Showing 1 words to 3000 words out of 53497 words
Chapter 1 - SO BAI SAN JINI BA COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
[3/25, 10:55 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘
*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*
*Cigaban*
*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*
AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*Ana tare fan's naji daɗin yanda kuke ƙaunar wannan book ɗin, yanzu ma dai ina son ku bani haɗin kai kamar yanda kuka bani a part One ta hanyar SHARHIN KU hakan shi zai bani ƙwarin gwiwwa wajen dagewa da typing*
*Dan Allah ku dinga bibiya kar sai nayi nisa wasu su dinga cewa na turo musu daga farko, hakan yana bani wahala gaskiya.*🙏🏻
*Muje karatu domin ana jone*🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P*••••••1️⃣↗️2️⃣
Gabaki ɗayan su komawa sukayi suka zauna, sai Sharifa wacce tabi bayan Indo ganin yanda ta fita a guje cikin kuka, gyaran murya Daddy Yayi kafin ya fara magana cikin nutsuwa Momy ya fara jefowa tambaya.
" A'isha me kike faɗa babu jininki babu waye? Maimaita min naji ko kunne nane yake min ƙarya"
MOMY tana huci kuma cikin fushi ba tare da ta dubi Daddy ba tace.
" Cewa nayi babu JININA babu Indo domin kuwa bazai ɗebo mana irin tsiya ba, sanin kanka ne wannan yarinyar iyayenta ma bata raga musu ba, akan me ɗana zai aureta nima azo a yaɓa min baƙin iri gaskiya bazai yiwu ba."
Murmushi sosai Daddy Yayi yana duban Momy kafin yace.
" Ni kuma nace akwai *JININ ALHAJI HARUNA DA JININ MALAM MUSA* domin kuwa kusan jini ɗaya nake ɗaukar su, A'isha ki sani cewa muddun cikin waɗannan ƴaƴan nawa, ɗaya cikin su ya daidaita da Indo, muddun kuma suna son juna, to ki sani cewa sai sunyi Aure, idan kuma basuyi ba, to ki ɗauka cewa Allah ne ya ƙaddara babu rabon Aure a tsakanin su, waima na tambayeki, shin wai Indo kam tana bin maza ne koko ta taɓa zaginki ko ɓarauniya ce? Bani amsa.?"
Shuru Momy tayi Zuciyarta na tuƙar baƙin ciki domin ita bata ƙaunar Indo cikin rayuwarta idan tace Indo tana da ɗaya daga cikin wadannan abubuwan da Daddy ya lissafa tayi ƙarya sai dai tasan yarinyar bata jin magana ga yawan faɗa duk da taga yanzu ta daina amma ita bata sonta har cikin ranta duban Daddy tayi tace
" Babu ko ɗaya amma ai kasan........"
Haɗa ransa Daddy Yayi tare da dakatar da Momy ta hanyar ɗaga mata hanu yace.
" Enough enough A'isha baki da wani abun faɗi, ki sani cewa Ƴata ta ciki na na ɗauki Indo sannan duk sanda na kalleta ina hango fuskar mahaifiyata a tattare da ita duk sanda na mata abu kuma ji nake kamar Inna na yiwa idan tana farin ciki tabbas nasan farin cikin Inna ne ki faɗa min taya zan kasa riƙe farin cikin mahaifiyata?" shuru Daddy Yayi kafin ya ɗago ya kalli Momy da Aunty Hindu cikin kausasshiyar Murya ya cigaba da magana " wannan dalilin yasa bazan iya bawa Hindu Indo ta koma da ita Egypt ba, ko yanzu nasan na cika umarnin Inna na bawa Hindu riƙon Indo na tsawon wannan lokaci, dan haka Hindu kiyi hkr bazan iya baki Indo ba, ki haɗa mata kayan ta gobe ta dawo gida, idan yarinya kike buƙata a gabanki ki ɗauki *Sharifa* na baki ita duniya da lahira, amma Indo ni zan riƙeta da kaina, ke kuma A'isha idan zaki cire mungun niyyar ki kan wannan YARINYAR ki cire bamu taɓa samun matsala dake ba tsawon zaman Auren mu, yau shekara 30 amma ki sani cewa muddun kika cigaba da wannan abun da kikeyi wa Indo kika cigaba da takura mata to tabbas zamu samu mummunar matsala kuma komai zai iya faruwa tsakanina dake."
