Showing 33001 words to 36000 words out of 85666 words
Chapter 12 - BAZAWARA CE ITA COMPLETE BY FADILA LAMIDO.txt
"lallaima kun cika 'yan rainin wayo,wato sunema zasu bani kud'in dacan su suke bani kud'in dazanyi amfani dasu."
Aysha tace "zomuje Zulaihat ninasan inda zamuyi musamesu."
tafad'a tareda ruko hannun ta suka nufi kofa,
Cikin d'aga murya JUHAIFAH tace "banzaye marasa zuciya wai ku zaku bisu nidai idan yarinya tasa dasunana wlh sai an jimu daku."
Zulaihat zatayi magana' Aysha tace "kyaleta kinsan amarennan sai ahan kali saidai murika yimusu uzuri saboda giyar amarci ked'iban su."
Koda sukafita part d'in Ammee sukaje,
Aysha tsayuwa tayi tana kallon kayan,
Zulaihat takalleta tana fad'in "dadai kin sa hannu cikin kayan sai idanunki sunfi koshi."
Aysha tayi dariya tace "ai ko a'iya hakan natsaya natabbatar da idon nawa yakoshi,keni nama rasa ta'in'da zan fara."
Zulaihat tazauna gaban d'aya dagacin set d'in akwa tunan,
Tace "zauna Aysha Daman ban leka cikin wannan set d'in ba."
Aysha tayi dariya tareda zaunawa suka shiga bud'e akwatunan suna ciccire kayan cikin,
Goggo Hadiza takallesu tanafad'an "bazaku tab'a barin nanba har sai kun maida kayannan cikin akwatin Dan nagaji da maida kayan saidai kowa yacire yakasa mayarwa abarni da maidawa,tonima nagaji yanzu."
Zulaihat tamike tsaye tace "Aysha mumaida Wanda mukaciro yasin Nima nagaji idan muka ciro duka saidaifa nagudu."
Goggo Hadiza tace "maza kumayar dashi yanzun Nan."
Suka shiga maida kayan sunayi suna dariyar Goggo Hadiza data tsaya kansu tana fad'in "ai baki isa kiguduba ina tsaye akanku harsai kun mayar."
Mommyn Jos da yanzu fitowarta daga bedroom inda sukayi masauki rikeda wata 'yar madai daiciyar roba Mai murfi da cup d'aure akansa,sai wani Cup d'in shima rike ad'aya ahannun ta,takaraso cikin parlour tace "Aysha Zulaihat zo kurikemun wannan muje d'akin' JUHAIFAH."
Sukace "tom.
Aysha takarb'i cup d'in Zulaihat Kuma takarb'i robar suka nufi part d'in Ya Al'ameen,
Mommyn Jos tatura kofarta tashiga da sallama su Zulaihat sukabi bayan ta,
Tanan kwance inda suka barta, suka karasa ciki tareda aje roba da cup in hannunsu, Mommyn Jos tazauna kusa da ita tace "tashi maza kizauna."
Mikewa tayi tazauna tanafad'an "Mommyn Jos ni saiyanzun ma naganki tu zuwanku ban gankiba."
Mommyn Jos tace "inakuwa Zaki ganni kullum kina cikin d'aki kaman Amaren da.tadubi Zulaihat tace "mikomin mikomin cup d'innan."
Zulaihat tad'auka Tamika mata,ta Amsa tareda mikawa JUHAIFAH tana fad'in "karb'a kisha."
JUHAIFAH takalleta sannan tamaida kallonta cikin cup d'in "Mommyn Jos menene wannan nake ganinsa wani kala haka'?."
"Tace au saina fad'a Miki ko menene akan baki sani bane to maganin matane tunda abunda kk so kiji kenan."
Dariya su Aysha sukayi,
Ido tawaro taredafad'in Toni mezan dashi?.
