Showing 1 words to 3000 words out of 137802 words

Chapter 1 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

*KURA DA FATAR AKUYA*






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*




*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*


*Page 1-2*












BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM




Cikin sasarfa take saukowa da ga matakalen benen, yayin da fuskarta take cike da matuƙar farin ciki. Kallonsa ta yi daidai lokacin da ta miƙa masa agogon da ke hannunta ta ce, "Please dad help me."
Karɓar agogon ya yi yana murmushi, zuwa can kuma ya ɗaure fuska yana kallon ta. "Jannah, na ga ya miki ki daina saukowa benen nan da garaje, kina dai tune da faɗuwar da ki ka yi."
"I’m sorry, dad, ka san yau ina cikin farin ciki shi ya sa."
Dariya ya ƙara yi jin abin da ta ce tare da duba agogon hannunsa."Anya mom za ta dawo da wuri kuwa? Na fara jin tsoron kar ta ƙi dawowa, ka san halinta. Ga shi friends ɗina sun kusa ƙarasowa."
Ɗan yaƙe ya yi, amma shi kansa zuciyarsa ta fara karaya. "She will be back, we still got ten more minutes." Ya ce mata cikin ƙarfafawa. Ƙaramin tsaki ta ja, tare da kallon tanƙamemen falon da ya sha ado da kwalliya sai ɗaukar ido ya ke yi.
"Sam bai kamata ta je aiki ba, kasancewar yau rana ce ta musamman, amma abin takaici na san da ƙyar ta dawo kan lokaci."
Ƙarasowa ya yi gefenta ya zauna tare da miƙa mata wayarta. "Ungo wayar, kira ta ki tuna mata da muna jiran ta."
Ba tare da ta ce masa ƙala ba ta karɓi wayar. Sai dai, har ta yi kira sau biyar ba ta ɗauka ba. Jifa da wayar ta yi daidai lokacin da ta ji alamar buɗe get, wanda da sauri ta ruga tare da buɗe windo a tunaninta ita ce. "Oh my God! Dad, friend dina ne, and she isn’t back yet." Sai ta tsaye cikin ɓacin rai lokaci guda idanunta suka kawo ruwa.
"No, please don't cry. Ma za ki je ki tari ƙawayenki."
Cikin rashin karsashi ta ƙarasa ƙofar tare da ƙaƙalo murmushin dole. "Wow you look lovely!" Suka haɗa baki gurin faɗi hakan, tare da mai da hankali gurin gaishe da dad, da yake kallon su fuskarsa a sake.
Ganin tana shirin yin kuka ya kama hannunta zuwa bedroom. "Ina ga bari na je na ɗauko ta, kin ga kar su yi ta jira."
"No dad." Ta furta tare da kama hannunsa cikin damuwa.
"Kyale ta ba sai je ba. In har ba za ta iya yiwa rayuwata adalci ba, ta ba ni minti talatin a lokacinta, don na taya ta murnar birthday ɗinta, ba na buƙatar zuwan ka." Ta dasa aya tare da juyawa ta nufi hanyar fita falo. "Bari na je na sallame su." Ta ce ba tare da ƙoƙarin fita.
"Alhamdulillahi! Jannah ga hon ɗin motarta can, ma za je ki gani nan zuwa." Ya furta tare da yaye labulen ɗakin yana murmushi. Jin abin da ya faɗa ta saki fuskarta tare da share hawayen fuskarta.
Da sauri ta ƙarasa falon tare da yi wa ƙawayenta umurnin su ɓoye ta kashe wutar falon bayan dad ya ɗauko fulawar da ya adana don ba ta kyauta.
Mom da ke tafiya cikin tsananin gajiya ya yin da take jin wani irin bacci yana fisgarta. Da sauri ta miƙa wa Moses jakarta burinta bai wuce ta ji ta a kan gado ba.
"Ma’am, I’ve collected all the document and I’ve sent them to him, he said that he would email you."
"Okay," ta ce tare da karɓar jakarta ta cire wasu files ta miƙa mi shi, wanda ya karɓa cikin girmamawa. "Take this and give it to him."
"Okay, Ma’am"
Tana ƙoƙarin shiga falon wayarta ta yi ƙara a kasale ta kai hannu za ta kashe, sai dai ganin mai kiran ya sa ta ɗauka da sauri. "Hello, uwa ba da Mama, kina jina?"
