Showing 1 words to 3000 words out of 19791 words
Chapter 1 - Sanadin Boko Book 4 end complete by Halima Abdullahi k Mashi .txt
Sanadin Boko 4-01
Posted by ANaM Dorayi on 06:21 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Kalmar ta dake ni tamkar saukar aradu jikina yayi sanyi
matuka.Tsam na mike daga gabn madubi na koma gado
na zauna cikin matsanancin kunan rai.Sai naji tamkar
mazaunan nawa ba zasu iya rike ni ba, don haka sai na
kashingida tare da lumshe ido. Duk iya kokarin da nayi
don na tsaida hawayen idona abn d yaci tura,sai da suka
sulalo ta gefen idona, idon haguna kuma hawayen ya
biyo ta karan hancina. Yayi dan murmushi ba shi da
burin da ya wuce yaga 6acin ran Hafsat,duk da son da
yake mata.In ya tuna yanda ta mike tana fada mishi
cewa ita karuwa ce sai ya ji tamkar ya binne kanshi don
takaici. Ya dubi ni Ki tashi mana kin wani kwanta. Na
sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya na ce. Ban san
cewa gasar kyau zamu je ba da ban 6ata lokacina gurin
shirin tafiyar ba., Kaje ka bata Award din da ka tanada
na mika wuya. Ya dan yi shiru. Kila yana nazarin
maganar da na fadane can sai ya fita da cewa in kin
gama ina jiranki a mota in har ina da izinin bada umurni.
Tamkar kada na tashi,amma bani da damar yin haka,dole
na koma gaban mudubi. Jallabiyata na saka baka mai
ratsin ja, tana da tsukakken hannu shima ja, na nade
kaina da dan mayafin, shima yana da ratsin ja. Takalimi
da 'yar post din da na saka duk jajaye ne. Na feshe jikina
da turare, da na kalli madubi sai nayi dan murmushi don
nayi kyau. Zuciyarta ce dai ba dadi sakamakon
maganganun da ya ya6a min. Na isa gefen direba in da
yake zaune cikin sanyin murya na ce, bari nayi ma su
Gwagwal sallama. Ya dago ya dube ni, muka kalli juna
cikin ido. Da sauri na rausayar da kaina gefe tare da
harde hannuwana a kirji, ya ce to kije mana kin tsaya
min kerere. Na dubi shi, "Ai dama umurninka nake jira.
Duk sai da na bi kowa gurinta na ce sai mun dawo,duk
sun ji dadin cewa gurin Fadima zani. Abin da na lura shi
ne, suna son a girmama 'yar uwarsu.Na dawo na shiga
gaba kamar yanda ya bude.Tsararran gida ne mai
matukar kyau, ga furanni masu bn sha' awa, ina biye da
shi hr kyakkyawon falon. Wani dankareren zanen hotonsu
ne yake fuskantarka an jingine shi da bango a kasa.
Kallo daya na yi wa hoton na kauda kai, tamkar jinsin
Larabawa ko Indiya. Ya dube ni ya ce," zauna, bari in
kirata."Ya tafi yana fadin "Sweety.," Tamkar in toshe
dodon kunne na don kishi. Na nutse cikin kujerar ledar
mai kalar siminti. Na dinga bin ko'ina da kallo. Wasu
abubuwan ma bn san su ba, ban ta6a ganinsu ba, daga
karshe na maida kaina ga dankareren TV bangon da
wasu Indiyawa suke ta rawa. Ba rawarsu ce ta birge ni
ba, da har na tsura musu ido,tsabar takaici ne ke cina.