A matukar razane Momy ta ɗago tana duban Daddy, domin kuwa bai taɓa mata wannan furucin ba, cikin Zuciyarta ta furta cewa ( lallai wannan YARINYAR tana shirin tarwatsa min gida tunda harta ɗauko ɗamarar haɗani faɗa da miji na to kuwa kafin ki tarwatsa ni saina fara tarwatsa ki tabbas kin kusa barin cikin garin nan gabaki ɗaya, zan ɓatar dake daga wannan garin ki tafi can inda babu mai jin labarin ki har abada baki san waye A'ISHAH ba, ko nace baku san waye niba, zaki san dani kike) juya kawai tayi ta haura sama ba tare da ta kalli kowa ba, runtse idonsa Mustafa Yayi cikin jin Zafin maganganun Momy ya tashi shima ya fice daga cikin gidan gabaki ɗaya, babu wanda yayi ƙoƙarin dakatar dashi, Habeeb kuwa kansa na sunkuye shi kaɗai yasan Abunda yake ji a cikin ransa ko magana ya kasa gashi nanne dai yana zaune kamar gunki, Aunty Hindu ko kaɗan bataji Zafin maganganun Daddy ba tafi jin na Momy, tasan tana son Indo har cikin ranta, sai dai soyayyar da take mata bazai sa tayi faɗa na faɗa da ɗan uwanta ba, tasan tabbas Indo zatasha wahala hanun Momy amma ba komai akwai Allah shi zai kareta duban Daddy tayi tace.
" Babu komai Yaya Sharifa ma da ka bani na gode sosai Allah yasa hakan shi yafi Alkairi, nasan kai mutum ne na gari tabbas zaka kula da rayuwar ta, na barka lafiya." Tana gama faɗin haka ta miƙe tsaye.
Murmushi kawai Daddy Yayi sannan yace
"na gode Hindu Allah ya miki Albarka ki gaida mai gidan naki."
" Zaiji kawai ta furta sannan ta fice da haushin Momy na munguwar ƙiyayyar da take gwadawa Indo.
Daddy duban Habeeb yayi wanda yayi shuru ya sunkuyar da kansa kasa duk maganganun da ake babu wanda yasa bakinsa ciki sai dai daga kallon yanayin sa zaka fahimci akwai Abunda ke damunsa, Daddy ne yace.
" Yaya dai Habeeb lafiya kuwa naga ka sauya lokaci ɗaya meke damunka.?
Habeeb bai ɗago kansa ba domin kuwa ya tabbata yana haɗa ido da Daddy zai fahimci Halin da yake ciki, kansa sunkuye yace.
" Babu komai Daddy kaina yake ɗan ciwo."
Murmushin manya Daddy Yayi domin kuwa ya fahimci halin da ƴaƴan nasa duka suke ciki.
" Allah ya sauwaƙa ka tashi kaje kasha magani ka huta koh."
Tashi Habeeb yayi tare da furta amin ya fice cikin sauri Hasina tashi tayi tabi bayan sa da sauri itama RAUDA kuwa tashi tayi ta haura wajen Momy suka bar Daddy shi kaɗai da su Sharif a wajen.
💢💢💢💢💢💢💢💢
" Ki tsaya Indo ina zakije? Magana fa nake kina jina bazaki tsaya ba? Sharifa ke wannan maganar.
INDO tana huci tace.
