Showing 1 words to 3000 words out of 118783 words
Chapter 1 - MAZAUNA GIDA Hausa Novels By HAERMEEBRAEH.txt
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 *MAZAUNA GIDA* 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE :1
Garin Kano gari ne wanda Allah ya cika shi da albarka kala-kala wadda baza ta qirgu ba, kamar yanda ake ma kano kirari da Kano tumbin giwa koda me kaje an fika to tabbas fa haka maganar take, in da ustazanci kaje zaka samu wanda ya fika, in kuma da akasin haka ka je nan ma zaka tadda wanda ya fi ka a fagen.
Jameelah yarinya ce kyakkyawa ta bugawa a jarida, ta na da kyau mai ɗaukan hankalin mai kallo,fara ce tasss irin farin nan da kowacce mace zata yi fatan ace da ma haka jikin ta yake,ita ba 'yar kowa bace a garin Kano amma Fatar ta kamar gilashi dan ɗaukan idanun mai kallo,unguwar da Jamila take unguwa ce da ke tsakiyar garin Kano, unguwa ce da ta amsa sunan ta ta fannoni da dama musamman kasuwanci, kusan za a iya kiran unguwar da cibiyar kano, gidan su Jameela gidane na haya wanda yake ɗauke da d'akuna kimanin bakwai, band'aki ɗaya, sai tsakargidan da ba wani girma ta cika ba zaure biyu, zauren dake tsakiya anan matan gidan ke sana'o'in su,musamman masu abincin siyarwa da abun sha na siyarwa, tare da saide-saiden 'yan kayan abin amfani na yau da gobe.
Zaure na biyu masu ɗaukan talla da kuma 'yammatan dake kaiwa maza abinci dik nan suke zama tare da qalilan ɗin mazan da aka saba da su a unguwa,wasun su ma sukan shiga har zaure na biyu.
Iyayen Jameela ba masu qarfi bane, mahaifin ta dattijon kirki ne mai suna Malam Jameel, sai mahaifiyar ta mai suna Ramatu suna kiran ta da Ramai,Jameelah na da qani guda ɗaya mai suna Abubakar suna kiran shi da Bukar, Abubakar irin yaran nan ne marasa tarbiyya baya jin maganar kowa sai wanda zai bashi 'yan canji, su biyu ne yaran da Allah ya azurta Ramai da Malam Jameel.
Malam Jameel yana aikin gyaran babura ne a nan unguwar ta su Jameelah,nesa sosai da gidan shi, ba laifi yana iya qoqarin shi dan ganin ya aje ma iyalin shi dik abinda Allah ya hore masa na kuɗi ko abinci kafin ya fita, sannan yana kawo masu na rana da kuma dare ko da babu yawa, Ramai da mijin ta suna zaune lafiya cike da so da qauna tare da kulawa, abu ɗaya ke haɗa su faɗa a Koda yaushe, wannan abun kuwa shine tarbiyyar yaran su, wanda Malam Jameel ba k'aramin qoqari yake yi ba dan ganin yaran shi sun zama masu tarbiyya, amma ina ba shi da ikon tsawatar masu face Ramai ta shiga ta fita ta hana shi ko ta rusa abinda ya koyar da su, da sun yi laifi ya yi magana zata nuna masa yana ma yara faɗa a gaban maqiyan su za a yi masu dariya, in sun shiga ciki kuma yana yi masu nasiha nan ma tace ba a matsawa yaran yanzu sai su lalace.
A haka yake haɗawa har ita ya mata nasiha,ranar haka zata wuni ta na zumb'ura baki da murgud'e-murgud'en baki ita a dole an ci mutuncin ta, dayaa fita zata hau faɗa tana rushe dik abinda ya koyar da yaran shi.
Ramai na yin wake da shinkafa na siyarwa ne a gidan,suna yi ne da rana zuwa dare, dan haka Jameela bata zuwa makarantar boko sai ta islamiyyar safe wadda ake tashi sha biyu na rana, in ta dawo tayi wanka ta sha adon ta wuce zauren gidan su wajen talla,a nan zata zubar da dik wani karatu da aka koyar mata a islamiyya dik da cewa kuwa hadda ake yi a makarantar, ita kam kullum sai an dake ta dan kuwa bata iyawa, ko kuma ta gudu bayan aji har sai an gama dukan sannan ta shiga.