Mommyn Jos tace "jimin shashanci, mezakiyi dashi yanzu harsai ance Miki kiyi amfani dashi kafin kiyi?,kokin mance saurayi Zaki aurane idan baki gyara kankiba kina ganin tafiyar zatayi kyau kuwa,kadafa kiman ce kin tab'a aure, yakamata ace tun biki na sauran wata yakamata kifara shirya jikin ki, karb'a maza kisha,kada kiyi wasa hannun saurayi Zaki koma,dukda dai yasan kintab'a aure ammadai yajiki dad'an dama, Dan haka kiyi gyara dakyau."
karb'ar cup d'in tayi tana yamusa fuska aranta tace "wai saurayi Allah yasa sha'awace shi Wanda baimazo ba."
takai cup d'in bakinta tad'an d'ofana baki tareda kurb'ar maganin kad'an,
Mommyn Jos tace "bud'e baki zakiyi Kishanye duka."
Takafa Kai tashanye taciro cup d'in abakinta tana b'ata fuska,
Mommyn Jos takarb'i cup d'in ta'aje gefe sannan tacewa Aysha "tsiyayoyin ruwar cikin robar can".
Tace "to". Tabud'e robar dake d'aukeda had'en itatuwa namusamman tatsiyayi ruwan acikin cup d'in dake kan murfin robar,tamikawa mommyn Jos,
Mommyn Jos takarb'a tamikawa JUHAIFAH,tana fad'in "karb'a wannan ma Kisha".
Jitayi kamar tasa ihu takarb'i cup d'in tana b'ata rai haka tashanye ruwan,tadangwara cup d'in saman kati,
Mommyn Jos tace "to wannan ruwan robar shine zai zama ruwan shanki duk bayan minti 20 Zaki rikashanshi". tamike tsaye tadubisu Zulaihat tace "duk bayan minti 20 kutsiyaya mata ruwan tarikasha".
Sukace "tom".
Mommyn Jos tafita takoma part d'in Ammee,
Suko suka zauna kusa da ita,zuwacan Zulaihat takalli agogo tace "Aysha lokaci yyfa".
Aysha tace "to bari natsiyaya mata."
Tatsiyaye ruwan tamika kamata,harara tadalla musu tareda fad'in "wani shegen gulma".
Sudai dariya sukarika yimata,sunanan zaune duk bayan 20min zasu tsiyaye maganin sumika mata,Itako kafin takarb'a saita zagesu.
Dasauri yafito daga bedroom insa yanufi step yafara sauka daga steps,ganin mutane cike dam a parlourn kasa yasanyashi komawa da baya yanufi kofar baya yasauka kasa,
Dasauri sauri yake tafiyar Yana zuwa daf dawani lanbu da aka kawatashi da fararen kujeru kamar aturai, cak yaja yatsaya sakamakon Jin muryar Daddy dayaji yanafad'in "Kai MAHFUS inazakaje kk sauri haka."
Juyowa yy dasauri Dan baiyi zaton Jin muryar Daddyn anan ba,keyarsa yashiga susawa,yace "am dama..dama sonake naje naduba kayan da akayi odern sune karfe 12 zamu tashi." yafad'a tareda duba agogon daje d'aure ahannun sa,
Daddy yakura masa ido saf yafahimci nufinsa so yake yagudu shine Allah yasa yaganshi saikuma yab'ullo da wata zancen,Daddy yagirgiza kai sanna yace
"To ai tunkan kayan su'isa nasa akula dasu Kuma duk abunda idan kana gun za'ayi duk nasa anyi,sannan Kuma an baka hutun wata biyu bayan biki."
Ido yawaro tareda fad'in "what Daddy wata biyu?wata biyu fa kace Daddy Toni mezan zauna nayi har tsawon wata biyun."
Daddy yace "kazauna kakula da matarka bayan wata biyun saika koka dai-dai lokacin tasaba da gidanka."
Kasa magana yy sai kawai yajuya dasauri kamar zai tashi sama yakoma ciki,Daddy yabi bayansa dakallo tareda girgiza kai.