Amma na lallashi zuciyata da cewa tayi hakur, na sani
wata rana dai labari. Hannuwansu sarke da juna suka
fito, kama suke sosai da shi,wani abu yazo ya tokare
kirjina tamkar in rufe su da duka. Wata zuciyar ta ce,
Tashi ki shaketa. Da sauri na ce, "A'uzubillahi
minasshaidaninrrajim" sau 3 sannan na ce, Allah ka yaye
min wannan duhun da ke zuciyata, ka bani ikon yin
dauriya,kasa nafi karfin zuciyata. Suna isowa na mike
tsaye,take naji zuciyata wasai, na saki wata fara'a wadda
bn san ma ina da ita ba,tare da mika mata hannu. Na ce,
Amincin Allah su tabbata a gare ki da rahamominsa da
albarkatunsa. Itama ta miko nata tare da cewa, Amin
kema amincin Allah ya tabbata a gare ki. Muka sarke
hannu.Sannan muka saki na zauna itama ta zauna, ta ce,
kullum ina son ki zo mu gaisa. Na ce"To ai yau gani
nazo." Ta mike ta nufi gurin da nafi zaton kicin ne, shi
kuma ya dauki remote yana canje-canjen tasha. Ya kuma
ajiye ya nufi dakinshi, ta iso da kofin tare da kwalin jus a
hannu fara'arta dai ba sosai ba. Ta dora kan stool ta
dauko shi ta kawo gabana,sannan ta zauna. Na dauki
kofin na jingina da kujerar ina kur6a ina kallon TV.Ta
mike ta nufin ciki,dakin da ya shiga nan ta nufa. Dakin
shi kenan,suka bar ni nan zaune. Tuni na dire kofin jus
din don sai naji ya daina zakin sai daci, don tsabar
takaici. Kusan minti 10 sannan ta fito shima haka. Ta
shiga dakinta shi kuma ya nufo gurina, na kalli agogon
bangon falon wanda hoton sune a jiki. Na ce, Tunda mun
gaisa zan tafi gida."Ya dube ni "Nan ma gida ne. "Yar
aikinta ta soma jera abnci kan dinning. Ta fito ta iso
gurinmu "Honey kuzo muci abnci." Ya dube ni " tashi
muci abnci . Na ce Tuni naci abnci. Ta ce, Ai kam ba ki
isa ba, dole sai kin ci. Ni da ita muka jeru, shi kuma ya
zauna saitinta, ta ce In zuba mana? na ce Ban san
cikinku ba, yaja plate ya zuna musu. Ya ce ke kuma
zuba naki, Ya kalle ta ya daga mata gira tare da kashe
mata ido daya. Ta kai masa dan duka cikin wasa, ya
cafe ke hannun ta ya sumbaci tsakiyar hannun. Tayi
wata 'yar kara na dauke kaina ga barin kallonsu wayata
ta soma ringing a cikin pos dina. Na mike na nufi kujear
da na taso don nan ma na bar pos din. Ya dube ni Ina za
ki? Na ce Amsa waya zan yi. Na dauka, yaya Umar ne.
Nayi kasa da murya muna gaisawa ya ce Dama Inna ce
za kuyi sallama, suna gidana yanzun zan je in sha mai in
maida su." Na ce To yaya Umar. Ya ba Inna muka gaisa.
Na ce Ashe tafiya zaku yi?" ta ce," Eh, mun shirya ma
yanzun zamu tafi. Dama ina so ne in sake yi miki nasiha
Hafsatu!!kiyi zamanki a dakinki, kiyi ta hkr don Allah na
roke ki duk rintsi ko yaji bn amince kiyi ba. Ki rufa ma
kanki asiri, kin dai ga gatan da Ubangiji ya miki, ya baki
miji dan mutunci, ki rufa min asirin nan da Allah. Na
fashe da kuka, na ma manta ko a ina nake, take lkcn
baya ya fado min lkcn d Innarmu ke rokona cewa in lura
da kaina in tsare mutuncina,amma bn yi hakan ba. koda
dai ba son raina ba ne, na ce Inna in sha Allahu mutuwa
ce kadai zata raba ni da gidan Abubakar. Na miki
alkawarin duk rintsi ba zan ta6a yin yaji ba. A hankali
nake maganar cikin Kuka. Abubakar ya tsura mata ido
daga in da yake yana fuskantata ne. can ya taso ya nufo
ni daidai lkcn da muka yi sallama nayi musu fatan sauka
lafiya. Na saka fuskata cikin cinyata ina yin kukan
takaici, da me zan ji? Da wulakancin Abubakar ko da
kishinsa? Ga furucin da mahaifiyata ta min. Muryarshi
naji daf da ni. Me ya faru?" ya tambaye ni . Da sauri na
dago kaina tare da share hawayen naki kallon in da
yake,amma sai na ce dashi. Ba komai. Ya dauki wayata
ya shiga duba lamabr da na gamawa wayar yanzun nan.
