Showing 93001 words to 96000 words out of 268365 words

Chapter 32 - Tana Tare da ni complete book document .txt

29 Aug 2024

54127

nasan mace kake b’oyewa cikin d’akin kawai zan maka shiru ne. “Taho muje Amal” hannunsa ta kama sun juya zasu tafi kenan Fannah ta saki ihu “Arghhhh!!!” daga cikin d’akin kunya ne ya kama Anas kaman ya nitse k’asa. Shettima da Amal ‘yan gulma tuni suka juyo.
“Ya Anas yanzu dagaske akoi mace cikin d’akin nan?” cewar Shettima ido waje.
“Ya Anas wannan ba muryar Ya Fannah bane?” Amal ta tambaya.


“Wani erin Fannah?” kuma ya fad’a baki na rawa. “Masu giaran ne maybe d’ayan ta fad’i a toilet d’inne.”
“Toh mu shiga mu duba ta mana” Amal ta fad’i.
“Angel ba kinajin fitsari ba kuje, I’ll handle this myself.” Wani ihun Fannah ta sake k’urmawa tana bubbuga k’ofar.
“Ya Anas Fannah ce open the door plasse.” Cewar Amal tana matsowa kusa da k’ofan.
“Ya Anas k’aryan ka fa ya k’are bud’e k’ofar kawai muga Fannan ko Amal?”
“Mr. Fauzi please open the door, wayyo Allah.” cewar Fannah cike da rashin hankali. Ran Anas in yayi dubu be b’aci ba lallai Fannah tanasan mutuwa yau. A fusace ya bud’e k’ofar kamar fara tafito tana kakkab’e skirt nata da hijabi. Ko lura dasu Amal ba tayi ba sanda ta tabbatar eh ba kenkeson data ga na binta a d’akin tattare da ita, tana d’ago kai suka had’a ido hud’u da Shettima daya sakar mata da murmushi sosai taga kamanninsa da Mr. Fauzi.

“Ya Fannah!” Amal ta fad’a tare da hugging nata. Hugging nata back Fannah tayi, “Amal dear ya kike?”
“Lafiya Ya Fannah mesa Ya Anas ya rufeki cikin d’aki ko kin masa wani abu ne?”
Anas dake watsa wa Fannah wani mugun kallo yace, “Angel banasan suratan banza Shettima ka kaita toilet d’in daga chan ku wuce gida.”
“Rowanta ake mana ne Ya Anas? Amal dama wannan ce Fannan?”
“Eh itace Ya Shettima ka ganta kyakkyawa ba.”
“Shettima kasan zan sab’a maka koh?” Cewar Anas yana galla wa Shettima harara.
Yi yayi kamar beji abinda Anas yace ba, “Ai sosai ma Amal, Fannah Hi” yace da ita.
“Uhm Sannu Shettima” tace dashi tana murmushin jin kunya. Kamar kyaftawan ido Anas yaja hannun Shettima da Amal yayi waje dasu tare da rufo k’ofar sa. Amal se knocking takeyi ignoring nata yayi, da ita da Shettiman suka gaji da kansu suka tafi. Bayan ya iso office d’in ya watsa wa Fannah wata erin mumunar kallo, cikin ta taji ya rud’e a lokaci guda.


“Kin d’au wasa nake ko? 500 d’innan zaki giara yau.”
“Mr. Fauzi wallahi ba haka bane kenkeso ne yabiyoni na rasa daga ina yafito.”
“K’arya kike, bawani kenkeso kede kawai kice kinasan su Shettima su ganki, sun gankin kuwa kinji dad’i ai yanzu.”
“Mr. Fauzi wallahi ba haka bane kayi hak’uri please.”
“Nak’i, barinyi ba.” Table nasa ya nufa yaciro 500 copies tare da ajiyewa kan table d’in “ungo ga pencils anan d’auka.” Bata ko motsa daga inda take ba. Kamar wacce zatayi kuka tace “Mr. Fauzi please, I’m sorry plea-” katse ta yayi “the next time nace kizo ki d’auka zanyi doubling.” A tsorace taje ta d’aga papers d’in da pencils guda biyu. “Good wuce ki zauna ina kallon ki har ki gama.”