Shiko bedroom insa yakoma Yana shiga ya'isa yazauna bakin bed yad'an kishin gid'a,yarika nanata maganar Daddy acikin ransa afili kuwa tsaki yarikaja,
Wayarsa ce tafara ring yajuyo gefen dawayar take daga inda yake kishin gid'en Yana iya hango fuskar wayar,sunan Sadeeq ne keyawa akan screen in wayar har kiran takusa yankewa kamar bazai d'agaba sai Kuma yamika hannunsa yad'au wayar tareda picking na call d'in yakara wayar akunnen sa,
Daga cikin wayar Sadeeq yace " man kafito gamu a cikin gidan."
Yace "Kai ni bacci nakeji kakoma sai anjima."
Sadeeq yy saurin cewa "bafa nikad'ai nazoba muna tareda su Ammar Taddan nefa pls kafito Dan Allah."
Tsaki yaja tareda fad'in "banza nace ma bacci zanyi Kuma, kace musu kukoma anjima kudawo."
Sadeeq yace "haba MAHFUS mutanennan subar duk harkokin gabansu saboda Kai suzo Amma shine zaka Nima yimusu wula kanci."
Yaja guntun tsaki tareda fad'in "ni matsalata dakai shegen naci."
Sadeeq yace "Eh nayarda."
Yakashe wayar yamike yafito,acan kusa da get yahangosu yanufi inda suke,tunkan yakaraso suka fara yimasa kirari ya iso inda suke, Ammar Taddan yace "kaji ango maijiran gado Kai Allah yasa daren jibi a tsuga ruwan sama Dan saikafi Jin dad'in karya gadon."
Sadeeq yy dariyar shakiyyan cinnan nasa yamikawa Ammar hannu suka tafa yace "Kai gaskiya Taddan wanna kirarin naka har naji Nima kamar gobe a d'auramin aure,amma fa gaskiya sai mun zaunar da angon jibinnan Dan kada yaje garin zalama yab'alla kugunsa abanza yabarmu da sintiri agun jinya kokuma yab'alla na 'yar mutane,kasan sabbin shigannan fa sai ahankali."
Ammar yakece da dariya yace "gaskiya kam kasan farin shiga gashikuma andad'e kafin akagamu dole ayimata kurb'ar sauri."sauran abokan nasu suma sukasa dariya,
Cikin had'e rai yy magana
"Dama wulakanci kkzo kuyimin shiyasa kadage nafito ko?."
Yy maganar tareda nuna Sadeeq,
Sadeeq yace "sorry Man nisiha muka fara yimaka kafin mukaiga rakaka d'akin' amarya, munzone muje gidansu amaryar tamu so ga mota Nan shiga kawai muwuce."
Wani kallo yawurga wa Sadeeq saiyajuya saikoma dasauri Ammar yadakatar dashi tahanyar fad'in "yakuma muna magana' zaka tafi kasanfa tun shekaran jiya yakamata muje gidan nasu Dan musan medame za'tayi abikin so munji kayi shirune shiya mu mukazo da kanmu,nifa lokacin aurena tun nasaura sati mukatsara komai da lollipop ina,kaiko jibine fa d'aurin aurennan Amma baka motsaba."
Sadeeq ido yaketa masa tareda girgiza masa Kai Dan bayason sauran abokan nasu Susan komai gameda auren.
Yabud'i baki zaiyi magana' dasauri Sadeeq yakuma girgiza masa Kai,
Kawarda kansa gefe yy sannan yace "banason wata shirmen biki a aurennan Dan banason ayi wata bidi'a albarkanta kawai nake bukata."
Numfashi Sadeeq yasauke yaji dad'in kalmar datafito abakin sa yatabbata bazasu fahimci tsaman dakecikin wannan aureba, Ammar zaiyi magana' Sadeeq yy saurin cewa "to shikenan kace wani'abu, ammadai kasan dole za'aje akaimata kudinsu kitso da lalle dadai sauransu, Kuma idan tace zatayi biki daga gurintama dole za'abata kud'inda zatayi amfani dasu ko."
