Showing 105001 words to 108000 words out of 146065 words

Chapter 36 - KAINUWA (Dashen Allah) Book Complete Document by Ayusher Muhd.txt

dai kinsan Juma'a dole ne d'a ya kwashi gaisuwar iyaye."
Baki tad'an tabe, jujuyawa yai kamar yana neman wani abu yace " Banga Abdulmajid da Waziri ba, na d'auka nan sukazo."


Kallansa tai tace " baka gansu ba anan kuma ka d'auka nan suka zo? Wace irim tambaya da amsa ce wannan?"
Turab yace " naga sun fita tare da aka idar da Sallah shiyasa na garzayo saboda ingaida Baban namu."


Shiru tai sun fita tare? Me kenan? Badai Hisham baiji fadanta ba?


Turab yace " Hala sun shiga garine zumunci, abinka da d'a da mahaifi."


A hankali ya karasa maganar.
Kallansa tai tace " me kace?"
Turab yace " me nace? Nikaina na manta."


Idanu ta kafa mai tace "kamar zance d'a da mahaifi kai...."


Dariya yasa yace " d'a da mahaifi kuma? Wa? Abdulmajid da Waziri? Ta yaya?"


Kallansa tai tsoro ya gama kamata, duk yanda taso ta b'oye sai da Turab ya gano hakan, yace " Umma?"


Kallansa tai tace " wani shirme kake fad'a, kai da Sarki nake magana ai."


Yace "Ahhh ni da Abba? Ko Abba da Abdulmajid?"


Magajiya ta makamai harara, yace "Au ashefa ni Abban nawa sun zama biyu tunda akwai Waziri."


Magajiya tai murmushi tace " Wai kana shirye shiryen bikin kuwa? Ko kuwa kana nan kana neman auren wacce ba baka za'ai ba?


Turab ya mike yace " Umma ki tabbatar komai na bikina ya tafi lafiya yanda ake so, in har kinaso bakina yai shiru kenan, sannan auran Khadija sai dai in ni ince bazanyi ba badai ku ba, daga ke har Wazirin saboda......."
Sai kuma yai wani murmushi yace " a bar dai maganar ko Umma? Banasan ciwo ya kamamin ke kafin bikin d'an naki."


Kallansa tai idanunta sun kasa d'aukewa daga kallansa tace " ko? Zamu gani ai."


Gira ya d'aga yace " ya kamata mu gani kam."


Ya juya yai waje.


Yana fita ta fara maimaita kalamansa, ta rasa me suke nufi, tabbas dole ne tasan me dan iskan yaran nan ya sani.


Mikewa tai tace "Hisham dani zakaja?"


A can gidan kuwa, sun isa gidan Waziri, khadija ta fito daga wanka kenan, mai kawai ta shafa ta saka doguwad riga ta zauna a bakin gado, ita yanzu komai ma baya mata dadi, in har ta tuno da kazanta da kuna rashin imanin da suka aikata.


Muryar Umma taji tana kiranta, fitowa tai tare da amsawa, ganin Umma tai bakinta yaki rufuwa saboda tsantan farinciki.
Umma tace mata " Khadija yarima ne yazo, yana nemanki."


Sam bata kawi Abdulmajid ba dan bai taba zuwa gidansu ba, ta d'auka masoyin ranta ne.


Da sauri ta koma d'aki ta shafa hoda da turare sannan ta yafa mayafi ta fito.
Sallama tai a falon, muryar data amsa ne yasa tasan ba muryar masoyin nata bane, bud'e labulen tai tare da cewa "Yaya?"


Abdulmajid ya kalleta sannan ya kallu Umma wacce ta taho rike da tire.
Matsa mata khadija tai Umma ta mikama Khadija tire mai dauke da lemon zobo, sannan tace " a kawo abinci?"


Khadija ta kalli Abdulmajid tace " Yaya wai a kawo abinci?"
Murmushi yai dan shi ya rasa me yasa Goggo take kunyarsa, sam Bata iya tsayawa suyi magana ko zuwa can tai, yace " na koshi khadija, zobon ya isa."
Umma ta juya, kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tsantsar farin ciki.


*Turab*

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)





*HASKE WRITERS ASSOCIATION*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*Na Ayusher Muhd🤸🏼*


*68*


Khadija ce ta karasa ciki ta zauna sannan ta gaisheshi.
Kallanta yai yace " Khadija meye tsakaninku da yaran can?"


