawa.
Lokacin da suka isa gidan doctor surayyah tsura mishi idanu tayi tana kallo da tunanin anya wannan ne gidan data sani shekaru talatin baya? Gaba d'aya wannan baiyi kama da wancen gidan ba amma duk da haka sai batayi k'asa a gwiwa ba tabi bayan su har inda yake ganin bak'i cikin weekends, (da yake akwai wasu shugabannin kungiya ta taimakon marayu da yake meeting dasu kowanne k'arshen sati yaji abinda ake buk'ata, sannan yawanci wanda suka zo wannan satin basu suke zuwa wani satin ba)
A lokacin da suka tsinci kansu cikin parlon shiru sukayi barin ma surayyah da zuciyarta take matuk'ar bugawa da sauri.
Sun jira na tsawon wasu mintuna kafun ya samu futowa garin su.
Aikuwa sallamar farko yayi surrender ya tsaya cak yana bin fuskokin mutanen parlon da kallo, dama da farkon farawa da Suraj ya fara tozali kafun daga baya idanun shi su sauka a kanta. Surayyah kam data kasa nutsuwa tun zamanta a parlon da hanzari ta mik'e ta nufe shi a guje, shima k'arasowa yayi ya rungumeta yana kiran sunanta, "surayyah me yasa zaki tafi ki barni, Ina kika je tsawon shekaru? Me kikeyi a can inda kika je? Surayyah mune mukayi silar tafiyarki ko?......". Duka wad'annan tambayoyin yana jera mata sune a lokacin da take rungume a jikin shi, daga ita har shi kuka sukeyi, cike da tausayin su sauran mutanen parlon ke binsu da kallo. Sun jima suna kukan farin cikin had'uwa da juna kafun sauban yaja hannunta ya zaunar da ita gefe d'aya na parlon, yana son fad'awa Sarah abinda ke faruwa sai dai yana tsoron barinta kafun ya dawo ya zam ta sake b'ace mishi, sai yayi amfani da wayarshi ya kirawo saran yace tazo ta same shi a parlon bak'i, a lokacin tana tare dasu maheer a parlon k'asa, jin wayarshi sai mamaki ya lullub'e ta har ta fara tunanin lafiya kuwa, Abeed ne yace, "Mom wani abu yana faruwa ne?". Maganarshi ta janyo hankalin ragowar y'an uwanshi suma suka dawo da hankalin su kacokan gareta, "dad ne yace inje parlon bak'i yanzu, amma muryarshi tana nuna kamar akwai abinda ke faruwa ba dai dai".
Duk mik'ewa sukayi ba tare da sun jira taba sukayi parlon bak'i da yake kusa dasu, itama ta maara musu baya. Dukkan su daga bakin k'ofa suka tsaya suna kallon bak'in fuskokin.
"Sarah shigo kiga surayyah, surayyah ce ta dawo da y'ay'anta data haifa".
Kamar wadda bata tab'a gani ba haka take shigowa cikin parlon sosai tana kallon ta, sai da tazo tsakiyar d'akin surayyahn ta taho gurinta da gudu ta rungume ta, nan ma suka b'arke da kuka........

*BAYAN WASU AWOWI*
Surayyah ce da andal, malam, iya, Sarah, sauban da Suraj a zaune cikin parlon sauban d'in suna maida labarin komai da yadda ya faru, sauban ba k'aramin tausayinta yaji ba, a lokacin yake fad'a mata shi ba da gaske yayi wancen furucin ba, a lokacin idon shi ya rufe baya son ta auri bahaushe kwata kwata shi yasa ya mata wannan barazanar, tunda ta bijire mishi kuma jikin shi yayi sanyi ya hak'ura don baisan abinda Allah ya b'oye a auren su ba.
Nan fa kowa cikin su ya fara k'ok'arin neman yafiyar juna, aka sasanta a take komai ya huce.
Duk yadda suka so tafiya a ranar hana su sauban yayi, dole Suraj ya tafi ya barsu a nan zasu kwana mishi biyu zuwa uku sai su dawo.

Raihana taga karramawa da mutumtawa a gurin matar wan auntie, don tayi musu komai da kanta sai nan nan take dasu. Ita tana tare da matan, su khaleefa kuma suna tare da mazan suna k'ok'arin fahimtar juna da k'ulla k'ak'k'arfan zumunci.

Sunyi kwana ki uku a gidan wan mahaifiyar tasu kafun su koma gidan late Abdallah tofa, sun tarar anyi gyara mai kyau na b'angaren suraj inda surayyah ta tare, babu wani biki ko bidi'a ta shige d'akinta.
A daren ranar aka tattauna da likita andal game da soyayyar Ayman da suhaana, bata b'oye musu komai game da case d'in da akayi da yaron da aka fara musu engage d'an wan mahaifinta ba, da yadda suka dinga zugo shi kar ya barta ta k'arasa karatun in ba haka ba kuma ya fasa, a k'arshe dai sati biyu kafun tahowar su Nigeria komai ya lalace aka rushe maganar auren. Da wannan ta bada hujjar a neme su ita da Ayman yadda suka ce sai aje Sudan gurin dangin mahaifinta a nemo auren.
Anyi kamar yadda taso, aka kira Ayman da suhaana suka tabbatar suna son junan su. Sai duk akayi hamdala da tsaida lokacin tafiya neman auren, lokacin zai zo dai dai dana zuwan surayyah gida.

Lokacin da raihana ta samu labari ba k'aramin dad'i taji ba, ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login