Baki yatab'e batareda yace komai ba,
Sadeeq yace "shiga mota muje gidan nasu."
kawar da kansa yakumayi tareda Jan guntun tsaki yace "kuje anjima ni zanzo yanzu muna maganane da Daddy idan muka gama zanso." Yana kaiwa Nan yajuya yanufi hanyar komawa ciki.
Sadeeq Daman yasan ba abubane maisauki MAHFUS yayarda suje gidansu JUHAIFAH,sai yadubi abokan nasu yace "to mujenku yazo yasamemu acan d'in."
suka shige cikin motar Ammar yaja motar sukabar cikin gidan,suna fita daga eriyan unguwar Kira yashigo wayar Sadeeq,Koda yaduba saiyaga MAHFUS ne maikiran,Koda yy picking na call in rage volume d'in wayar yy sosai Wanda iya shi kad'ai daya d'aura wayar akunnen sa zai iyajin maganar da'ake acikin wayar batareda Wanda ke kusa dashi yajiba,
Sadeeq yace "hello."
MAHFUS yace "kanajina ko?.
"Eh inajinka." cewar Sadeeq,
Yace "kada kakuskura kukaiwa yarinyar Nan kud'i kace daga gurina yafito, kukarata can kudakukayi lamuni,kadaiji nafad'a maka kenan."
D'if yakashe kayar,
Sadeeq yaciro wayar akunnensa Yana binsa da kallo kamarshine MAHFUS d'in saikuma yagirgiza Kai yamaida wayar aljuhun sa.
Koda suka iso bakin get in gidan hon sukayi maigadi yawan gale musu get,
Suka kusa hancin motarsu ciki, a farfajiyar gidan suka faka motar,
Ammar yace "todai gamu mun'iso yanzu yazamuyi amaryar tafito?."
Shiru Sadeeq yy Dan shima baisan ta'ina zai faraba gashi bashida numbern bare yakirata dukda bashida tabbacin idan yakirata zata fito.
Aysha da Zulaihat dake zaune kusada JUHAIFAH, haryanzu, Zulaihat takalli agogo sannan tadubi JUHAIFAH tana fad'in madam lokaci yayifa bari natsiyaya Miki Kisha."
Yamutsa fuska tayi tareda fad'in "bazan shaba ina yanzunnan nasha, yanekam kk Nima kitsauwalawa rayuwata ne kam?."
"Au tsauwalawa rayuwar kinema ko? tobari naje nafad'awa Mommyn abunda kk fad'a tazo dakanta Dan naga alama anji saidai kirufemu da duka."cewar Zulaihat,
harara ta dalla mata tana fad'in "basai kije kifad'a matanba, kawai asani nayita d'inrka wani itatuwa acikina kalan suje su sauyawa hanjina halitta."
Aysha tace "cap aidakuwa kowa yamutu wlh bb abunda yakeyi kedai Kisha kawai ke zai Miki amfani ai."
Tace "kutumar can to kar Allah yasa yy min amfanin 'yarrainin wayo kawai."
Aysha tace "um Zulaihat tashi muje mukira Mommyn Jos d'in tazo dakantan."
Suka mike tsaye,harara tabisu dashi,soko sukayi gaba abinsu.
Dasauri Sadeeq yasa hannun yabud'e marfin motar Yana fad'in "gawasu 'yan mata can suna zuwa da'alama tanan zasu biyu sai musasu suyi Mana magana' da'ita."
Ammar yace "Yauwa badarabon musha zama ba."
Shima yabod'e gefen dayake yafito,
Tagefensu sukazo zasu wuce Sadeeq yy saurin cewa "Sannun KU 'yan mata."
Juyowa sukayi inda suke tareda fad'in "Yauwa. sai suka juya zasu wuce Sadeeq dasauri yakuma cewa "am kunedai."
Zulaihat tace "suwafa?."
Sadeeq yace "Amaren namu Mana."
sai Zulaihat tayi dariya,
Aysha tace "to kune kuma d'in."
Sadeeq yy dariya tareda fad'in Eh mune angwayen."
Aysha tace "to da angon akazone?."