Kallansa tai sannan tai kasa da kai.
Yace " Khadija me kike tunani? Kinaso kicemin yaran da na tsana shi kike so? A ma bar maganar so tunda nasan dama Kina sanshi amma me kike nufi da aurensa?"


Khadija a ranta tace " abinda nasan bazai taba yiwuwa ba kenan."
Amma a fili tace " Ya Abdulmajid."


Cikin fada yace " kinaso ki je gidan sarauta a matsayin kishiyar Gimbiya? Sannan a matsayin matar wancan yaran?"


Khadija ta kalleshi tace " Yaya wai me yasa ka tsaneshi da ya wa haka?bayan bai taba yima komai ba?"


Abdulmajid ya kalleta cikin b'acin rai yace " na tsaneshi, kallansa ma ba san yi nake ba, duk duniya shine mutum na farko dana tsana."


Khadija batasan sanda tace " bayan shine ya kamata ya maka wannan tsanar?"


Yace " mene?" khadija ta kalleshi tace "Yaya please ka dinga sa ruwan sanyi a ranka, in har wannan karamar maganar ta b'ata ma rai ya zakayi in babbar magana ta doki kunenka?"


Yace " babbar magana? Wacce iri kenan?"


Juya kai tai da sauri tace " ina dai fada ne saboda ni banga abin jin haushi a maganar ba."


Abdulmajid ya mike a zuciye yai waje ko zobon baisha ba.


Kanta ta dafe tare da rufe idanunta.
Hisham kam yana d'aki yana cire Babbar riga Umma ta shigo bakin nan nata a washe, tace "wai ya akai ya biyoka?"


Yace " sai ki rufe bakin ai, kin wani baje baki kamar yau kika taba ganinsa.


Kasa tai da kai tana murmushi.


Hisham ya shiga band'aku dan kama ruwa, yana fitowa yai falo inda Abdulmajid yake.


Me zai gani?"


Ba kowa a falon, da sauri ya fito yana kiran Khadija.
Fitowa tai daga d'aki tace " gani."
Cikin tsawa yace " ina Abdulmajid?"


Tace ya tafi.
Yace " ban gane ba?"
Shiru tai dan batasan me zata ce ba.
Waje yai da sauri cikin tashin hankali.
Umma ce ta karaso gunta tace " Me kika ce masa da har zai tafi ba ko sallama? Yanzu khadija bawan Allahn nan bai taba zuwa fa gidan nan ba sai yau, amma ki koreshi? Ta ya ya zaki......"


Kasa karasawa tai, Khadija cikin tausaya mata tace "kiyi hakuri Umma amma ba korarsa nai ba."


Umma tai shiru kafin tai ciki.
Khadija ta bita da kallo cikin tausayawa.


Abdulmajid yana fita yai gida.
Har zaiyi bangarensa aka sanar dashi kiran Magajiya.
Yana shiga ya taddata a tsaye da alama yawo take a tsakar falon.
Shiga yai ya kalleta yace "Umma ga......"
Wani wawan mari da ta sakar mai ne yasa ya kasa karasawa, tace " Uban me kaje yi gidan Waziri?"


Kasa magana yai sai kuncinsa kawai daya rike yana kallanta.
Magajiya ta kara hasala tace " wato bakajin maganata ko? Na d'auka na sanar dakai ba kai ba keb'ewa da yaya? Wato shine har da zuwa gidansa ko? Ka nunamin yafini matsayi a gunka ko?"


Abdulmajid yai shiru, tace " fitarmin daga falo, sannan wlh karka kuskura inkarama magana akan wannan zancen, na fadama."


Abdulmajid yai waje jiki a sanyaye, mota ya fada ya ja ta da gudu yai waje.


Abu Turab na kallan sanda ya fita, ba shakka yasan Magajiya ta haushi da fada ne, a fili yace " am sry, sai dai kaima kayi abubuwa marasa dacewa wanda dolene kaima kaji ba dadi."


Juyawa yai ya koma b'angaren sa.
Har zai zauna ya fito ya nufi bangaren Umma.


Tana zaune tana ta raba cingam ya shiga.