Bayan ta zauna ta soma giarawa a yayinda ya zauna kan kujerar sa shima kaman TV yana kallonta harda crossing arms da legs, chan ya ciro popcorn yana d’an chi yana kallonta yana me jin dad’i. Guda ishirin tayi ta d’ago kai ta kallesa taga shima ita yake kallo ko d’an kunya yaji ya kawar da kansan nan beyi ba. Gira d’aya ma ya d’aga mata erin se meh dan kin kamani ina kallonki d’innan. A sanyaye ta mayar da kallonta kan papers d’in ta cigaba ita kanta tasan barata iya k’arisawa ba tunanin me zatayi take, “kuka? A’a koda nayi kuka ba sparing d’ina zeyi ba” chan idea ya fad’o mata. Pencil d’in ta jefar a k’asa tare da yin watsi da papers d’in ta sauk’a har k’asa tana rik’e da cikinta. “Wayyo Allah Mami! Wayyo ciki na!” A rikice Anas ya jefar da popcorn nasan ya taso daga kan kujeran sa ya d’aga ta tare da zaunar da ita kan kujerar.

“Sannu koh? Ina ke miki ciwo?” ya tambayeta cike da damuwa.
“Ciki na, wayyo zan mutu.”
“Sorry zauna anan bari inkira driver yazo ya kaiki asibiti.” Kai ta giad’a masa se wani “awshh” take tana matse cikinta duk kuma na k’arya. A rikice ya kira driver’nsa “Hello Moosa? Kabar duk abinda kakeyi kazo right away.” Ding! ya katse tare da dawowa wajen Fannah.
Fannah harda hawayen k’arya. “Ni kawai akaini gida wajen Mami, wayyo ciki na!”
“Okay bari yazo sannu.”
“Sir papers d’infa? I’ll go home in k’arisa su in na samu sauk’i.”
“Forget about them, bakida lafiya kibarsu kawai.” Fannah dad’i kenan, ji take kamar ta taka rengem. Ai bada dad’ewa ba Moosa ya iso da k’yar ta mik’e dan munafirci. “In kira azo a d’auke ki neh baraki iya tashi ba?”
Kai ta kad’a masa kawai “ya d’auko min jaka na a office kawai. Wayyo ciki na!”
“Okay toh, Moosa je office nata ka d’au mata jakarta.”
“Wayyo ciki na!” ta gwada yunk’urin tsugunawa taro ta yayi “sorry yanzu Moosan ze dawo kikace bara kije asibiti ba?” Kai ta giad’a a wahalince “ni kawai akaini wajen Mami Argh!!”


“Bari ya dawo sannu koh, Moosa hurry up mana!” ya kirasa a tsawace. Nan da nan ya dawo da jakar ta. “Oya walk her down kuma bawai nace ka tab’a ta bane do you get me?”
“Yes Boss.”
“Mis Aleeyu lets go.” A hankali ta soma bin bayansa tana taka k’afa kamar barata iya ba. “Get well” Anas yace mata bacan da k’arfi ba amman tajiyo sa, kai ta giad’a masa as an answer. Haka har k’ofar gidansu Moosa ya kawo ta, godiya ta masa yana jan mota ya fice ta b’alle da dariya. “Ai nan gaba abinda zan na maka kenan, dan mugunta yaushe zanyi zaman gyaran 500 papers. Oh ni! Fannah, dama bacci nakeji barin je in huta.” Tana shiga ciki taci karo da Mami dasu Afrah anci gayu sekace za’a gidan suna.


“Fannah ya haka? Yau da wuri” Mami ta tambayeta tana daidaita wa Aiman rolling nata na abaya.
“Banida lafiya ne shine Mr. Fauzi yasa a ka dawo dani.” Daga yadda take maganar ma Mami ta gano k’arya take.
“Wato seda kika rantse baraki wuni a office bako Fannah?”
“Mami kamar ya kuma na rantse?” Ta wani turo baki. “Banida lafiya ne fah ki kira ki tambayesa mana.”
“Toh Allah sawak’e in dagaske kike, mu zamu fita unguwa inkuma zaki bimu toh.” Har ga Allah Fannah nasan binsu amman saboda kar Mami tasake ganewa k’arya ta ma Mr. Fauzi ta hak’ura. “A’a ni zan huta adawo lafiya. Kekuma Afrah kallon ya isa ko?”
“Hmmm!” Taja numfashi cike da gatsine “Allah kawo sauk’i in ciwon gaske ne.”
“Sekiyi da ali garu kuma yanzu”,tana kaiwa nan ta fice d’akinsu bayan da su Mami suka tafi taje tasamu Baba suka sha hira sosai shima bada jimawa ba ya d’an fita cikin unguwa dan strolling yarage Fannah kad’ai. Tana rigingine jikin gadon d’akinsu tana buga game dan takasa bacci.


