Showing 156001 words to 159000 words out of 268365 words
Chapter 53 - Tana Tare da ni complete book document .txt
ba I will saboda nasan kin gama wankan tun d’azu. One... Two...” Duk tana tsaye tana jinsa “Three!” Karap ya bud’e k’ofar tsaye yaganta gaban mirror “awww kinaji na dama?”
A ranta tace kad’au yanzun ma ba kaya zaka ganni ko? Seka koma.
“Fannah I’m talking to you.” Ko d’ago kai ta kallesa batai ba dan batason sake had’a ido dashi gefensa tabi ta fice nan yayi treating ciwon nasa yafito shima.
Bayan fitowarsa ya tarar da ita zaune kan gado tayi jugum ga d’an hawayen dake forming cikin idanunta. A farko yayi niyyan ignoring nata sekuma ta basa tausayi, itan da ko cinyar ta batason agani bale ache duka aka ganta. Takowa yayi zuwa gabata batako noticing nasa ba saboda yadda tayi zurfi cikin tunani. “Fannah” ya kira sunanta a nitse, nanne hankalinta ya dawo jikinta kai ta d’ago, idanunsu na had’uwa tayi saurin kawar da kanta tare da sa hannu tana share hawayenta. Mik’ewa tayi dan ciro mai nata ta shafa tazo bin gefensa kenan ya rik’o hannunta tare da dawo da ita baya. Kukan da take k’ok’arin had’iyewa ta soma, kallonta ya tsaya yi be hanata yiba seda tayi me isarta sannan yasa hannu yana share mata hawayen. “I said I’m sorry I didn’t mean for it.” yace cikin wani irin salo. Kai kawai ta gyad’a masa tana k’ok’arin karb’an hannunta.
“Baki hak’ura ba?”
“Na hak’ura” tace ba tare da ta d’ago kai sun had’a ido ba. Hannu yasa k’ark’ashin hab’anta tare da d’ago ‘yar fuskarta yana kallo har a yanzu tak’i barin su had’a ido.
“Fannah you’re not, look at me” k’in kallonsa tayi. “Please...” anan ne ta d’ago idanunta ta azasu kan fuskarsa “I’ve looked at you, shikenan?” Tasa hannu ta sauk’e hannunsa daga fuskarta. Gefensa tabi ta d’au mai nata zata shiga toilet dan shafawa ya dakatar da ita ta hanyan kiran sunanta. Chak ta tsaya “I’ll excuse you kinji? You don’t have to go in there.” Be jira jin me zatace ba ya fice, ajiyar zuciya ta sauk’e. A nitse tasamu ta shafa manta tasa wani sabon atamfa d’inkin riga da skirt tagama shirinta tsaf sannan ta mik’e a kan gado. Har ayanzu Anas be dawo ba, da kwanciyarta bekai da minti biyu ba akayi knocking bisa k’ofar. Tashi tayi dan bud’ewa seta tuna da dokar da Anas ya kafa mata seda tasanya hijabi sannan taje ta bud’e.
Tsaye ta tarar da Anas, “can I come in?” Ya tambayeta. Kai ta gyad’a masa tare da matsa masa. Bayan ya shiga ta rufo k’ofar tare da ajiye hijabin a gefe, tayi miqarta kan gado. “kishirya Amal said she wants to see you.” Dama zaman nan d’in ya isheta ba musu ta mik’e ta soma shiri shima haka. Mayafi kalan atamfarta ta yafa duk Anas na kallonta seda ta gama shirin sannan yace, “ina zakije ahaka?”
“Kamar ya ina kuma? Kaifa kace Amal wants to see me.”
“I know I mean da wannan shirin.” Ya nuna ta da hannu.
Kallon kanta tayi up to down bataga wani abin aibantawa ba. “Anas wani abu ne?”
“Yes kisa hijabi baraki fita da wannan gyalen ba.”
“Anas gidanku fa kace zamuje ba wani wajen ba”
“Nasani nide ki cire kisa hijabi.”
“Haba mana Anas nan da gidan kun ma sena sa hijabi ai naga bawani gun zamuje ba gidanku fa zamuje, waze kalleni achan?”
“Shettima da me gadi zasu kalleki nikuma banaso.”