Yace " Umma amma dai harda 'yan katsina zaki aikama ko?"
Tace " kanaso kenan bikinka ya lalace daga biki zuwa gulma, gulmar da zata zama silar rugujewar komai."
Turab ya kalleta yace " Kina tunanin zasuyi zancen anan?"


Tace " Abu Turab kenan, bakasan mutane ba, kai a ido ne zaka ga kamar 'yan uwa ne amma a zahiri ba haka bane."
Kallanta yai sai dai baice komai ba, a kasan ransa shikansa yana san yaga 'yan uwansa.
Basira ta cigaba, kun had'u da Mai Martaba?
Yace " a'a."
Tace shikenan.
Kallanta yai cikin kulawa yace " lafiya dai ko?"
Tace bakomai.


********


Abdulmajid kam bai tsayar da motarsa ba sai a kofar gidansu Mairo, kallan kansa yai a madubi yace " baka da inda zaka sai nan?"


Kofar gidansu ya kalla sannan ya kwantar da kansa jikin sityarin motar ya dade a haka kafin ya tada motar yai gaba.


Yayanta ne ya shigo lokacin taba tsinke alayahu.
Yace " Yauma kin fita kikai?"
Mairo tace " infita zuwa ina?"
Harararta yai yace " wlh ki kiyayi kanki da wulakanta mutum, mutum ma irin Yarima wanda kalma d'aya zai iya sa rayuwar gidan nan ta ruguje, tun dazu bawan Allahn nan yake waje har ya gaji yai gaba."
Baki ta tabe tace " ni bai aikomin ba dan bansan yazo ba."
Ciki yai tare da yin kwafa.
Mairo ta cigaba da tsinke alayahunta, can tace " me ya kawoshi da ranar nan? Sannan bai aiko ba?" tsaki tai tace " damuwarsa ce."


************


Washegari kuwa Magajiya tasa aka kira mata Hisham, yana shiga ta rufeshi da fada kai kace itace uwarsa ba ma yayarsa ba balle kuma kanwa.


Ganin abin ya zo mai wuya yasa yace " Wai Magajiya inada tambaya."
Yaran nan da kike fada akansa na waye?"


Tashin hankalin da ba'a misaltawa.
Idanunta kadai sun isa su nuna maka tsantsan tashin hankalin da take ciki, tace " Yaya?"
Yace " kwarai ni yayanki ne, sai dai abun ya isa haka, akan yaran nan yaje gidana zaki sani a gaba da fada haka? Cinyeshi nai a gidan nawa ko me?"


Kallan mamaki takemai yanzu, yauce rana ta farko da Hisham yake maida mata murtani.
Tace " yaya ni kake fadawa magana?"
Yace " an fada miki d'in, duk yanda naso in kyautata miki na kula bakya gani, yanzu kwata kwata kin zama sai a hankali komai fada, ina Magajiyar da na sani wacce tsoro baya cikin zuciyarta?"


Tace " nikaina bansan meke damuna ba Yaya, sai dai tundaga sanda yaran can ya ce yasan sirrina nakejin kamar komai na rayuwata xai ruguje, yaya ka taimakeni ka kashe yaran nan da uwarsa, ni har itama banasan gani ba shi ba."


Hisham yace " in taimakeki? Duk abinda kike min?"
Tace " amma ai kai kasab burina ko? Dolene mu kawar da duk wata matsala da zata kawo mana kai akan nad'a yaran nan mulki."


Hisham ya kalleta a ransa yace "Magajiya kenan, zanyi duk abinda kikeso saboda d'ana, sai ya hau mulki in shekaki kema barzaho."


Hannu ya saka zai murd'a kofar shiga, abinda yaji ne yasa ya tsaya cak sai jikinsa da hau tsuma saboda tsananin tsoro da razana.


Magajiya ce ta katseshi tare da cewa " yaya."
Kallanta yai bai amsa ba.
Tace " na fasa kashe basira, mai kake gani in muka haukatata?"


Hisham yace " hauka?"
Tace kwarai " idan muka halaka Turab a ranar auransa ita kuma sai musa a haukatata kaga sai ace rashin d'anta ne yasata yin haukar."


Hisham ya sheke da dariya yace " gaskiya Magajiya ba digon imani a ranki, duk duniya kece mutum ta farko danasan yasan salan mugunta, ko shed'an sai dai ya sara miki."