Daga can bangaren aka ce, bayan ta yi sallama. "Eh, Hajiya turai. Na san tun da kika kira ni bayan ba mu daɗe da gama waya ba akwai matsala, me ya faru?"
"Haka ne wallahi, kin ga wani ces aka kawo mana yanzu akan fyaɗe, kuma abin takaici yarinyar shekara uku ne kacal."
Da sauri ta rintse idanunta sai ta ji tamkar ta sanya kuka tsabar tausayin yarinyar. "Subuhanallahi! Don Allah ki yi duk abin da za ki yi, yanzu zan yi magana da Barrister Tukur. Don Allah ki yi ƙoƙarin da kika saba."
"To shikenan, zan yi ƙoƙarin, amma wallahi lamarin nan yana ci mini tuwo a ƙwarya! Ba mu da wani aiki a Ƙasarmu sai kisa da fyaɗe."
"Allah ya kyauta! Ya kawo mana agaji." Ta ce tare da kashe wayarta tana jin yadda zuciyarta ke suya. Ƙoƙarin neman numbar Barrister Tukur ta fara yi.
Jannah da ke laɓe a bayan ƙofa zuciya ta ciyo ta, ganin kusan mintin goma da shigowarta amma ba ta shigo ba. Da sauri dad ya kama hannunta yana girgiza kansa da alamun kar ta je.
Daurewa ta yi ta koma gurinta idanunta na zubar hawaye. Kimanin mintina ishirin da shigowarta sannan ta murɗa ƙofa ta shigo bayan ta gama waya da Tukur. "Happy birthday too you! Happy Birthday too you! Happy birthday too you!" Gabakiɗaya suka ɗauka suna rera waƙa tare da yin tafi.
Mom ta saki nannauyar ajiyar zuciyar sai ta ja ƙaramin tsaƙi. Zama ta yi a kan kujera tana murmushin da ga gani kasan ƙaƙalo shi take yi. "Kai! Wallahi sam na manta yau ranar birthday ɗina ne, sai da aka rinƙa kawo mini gift da wishes na tuna. Na gode sosai Jannah."
Miƙa mata flowers ta yi tare da rungume ta amma sai ta janye ta daga jikinta tana faɗin, "Thanks, my baby. Bari na je na kwanta kaina ciwo yake, na gaji matuƙa." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin yin hanyar ɗakinta.
Tsananin baƙin ciki ya rufe ta sai ta ji kamar ta sanya ihu, kallon dad ta yi da ya ji kamar ya rufe mom da duka. "Mom, za ki yanka cake. Please don't say no."
"Okay, bari na yi wanka." Ta ba ta amsa a gajarce tare da karɓar flower da dad ya miƙa mata, ba tare da ta ce masa komai ba. Ƙarasa shiga cikin ɗakinta yi tana ƙoƙarin cire kayan jikinta. Idanunta suka kawo ruwa sai ta yi ƙoƙarin sharewa."Da ma na san hakan zai faru, na san cewar ba za ta tana ba ni lokacinta ba." Sai ta miƙe cikin azama ta bi bayanta amma lokacin har ta tuɓe kayanta ta shige bayi. Ba ta ɗauki dogon lokaci ba ta fito. Ba tare da ta ce mata uffan ba, ta wuce wadrop tana neman kayan da za ta sanya.
"Mom, why you behaving like that? Ƙawayena ne na gayyato su, don su taya ki murnar ƙarin shekara, amma you just embarrassed me and dad in front of them!"
Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta juya ta kalle ta. "Don't stress me, I said I would come." Ta faɗa a gajarce cikin rashin kula.
Tsananin takaici ya ƙara kamata ta buɗe baki za ta yi magana daidai lokacin da dad ya shigo."Give her a few minutes, she needs to get dressed." Kama hannunta ya yi suka fita.
Tsuka ta yi, tana kulle ƙofar da suka bar ta a buɗe. "Jannah rigima! Sam ba ta tausaya rayuwata." Ta ƙarashe maganar tana warware tawul ɗin da ke jikinta.
A maimakon ta shirya ta fito kamar yadda ta ce, sai kwanciya ta yi da nufin ta shingiɗa sai dai baccin ya fi ƙarfinta.Ta fusata iya fusata da sauri ta buɗe ɗakin ga mamakin ta sai ta ganta kwance wanda hakan ya sa ta saka kuka."Mom, please!"
"Get out! I got to rest." Ta ce cikin tsawa tare da nuna mata hanyar fita.