" Ki koma kawai Aunty Sharifa babu inda zan dawo."
" Kifa dawo Indo magana fa ake kika fito aiko ba komai zaki tsaya a ƙarasa wannan meeting ɗin dake."
Ko inda Sharifa take Indo bata kalla ba ta cigaba da tafiyar ta mai adaidaita ta tsayar yana tsayuwa kuwa ta shige tana ce masa Gidan gomnati zai kaita, ja yayi suka tafi, dakatawa da tahowa Sharifa tayi tana cizon yatsa kafin ta koma, kwantar da kanta Indo Tayi jikin sit din napep ɗin tana tuno Abunda ya faru yanzu ( wai yana sona ko Kunyar faɗa baiji ba, dake ance masa ni kuma shegiya ce saina soshi aiko sai dai sonka ya kasheni wawa mungun banza, kuma muddun baka fita harka ta ba, saina saka cikin bala'in da baka taɓa tunanin zaka shiga ba, bana sonka na tsaneka mungun azzalumi, me zakayi dani *ƘAZAMAR ƘAUYE KUMA ALJANA* ) ta furta cikin Zuciyarta tana cije yatsa a ƙofar gidan su zarah aka sauƙe ta, ta biya mai napep kuɗin sa, bata wani sha wahala wajen shiga gidan ba, kasancewar ta saba da securities d'in.
Suna zaune dukansu a babban falon har momma, gaishe da momma Indo tayi sannan ta shige bedroom ɗin Zarah tashi zarah tayi tabi bayan ta tana tubanin meya sami Indo ta shigo kamar a fusace, kusa da ita Zarah ta zauna tace.
" Malama lafiya na ganki a wani harzuƙe?.
Fashewa da kuka Indo tayi ta dafa kafaɗar Zarah tace.
" Sai yanzu sai yanzu Zarah sai yanzu." Ta ƙarasa maganar cikin kuka.
" Sai yanzu sai yanzu me? Please kimin magana yanda zan gane me akayi yanzun.?
Dubanta Indo tayi hawaye shar kuncinta tace.
" Sai yanzu da lokaci ya ƙure ya furta min kalmar so, na soshi abaya amma a yanzu na tsanesa sakamakon ƙyamar daya nuna min, bai taɓa sona ba sai ƙyama ta, sai yanzu dana dawo mutum cikakkiya shine yace yana sona, sai yanzu ya Mustafa zaka furta min kalmar so meyasa baka soni tun ina ƴar ƙauye ba meyasa? Ta ƙarasa maganar da ƙarfi.
Tsuka mai ƙarfi Zarah taja tare da cewa.
" Mtsssssss! Aikin banza, to sai meye danya furta miki kalmar so, har zaki ɗaga hankalin ki a banza nasan kina sonshi har yanzu, to bari kiji na sanar dake gaskiya, *Mustafa ƙarya yake ba sonki yake ba tsabar iya yaudara ne, so yake ya kaiki ya baro ki duk da bansan nufinsa a kanki ba, amma dai nasan tabbas mutumin da bai soka tun kana cikin ƙazantar kaba, sai da ka dawo mutum tukunna wannan mutumin ba MASOYIN GASKIYA BANE* A'isha ina mai baki shawara da karki kuskura soyayya ta kaiki ta baroki koda wasa karki yadda da Soyayyar sa domin mayaudari ne Mustafa ba mutumin kirki bane ƙawata kuma kema kinsan haka."
A wannan lokacin kukan Indo ya fara tsananta cikin kukan ne tace.
" Gaskiya ne Maganar ki ƙawata tabbas bazan taɓa yadda na faɗa tarkon sa ba, duk da nasan ina sonshi, amma bazan taɓa aurensa zan jira me sona da gaskiya yazo zan kuma rufe ido na na kawar da Soyayyar da nake masa, na Auri na ƙwarai ba irin Mustafa na banza ba."