Ya kira hr lkcn wayar na hannu Innarmu. Ta daga ya ce
Salamu alaikum, Umar. Inna ta ce, Ba shi ba ne yaje
shan mai, mahaifiyarsa ce, Abubakar ya kara rage murya
tare da zama. Inna ina yini? Abubakar ne mijin Hafsat.
Ta ce Lafiya lau, kuna lfy ko? Ya ce lafiya lau, dama
naga Hafsan ce naga ta gama waya kuma tana kuka shi
ne na biyo layin in ji ko lafiya??Inna ta ce, Lafiya lau ban
kwana muka yi da ita na kuma yi mata nasiha. Ta dan
saurara kadan, sannan ta ci, gaba da magana, kai ma
don Allah ina son kayi hakuri da ita. ka kuma yi adalci
tsakanin matanka,Allah ya tayaka riko. Ya ce Na gode
Inna Kuma in sha Allahu zan kula. Ya dube ni bayan ya
kashe wayar. Da yake ba kyason gaskiya shi yasa ki ka
hau kuka don kawai an miki nasiha. To kiyi yanda ki ke
so tunda nasihar ce ba ki so, ai ba yau ce rana ta farko
da tace kiyi kaza ki bar kaza ba ki ka ki. , Don haka kiyi
son ranki kamar yanda ki ka saba. Ya aje wayar a kan
ciyata ya nufi gurin matarshi. Wadda dama duk
hankalinta yana gurinmu. Sai dai bana zaton cewa taji
abn da muke tattaunawa, sun gama cin abncin su suna
ta hirarsu cikin harshensu na Fulatanci suna dariya.
Hakan yasa na tsargu cewa zancewa suke yi don haka
na maida kaina baya na dora kan majinginar kujera. Na
lumshe ido ina son tuno kowace Amarya ce tayi rahin
dace irina a cikin dimbin amaran da suka yi aure a ranar
dana yi bana zaton za a samu Allah ka bani hakurin da
juriya daure wannan abn. Ina gidan hr lkcn da aka kira
Sallar La'asar ya wuce ni ya nufi Masallaci, itama ta nufi
dakinta ba tare da ta kalle ni ba,tamkar in fita in tafiyata,
duk da cewa bn san hanya ba, amma na cije.Me aikinta
ta fito na ce ina ne gurin Alwalarsu? Ta ce Duk a bayikan
daki suke yi. Na ce, ba ku da ko famfo a waje? Ta ce,
ita ma bakuwa ce, jiya ta zo amma taga can fulawoyin
can ana basu ruwa, kila akwai famfo a gurin. Na ko
samu famfo nayi alwala nazo nan in da na tashi nayi
sallata. Ina zaune ya dawo. Ya kalleni, kamar zai yi
magana amma sai ya fasa, ya nufi ciki koda suka dawo
falo suka zauna. Sam nayi nisa cikin tunani ban san me
suke fada ba, suyi da yaransu suyi da turanci, wani lkcn
har da hausarsu kamar ta 'yan koyo. Da Magriba ma da
ya fita dakin ta nufa da ya dawo ina azkar ya zauna
sannan ya kirata da wayarshi. Ta fito ta sake wanka da
sabon ado cikin koren yadi mai ratsin ja, doguwar riga
ce, tayi kyau sosai, ga kamshi turaren amarci na tashi. A
raina na ce, Lallai wannan sai na dage a gurin kwalliya.