Shiru Sadeeq yy Dan tuno tigimar dasukayi kafin yabarsu sukazo sai yawayance dafad'in "No badashi mukazo ba shi yanacan tareda ba'i so mun raba kafane shi yarike can mukuma mukazo rike Nan."
Zulaihat tace "gaskiyane hakanma yy daman hidiman biki sai ahankali musamman bikin manya."
Sadeeq yace hakane kam ai abun sai ahankali."
Sauran abokan nasu nacikin motar suka fito,
Ammar yadubi su Zulaihat yace " yanzu menene yake akwai so muke musan me kuka shirya nashagulgulan bikin sai musan yadda za'ayi."
Shiru su a
Aysha sukayi yayin dasuka tuno gargad'in da JUHAIFAH tamusu akan idan sukace za'ayi wani shagalin biki a aurennan dakuma alwashin dataci har idan hakan yafaru.
sai Zulaihat tayi saurin cewa "hm ai amaryar taku ustaziya ce tace bazatayi wani bikiba walima kawai za'tayi bayan an d'aura aure da yamma."
Sadeeq yace "to ashedai tafiyar tasu tazo d'aya itada angon nata Dan shima yace bayason bidi'a,to Allah yanuna Mana ranar."
Suka Amsa da Amin,
Sadeeq yamasa jikin motar yamika hannunsa ciki yad'au ( )guda biyu yamika wasu Aysha Yana fad'in "ga wannan saikuyi duk abunda yadace idan bai isaba sai kunimemo."
Aysha takalli (. )d'in maid'auke da kud'i acikin sa Wanda akalla kud'in dakecikin kowani (. ) D'aya yakai 100K.
Sukayimusu godiya,sukuma su Sadeeq sukayimusu sallama suka shige motarsu suka bargidan..............
08034690723
Mommyn Twins ce
🅿️11
Bayan fitarsu Sadeeq su Zulaihat komawa sukayi d'akin' JUHAIFAH Koda suka shiga zama sukayi kusa da ita,
Zulaihat takalli JUHAIFAH sannan tace "dakike wani cewa wai muzamu bisu to gashi mu sunbiyomu hargida." Aysha ta'aje mata kud'in akafarta tana fad'in "gashi mun anso kud'in walima Dana kwalliya saiki tashi muje mufara shirya abunda yakamata."
Wani kallon shekeke tabisu dashi, tad'au kud'in tayi wurgi dashi cikin masifa tace "kudai dakuka roko saikuje kuyi amfani dashi."
Tana kaiwa Nan tamike tashige bathroom,
Tattara kud'in sukayi suka nufi part d'in Ammee,Koda suka shiga direct d'akin' Ammee sukawuce Nan suka tadda Ammee da Mommyn Jos suka mikawa Ammee kud'in,takarb'a tareda juya kud'in tanafad'an "wannan kud'in fa." Zulaihat tace "abokan angon ne suka kawo Mana sunce muyi duk abunda yakama,munkawai JUHAIFAH tace bataso."
Ammee tajin jina Kai,
Mommyn Jos tace "Him JUHAIFAH kenan."
Ammee tamikawa Mommyn Jos kud'in tanafad'an "gashi sai sufad'a Miki medame dama suka tsara zasuyin."
Aysha tace "ai walima kad'ai za'ayi Dan wlh tace bawani shagalin da za'ayi."
Mommyn Jos takirga 50K tamikawa su Aysha "kuyi amfani dashi wajen hidimar waliman."tasaka 100K ajakarta sauran 50K d'in Kuma tamikawa Ammee,
Mommyn Jos tace "nidai bari nafara nawa aikin.
Tamike tsaye tanacigaba dafad'in "kasuwa zani indai akwai abunda zaku tsiya dan ba'inda zaku Tara a walimar saikuzo muhad'a hanya."
Mommyn Jos sana'artace had'a yanmata da zawarawa idan zasuyi aure,tundaga nisan doniya ake zuwa mata Dan kyaran ciki da waje.
Koda suka tafi kasuwar
Sayayya sosai Mommyn Jos tayi harsaida dubu d'arinnan yakare takuma karawa da kud'in ta,
Koda suka dawo gida d'kin JUHAIFAH suka nufa direct.