Dafata Zarah tayi tace.
" Ƙawata ba sai kin jira na ƙwarai ba, domin kina tare dana ƙwarai kuma mai sonki da gaskiya, wanda ina da tabbacin cewa zaki samu farin ciki a gidan sa, wanda zaisa ki manta da wani Mustafa cikin wannan duniyar, ki basa dama na tabbata shi kuma zai baki farin ciki."
Kallon Zarah Indo take cikin alamar tambaya da kuma mamakin waye kuma mai sonta da gaskiya, duban ta Zarah tayi cikin murmurshi tace.
" Kin shiga cikin tunanin cewa waye mai sonki da gaskiya ko? To ba wani bane sai *YAYA HABEEB* yana sonki da gaskiya mutumin kirki ne, ya soki tun kina cikin ƙauye ya ƙaunace ki tun kina cikin ƙazantar ki bai taɓa nuna miki ƙyama ba, haka kuma yana daga cikin waɗanda suka kawo miki haske cikin rayuwarki, kuma na tabbata yana sonki, mai zai hana bazaki bawa wannan Adalin mutumin Soyayyar kiba, Indo ta wannan hanyar ne kawai zaki saka masa da alkairin daya miki cikin rayuwarsa, duk da bazaki iya biyansa ba, amma idan kin soshi zaiyi farin ciki kuma kema zakiyi farin ciki a gaba."
Zaro ido waje Indo tayi tace.
" What kin san me kike cewa kuwa Zarah yaya Habeeb fa kike cewa yana sona, kinyi kuskuren fahimta ƙawata babu Soyayya tsakanina da ya Habeeb illah ƙauna Irin ta ƴan uwan da suka fito ciki ɗaya, TAUSAYINA kawai yake ba soyayya ba."
" Hmmm A'isha kenan kece kike ɗaukar hakan a matsayin ƴan uwantaka shi ba haka ya ɗauka ba, shi matsayin masoyiya yake ɗaukar ki, kince tausayin ki yake, to ki sani duk inda tausayi da shaƙuwa yayi yawa to tabbas akwai Soyayya koki yadda ko karki yadda HABEEB yana sonki tamkar yanda yake son ransa, ki koma kiyi tunani kan magana ta, ki kuma fara lura da *TAKUN SAƘAR SA* na tabbata zaki gaskata magana ta."
" Ki daina faɗin wannan maganar Zarah kin manta waye ya Habeeb yake Aure, *AUNTY HASINA* ce fa wacce take ɗaukata tamkar ƴar uwarta, da ita kike nufin nayi kishi naso mijinta, ina hakan bazai taɓa kasancewa ba, ya Habeeb da Aunty Hasina kawai ya dace su biyun su za suyi rayuwar su bana mata fatan kishiya cikin rayuwarta, kinga Zarah kunne na bazai iya ɗaukar Maganar nan ba dan Allah mubarta haka."
" Okey shikenan tunda haka kika ce, na barta amma zakice na faɗa miki."
Jingina kanta tayi ba tare data ce komai ba tana tunanin Maganar Zarah.
Allah ne kawai ya kawo Habeeb cikin gidan lafiya tun kafin ya gama gyara parking ya fice daga cikin motar ko key ɗin bai cire ba, yana ƙarewa motar Mustafa kallo da alamu dai yana cikin gidan, Hasina da take bin Habeeb da kallo tun fitowar su ne tasa hanu ta zare key ɗin motar, sannan ta fito tabi bayan sa, kafin ta isa ma tuni ya shige bedroom ɗinsa ya danna key, jin ginuwa Hasina tayi jikin ƙofar tana riƙe ƙirjinta da taji ya fara mata nauyi, sosai take jin kishin Indo cikin ranta domin kuwa taga abun Habeeb ya fara yawa TABBAS yau zarginta ya kasance gaskiya, ƙarar zubar da abu cikin bedroom ɗin da tayi ne yasa nutsuwa tana sauraron maganganun Habeeb wanda baima san tana tsaye a wajen ba.
