Showing 3001 words to 6000 words out of 10311 words
Chapter 2 - AUREN DOLE BOOK COMPLETE BY 'YAR MUTAN DIKKAWA.txt
ta kalli,iyayenta Wanda hasken annuri da farinciki ya bayyana afuskokin su,itama murmushi tayi tace,Ina alfahari da Ku,A kullum ina rokon Allah yasa inyi rayuwa irin taku,Wadda dole sai nasamu miji,nagari hakan zata kasance Alhamdulilah Abbu ya zaba min Alaramma najibullah,mai addi,mai ilimi,mahaddacin Alqur ani,Nagode Abbu,na yadda na amince koda za'a iya kiran aurena da *AUREN DOLE* na tabbata agurina aure ne Wanda iyayena sukaga yadace da ni dan haka agefena babu *AUREN DOLE!*."
"Umma,Tabbas ina da hakki akanku,Amma naku yafi yawa akaina,saboda duk abinda yakamata kuyi mana kunyi mana shi.."Bazan manta Acikin suratul Isra'i,Allah (SWT)Ya ce"Kuma ubangiji ya zartar da hukunci kar abautawa kowa sai shi,kuma dangane da iyaye biyu Ku kyautata musu,ko da dayansa yakai ga tsufa to karkace dasu tir!"Kuma karka tsawace su,sannan kuma ka gaya musu magana mai karamci."
Sannan Manzon Allah (SAW) yana cewa yardar Allah tana tare da yardar iyaye,kuma fushin Allah yana tare da Fushin iyaye,"
"Dan haka umma
...Abbu nabi Allah da manzonsa,kuma na biku,kuma in shaa Allah zan cigaba da bin umurninku tare da yimuku biyayyah har karshen rayuwata..."Yaseera tace cikin ladabi.."
"Ajiyar zuciya Abbu ya sauke yace Alhamdulillahi Alaa kulli haliin..Tabbas nasamu mata,kuma uwa tagari wacce tayima yarana tarbiya tagari,Juwariyya nagode abisa namijin kokarinki akan yaran nan,Domin kece mai kula da su tare da sanya ido akansu da duk wasu lafuzza dazAsu fito daga bakinsu..."
"Umma tayi murmushi tace"Mallam kenan, ai Kaine ka karantar da ni har nike sanarda su,karfa ka manta Kaine jigon gidannan...daga ni har su muna bisa turbar inda ka ajiye mu,wannan tsarinka ne,kuma kokarinka ne,Domin ko kana gida ko baka gida,ka tsara yadda za a tafiyarda rayuwa da kuma mu'amulat agidanka."Sai dai mu godewa Allah nida yarana da yabamu garkuwa mai kyau,mai kuma inganchi amatsayin jagoran mu."
"Dariya Abbu, yayi yace Masha Allah, Ya kalli yaseera da ke wasa da zoben azurfa dake yatsanta,Ya ce Yaseera....."
"TaceNa'am,Abbu tare da dagou kanta.."
"Ya ce,Allah yayi miki,Albarka kinji,Kuma yadda kikayi mAna biyayya Allah ya ba ki wadanda zasuyi miki,Hakika akullum ina alfahari da Samun 'ya macce irinki!"Allah ya sanya alkhairansa da albarka a lamarin nan."
"Ameen,Ameen."umma tace tana murmushi.."
"Yaseera murmushi tayi cike da kunya,sai Abbu yace zaki iya tafiya abinki.."Aykuwa da gudu yaseera tabar falon."
"D'akinta ta fad'a,da yake cikin dakin falon umma yake,A falon,akwai dakuna uku, biyu da falo na umma,dayan nata,Shi kuma Yaya yaseer nashi na daga waje,Abdul kuma nashi na daga cikin falon Abbu,na shi daga gabas na Abbu daga yamma."Haka suke rayuwarsu kowa da dakinsa daban agidan,mazan ba ruwansu da harkokinta itama bata shiga lamarin su,wannan tsarin yasamo asaline daga iyayen su,Kuma wannan bai hanasu so da kaunar junansu ba,tare da sanin girma da kimar kansu Sam babu raini atsakaninsu."