*****



Tun tafiyar Fannah Anas ya kasa samun sukuni, ya take yanzu? Ciwon cikin ya dena ne?
“ANAS IBRAHIM FAUZI!!!” Ya kira sunansa. “Get a brain and stop all these, mesa nake damuwa da Fannah? Badan ina santa bane saboda PA ta ce lafiyarta as well as lafiyar duk masu min aiki ya shafeni sesa nake damuwa amman badan wani manufa bane right?” Ya tambayi kansa tare da giad’a kai as an answer. Wayarsa ya d’au tare da kiran Moosa.
“Boss yanzu na ajiyeta.”
“Are you sure? Har gaban gidansu?”
“Yes Boss.”
“Good” yace masa sannan ya katse. Se ya d’au wayarsa ze kira Fannah se girman kai ya hanasa. Yayi hakan kusan sau talatin but still ya kasa kiranta da k’yar d’in k’yar ya iya ya kira ta. Tana cikin game call d’in yashigo batare da b’ata lokaci ba ta d’aga. “Hello Mr. Fauzi.” Tace a hankali kan me lafiya.
“Miss Aleeyu kinsha maganinki?”
“Yes nasha.” ta amsa a takaice.
“Good get well...” Se yayi shiru. “Soon” yace can k’asa k’asa.
“Thank you” tace dashi daga nan ya katse wayar.


Fannah de mamaki take har yanzu yadda Mr. Fauzi ya rikice gabad’aya daga ganin batada lafiya. Bata kawo komi a ran ta ba, a cewarta kawai yanada tausayi ne inyaga mutum baida lafiya.


Shima Mr. Fauzi bada dad’ewa ba ya wula gida. Ummie da Amal sun fita unguwa, Abuu kuwa ya tafi office, Shettima kad’ai ke gida ya baje kan dining chair tare da aza d’ayan k’afansa kan table d’in yana wani kakkad’awa sekace alhajin gidan. Anas na ganinsa ya sunkuyar dakai tare da k’ara saurin tafiyarsa dan sarai yasan yau Shettima seya tak’ura sa da zancen Fannah. Aiko Shettima na ganinsa ya mik’e daga inda yake zaune. “Fannah sannu awww ashe Ya Anas ne sorry kasan d’azu na kirata muka gaisa na amshi lamabrta gun Amal.”
Cak Anas dakeson ignoring nasa ya tsaya tare da kewayo wa yana kallon Shettima, ba komai inbanda zallan kishi tattare da shi. “Kayi meneh?” ya tambaye.sa
“Nace na kirata mun gaisa” ya kuma nanata kansa. “Tana da kirki ni wallahi ma santa nake, daga ganinta kawai naji ta kwanta min a rai.” Ya k’are maganar da hannunsa dafe kan zuciyarsa yana wani murmushin soyayya.


“Shettima kaji na rantse wallahi kafita daga harkan Fannah, kai yaushe ma ka fara karatun har kana tunanin soyayya, da bakinka zaka ajiye mace in ka auro?”
“Toh meh? Ba love bane? Ni inasan Fannah gaskia gashi kuma na karanchi bame girman kai da san abin duniya bace.”
“Shettima you do wanna die right? Wallahi ko ka fita harkan Fannah ko ni da kai mu sasanta.”
Dariya sosai Shettima ya kwashe da harda rik’e ciki. Cike da mamaki Anas ke kallonsa. Sanda yayi me isarsa sannan ya d’ago kai har da hawaye. “Ya Anas wallahi rantsuwa ba kaffara kana son Fannah, ji kishi karara, akanta yanzu har zakayi fad’a da ni wanka ma kenan. Heheh LOL Mr. Fauzi you are in love.”


Fuskarsa a sake yace, “sake fad’a inji.”
“Mr. Fauzi you are in love” Shettima ya nanata kansa. Ajiye jakar laptop nasa yayi tare da ciro takalminsa d’aya ya nufa wajen Shettiima haka suka riga guje guje manya dasu cikin parlour basu hak’ura ba seda suka fasa wani had’ad’d’en flower vessel.
“Dandan! Wallahi in Ummie tazo kaine bani ba” cewar Shettima da hannu a saman kai.
Tsuka Anas yaja “mschww dama ni na sayo kuma 50k ne ba se a sake siyo wani ba. D’au tsintsiya ka share ni na wuce d’aki na.”
“Toh Fannah I mean Anas, ni sunayen ku ma sirke min nake.” Anas bece dashi komi ba ya shige d’akinsa kawai dan inze biyewa Shettima har fad’a se sunyi. Uban neman tsokana ne da Shettima, be bar Amal bama waye ze bari toh?






