Showing 219001 words to 222000 words out of 268365 words
Chapter 74 - Tana Tare da ni complete book document .txt
Ya Khaleel bayan ya d’aga aka had’asa da police fitsari ne kawai beyi ba daga jin muryan police. Minti goma kacal aka basa da yazo sa gidansu Fannah if not za’a iya using rashin zuwansa against him ayi arresting nasa.
_8 minutes later..._
Daidai nan shigowar Ya Khaleel sekace salihin asali sewani behaving innocent yakeyi tambayoyi da dama aka masa wanda duk ciki be bada amsa d’ayan daya kasance gaskia ciki ba, “ya akayi Farouq yafito daga gidan yari?”
“Bansani ba wallahi ranka shi dad’e.”
“When last rabuwanka dashi?”
“Sati uku da suka shud’e kenan yanzu, tun daga ranan dana kai masa visit dana sake komawa washegari akace min anyi bailing nasa nata gwada layinsa bana iya samunsa, ku tayani nemo d’a na please.”
“Are you sure Mr. Khaleel danko kamana k’arya zamuje mu duba record.”
“Www... Wallahi Ba k’arya nake ba” ya k’are maganar yana had’a gumi. Ko da aka buk’acesa da ya kawo wayarsa aduba aga, ba fargaba ya bada saboda Farouq ya fad’a mai aduk lokacinda sukayi waya yana deleting logs nasa dan haka ba’a samu aka gano wani abu ba.
“Abuu wallahi he is lying he is definately lying yasan duk wani whereabouts na Farouq b’oyewa yake munafikin Allah kawai.”
“Haba Anas d’ana-” katsesa Anas yayi “shut the f*ck karka sake misantani da d’anka criminal ass kaji na rantse Ya Khaleel kome kake wallahi in na gano you also have something to do with the disappearance of my wife I won’t hesitate to kill you da hannu na zan kashe ka irresponsible father kawai.”
“Nasan da ky-” be k’are maganar ba Anas ya mik’e a fusace tare da shak’uresa jikin bango “ina Farouq yakaimin Fannah?! Tell me! Ina yakaita?!” Abuu ne dasauran police d’in suka yi sauri suka k’wato Ya Khaleel kafin Anas yayi masa illa, d’an banza tuni nishinsa ya canza idanunsa suka wani fito waje dan azaba.
*FANNAH* 1:50PM
A hankali aka bud’e d’akin da aka rufeta ciki, a firgice ta maida kallonta wajen idanunta suna tsiyayar hawaye. Bak’in fuska taga d’auke da abinci da ruwa a hannayensa nan tashiga rawa daidai gabanta mutumin ya ajiye abincin tare da since mata bakinta da hannu d’aya yace “ga abincinki inji Boss kichi.” Seda ta bari yakai bakin k’ofa sannan takirasa da “bawan Allah” chak ya tsaya. “Wani abu ne?” Ya tambayeta tare da kewayo wa.
“Bawan Allah muslimi ne kai?”
“Eh me kika ga?” ya bata takiacaccen amsa.
“Masha Allah k’arfe nawa ne dan Allah?” Bayan ya duba agogon hannunsa yace, “1:52PM” numfashi ta saki “dan Allah ka sinceni inyi Sallah banyi Sallan Azahar ba.”
“Boss bece in sinche ki kiyi Sallah ba so eat insamu inbar nan.”
“Be fad’a ba amman ai kai kasan haqqin Sallah dan Allah ka sincheni.” Wayarsa yaciro ya kira Ya Farouq alokacin yana a airport yana proceeding abubuwan tafiyansa Ukraine da Fannah dakuma Ya Khaleel kasancewar yasamu passport nata acikin jakarta.
“Hello Boss gata nan na kawo mata abincin amman tace setayi Sallah.”
“Karka damu kabarta tayi amman ka tabbata kana tsaye a kanta har tagama okay?”
“Okay Boss”
“Good bayan ta gama kuma ka kuma d’aureta karku bari tayi escaping.”
“Angama Boss” yana gama wayar ya maidashi cikin aljuhunsa sannan ya nufo gabanta ya sinche mata chain d’in da kwad’on da aka datse. Kamar wanda k’wai ya fashe ma aciki ta shiga bayi tayi alwala sannan tayi Sallah duk mutumin na kallonta, jira yake taci abincin yayi tafiyarsa amman tak’i koda bud’ewa.
“Hey Miss kiyi ki ci abincin mana banason wasan cha-chan nan ya wuceni fah.”
“Kayi tafiyar ni barin chi ba.”