“Yanzu Anas kishin Shettima kakeyi?” Ignoring nata yayi ya nufa wajen akwatunanta, medium red d’in ya bud’e sannan ya d’ago kai yaga kalar atamfar tata yaciro color’n hijab daze shiga dashi. Daga nan ya nufa wajenta mutuwan tsaye tayi takasa koda motsawa se binsa da kallo kawai take. Gyalen nata ya cire ya ajiye a gefe “gashi sa wannan lets go.” Se ayanzu hankalinta ya dawo jikinta “but An-”
“Fannah banason surutu just wear it” ta gefen idanunta ta watsa masa harara sannan ta cire d’an kwalin nata ta b’urma hijabin.
“Perfect!” yace a lokacin dayake kallon ta. “Lets go” ba abinda Fannah ke banda bin Anas da harara ahaka har suka isa zuwa wajen motarsu ya bud’e mata tashiga sannan ya rufe.
★‡★‡★‡
Haka de rayuwa tacigaba da kasance ma Anas da Fannah. Anas yana tsantsan kishin Fannah, ko kad’an bayason wani d’a na miji yagane mata jiki musamman inya tuna ranan da ya ganta a bathroom. Shi karan kansa yasan yasoma sonta yanzu saide bayya tsammanin ze tab’a fad’a mata ‘cause har a yanzun bawai yayi accepting bane yasan sarai da ze samu wani yayi mai bayanin how he feels towards Fannah cemasa za’ayi yana sonta, abinda bayya son ji kenan. Sesa har ayau yak’i yarda wai sonta yake. Ko zaune yake a office muddin da pen a hannunsa bai sanin seda yake soma rubuta sunanta akan paper, a kullum burrinsa yadawo hotel nasu ya samu Fannah.
Ta b’angaren Fannah ma duk kanwan ja che, sede ita tayi accepting son da take masa amman kuma barata bari son yaje ko ina ba saboda rashin martabar ta, she don’t want to be broken.
Ba laifi Fannah da Anas suna shiri yanzu danko se su d’au kwana biyu basuyi fad’a ba amman gasa bak’ak’en kalamu kam na nan, da abun ya tab’o Mr. Fauzi kuwa se yayi dalilin dazesa zasuyi fad’a at the end kuma yazo yana bata hak’uri.
*****
Da bikin auren Anas da Fannah wata d’aya cus kenan, cikin wattani shida dasukayi agreeing akai. Anas ya biya Fannah first salary nata wanda yake N500,000 duka ta d’au ta dank’ala wa Mami akan sukai Baba National Hospital Abuja a dubasa dakyau amasa duk wani abinda ya kamata. Koda da Mami ta tambayeta a ina tasamu uban kud’i haka ce mata tayi Anas ne ya bata shiko koda da Mami takira sa dan masa godiya be nuna mata wani abu ba.
Alhamdulillah! Su Mami sunje sun dawo lafiya qalau da zaran Baba ya shanye magunansa ana fatan masa waraka.
****
Yanzu Fannah take gama had’a musu kayakinsu ansamu an gama masu sabon gidansu, she is super excited taga gidan musamman ma dataji Anas ne ya zana da hannunsa. Bayan ta gama had’a musu kayakinsu duka yasa aka sauk’o masu dashi aka kai mota wajen biyan bills ya nufa yayi settling. Fannah na zaune a mota tana jiransa. “Lets go?” Yace da ita alokacin daya kunna motar. Kai ta gyad’a masa cike da jin dad’i “yes.”
Unguwar Giwa Barack yajasu chan inda sabon gidansu yake, daidai gabar wani mansion Anas yasa kai, gate d‘in na identifying plate number’n motar nasa seya bud’u da kansa. Baki Fannah ta sake cike da mamaki, kasa b’oye mamakin nata m tayi ta tambayesa. “Anas dakansa yake bud’uwa?” Be amsata ba seda yayi parking a lot sannan yace, “yes ‘yar k’auye dakanshi yake bud’uwa dakuma kulluwa muddin anyi registering plate number’n.”