Kamar yanda kuka karanta tun a farkon labari Jameela yarinya ce data amsa sunan ta Jameelar wato (mai kyau) a shekarun ta sha biyar Jameela ta mallaki dik wani abu da 'yar shekara sha takwas ta ke ɗauke da shi har ma za a iya cewa ta fi wasu masu shekara sha takwas ɗin zama budurwa, Jameela na ji da wannan kyauwu nata ainun, kusan dan ita yawancin mazan dake zuwa gidan siyan abinci suke zuwa, mutanen gidan dake sai da abinci na matuqar jin kishin Jameela da mahaifiyar ta, dan a ganin su sun kwashe masu masu siyan abincin su baki ɗaya sai na su Jameelah ya qare sannan a sayi nasu.
Makarantar su Jameela ba qaramin karatu ake yi ba, wannan shine dalilin da yasa ake kawo yara daga mabambantan unguwanni dake garin Kano, makarantar ta yaye manyan mutane da suka zama wasu a Kano da ma Nigeria baki ɗaya.
Umaimah yarinya ce da suke sa'annin juna ita da Jameela ajin su ɗaya hatta da wajen zaman su ɗaya ne da Jameelah ,Umaimah sabanin Jameela ce a halaye da dabi'u da kuma matsayi, dan kuwa iyayen Umaimah suna da rufin asiri dai-dai misali,mahaifin Umaimah Malam Ibraheem Ayyub aikin gwamnati yake yi,inda mahaifiyar ta Hauwa'u ke aiki a asibiti a matsayin Nurse, tana da babban yaya mai suna Umar, sai da Umar ya shekara goma sha ɗaya a duniya Allah ya azurta Iyayen su da samun haihuwar Umaimah, dan haka akwai tazara sosai na shekaru a tsakanin su.
Gidan su gidane abin sha'awa da alfaharin kowanne musulmi, domin kuwa gida ne da ya jiqu da tarbiyya irin ta addinin islama, ga soyayyar junan su da kulawa da lamuran junan su, Yah Umar kamar yanda Umaimah ke kiran shi mahaddacin qur'ani ne shima makarantar da Umaimah take zuwa can ya gama a yanzu yana karatu a jami'ar bayero ta kano, yana karantar medicine bai da buri sama da ya ga ya zama likitan mata,a yanzu yana shekarar shi ta biyu ne a jami'ar, Umar na da matuqar qoqari kasancewar shi ya samu tubalin karatu mai kyau na haddar qur'ani da sauran littattafan musulinci kafin ya shiga makarantar boko, umar na matuqar son qanwar shi Umaimah baya son dik wani abu da zai taɓa ta in dai ba alkhairi bane,abun cutarwa kuwa Umar na kare qanwar shi daga riskar shi a zarar hankali da tunanin shi ya kai kan shi tun kafin ya kai gare ta.