“Suits you right” nan ya mik’e ya kamata ya k’uk’k’uleta again hawaye take sosai “bawan Allah nasan da akoi ragowar imani a tattare dakai dan Allah ka taimaka min nakoma gun mijina dan Allah nace.”
“Allah sarki kyakkyawar hallita sede yadda kika gannin nan barin iya cin amanan Boss d’ina ba” yana kaiwa nan ya fice haka tata kuka gawani erin bak’in yunwan da takeji. Har Sallan Maghrib Farouq be dawo ba kamar d’azu ya tura MB daya kawo wa Fannah dinner anan ne daya sinche ta tayi alwala ta had’a La’asar da Maghrib sede yunwa takeji sosai yanzu dan dole tad’an tab’a abincin.
Tana cikin chi wayar MB yasoma ruri a hanzarce ya d’aga “hello Mazzaaa yaneh?” On the otherisde aka amsa “gani nan fah ina cikin gari wallahi harka ya taso kana ina?”
“Ohh boi! Ina nan bayan gari ta wajen gidan man Mobil.”
Gidan man Mobil? Fannah ta nanata a ranta dad’a kasa kunnenta tayi tana sauraronsa.
“Mobil wanne d’aya kenan Mazzaa?” cewar abokin nasa.
“Mobil daya d’auki hanyar barin Maiduguri mana ta Yobe.”
“Oh okay toh zan iso semu had’u.”
“Okay toh ina jiranka” nan ya katse wayar tare da kewayo da kallonsa kan Fannah, yi tayi kamar bata masan yana kallontaba se chin abincinta take a hankali.
“Hey Miss ko Mrs kike kiyi sauri kina b’ata min lokaci.”
“Nagama tace dashi ba imani kaman d’azu ya sake k’uk’k’ulleta sannan yayi tafiyarsa. Tunanin ya zatayi tasamu waya tayi texting wa Anas location da take yanzu take tunda tagano location d’in, sede sam takasa batasan ina zata samu waya ba duk masu ma Farouq aiki zuciyarsu a karye suke kamar nasa.
*© MIEMIEBEE*
beeenovels.blogspot.co.ke
[12:59, 12/18/2016] +234 903 612 6826: •° ★°•❣🎀❣🎀 •°•★•°• °•★•° °• •°
°•°
*TANA TARE DANI...*👫
❣🎀❣🎀❣
*_written by miemiebee👄_*
In dedication to *Aunty Sis💕*
8⃣4⃣
9:30PM Farouq ya dawo gida all tired and exhausted kayan jikinsa ya rage, ya ragar da singlet da shorts zalla sannan yachi abinci. “Ya MB Fannah tachi abincin kuwa?”
“Eh Boss tachi dinner amman tak’i chin lunch.”
“Good ashe dama nasa mata maganin zubda cikin aciki koda shike nasan yadda zanyi na zubar da cikin.” ya sakar dawata muguwar murmushi. Bayan ya gama chin abincin ya nufa d’akin dayasa aka d’auretan, zaune ya sameta tayi shiru abin tausayi. Tana ganinsa tahau b’ari k’ok’arin magana take amman kasancewar bakinta arufe ta kasa, hannu yasa ya b’antare cellotape d’in yana wani shafa kan lips nata ganin bata maqe lips natan chiki ba bata kuma hanasa yi ba yasa sa shiga duhu. Meke faruwa?
“Ya Farouq please ka kunche min hannu nagaji dan Allah” tayi maganan cikin wani erin salo da siririyar muryarta me dad’in gaske. Ba musu bale gardama ya bud’e padlock d’in ya since ta.
“Ina kashiga yau Ya Farouq?” tayi maganar ba yabo ba fallasa.
“Naje processing mana abin international passport d’innan ne did you missed me?” Kai ta gyad’a, dad’i sosai sokon ya jiyo. “Well am here.”
“Ya Farouq akwai wata maganar da nakeson muyi dakai dama.” Ta k’are maganar da ‘yar murmushi kwance kan fuskarta.
“Mene ne wifey tell me.”
“A farko inason baka hak’ui game da abinda na maka d’azu kayi hak’uri bayan nan sekuma batun barin Nigeria dakace zamuyi na zauna nayi tunani tun ba yau ba nakeson zuwa k’asar nan Ukraine nayi nayi da Anas yakaini amman yak’i bature yace oppurtunity comes to life at once so banason missing wannan oppurtunity na yarda zan bika.” Kamar amafarki yake jin zancen. Idanunsa a waje yayi maganar “Fannah? Anya kece kuwa?”
“Sosai nice Ya Farouq zan bika Ukraine.”
“Why the sudden change?”
“Kamar yadda na fad’a maka na zauna ne nayi tunani.”