Ya zuba mata ido, hakan ne yasa na saki baki, kai Hafsa
bata yi sallah ba? ta dube ni.ta ce, Gidan ba bakonta ba
ne, ita ce ta ki ta shigo, Ya ce, A"a fadima Fadima gidan
nan bakonta ne a yanzun,don bata san in da zata shiga
ba sai in ki mata jagora. Nan da nan sai tahade rai ta
soma magana cikin Fillanci, shi kuma ya ci gaba da
magana da Hausa, yana cewa. Ba wani son kai ko
bambancin da na nuna miki, in dai kina son gaskiya. Na
ce, don Allah ku bar magana laifina ne, ni ceban bukaci
shiga cikin ba. Ya ce, mata,To shi kenan zan nuna mata
komai ni. Har zuwa lkcn da muka baro gidan ban sake
cewa komai ba. Mun biya gidan su Hashim, matarshi mai
kirki, daga nan muka nufi gidan iyayenshi. Ummi tazo da
gudu ta rungume ni. Rukayya kam tana ta danna waya
ko kallo ban ishe ta ba. Na zube a kasa na gaida Daada,
sannan na zauna a gurin .Tayi tayi in hau kujera na ce
mata kasan yayi. Ta ce masa daga ina? ya ce Gidan fadi
ya kai ta. Ta ce, ya hada mu ya yi mana nasiha? Ya ce,
eh, ni dai na sunkayar da kai ina tuna nasihar da ya
mana,wai mu zauna lafiya, muyi kishi irin na gidan
Annabinmu (S.W.A.) Ya ce wai in bi Fadi don ita ce ya
za6a uwargidansa, sannan in girmamata baya son raini,
ita kuma wai ta kama girmanta, sannan ta dinga hakuri.
Ummi ta katse min tunanina, Anty tashi muje ki gaida
Abbanmu yana falon shi. Na mike na bita,shima nayi
cikin kunya da girmamawa na gaida shi, yayi mun nasiha
da in yi hakuri, in yi biyayya sannan in saba da zuri'arsu.
Kada kuma na yi wani abu na 6atanci wanda zai sa
zuri'arsu suyi da sun sanin shigowata cikinsu. Nayi
godiya tare da yi mishi alkawarin kiyayewa. Da zamu tafi
har bakin mota suka raka mu. Daada da Ummi, amma
Rukayya sai da ya yi mata magana sannan ta gaida shi.
Kafin mu iso gida sai da muka tsaya a wani super store
muka yi parking ya shiga. jim kadan ya fito da ledoji kuda
biyu ya shiga muka wuce.shine ya ruko ledar har
dakina.Na fada bandaki donyin alwalar sallar ishai ina
fitowa yacemin shifa xai wuce nace toh,har ya kai da
kofar daki nace masa ledar ka manta ya waiwayo
sannan yace taki ce.na dauka na duba kaxa ce da kayan
lashe lashe na zaki nace ka kara muku ni yayi min yawa
tunda kaga ku uku ne duk da yar aikin gidan nikuma ni
daya ce.ya juya tare da cewa na fiki sanin mu uku ne ai!