****************************
Kamar koda yaushe , yau ma Jameela ce ta fito daga ita sai daurin qirji daga wanka ta tattare gashin ta cikin hular wankan ta, kasancewar tana da matuqar son rayuwar hutu da gayu shi yasa komai nata take yin shi kamar na wata 'yar hamshaqan mutane ,Jameelah na yawan tunani da jin cewar dama ba a wannan gidan aka haife ta ba kyawun jiki ta kamata ya yi ace ita 'yar masu kuɗi ce,haka ne zai bata damar cin karen ta babu babbaka,duk da ta san cewar akwai masu kuɗin da ke zaune a gidan haya Itama za ta so ace ko za suyi haya zataso ace a irin gidajen nan ne manya masu kyau ba irin wannan gidan yawan ba,rayuwa ta zo mata ba a yanda ta so ta kasance ba,gata duk gayu da kyan ta ta qare rayuwa a cikin gida kamar wannan quntatacce na talakawa, tsaki ta ja da qarfi kamar bakin ta zai tsinke sakamakon ganin baban qawar ta da ke cikin gidan na ta kallon ta kamar zai kife, har wani lashe baki yake yi kamar wani maye,cikin hasala Jameelah ta ce,
"Aikin banza aikin wofi ma malam,mutum gemai-gemai da shi ya tsaya yana qurawa 'ya'yan cikin shi ido, Allah ya wadaran naka ya lalace,"
Matar Malam Buba ce ta fito wadda ake kira da Larai,ganin abinda ke faru wa ne ya sa ta sanya baki cikin maganar dan ba yau mijin nata da sauran mazan gidan suka saba daukar ma matan su magana ba wajen kallon Jameelah, cikin qunar rai ta kalli mijin nata ta ce masa,
"Kai dai ka ji kunya da kai da mazan gidan nan marasa kamun kai, ke kuma ba babbar 'yar iska sama da ke ai, daba dan baban ku ya fita ba ai baki isa fito wa wanka daga ke sai wannan tawul ɗin ba iya guwowin ki, ga qwaurin ki nan dik a Waje, dibi d'aurin qirjin ma da an gani an san da gayya ki ka yi shi, in ba rashin tarbiyya ba wace yarinya baliga kamar ki ce a gidan haya zata yi hakan? Allah wadaran halin ki Jameelah"
Jameela kuwa murgudawa Larai da Buba baki ta yi, sannan ta shige d'aki, ba tare da ta amsa Larai ba,ta na shiga Ramai ta hau yi mata kirarin da ke sanya ta jin cewa ita ɗin wata ce.
"Farar mace alkyabbar mata (dik da dai wasu sunce baqar mace) Jameela jarin Ramai, Allah ya kare min ke daga idon maqiya mahassada'yan sa ido, Ameen ya Allah,"
Tsakargidan Ramai ta qarasa fitowa ta fara tattare kayayyakin wajen, tana yi ta na masifa tana habaice-habaice, ta yi da matan gidan ta had'a da mazan su.
Sai da Jameela ta d'auki wajen minti talatin da biyar tana kwalliya da shirin tafiya makaranta, kasancewar yau asabar za a bada hadda shi yasa bata damu da zuwa da wuri ba, dan in ba izu uku daga qasa ba ba zata iya bada izu ashirin da takwas da suke ba, ganin ba za ta iya hadda bane ya sanya ta dagewa ta iya baqi dan haɗa harufa da wasula ta karanta karatun ta.
Sai qamshi take zabgawa ta fito daga d'aki fuskar nan tasha kwalliya gwanin burgewa kamar ba makarantar islamiyya zata je ba.
"Larai Mamalo ta shirya ne? Ko nai tafiya ta?"
"Ban sani ba nima, nan kika gama zage mata uba da ni kai na, ke da uwar ki da baku son a fada maku gaskiya to ta yi gaba, ai itan ba shegiya bace da zata tsaya jiran ki,"
"Ta yi wa kan ta, ni na ke d'aga ajin ta ko a makaranta, dan ba ta jirani ba sai me?"
Tsaki ta yi ta sa kai ta wuce makaranta, tin daga vakin gate take jin karatun yara, gwanin dadi, jan hijabin ta tayi har zuwa fuskar ta, ta samu ta yi zaman ta a bayan ajin su akan dutsen da ta saba zama har zuwa sanda za ayi break sai ta shige da sauran dalibai.
Ta dad'e zaune tana jira a gama karb'ar hadda, dik ranta ya gama baci, ba ta san ta inda ya biyo ba sai jin bulalai tayi suna kewaye ta, ihu ta zunduma tana qoqarin yaye hijabin data rufe fuska da shi, malam isyaku ya riqe hijabin ta fuskar ya ci gaba da kewaye ta da bulalai.