Kuka ta ƙara saki ta faɗa jikin dad. "Na fara tantamar mom ba ita ta haife ni ba Dad! Anya ba adopting ɗina ta yi ba?" Ta fara magana cikin kuka tare da ƙarashe maganar da tsigar tambaya.
"Kar ki ce haka Jannah, mahaifiyarki ne."
"To me na yi mata take mini haka? Ka na ganin abin da ta yi mini agaban ƙawayena. Ina ganin yadda iyayensu suka gina na su rayuwar da soyayya."
"Ki ba ta lokaci za ta daina." Sai ta ƙara sakin kuka tana ƙoƙarin zama a kan kujera" Jannah, we’ve waited for a long time, I think we should go."
Shiru ta yi ba ta amsa musu ba wanda fanin hakan ya sa suka fice daga falon. Sosai ta sanya kuka don ta yi matuƙar muzanta ba ta san da wani ido za ta kalle su ba in ta je makaranta.
"Ki yi hakuri mom ɗinki na buƙatar lokaci, kin san wace ce mahaifiyarki"
"Kai kaɗai nake so; I hate her. Ka yi mini alƙawarin za ka ci ga ba da ba ni kulawa?"
"You don't have absolutely anything to worry about. I’ve got this."
Share hawenta ta yi tare da rungume shi. "Ina son ka, dad."
Sai ya shafa bayanta cikin sigar rarrashi da tausayawa domin ya fita jin hashin abin da ta yi mata.
Watsi da alatun da suka shirya akan taburin ta yi. "Tunda ba ta buƙatar hakan, ba zan ƙara wahalar da kaina gurin girmama ranar haihuwarki ba." Ta ce tana tare da sa ƙafa ta tattaka cake ɗin.
Washegari da safe ƙin fitowa ta tare da kulle ƙofarta. Sai misalin sha ɗaya saura miniti biyu ta fito, domin ta san cewar zuwa wannan lokacin ta fice aiki.
Wanka ta yi ta shirya cikin riga da wando ash colour tare da yafa gyalenta ta ɗauki makullin mota da fice. A kan hanya ta tsaya ta siyarwa ƙawayenta ƙaton cek da drinks ta kai musu tare da ba su haƙuri.
Ba ta dawo gidan ba sai misalin takwas na dare wanda shi ma kiran dad ne ya sanya ta dawo, amma ta yi niyar ta sai ten.
"Ki daina zama har dare ba ki dawo ba, kin san ba na son yawon dare."
"Okay." Ta ce tare da shigewa ɗakinta.
Dad ya shigo ɗakin tare da ije mata tsarabar da ya yi mata kana ya ce, "Mom ɗinki ta tafi Malaysia and she’s gonna stay for two weeks."
Shiru ta yi, ta ƙi ce masa komai ba don ba ta ji shi ba: Allah ya sa ta tafi gaba da can, Ta ce a ranta.
Cikin dare ta kasa bacci sai juye-juye take ga shi wani irin sanyi da yake shiga jikinta. Da sauri ta miƙe ta ɗauko maganinta, domin tana jin kamar ciwonta ne zai tashi, amma sai dai ko da ta sha maganin ba ta ji sauki ba, sai ƙaruwa da yake yi. Miƙewa ta yi a hanakali ta yi ɗakin dad.
"Dad ka buɗe mini ƙofa ba ni da lafiya." Ta ce jin ya ji ƙwaƙwansa ƙofar da ta yi.
Da sauri ya buɗe ƙofar ya kamata suka shiga. Maganinta ya ɗauko ya ɓalle mata tasha, sannan a hankali sanyin ya fara ruguwa bacci ya kwasheta.
Kamar yadda ta faɗa sai da ta yi sati biyu sannan ta dawo da misalin bakwai na yamma. A ranar ba su gaɗu da Jannah ba, don tana dawowa ta kulle kanta ta fara baccin gajiya. Jannah kuwa da ta dawo daga school ta samu ta dawo, tsaki kawai ta yi ta shige ɗakinta, ko kaɗan ba ta yi murnar dawowarta ba. Dad ne yake da rawar jiki da murna, har take away fita ya yi mata, wanda ba ta ci ba sai dai aka sa a frig sakamakon naunanyar baccin da ya kamata.
Washe gari da safe tana zaune tana shan tea Jannah ta fito cikin doguwar riga iya gwiwa. "Hi," ta ce mata tare da neman guri ta zauna tana ƙoƙarin zuba abinci.
Sai abin ya ba ta dariya sosai, ta san haushin abin da ya faru take yi."Jannah na dawo kuma.."
"Excuse me please, I got to take this call." Ta ce tare da ɗaga mata hannu ta shige ɗakinta. Ganin hakan ita ma ta shirya ta tafi ofis.