“Oh sweet wifey” ya shafa fuskarta na d’an lokaci ganin bata hanasa ba yasake jin dad’i shi da kansa ya zaro hannun nasa daga baya. “Wifey ina ba wasa kikeson min da hankali ba koh? Dan wallahi nagano tricking d’ina kike me hanani illata ki se Allah.” Zuciyarta taji ya mugun bugawa ji tayi she can’t proceed with the plans sosai tasan halin Farouq har kasheta ze iya in yagano tricking nasa take, nan tabar maganan zucin.
“Ya Farouq na tab’a maka wasa ko k’arya ne? I mean what I said just now.”
“Toh Anas fa ya kikeson muyi dashi?”
“Ya Farouq muddin baraka rabani da abinda ke cikina ba zan iya sadaukar da son danake wa Anas maka.” Baki ya wage wangalau cike da mamaki. “Fannah kinsan me kike fad’u kuwa? Anas fah? Mr. Fauzi!”
“Tabbas nikuwa nasani, Ya Farouq a iya ganinka da banyi ba yau na d’an wani lokaci sena jini incomplete na rasa dalili, dana zauna nayi nazari sena gama soyayya ce Ya Farouq kamar yadda kake sona nima haka nake sonka kawai I failed to notice it ne a da se a yanzu ina fatan am not late zaka karb’i soyayya na.”
“Kina sona Fannah? Baki tsaneni ba again?”
“Ban tsaneka ba Ya Farouq abu d’aya nakeso agareka kamin shi toh I will be all yours zanyi duk wani abinda ka buk’ace ni.” Baki na b’ari dan jin dad’i yace, “fad’i koma meh Fannah, tell me meh kikeso?”
“Karka zubar min da ciki, karka rabani da Baby na kamin wannan ka gama min komai. Shiru yayi na d’an lokaci. “Fannah amman aikema kinsan d’an ba nawa bane cikin Anas ne d’an ze zame mana ciwon idanu a rayuwa.”
“Ko kad’an Ya Farouq wannan shine ciki na na farko zanso ace na raine sa nakuma haifar, kaga daga nan kaima se in raini naka cikin ko ba haka ba? Ba kace zamuyi aure ba?”
“Tabbas na fad’i haka sede kince baraki aureni ba kinada igiyan auren Anas akanki.”
“Ada kenan Ya Farouq, ka kwantar da hankalinka a yanzu haka ban damu da igiyar auren ba ni kawai ka kaini Ukraine dreamland d’ina.”
“Amgama wifey zakije Ukraine zakiyi zaman Ukraine achan kuma zakiyi rainon ‘ya‘yanmu.”
“Kai amman naji dad’i Ya Farouq toh kud’i fa kanada enough? In babu kayi demanding Anas yamaka sending.”
“Eh inada, ina guy daya ara min miliyan biyar d’innan? ba nace miki na miyar masa da kud’in sa ba?” Kai ta gyad’a nufin ta gane. Ya cigaba “toh ai andawo da kud’in d’azu sabida yayi tafiya seko wani sati ya dawo kngga ko kafin wani satin mun tafi Ukraine meaning barin biya sa kud’in nasa ba kenan.”
“Are you sure Ya Farouq? Barezo ya kama min kaiba? Kasan banason wani abu ya tab’aminafiyarka.”
“Yes wifey kinga yanzu inada miliyan 10 kenan ze ishemu settling a Ukraine.”
“Sosai ze isa I really can’t wait so yaushe ne tafiyar? Amman still zanso ace miliyan shabiyar mukeda ina gudun kar goma ya kasa.”
“Angama wifey zan kira Anas inche ya dad’o min miliyan biyar.”
“You will need my help but.”
“Ban fahimce kiba wifey” yayi maganar cikin rashin fahimta.
“What I mean is that zaka d’aureni kamar yadda ka saba seka d’aukeni hoto ka masa sending nasan yadda yakesona yana gani na a k’ulle ko miliyan nawa kakeso ze baka.”
“Wow wifey wallahi you are a genius!.”
“Thank you nace yaushe ne tafiyar namu?”
“Bare kai nan da sati ba by God’s grace.”
“Okay...” Tace blankly.
“So wifey yau zamu kwana tare?”
“Don’t rush through Ya Farouq nafison se in munyi aure semu soma had’a kwanciya ka gane?” Kai kawai ya gyad’a “Fannah kalleni.” Idanunta ta d’ago tana kallonsa tare da murmusawa.
“Wallahi karki min wasa da hankali I love you amman inhar na gano yo are pranking on me wallahi kinji na rantse ba me iya k’watanki.”