ya atfi abinsa na tada salla ta.A randa na cika kwana
biyar, misalin tara na dare yace in shiri gobe da taran
safe xamu wuce kano ,ina murna harda da dan tsalle
na.Allah na gode maka da har nacire rai da karatuna,nan
take na soma hada shirgi na.da safe dana gama shiri
naje na gaida mutan gida na kuma fada musu xan koma
mkrtn yau.duk suka min addu'ar fatar alkairi don doki
kasa break din kirki nayi.ya iso sanye da na kalar sararin
samaniya.yayi kyau,ni na shirya ya kalli kayana.Uhumm
dama duk kin kosa ki koma koh?saboda mu cin namar
jikin muke yi koh?na sunkuyar dakai bance komai ba ya
dauki babbar jakar niku na dauki karamar da ta
ratayawa.duk yan gidna sun min ftan alkairi da sauka lfy
usaman kanishi ne yaja motar.shi da hashim suka kaimu
filin jirgin sama gabana sai faduwa yake.yau ce rana ta
farko da xan fara hawa jirgin sama jikina sai bari yake
tayi.ina xaton abubakar ya dagoni sai ya tallafoni xuwa
gefen kafadarshi ,na lumshe idanu har muka shiga muka
xauna sannnan ya sake ni.jikinsa mai laushi da kamshi
wani sonsa ne ya ratsa ni tamkar in kwanta a
jikinsa...ckn lkc kankani muka sauka a kanon dabo inda
rahma da sagir ke jiran mu.ckn murna na rungeme
rahma sukuma suka kama hannu suka gaisha.gidan sagir
muka je sai d akarfe uku sannan muka fita. na kosa muje
gidan dana ke don inje gidan maman rahma inga shadad.
Kai tsaye gidan maman muka wuce muna shiga naga
shadad na wasn kwallo.da gudu ya taho sai na bude
hannu amma sai yaron nan ya wuce wurin Abubakar ya
daga shi sama nikam nayi ciki.mun gaisa da maama inda
na amshi dan mukulli sannan nayo gaba.su kuma suka
biyo cikin motar sagir daya amsa.mun hadu da wasu
makota daidai ku, sun mun murnar aure nayi godia.na
bude gidan cikin xakuwar shigarsa.yana nan yadda na
barsa.na bude daki xan shiga shikuma yace toh ni xan
tafi.nace toh sai ka dawo shi da shadad suka tafi.na
gama na sa turaren wuta,shawarar rahma ta fadomin
lkcn da muke kulle ckn daki.kafin ya tafi kiyi kokarin
janyo shi gare ki ta hanyar ado da sauransu yasan ke
mace ce "nace hmm shi da matarshi tamkar india,ga iya
ado tamkar dawisu ,har wani burge shi xanyi.tace tabbas
xaki birge shi yasn da mai kmr indaiyar yanace sai daya
same ki,nace toh hum xan gwada. bayan maghrib suka
dawo yana dauke da ledoji suka ajiye suak ce sun tafi yin
ishai nima sallar nayi na sake fenta fuskata na sake
kaya.riga ce doguwa rahma ta yadi ta bani mai rawa ce
sannan ta ilahir jikin duk motsin dana yi sai ya
bayyyana.yau ce rana ta farko daya shigo ckn dakin
gefen katifa ya xauna shadad ya xauna kusa dashi.ya
kalli abubakar yace anty bata ci abinci bah"yace xata ci
ya kara cewa uncle in xaku kara tafia ku tafi dani.yace
toh xamu atfi da kai.haka suka yi ta hirar su ina ta
kallon shi yana satar kallona.na xauna tare da janyo
ledar na duba madara mai snayi ce.na dauka na sha.na
kalleshi muka hada ido sai ya kauda kai ya ciro waya
yana kirar layin matarshi.ya kishingida yana magana
cikin fillanci haushi ya kama ni.sai kawai na fita tsakar
gida.ya jima sannan ya fito lokacin shadad yayi bacci,
yace na kam na tafi masaukina.da suari na dube shi
nace masauki?bansan ma ya fito bah yace eh masuakina
nace hum!!sai da safe.yace toh takaici ya isheni me
yake nufi dani?me yake son mai dani.ina kwance dare ya
tsala amma na kasa bacci juyi nake yi kurum a kan
katif.ni mutum ce kuma mai lfy ina matukar son ganina
kusa da maigidana.naja tsakin takiaci me yasa da ban
damu da wani namiji ?wata xuciyar tace lokacin ba kida
aure, yanxu kuma kina da miji wanda kuma kina so.daga
karshe dai na mike nayo alwala nayi sallah wanda ita
kadai ce mai mun magani damuwa.