“Owwww!” tayi exclaiming tana gyad’a kai. “In d’an wannan kina sake baki nakega by the time muka shiga ciki zakimin littering marble floor na miyau.” Harara ta galla masa ta gefen ido. “Lets go in” yace da ita. Atare suka fito ta tsaya k’are wa gidan kalloi, flat mansion ne me penti fari daga sama se divider milk k’asan kuma brown, tunda Fannah take bata tab’a ganin gida katafare me kyau ba kamar wannan ba sede a TV show. Juyowa yayi ya kalleta seyayi murmushi ganin yadda ta kasa rufe baki, hannunta ya fisga “lets go” wajen garden yasoma kaita gabad’ai wajen green carpet ne seda coloured flowers wanda suka sake k’ayata wajen, a gefe guda kuwa bishiyoyi ne da dama kamarsu guava, mango, banana, dates (dabino) da sauransu. Gaba da wajen kad’an aka yi wani ‘yar runfa me kyan gaske, cikinsa tables ne guda biyu da kujeru hud’u-hud’u a kowanne. Daga gun garden ya wuce da ita swimming pool an k’ayata sa sosai, daga chan suka sake dawowa gaban gidan inda yake ajiye motocinsa da ko plate number ba’a sa musu ba alaman na kwalya ne bawai na hawa ba. Sabin motoci ne pil sauran ma ko b’are ledojin jikin ba’ayi ba, irgawa ta soma da Anas ya gano haka seyace “ba sekin b’ata lokacin ki ba guda 7 ne kacal lets go in.” Haka yajata zuwa main door d’in. K’ofar kad’ai ma abar kallo ce. Irin manyan security doors d’innan ne. Password d’in yasa anan k’ofar tayi kukan “welcome home Mr. Fauzi and unknown.” Nanma seda Anas ya rufa ma Fannah baki yau tana ganin ikon Allah k’ofa na magana. ‘Yan danne danne yayi jikin k’ofar se ya sake managa “Mrs. Fauzi added to family list, welcome home.” A hankali ya bud’u suka shiga ya sake rufe kansa.
Kaftareren parlour ne da had’ad’d’un frames, wallpaper da verses, cushions na cikin farare swal seda colourful throw pillows jere akai. Rug d’in dake parlour’n na nan colourful shima. Cinema (babban TV) ne manne jikin bangon kai tsayuwa dan bayanin had’ewan gidan youngest billonaire b’ata lokaci ne ayita imagining kawai nagaji(LOL) Haka yabi ko ina cikin gidan ya nunnuna mata Fannah de takasa magana har a yanzu inbanda wow datakeyi ba abinda ta iya tace, jacuzzi ko ina cikin bathrooms banda d’akin Anas dake nan harda Live CNN connected ciki.
Bayan da suka gama biye ko ina cikin gidan suka sake dawowa parlour, daba dan Anas ba da Fannah ta b’ace cikin gidan danko ta manta hanyan da suka bi. “So kinga d’akin ki ba? The purple one, nikuma nawa ne farin, we will no more be sharing a room.” Cewar Anas, da biyu yayi maganan danko yasan sarai Fannah da uwar tsoro barata iya kwana ita kad’ai a d’aki ba. Idanun ta ta d’aga ta aza akansa. “Eh nagani this is a wonderful house, kudos to you. Amman Anas nikad’ai zanna kwana cikin makeken d’akin chan??” Ta tambaya tana zaro idanunta.
“Yes ke kad’anki-” katsesa tayi.
A’a dan Allah Anas wallahi barin iya kwana ni kad’ai ba kayi hak’uri please, ko a k’asa ne a d’akin ka zan na kwana.”
“Why?” Ya tambayeta yana me jin dad’i amman se nuna ma ta yake kamar bayyaso.
“Anas a list na contract namu ai bakace za’a na raba kwanciya ba, kuma kafa san mutumin, wallahi ze dawo dan Allah karka min haka.” Cruel smile ya saki, “I will think about it.”
“Anas please...” Ta rok’esa.
“Okay naji” yace ganin zata soma masa kuka. Dad’i taji sosai wanda ta kasa b’oyewa.
“Ermmm... Anas nace d’akuna nawane a gidan duka?”
“Ke wani irin brain ne dake daman ba k’irgawa naga kinayi ba d’azu?”
“Nafara irgawa sena rikice.” Kallonta yayi ta gefen ido, “fish head” yace a hankali. Sarai tajisa amman tayi shiru. “Guda 7 ne including guest room seda parlour biyu dakuma toilets 7 se kitchen d’aya da store room biyu. Clear?” Kai ta gyad’a a hankali tare da had’iye miyau. Sede daya kalli fuskarta ya gane tanada tambaya.
“Say it out”,yace da ita.
“Ermm. Anas duka d’akuna 7 d’in zanna sharewa ni kad’ai?”
“Eh da meh aikin ki? Aure fa kikazo yi ba hutu ba Fannah.”
“Anas nasani amman...” se kuma tayi shiru “kad’an taimaka please ga shara ga mopping gakuma girki yi hak’uri.” Murmushi ya saki wanda fararen hak’waransa na sama kad’ai suka bayyana.