"Wayyo na shiga uku dan Allah malam Isyaku kayi hakuri, kaina ne yake ciwo shine na fito waje na sha iska, wayyooo Baba Wayyoo Ramai ki taimake ni, zai kashe ni,"
Sake mata hijabin yayi, ya sa hannu a leben shi yana zaro mata ido,cikin takaicin halayen ta ya ke magana,
"Shiiii rufe min bakin ki, mara d'a'a kawai, yarinya kamar mai aljanu, dik makarantar nan kin fi kowa rashin ji, wai ciwon kai, a haka da wannan uwar kwalliyar kamar qanwar aljani kike kiran ciwon kai ko? Bari na maki dukan tsiya in yaso ciwon kan gaske ya kama ki da kyau,"
Wani zillo tayi ta kwace hijabin ta ta keta cikin makarantar da gudu tana zunduma ihu, malamai na jin haka sun san ita ce, ba mara kamun kan da ke wannan abun sai ita.
Umaimah na ta karatun ta ta ji an fado mata da qarfi an duqunqune ta, tabbas ta san in ta yi haka ta tsira dan malam Isyaku ba zai dake ta ba gudun kar ya samu Umaimah, best student din shi.
Nuna ta ya yi da bulalar fatar yana ta yi mata faɗa, sannan yace ta je gaban allo ta bada haddar ta ko ya sake yi mata wani sabon dukan.
Mamalo ke ta dariya qasa-qasa, wani irin ashar din tasha ta lailayo ta maka mata a gaban malamin nasu,wanda hakan ya jawo sai da yaran ajin suka tsorata da jin zagin, Malam Isyaku gani ya yi idan ya biye mata haka zata yi ta halin rashin tarbiyyar ta da d'a'a a makaranta baki ɗaya, sai ya koma mazaunin shi, tare da yi mata alqawarin mugun duka.
Lokacin yin break na yi bayan ta gama cin abincin Umaimah wanda kullum sai tayi santin shi da fatan Allah itama ya kaita matsayin da zata na cin irin wannan abincin mai daɗi kullum.
Suna kammala cin abincin ne Umaimah ta juya gefe dan wanke hannu, tana wankewa tana yi wa qawar ta ta nasiha akan abubuwan da take aikatawa marasa kyau,sai ta waiga dan ta miqawa Jameela ruwa itama ta wanke nata hannun ta,amma wayam ta ga ba kowa a wajen, daga kwanon abincin nasu sai ledar awara da Jameelan ta siyo dan su qara, ba su samu damar ci ba dan sun qoshi ainun, dubawa ta hau yi, ko ina dan neman qawar ta ta, cike da mamaki ta buɗe baki tana kallon ikon Allah.............
*Jameela 'yan matan zamani, ko me Umaimah ta hango kuma? Ku dakace ni a shafi na gaba inshaa Allahu*
[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 2:
Jameelah ce ke tafe tana ta surutu dan kuwa bata son abinda Umaimah take yi mata sam,cikin quluwa take fad'in ,
"Ita da an zauna da ita sai ta dinga yi wa mutum nasiha kamar ta maida mutum jahili, a qalla dai nafi wasu sanin Allah karatun nan in dai qur'ani aka ban ba inda ba zan kawo ba indai an yi mana wajen, hadda ce kawai matsalata,kuma itama haddar in an min uziri ai kai na ne baya ja, ita da take ja ba gashi har boko take zuwa ba, haba malam, ni bana san kinibibi a bi a ishe ka."
Ji ta yi an bangaji kafad'ar ta da qarfi,cikin sauri ta dafe wajen tare da ayyano wadda zata yi mata wannan ɗanyen aikin a saman titi,cikin masifa ta juya suka yi ido huɗu da Mamalo kuwa nan take ta ce,
"Mamalo kina da hankali kuwa? A fa kan hanya muke, shi yasa fa wataran bana son jerawa da ke sai a dinga ganin mutum mara aji, ki bari muje gida, ɗazu ina gani harda ke akai min dariya a aji da malam na duka na, kin san ai zan rama ne indai ni ce baki yi dariya a banza ba sai ta zame maki kuka watarana,"
Magana take yi cike da yanga, ba mai gane masifa take yi saboda yanda take kare ajin ta wajen samarin unguwar su,jikin Mamalo ne ya yi sanyi saboda tsoron abinda Jameelar zata aikata mata dan ɗaukan fansa,sarai ta san halin Jameela ba a yi mata bata rama ba, sannan bata ɗaukan rainin wayo.