“Shikenan Ya Farouq tunda baka yarda dani ba ka sake d’aureni kabani waje, dama ku maza duk haka kuke Anas yak’i kaini Ukraine yanzu kai da kace zaka kainin ma dan kaga inaso kafara corner-corner kaima ba damuwa ka d’aureni ka gudu dani Ukraine amman kasani I will never ever love you.”
“Ohh wifey dan Allah karkiyi magana haka I’m sorry kawai I want to be sure ne kuma na tabbata dan Allah karkiyi fushi kinji? Yi hak’uri.” Shiru tayi bata ce komai ba.
“Please mana Fannah” ya k’are maganar hannunsa kan nata cike da dabara ta janye hannunta daga nasa “naji amman please karka sake cemin haka zuciyata barata iya d’aukawa ba kasan kalan tashin hankalin dana shiga yau kuwa da bansa wannan kyakkyawar fuskar takan a idanu na ba?”
“A’a” ya amsa a takaice yana kad’a kai kamar zombie. Daidai kunnensa ta matso ta rad’a masa wani abu ba tare da tabar wani sassan jikinta ya tab’a nasa ba.
Tsabagen dad’in daya ji yayi excusing kansa akan bari yaje ya d’auko mata wani abu yana zuwa. Yana ficewa taja wata doguwar tsuka “Allah ya tsine min ne in fad’a soyayya da azzalimi kamar ka Ya Farouq?” Hannu ta d’aga sama “Ya Allah ka jagoranceni in samu in k’wato ‘yancina k’ark’ashin wannan mugun, Ya Allah kabani sa’an gudanar da wannan plan.”
Bada dad’ewa ba yadawo dawani package a hannu “gashi its yours.”
“Meshi?” Ta tambaya tana k’ok’arin bud’ewa. Wani had’ad’d’en silver bracelet ne ciki. “Uhm Ya Farouq na waye wannan kuma?”
“Naki ne wifey yau nagani a store kawai naji I want you to have it.”
“Oh is that so? Thank you” ta miyar ta rufe.
“Bara kisa bane?”
“Zansa mana, meyesa barinsa ba? Sede Ya Farouq nafison se in munyi aure tukuna in fara sa gifts naka kaji?”
“But wifey meh aciki dan kinyi accepting bracelet dana baki.”
“Ya Farouq trust me ai yanzun ma nayi accepting zan ajiye a wajena kawai sawane barinyi ba ka gane?”
“Nagane wifey muje mu kwanta koh?”
“Not yet ka manta zaka tambayai Anas kud’i.”
“Ohh haka fa!” Nan ya sake d’ad’d’aureta kamar jiya yayi sending message da pictures d’in wa Anas. Hankalin Anas inyayi dubu be tashi ba ganin pictures na Flowersa d’aure again.
*****
“Hello Farouq dan Allah me kakeso? Me kakeso please kadena bata wahala what is you problem?”
“My problem? My problem is money kabani kud’i se in sake ta takwanta.”
“Jiya jiya fa na maka sending 3 mil be isaba ba?”
“Be isa ba dan bance kayi signing sunan FAHNAS enterprises koh? Eh Fahnas enterprise under my name ba shine zaka tsaya kana gaya min magana? Karka turo kaga d’anyen aikin Farouq.”
“Wait.. Wait zan turo nawa kakeso please let her go”
“Miliyan biyar nake buk’ata.”
“Miliyan biyar Farouq?” Ya zaro weak blue eyes nasa. Me ka miyar dani? ATM machine? Kanada ma hankali kuwa? Ko an gaya maka bana calculating millions da nake maka sending ne? Ina zaka kai 15million please?”
“Ina ruwanka? Oversabi zaka turo kokuwa inbar matarka ta kwana haka?”
“Zan turo son of a b*tch zan turo please ka saketa.”
“Inga alert” ding! Ya katse wayar. Bayan minti goma alert ya shigo masa wani shu’umin murmushi ya sakar “Allah sarki d’an amanah.” Bayan ya dawo da kallonsa kan Fannah yace, “stupid d’in har ya turo.” Sosai zuciyarta ke mata k’ona jin yadda hankalin Anas nata ke a tashe “Anas Habeebi very soon in shaa Allah all this will be over more patience please.” Tayi wannan magana a zuci.
“Wifey baki jini bane?” Firgit ta dawo reality. “Na’am kace?”
“Nace yayi transferring kud’in we good to go now.”
“Wow great!”
****
“Wifey are you sure zaki iya kwana achan?” Farouq yayi maganar yana miqe kan gado ayayinda Fannah ke maqure bisa 3 seater dake d’akin ta nannad’e jikinta da bargon ruhuwan daya bata.
“Yayi Ya