"Yaseera saman gadonta da ke dakin tafada wasu hawaye masu zafi da ta kasa bambance ko na meye, ke zuba afuskarta!"Abincin da bataci ba!kenan adaren, duk da kasancewar tanajin yunwa,Tashi tayi,bayi ta fada domin dauro alwala,sallah ta tada bayan ta fito,sai da tayi Nafilfili,tare da azkharul naumy,sannan tayi shafa'i da wutiri,Akarshe addur ar istihara, ta karanto tare da fatan wannan zabi yazamo mata nagari,sannan ta tashi, kwantawa"Har kasan zuciyarta taji sanyi da nutsuwa yana yatsa dukkanin jikinta..."
*WANENE ALH.KALLE*
"Alh.Kalle babban dan kasuwa ne,da yayi suna agarin Argungu,Yana kantina da dama na kayan masarufi."Yana da arziki kwarai da gaske amma kuma kowa yasan jahili ne,ba boko babu mahammadiya,yana da mata uku a halin yanzu,wad'anda yake aure yana saki basu kirguwa, saboda haihuwa yake rabuwa da su,Da zarar macce tayi ciki yagama da ita matsawar bazata zubar da shi ba!"kuma da ya gama yayin macce shikenan,Duk da hakan yana da tsabar yara goma sha bakwai,cikin daga wasu na hannunsa wasun kuma suna ga iyayensu mata."
"Alh.kalle Sam baida addini ko sallah da kyar yake cika biyar ayuni,Katon gaske ne ga girma ga tsayi bakine wulik Wanda akalla zai kai shekara sittin adunia."Yanada yara yammata biyar da sukayi aure har sun hayayyafa,harda ,maza uku,yayiwa aure,ko yanzu tare da diyan sa uku mata za'ayi auransa,rana daya.zasuyi sa'annin Asmau"Bai da mutunci ko kadan,duk matansa suna tsoronsa da shakkun masifarsa,Sakin mace da aurenta awurinsa yafi sanya hula da sauketa akai sauki."Gashi da sakewa mata kudi awaje,amma da zarar sun shigo wayam,sai wuya da wahala,yaransa kullum kamar almajirai saboda baya kula da suturunsu acewarsa sunyi yawa,cishesu kawai aikine,Idan Alh.kalle yaga macce ya hadiye mata miyau to saidai wani ikon Allah,Domin kudi zaisa ko da so ko da *AUREN DOLE* sai ta shigo gidansa."Hakan ce tafaru domin tunda yaga Asma'u fara kyakkyawa yar kimanin shekaru sha takwas,ya liqe mata tayi masa wankin babban bargo!"Tana tare da kamalu,shima ya ci mutuncin Alh.kalle,suka wuce abinsu,shine yaji zafy!"Yayi alwashin rabata da kamilu,sai kawai ya mannewa kakanta malam Buba akan sai ya aura masa ita,kudade masu yawa yake damkawa mallam Buba,Dan kawai ya samu Asma'u wacce suke kira da (Ma'u)"
"Daman Hausawa sunce rana bata qarya, sai dai uwarda bata shirya ba,taji kunya."Domin yau takama Assabar tun safe ake kid'e kid'e da wasannin Al'ada da kuma gadon gida wato na mak'era,Kofar gidan mallam Buba mak'eri cike take timjin da yara matasa,da mutan gari,Mallam Buba ansha babbar riga sai washe baki yake yana d'aga robar fanta sama,yana sha,shi da abokinsa mallam iro ."Zaune suke akan kujerun roba da aka dazAwa mutanen da ke zaune,kofar gidan suna kallon jikokin gidan dake wasa da wuta.."
"Hatta yara qanana yan kimanin shekaru bakwai,Da mazan gidan an zuba musu kalanzir ajiki, an kunna wuta ajikkin kayan nasu,wasu a zaune cikin wutar,wasu ko suna tura makamashin wuta abakinsu,Amma sam wutar bata cin jikinsu,kuwwa sukeyi da shewa suna fad'in gado sai dan gad0,saimu diyan mak'era ba dai wuta ta ci mu ba,sai wani ikon jallah,Mune jikokin mallam Buba mak'eri ikon Allah,Ina Wanda wuta taci taki warkewa,ina Wanda wuta kema gaddama!"Kuzo ga yayan guduma,....."Masu kida ko sai kara kaimi sukeyi...can farinciki ya kama Baba Malaam."