Murmushi tai tace " ni dai yaya ka taimaken ka kyalemun yarona, wannan shi kadai ne abinda nakeson ka dashi, mu samu komai ya kammala, banasan wani abu ya tare mai hawa mulki."


Kafafunsa ne suka kasa d'aukansa da sauri ya dafa bango, dan gaba d'aya jikinsa kaurewa yake da rawa......


*Turab*



🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)


*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*


*Wattpad :-AyusherMohd*


*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


*69*


D'aki ya koma da sauri ya shige cikin d'aki shi kadai, labulayen d'akin ya rufe duka, ya shige lungun gado ya kankame kafafunsa.
Kalaman dayaji ne suke dawo masa, a haukata Basira? A kashe Turab ranar auransa?


Me ke faruwa? Me kunensa yakeji haka? Tsoro da fargaba sun hanashi fita, adaren ranar kuwa da zazzabi ya kwana.
Cikin dare kuwa yayi mafarkin wannan abu yakai sau nawa.


A zabure ya mike ya shiga cikin bargo, me Umma da kawu suke shirin yi? Kisa? Duk yanda yaso ya daure ko fitowa yai ya kasa.


Kwanan Abdulmajid biyu ko kofar gidansa bai fita ba, ya rasa menene abinyi dan abin duniya ya dameshi.


*****
Biki na ta matsowa, Gimbiya ansha gyara, gyaran da fadarsa ma bata lokaci ne, kullum Abu Turab na kiranta su gaisa.
Yau ma tsokanarta yai tayi a waya wai bata gajiya da killaceta da akai? Ba dama ko fita tai?
Sai dai tai murmushi tace " itakam bata ga wani abu ba."


Suna gama waya ya ajiye kan wayar sannan ya kalli Sabi'u yace " ya ya irin wannan sa ido haka? Ko kishi kake ne?"


Sabi'u yace " Gaskiya Turab da alama kanasan Gimbiya."
Turab yai murmushi yace " bai kamata in so ta ba?"
Sabi'u yace " ina na isa? Kawai dai da na d'auka kamar tursasa ma akai, amma yanzu naga kamar san ranka ne."


Turab yai murmushi tare da mikewa tsaye yace " Sabi'u kasan menene abinda ke halaka rayuwar zaman aure?"
"a'a."
Turab yace " nunama mace kiyayya."
Sabi'u ya kwashe da dariya yace " lalai Ango da alama ka fara shirye shiryen canza rayuwa."
Turab a ransa yace ina zaka gane abinda hakan ya jawo? Jiya da daddare ya dade yana tunanin wani abu, idan ya duba menene ya sa Magajiya ta zama tsantsar muguwa ba shakka rashin nuna mata damuwa da Sarki yai ne tun farko, wannan shine yasa take neman ta kwatarma kanta 'yanci na samun duk abinda takeso, tare da sashi ya so ta ya kuma kaskanta a gunta, wanda hakan ne ya jawo tai ta tafka kura kurai tare da kauce hanya, gashi yanzu tayi nisa wanda ta manta ma da dalilin dayasa ta cikin wannan halin tun farko.


Ajiyar zuciya yai tare da kallansa yace " Sabi'u kenan."


************


Gobe ne ake sa ran tafiya kano dan d'aurin auren Abu Turab, shirye shirye ake sosai da sosai, dan ma masu shirin suna Kano, masarautar kano kam ta cika ta batse da 'yan uwa na jini, na mulki da kuna na siyasa, Sarkin kano sosai yake cikin farinciki.
Dan ana sauran kwana hudu daurin aure yasa aka kiramai Turab ya kara bashi amanar 'yar tilon 'yar tasa da yake ji da ita kamar nama d'aya a cikin miya, yayyinta ma haka sukai ta bashi amanar ta, ba shakka ya fahimci tsantsar gata da ji da Gimbiya Bilkisu da akeyi, sai dai ko ina kalma d'aya yake fad'a _Baiyi alkawarin santa ba kamar yanda suke santa ba, sai dai ya musu alkawarin kula da ita, da kuma kaucema duk abinda zai sata dana sanin auransa._


Magajiya kuwa da Hisham sun gama shirinsu tsaf, ta rasa gane kan Abdulmajid dan sai yai kwana biyu kafin yazo gaisheta, inyazo kuwa gaisheta kawai yakeyi ya mike ya tafi, sai dai batasa wannan a ranta ba dan tana ta faman shirin yanda zasuyi gun halala Turab.