*© miemiebee*


beeenovels.mywapblog.com
[12:51, 12/18/2016] ‪+234 903 612 6826‬: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫


❣🎀❣🎀❣


*_written by miemiebee👄_*

In dedication to *Aunty Sis💕*
3⃣2⃣








Bece da ita komai ba yabiya masu kud’in abincin, ahaka suka dawo cikin motar suka koma office, a lokacin azahar yayi. “Sir excuse me zanje inyi sallah.” Ba tare da ya kalle taba yace, “you have 5 minutes to do so, in kuma kika tsaya hira da Yusuf kikayi delaying d’ina you’ll answer to me.” Kai ta giad’a a hankali ta ajiye jakarta ta fice bayan ta idda sallah suka had’u da Yusuf hira yakeson janta dashi amman sauri take kar ta makara Mr. Fauzi ya samu abin magana kai. “Yusuf kayi hak’uri please, minti biyar Mr. Fauzi yabani ko second na k’ara ze ci mutunci na kabari in aka tashi zanzo musha labari har se sanda ka gaji.”
“Toh Allah taimaka aiki as PA wa Mr. Fauzi kam seda hak’uri.” yace da ita yana tausaya mata, a haka ta koma office nasa,yana zaune kan kujera yayi focussing kan laptop dayake aiki akai kafin ta zauna yace taje ta had’a masa coffee bayan ta had’a tazo ta ajiye masa. “Kinga flasks biyu da suke can?” Ya nuna da yatsa. “Eh nagani” ta amsa a hankali.
“Good ki cika min su da coffee.” Ido ta bud’e tana kallon ikon Allah yanzu dan tsiya har flask biyu? Ya kai ina?


“Bakiji bane?”
“Naji” ta amsa a takaice. “Good off you go.” Bayan ta isa wajen ta juyo tana kallonsa, shan coffeensa yake hankali kwance yana duban laptop tare da yin wasu ‘yan rubuce rubuce time to time “Sir ba d’an wani babban roba ko kwanon da zan had’a ciki se injuye cikin flasks d’in tunda dayawa zan had’a coffeen?” Ta tambayesa a nitse.
“Babu kuma koda akoi ma ba barin ki zanyi kiyi amfani dashi ba ga cups nan kina had’awa ciki kina juye har ki cika.” Wannan wace erin mugunta ne kwata kwata cup d’in fa k’ananu ne erin teacups d’innan yaushe har zata cika wannan manyan flasks.
“Sir hakan ze d’au lokaci ba gara naje kitchen na ari bowl ba.”
“Bara kiyi ba, kinga banasan musu na fad’a miki stop breaking my rules in zaki had’a good in barakiyi ba kuma in kira Mami in sanar da ita kina min rashin kunya.”
Chan k’asa k’asa tace, “ba se kanada lambarta ba.” Murmushi kad’an yayi, “haka kikace?” Wayarsa ya d’aga ya kai kan contact na Mami da yayi saving just d’azu data ajiye jakarta zuwa yin sallah. “Zo kiga” bayan ta k’ariso taga eh fah lambar Maminta ne to ya akayi ya samu? Ba tare da tace masa komi ba ta koma ta fara had’a coffeen cikin teacup d’in tana juyewa cikin babban flask d’in. Tayi hakan kusan sau goma amman data gwada jijjiga flask d’in taji har yanzu da saura cikansa ko rabi, gashi ko soma cika d’ayan ma batai ba haka kamar tayi kuka ta samu ta cike d’ayan da k’yar ta zauna dan ta huta.


“Kin gama ne?” Ya tambayeta
Kamar wacce bara tayi magana ba tace, “da saura d’ayan.”
“Well? Me kike jira toh?”
“Sir hannu na yagaji barin d’an huta please.”
“Hutu?” Ya tambayeta yana murmushi. “Kin tab’a ganin inda aka huta a office? Get up ki cigaba we have thousand of things to attend to.” Haka kamar ta kashe kanta ta tashi ta soma cika d’ayan har tsayawa take tana mik’a hannunta Anas kuwa ganin haka dad’i yake masa nan gaba zata sake barin masa aiki ba tare da ta sanar dashi ba seya biya duka coffeen dayayi missing time da ta tafi. Tana gamawa ta koma zata zauna, kafin ta zaunan ya kirata fuskarta ta yamutsa kan kashi sannan ta nufa table nasa.


“Ina details dana rubuta a hannun ki d’azu?” Jakarta ta koma ta ciro wayarta takai kan inda tayi saving sannan ta tura masa gabansa “gashi.” Kallon wayar nata ya tsaya yi sekace bashi ya d’auka ya copy number ciki d’azu ba. “Wannan shi kike kira da waya?” ya tambayeta. Sosai tambayarsa ya bata mamaki haka kuma ya bata haushi taga de wayarta bara a zagesa ba, tecno ce D7 ba abinda bayayi, duk abinda iphone 6s nasa da samsung galaxy 6 edge nasa dayake tak’ama dashi taga nata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login