“Karki damu akwai masu aiki zasu na zuwa morning and evening suna duk wani aike-aiken, abinda zakina yi kawai cooking ne dan ba daga hannun kowa nakecin abinci ba, kema se kinyi sanitizing hannunki tukuna, clear?”
*© miemiebee*
[12:57, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
6⃣3⃣
*Assalam, as I promised zan bud’e new blog address, I did and its* beeenovels.blogspot.co.ke *so to my blog readers lets hit! Thanks for the love and support and also for the warm prayers, love you all!*
*Also masu cewa nayi repeating page 62 twice a’a ku gane mutane ke yi ba ni ba, ina miyar da hankalina sosai wajen numbering pages so take note bana mistake anan. Masu editing min pages nasan kwad’ayin son next page ke saku yi amman kuyi hak’uri ku dena please kuna janyo confussion*
Kallonsa ta tsaya yi danko be isheta da kallo ba wai har setayi sanitizing hannu tukuna ta masa girki, shima kallon nata yake da gira d’aya a d’age. “Baki jini bane? Nace you need to sanitize those hands” ya kalli hannun nata “before cooking for me” Kallonta ta kawar daga garesa ba tare da tace komai ba. Taku d’aya ya k’ara kusa da ita tare da rufe gab dake tsakaninsu da sauri tayi taking step backward, ganin haka ya k’ara 1 step forward haka suka tayi seda yakaita jikin bango, wani irin kallon tsiya yake mata da tuni yasa zuciyarta bugawa fat-fat.
“Kinji ni?” Yasake cewa da ita alokacin dayake kallon lips nata. Kai ta gyad’a cike da tsoro “nn... Na... Naji.” bending wuyansa yayi ta hanyar matso da fuskarsa kusa-kusa da nata dududu ratan dake tsakaninsu befi inchi d’aya ba. K’ara dad’uwa bugun zuciyarta yayi a yayinda k’arfin numfashinta ya dad’u. “Anas pl-” bata k’are maganar ba ta matse idanunta gam ganin Anas yasake matso da fuskarsa kusa da nata, har had’ewa numfashinsu yake.
Juyawa tayi zata bi gefen damanta dan guduwa, karap ya aza hannnsa jikin bangon ya dakatar da ita, haka ma yayi a gefen damanta “Anas please ka ba-” bata k’are maganar ba taji ya kunna switch d’in wuta daga jikin bango tare da matsawa baya. Shu’umin murmushi ne fal d’auke a fuskarsa “Da me kika d’au zan miki? LOL such a negative thinker. You thought I’ll kiss you right?” Wani irin kunya taji ya rufeta ji take kamar ta tone k’asa ta b’oye kanta, gabad’ai ta gama tsorata ta d’au kissing natan zeyi, amman dan iskanci ze kunna wuta shine seyayi kalan abinda ya mata? Mschww.
“Ni ba abinda nake nufi ba kenan” ta fad’a dan kare kanta tana kallon k’asa.
“Whatever ba sekin min k’arya ba.” ya fad’i da wani murmushin tsiya fal a fuskarsa. Ganin batada abinda zata ce masa kawai ta fara tafiya dan barin parlour’n although batasan ina take dosa ba. Kallonta yake ganin ta d’au hanyan store room ya tsayar da ita ta hanyan kiran sunanta, “Fannah!” Banza dashi tayi tana me cigaba da tafiyarta. “In d’akin ki kike nema that is not the way, you go right” ya nuna mata da yatsa. Bata ko tanka sa ba tabi right d’in ta fice. Achan ta samu d’akinta.
Akan gado ta zauna se kai take girgizawa ta matse idanunta gam har a yanzu kunyan abinda ya faru tsakaninta da Anas d’azu take. Tsuka taja a fili “mscwh! Ai seya d’au dama tunba yau ba ina expecting kiss daga garesa, Ya Salam!”
Knock ne yashigo daga k’ofarta. Kafin tace zata bud’e tajiyo muryan Anas “ga luggages naki and ba zama zakiyi cikin d’akin ba am hungry kifito ki dafa min dinner, kinji?”
“Naji” tace chan k’asa k’asa. Seda ta tabbata yabar wajen ta bud’o k’ofar tashigo da akwatunan nata tare da ajiyesu wajen ‘yan uwansu. Hijabin jikinta tacire had’e da kayan ta, sannan ta ciro wani silky white fitted doguwar riga me spaghetti hands tasa tare da sake maida hijabin