A ranar d'aurin auransa ne Abdulmajid sai zarya yake a d'aki, mai ya kamata yai?
Duk yanda yaso ya cire abin a ransa ya kasa, shi gani yake menene nashi a ciki? Sannan shima ai ba san Turab yake ba, sai dai gani yake kamar duk saboda shi Magajiya da Hisham suke neman halaka Turab, dan ya hau mulki ya kuma auri gimbiya, sannan su salwantar da mahaifiyarsa wanda take tushensa.

Har wajen karfe takwas yana ta zarya, gashi a lokacin mutane duk sun shirya ma sunyi gaba.
Magajiya ce ta aiko akan yai wanka yai shiri sosai na gani na fada.
Bai musa ba kuwa ya je yai wanka, kayan data aiko mai ya saka, kaya ne masu tsananin kyau da tsada, wanda ya tabbata ankashe kudi sosai a kansu.


Harya fita ya koma ciki tare da yanko yar takarda ya rubuta kamar haka _Ka tabbatar ka sanar ma mahaifiyarka kar taci komai yau, in har ba ita tai da kanta ba, kar kuma tasha komai._


Fitowa yai ya samu wata baiwarsa wacce take kurmiya, ya mika mata yace taje waje ta ba yaro ya kaima Abu Turab, sannan ta tabbatar bata fadama kowa ba wanda ya aikota sannan karta bari a ganta.


Hakan tayi kuwa, dan kurma Allah ya bashi iya rike sirri da kuma alkawari.


Turab yana zaune, Sabi'u na ta wani fesa mai turare kamar zai juyemai kulbar a jikinsa.
Turab yayi kyau na ban mamaki, Magajiya ta aikomai had'adun kaya sai dai bai sa ba, dan wannan Mahaifinsa ne ya aikomai.


Dole ne in ya wuce sai ka kalleshi saboda tsantsar kyan da yai, kwarjininsa da zatinsa kadai xai sa ka kalleshi ta baya.


Turab ya fizge turaren dake hannun Sabi'u yace " Ka bari in akazo naka auren sai ka fesa turare har a cikin bakinka ma, ba damuna zaiyi ba, amma ba ni ba."


Sabi'u yai dariya.
Shigowar Garzali ne yasa Turab ya kalleshi yace " Garzali ba na baka kaya nace ka saka ba?"
Kansa ya sunkuyar yace " Ranka ya dade kayan ai sunfi karfina."
Sabi'u ne yace " Gaskiya Turab ka d'au mataki da alama Garzali ya fara daina jin maganarka."


Da sauri Garzali yai kasa yace " Tuba nake ranka ya dade, yanzu zan saka."
Mikamai takarda yai yace " gashi inji wani yaro."
Turab ya amsa tare da bud'ewa.


Abinda ya ganine yatada masa hankali, yace " Garzali ina yaran yake?"
Yace " ya tafi."


Turab da sauri yai hanyar waje, dafashi Sabi'u yai yace " Lafiya?"


Turab yace " ina zuwa."


Waje yai da sauri sai dau ba yaran ba kuma alamunsa.
Fitowa yai ya nufi bangaren Mahaifiyarsa tana zaune kasanta mutane ne suna ta kukula Kayan robobi da su dubulan da zasu raba.


Mairo ya gani a gefenta, alama ya mata da hannu akan tazo.
Mairo ta mike ta fito.
Waje suka fita sannan ya kalleta yace " Mairo kina nan ai yau cir anan ko?"
Tace " a'a anjima nakesan tafiya."
Tai maganar fuskarta a had'e, irin wai kishin nan, balle yanda taga yasha kyau, haka kawai tana sanshi ba tun yanzu ba amma wata can a sama tazo zata aureshi...(😂nace Mairo ai dama haka rayuwa take, Matar mutum...Lol) dan itakam dan Basira ma ta aika tazone amma da bazata zo ba.


Turab ya mika mafa takardar nan, tana karantawa ta d'ago cikin tsananin tsoro tace "Yaya mekenan?"
Yace " ban san meke faruwa ba, sai dai na tabbatar akwai abinda ake shirin yi, ki tabbatar Umma bataci komai na gidan nan ba, ko ruwa in zatasha ki sa a kawo kara daga gidanku."


Tace "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login