Suna shiga tacewa su Zulaihat su'aje laidojin dasuka riko Mata sufita subasu guri,bayan fitarsu,tashiga harhad'a abunda za'tayi amafani dashi,sannan tadubi JUHAIFAH tace "tashi kitub'e kayanjikin ki yanzunan."
Tabud'i baki za'tayi magana' Mommyn Jos tace "bamagana nakeso ba tashi kawai karki b'atamin lokaci."
Yau d'aya JUHAIFAH tacanza kala Tasha gyara ciki da wajenta.
Acikin kwana biyun dasuka rage Mommyn Jos tagyara JUHAIFAH tatsumata da lafiyayyu ingan tattun magunguna.
*********************
Yau juma'a 25/10/2020
Damisalin karfe 2:00pm
Dubbannin jama'a suka shaida d'aurin auren MAHFUS TUKUR SHALI
DA AMAR YARSA HAFSAT YAHAYA
Asannu narika kusawa cikin taron jama'arnan inata baza ido ko zan hango ango,
Aiko can nahangoshi cikin abokan sa, fuskarnan tasa d'aure tamau,su
Sadeeq kuwa sai washe baki ake,
Fita yy acikin jama'ar ya'isa inda motarsa take shigewa ciki yy da saurin ya Ja motar yabar gun yanajin zuciyarsa nakuna, gudu yake shararawa yayinda zuciyarsa kecigaba da kuna,shikenan yanzu komai yakwab'e masa BAZAWARA Wanda 'yanfashi sukayimata fyad'e wai itace matarsa "ina!."
Yafurta da karfi tareda kunsa hannunsa yabugi jikin sitiyarin motar,
Tunkan yakaraso get yadannan horn,maigadi yabud'e masa get,yanashiga yafaka motar dasauri yabud'e marfin yafito yabi ta hanyar baya yanufi d'akinsa,yanashiga yawurga wayarsa asaman bed yawuce bathroom yasakarwa kansa ruwa batareda yatub'e kayan jikinsaba,
Yadamke idanunsa da karfi yanayinda yasaba shiga aduk sanda yatuno lokacinda ya'isketa agun 'yan fashinnan, yaziyar ceshi, tsananin kyamarta had'eda tsanarta suka dirar masa lokaci guda,
Asannun yashiga tub'e kayan jikinsa yananan tsaye ruwan nacigaba dasauka akansa,yanagama tub'e kayan ahankali yataka inda towel yake yazara yad'aura akugun sa,
Yafito a bathroom in,
Ya'isa gaban wardrobe yacire jallabiya yazura ajikin sa,yaje gaban mirror yafeshe jikinsa da turare yafita zuwa masallaci Dan gabatar da sallar la'asar.
Ana idarwa Yakomo d'akinsa yamaida kofar yarufe,yahaye gado yy kwanciyarsa.
Tunbayan da'aka d'aura auren Aysha da Zulaihat basu zaunaba,sunata kaikomo Dan ganin waliman dasuka shirya yatafi yadda yakamata, malamin dasuka gayyata DR IMAM IDRIS,yabasu tabbacin in Sha Allah zai ziyarci gun walimar damisalin karfe biyar darabi nayamma, Dan gudanar musu da walimar
Da karfe 5 aka gama tsara komai nawalimar antanadi runfuna da kujeru Dan zaman ba'i,agaban kujerun ba'in aka jera wasu kujeru guda uku Wanda aka kawatasu da kwalliya namusamman,
biyar da minti ashirin DR IMAM IDRIS ya'iso suka saukeshi amasaukin dasuka tanadar masa afilin taron.
sannan su Aysha suka nufi d'akin' JUHAIFAH.