" Meyasa meyasa Mustafa meyasa? Zakayi gaggawan furta mata why! Ba LAIFIN ka bane laifin Zuciyata ne data kamu da Soyayyar ta, baki min adalci ba zuciyata, kinsa ina mata Soyayyar da bazan iya rayuwa ba muddun babu ita cikin rayuwata, ina sonta fiye da yanda nake son Raina na shiga Uku ni Habeeb ya zanyi da dakon Soyayyar ta, anya kuwa Soyayyar ta bazata kasheni ba."
Wani irin kuka Hasina tasa tare da silalewa ƙasa ta zauna tana toshe bakinta karya jiyo sautin kukanta.
Karku manta da COMMENT idan kun manta nima zan manta da typing duk da nasan bakwa wasa wajen COMMENT.😄
*Vote*
*share*
*and*
*Comment*
*Alƙalamin Rasheedat Usman*✍🏻
*(Ummu Nasmah ce)*
[3/27, 10:11 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘💘💘
*S͓̽O͓̽ B͓̽A͓̽I͓̽ S͓̽A͓̽N͓̽ J͓̽I͓̽N͓̽I͓̽ B͓̽A͓̽*
*Cigaban*
*(I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽)*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
💘 💘💘
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*INDO A BIRNI*
AND NOW 👉🏻 *SO BAI SAN JINI BA*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P*•••••••3️⃣ ↗️ 4️⃣
" Ina sonki! Indo ina sonki ya zanyi da dakon Soyayyar ki, meyasa kika kasa fahimtar ina sonki, meyasa!?"
Ya ƙarasa maganar da ƙarfi tare da sakin kuka ya dafe saitin zuciyarsa, yana cigaba da sambatu cikin kuka kamar ƙaramin Yaro, HASINA dake zaune ta rufe bakinta tana rusar kuka marar sauti ta tashi da gudu ta faɗa bedroom ɗin ta domin kunnen ta bazai iya cigaba da sauraron Habeeb ba idan kuma ta saurara to tabbas Zuciyarta zata iya tarwatsewa, saman bed ta faɗa ta saki marayan kuka tana cewa.
" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! Ya Allah ka sassauta min nauyin da nake ji cikin ƙirji na, tabbas ina kishinka miji na sai dai Soyayyar da nake maka bazai rufe min Idona ba har na kasa tayaka yaƙin neman Abunda kake muradi tabbas kafi sonta da buƙatar ta fiye dani cikin rayuwarka, duk da nasan kana sona amma Soyayyar da kake mata tafi wacce kake min yau na shaida hakan sai dai kash wacce kake yi domin ita bata san kanayi ba, ya Allah ka sassauta min wannan kishin cikin raina ya Allah ka bani ƙarfin gwiwwar da zan iya taya miji na yaƙin neman Auren ƴar uwata Indo, domin ganin cikar burinsa da farin cikin sa, tabbas Indo mutumiyar kirki ce, sai dai sam zuciyata bata son haɗa kishi da wacce take kallo a matsayin ƴar uwar ta ta jin, *TABBAS WANNAN ITACE ƘADDARA TA* mijina zaka Aure ta da yardar Allah tabbas zaka aureta na tabbata Mustafa bazaiyi Nasara akanka ba, domin kaine wanda ya dace ka Auri Indo ka mata Hallaci kuma na tabbata Indo bazata maka butulci ba, tabbas zata rama maka Alkairi da Alkairi za kuma kayi nasara da yardar Allah."
Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka mai ban tausayi, Hasina ta daɗe tana kuka kafin ta tashi ta shiga tollet tayi wanka ta fito bayan tayi sallar la'asar ne ta shiga kitchen ta ɗaura abincin dare sannan ta nufi bedroom ɗin Habeeb, shi kuwa