Tsaƙar dare da misalin biyu saura kwata Jannah ta fito daga ɗakinta cikin rawar sanyi tana kiran sunan dad tunawa jin za ta mutu.
"Dad please ka taimaka mini." Ta furta tare da fashewa da kuka.
Mom ce ta ji kukan sakamakon ba bacci take yi ba aiki take yi a laptop ɗinta, wanda da sauri ta fito ta kamata." Lafiya Jannah, ciwon ne ya tashi?" Ta tambayeta ba tare da ta jira amsa ba ta ruga ɗakinta don ɗauko magani.
Duk da ta ba ta amma sai bai lafa ba, wanda hakan ya ta hankalinsu matuƙa musamman dad da ya ƙe jin kamar ya mai da ciwon a jikinsa. Sai kusan asuba sannan ta samu bacci ganin haka koda gari ya waye mom ba ta tashe ta aba akan su je asibiti sai da ta ba ri don kanta misalin sha ɗaya saura ta tashi.
A lokacin dad ya tafi gurin aiki sakamakon kiran gaggawa da ya samu wanda kan dole mom ita za ta kai ta.
Bayan sun isa asibitin likita ya yi gwaje-gwajen sannan ya ɗago kansa ya ce, "You should take Jannah back to Nigeria due to her situation. I believe that's the best solution for her illness. The climate in Nigeria is much warmer than in London, which might be beneficial." Ya karashe maganar yana duba files ɗin da ke kan teburinsa.
Shiru ya ratsa na wasu ƴan daƙiƙa daga bisani ta katse shirun, bayan ta ɗan dogon nazari tare da kallonta da take ta rawar sanyi haƙoranta suna haɗuwa, ya yin da ta takure guri ɗaya. Duk wanda ya kalle ta ya san tana jin sanyin har cikin bargon ƙashinta ganin yadda ta yi.
"I will make a decision, and whatever I decide, I’ll let you know. If going back to Nigeria will cure her illness, then I have no choice but to send her, even though I wanted her to complete her secondary school in London. I’ll be praying for the right solution," Ta ba shi amsa cikin jimamin halin da Jannah ta ke ciki."
"Alright, take your time to think it through and come up with a solution," ya furta ya na examining yanayin yadda take rawar sanyi.
Ɗaukar jakarta ta yi da kama hannun Jannah ta ce, "Alright, doctor. Let's catch up later. Thanks. Ya mike tare da rataye rigar likitancinsa yana taka mata ya ce, "it's my pleasure to assist someone as generous as yourself. "
Murmushin ta yi ba tare da ta ce komai ba ta fice daga ofis, zuciyarta cike da jimamin ciwon 'yar gudaliyarta.
Haushi ko tsabar takaici zata kira abin da ta ke ji oho, ganin yadda 'yan jarida suka cika gaban asibitin. Jannah ta kalli 'yan jaridar ta juya tana kallon mom da ta haɗe rai tamkar hadarin da ke shirin zubda ruwa, duk da yanayin fuskarta ya nuna she didn't have the time to give them her full attention, but she needed to do something that would provoke a reaction. After all, those journalists were just so frustrating to deal with.
Kamar karamar yarinya ta sake ihu da karfi. "Mum, I'm feeling absolutely frozen. Please do something that'll make you stop talking to those blabbermouths," ta furta cikin shagawaba da rawar sanyi a hakorarta.
Cikin sauri ta juya ta kalleta sai kuma ta maida kallonta ga direba Maris. Idanunsa suka firfito ganin tsantsar bacin rai a fuskarta. "I'm so sorry, ma'am. It's not my fault at all, and I had no idea how they managed to track down your whereabouts. I just saw them, just as unexpected as you did." Ya furta muryarsa cike da tsoron ta domin ya san abubuwa guda biyu ta tsana wanda yana fatar kada rana ta kasance ya karya doka.
Sai a lokacin ta tuna ta yi waya da sakatarenta, Pedris. It must be him! Ta ayyana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login