Suka iske Mmommyn Jos nafesheta da turaruka bayan tagama yimata had'ad'd'iyar kwalliyar data tsara matashi afuskarta,
Turus sukayi suna binta da kallon mamaki,inbadun sun shigo suntadda Mommyn Jos d'akinba saisuce ba'ita bace watace daga cikin wad'anda sukazo bikin,
Takara kyau nakarshe sai d'aukar ido take
Zulaihat taciro wayarta ajaka tana "Kai wlh dole nabaki pic gaskiya kinganki kuwa yasin kamar wata India."
"Kai Mommyn Jos shine bakiyi Mana irin kwalliyar taba."
Aysha tafad'a tareda Kuma leko fuskarta,
Mommyn Jos tace "kukalli d'iyar tawa dakyau kukagini ita tahaska kwalliyar bawai kwalliyarce tahaskataba,so kwalliya natafiya da kalar mutum ne,Koda nayimuku irin natama ahaka zaku tsaya dan iya kyan naku kenan."
Kai suka jinjina Dan sunyardan maganar Mommyn Jos d'in gaskiyace JUHAIFAH mekyauce,
Zulaihat tace "Mommy saura 8min afara walimar fa Kuma har malam ya'iso."
Mommyn Jos tace "ai angama ma mujenku."
Tariko hannun JUHAIFAH wacce tunda akafa maganar batace komaiba,sai fuska data d'aure tamau tana jiran kiris tafashe.
Suka nufi farfajiyar gidan inda Nan za'a gudanar da walimar,
Suna isa dangin ango suka shigo da motocin su,sunsami labarin walimar ne tabakin Sadeeq,shine suma suka garzayo Dan ayi dasu,dukda ba'asan da zuwan nasuba Amma cikin kankanin lokaci aka karb'esu hannu bibbiyu.Mommyn Jos Goggo Hadiza da Umma Rabi sukarika yimusu maraba dazuwa tareda basu masauki.
5:30 dai-dai akafa gudanar da walima,
DR IMAM IDRIS yy wa'azi Mai shiga jiki tareda narka zuciyar duk Mai sauraro, yanutsar da amarya falalar zaman gidan miji dakuma hakkokin miji akan mata.
Harsaida JUHAIFAH taji zuciyarta yakaraya,tasinci kanta cikin wani irin yanayi,ba'ita kad'aiba gaduk Wanda yahalarci walimar saida zuciyarsa tasosu.
Karfe 6:30 malam yarufe taron da addu'a.
Ana shafa addu'ar Aysha da Zulaihat suka shiga part d'in Ammee dasauri suka d'ibi kayan walimar Aysha narikeda na malam tayi saurin nufar motarsa tabud'e tasaka,suka Rika yimasa godiya yace "bakoma."
Tareda yimusu fatan samin miji nagari suma.
Sannan suka koma gun mutane
Nan suka rika raba kyatuttuka wamutane,
Umma Rabi taje tahad'owa dangin ango kayan walimar dazasu tafi dashi namusamman.nan dangin MAHFUS d'in ke fad'awa Umma Rabi cewa daganan zasu wuce da amaryar su, Umma Rabi tace "to bamatsala,Nan akafara shirye shiryen tafiya da amarya.
Mommyn Jos tariko JUHAIFAH sukayi cikin part d'in Ammee parlour Abba tawuce da ita Abba da Baba Salihu ne zaune acikin parlour,
Suka isa cikin parlour tazauna kasan carpet gefeda Baba Salihu,Baba Salihu yakalleta cikin kula sannan yace "JUHAIFAH kinason mijin da aka aura Miki?idan bakiso kifad'a tundaga Nan basai tafiyar tayi nisaba."
Jitayi maganar Baba Salihun nayimata yawo acikin kwakwalwa,
Tasaci kallon Abba Wanda yatsareta da ido sai ta sunkuyar da kanta,tabbas idan baso take tazamo butulu Mai saka alkhair da sharriba, to taza dole tasharewa Abbanta hawayensa awannan karo,Wanda yad'auki son duniyarnan yad'aura mata baya kaunar abunda zai b'eta matarai,bazata tab'a mance ranarda su Ya Al'ameen suka dawo da ita gida,bata tab'a sammanin idan tadawo gida Abba bazai yimata hukunci ba,tagama sammanin