Mazan qofar gidan su dake zaune zaman jiran dawowar ta daga makaranta na nan zaune ana ta hira,sun riga da sun san halin ta bata zama har a tashi da ta yi wani laifin ko ta ga za a bada hadda sai ta gudo gida abinta, wasan banza suka tsaya yi kamar ba ita ta gama d'agun kai ba a hanya ta na jan aji,cikin yanga ta ce,
"Dan Allah kayi hakuri Babawo, yau na maka alqawarin kai zan fara kawo wa abinci, na ji ma qamshin girkin kamar an gama, kasan girkin Ramai daban ne dana kowa a gidan nan,"
Wata sabuwar rarumar ya sake kaiwa hannun ta,ita ko tana ta dariya tare da sakar masa hannun yana ta latsawa.
"Allah in ki ka min irin na jiya na kama ki zaki san dani ki kayi ,"
Wani kallo suka yi wa junan su wanda ban gama gane wanne iri bane, dan a iya sani na mata da miji ko wasu masoyan da suka shaqu matuqa ne kawai ke yi ma junan su irin shi.
"To ka sakar min hannu na manaaa,"
"Na sake ki yanzu amma anjima bayan magariba zan zo idan na kama ki ba zan sake ki ba sai na maki hukuncin hana ni zubin farko da ki ka yi jiya sannan na kyale ki, yanzu ki je in an gama ki kawon naci na koma wajen aiki, baban ki daya duba yaga bai ganni ba kamar makaho haka zai hau kirana,"
"Kaga abinda ke haɗa ni da kai ko Babawo? ka mugun raina baba na,"
Murgud'a bakin ta ta d'anyi sannan ta fizge hannun ta ta shige gida.
Tin daga soron farko masu ɗaukan talla ne ana ta jera abinci a babban faranti da kwali, matan gidan suna zazzaune a qananan kujeru su na taya su lissafi da jerawa, wasu sun kunna kid'a a wayar su ana saurara ana ayyuka, wasu nata hira da shewa tare da 'yan gulmammaki irin na gidan haya,wata waqa dake tashe a wannan lokaci ta mutanen kudu Jameelah ta ji an kunna, nan take kuwa ta d'age hijabin ta ta baya ta yab'a shi a kafad'a ta hau rawar zamanin da ake yayi, yanayin yanda take rawar sai ya ba wa mai karatu mamaki da tsoron ko aljanu ke motsa mata sassan jikin ta, ihu wajen ya ɗauka da tafi,ita ko sai tiqar rawa take tana bin waqar cike da nishadi da jin daɗi.
Sai da waqar ta qare sannan ta faɗa gidan babu ko sallama, buta ta ɗauka ta yi band'aki babu ko addu'a a bakin ta, haka tayi abinda zata yi ta fito.Bayan ta ajiye butar ne ta kalli Lantai dake dafa nata abincin, tace,
"Lantai, Mamalo tayi wanka kuwa?"
Wani kallo ta bi ta dashi na qasqanci sannan ta ce,
"Ina na sani ina nan ina aiki na ni, ki duba mana da kan ki,"
Ganin irin kallo da amsar da ta samu ne daga Lantai yasa ta saki tsaki mai qarfi cike da rashin kunya ta doka qafa ta d'age labulen d'akin su babu ko sallama ta shige, tana masifar Lantai na yi mata abinda ta ga dama a gidan nan dan ma ta samu ta na neman 'yar ta? Ita fa ke d'aga ajin ta a dik fad'in layin nasu,to daga yau ta daina suje can su qarata da 'yar ta su zata ga kalar qawayen da za ta yi a unguwar, ta na gama masifa ta kalli kwanon da ke gaban ta ta sa qafa ta tura shi gefe sannan ta ce,
"Ramai wannan abinci na ne? In dai nawa ne na qoshi ni nan da ki ka ganni sai da nayi