***** ***** ********
Munnir yashiga gdansu cike da tunanin ta ina zai fara
yiwa iyayensa bayani, yace mum, tadubeshi cike da
tausayi, don tunda yaci karo da ciwon nan suke tausaya
masa, tace lfy munnir meya faru? Yace mom
eh....daman...wataran....sai yai shiru, tace kayi mgn
mana menene yafaru? Yarike kai, tace ciwo yakeyi? Tazo
gabanshi a rude, yace mum wani yaro nagani kuma
muna matukar kama, kuma ada maman yaron
budurwatace, IYE!!! Mekace? Tazauna gabanshi a kasa,
tace yimin bayani yadda zan fahimta, tace inba wani abu
yashiga tsakaninkuba toya daga ganin yaro dan yayi
kama dakai sai kace abaka? Yace mum shekarun baya
zaki tuna wata yarinya datazo gdan nan tace tanada
ciki? Tayi shiru tanason tanawa shikuma yayita mata
kwatance har saida tagane, yace to itace mum, kuma
nasan cikinane tunda nina mata ta karfin tsiya, (oh kuji
rashin ta ido) mum tace inane gdansu? yace nan abj
road ne, tace to bari dadynku yadawo saina masa bayani.
Da dady yazo tafada masa, nan da nan sai yau murna
tare da shan alwashin in zai karar da duk abinda ya
mallaka saiya amsa jikanshi da namiji, munnir cikin
murna yace, dady itace wadda yan yola sukazo daurin
auranta yau din nan, cikin mamaki dady yace, kana nufin
daurin auren damukaje? Munnir yace eh dady, yayi shiru
yana tunani, mom tace, ina ruwanmu don dan abokinka
ya aureta? Allah yakaimu gobe, nida kaina zamuje gdan,
hakan kuwa ta faru, misalin karfe 10 na safe munnir da
dadynshi sukayi sallama kofar gdan baban hafsa. Daman
baba yana zaune inda yayi sallar walaha bai tashiba........
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 4-02
Posted by ANaM Dorayi on 06:37 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Ya daddogara yafito, bayan sun gaisa, sai yace dama
yazone da batun yaro, wanda 'yarshi ta haifa, baba yace
banganeba? Munnir yace, baba baka ganeniba? Ninefa
munnir saurayin hafsa, kuma dan data haifa nawane,
shine na ganshi gurin bikin nan. Dady Yace, duk abinda
aka kashe zan biya, munzone mu sulhunta abamu
yaron,ran baba ya baci,ckn xuciyarsa kuma yaqi yadda
da yadda suke so.Tun farko matsalar me yana kawo cuta
da cin xali don suna takama da kudi shine xasu daurewa
dansu gindi yayi wa yarinya mugunta?Baba yace gaskiya
ni bansan da wannan xancen ba "yata kuma ba a nan
take ba a kano take sannan dan da kake magana yana
da ubanshi.Daddy ya kalli munnir toh kaji?Munnir fa
daddy yaron yayi kama dani sosai.baba yace itace
hujjark kawai?nan gaba wannan ba hujja bace don nasha
ganin masu kama dani da sai in bisu ince yayana ne?
Daddy yace to wai yanxu ina yaron yake?baba yace sun
tafi gidansu sai anjima.ya nufi gida daddy ya hau munnir
da fada wai ya musu karya.suka shiga mota suka tafi
,shidai munnir ya tabbata danshi ne kuma xai ta bin
diddigi sai ya amshi dansa.ya lumshe ido ya tuna
kyakyawan fuskar yaron mai kama dashi mai cike da
wayo da dabara gami da lfy.Mom tayi jigum dajin cewa
xancen