"Baisan lokacin da yafada filin wasan baa,domin tuni yace yabarwa diya da jikoki,Cikin kwarewa Jikinsa sai mazari yakeyi galan din fetur yatada yana zubawa ajikinsa, wutar kara ya dauko tana ci ya goga ajikin kayan sa,amma Sam wuta taki kamasu....shewa aka dinga yi, mallam buba kudinsaya kwakulo duka ya zube aqasa yasa wuta ajikinsu, taki cinsu...sake kuwa akayi"daga yan kallo har jikokinsa kowa tsaye suna kallon Baba malam sunajin dadi,tofi yayi awuta sai kawai takama ajikinsa da kudin harda tururin hayaki amma ko alamun cinsu batayi ba....Yace,ina mai ja da Buba dan gambo jikan ila makerin manya!kowa yabar gida,"gida ya barshi,Cigaba yayi aikin gadou mai kidi naqara kashe kid'a...."Mallam iro ne dai yazo da Sauri ya janye malam Buba hakan nan."Nan wasa ta cigaba da kyau kowa na nuna tashi gwaninta."
"A cikin gida kowa sai hidima akeyi anci an sha masu farinciki da murna nayi masu bakinciki kuma sunayi."
"Asma'u kuka takeyi kwarai tun alokacin da taji labarin an dawo daurin aurenta da Alh.kalle."Ko wanka da kyar su Gwaggo husai suka tilasta ta,babu abinda takeji sai haushin kanta da batayi tunanin guduwa tun wuri ba,Kamalunta ya dade da cewa su gudu wani,wurin daban har ayi aurensu,sai su dawo!Amma tsoronta ya hanata binsa gashi yanzu ya Shiga dunia sanadin soyayyarta!,Kuma Batasan a ina yatafi ba, domin ahalin yanzu tafi son ta fada uwa duniya,da akaita gidan Alh.Kalle,kazami mai Faso da warin baki,kuma tsoho..."Kukanta ta cigaba da yi har lokacin da aka zo daukarta bayan tasamu horo awurin iyayenta,Baba mallam ko kashedi mai kyau yayi mata akan ta zauna da mijinta,kishiyoyinta,da tawagar yaransa lafiya."A lokacin hankalin Asma'u ba ya tare da su, ko A bata kama ba, acikin horonsu zuciyarta na ta shirya mata yadda zatayi,jin takeyi arantà!zata iya yin komai harta kisa! matukar kalle bai saketa ba!!!"
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA HUD'U*
*ALKALAMIN NABEELA DIKKI*
"Yaseera da qawarta Raudhat a hanyarsu two dawowa Islamiyya,Fira sukeyi sosai,Nan ne Yaseera ta labartawa Raudhat Mas'ud duk abinda ke faruwa."
"Dan tsakaita tafiyar sukayi,Raudhat ta dafa qawarta cikin nutsuwa,Ta ce,Yaseera nasanki kuma nasan dukkanin halaye,Ba sai na baki shawara ba,A kan cewa ki amshi zabin su Abbu."
"Na tabbata wannan aure naki da Najibullah alheri agareki!Ina miki fatan Alheri,Allah ya nuna mana lokaci,wallahi nayi farin ciki matuka domin kin samu miji na idon duniya,Ga ilimi,mutunci tarbiya da asali mai kyau,"Kinsani sarai wadannan su ne halayen miji nagari,Ina son ki kwantarda hankalin ki,Kada ki sanya musu acikin lamarinki sai karshen sa yayi kyau."Raudhat ta qarashen zancen tana murmushi tare da zubawa aminiyarta ido."
"Hannayenta yaseera ta hade da nata,Ta ce tabbas kice kawa tagari mai sona,nagode Raudhat hakika shawararki mai kyau ce,Daga yanzun nan zan dauki najibullah da zuciya daya, amatsayin mijin da nake fatan yazamo uban yaranah.."
"Haba tawan ba godia haka atsakanin mu, Raudhat..Ta ce tana dariya."
"Saleem da Abdul suka zo,Inda suke tsaye."
"Abdul ya ce kagan su ko sale,daman nagaya maka sai mun cimma su,suna nan suna surutu..."
''saleem qanen Raudhat yake,yayi yace tabbas abokina naga zahiri kamar kullum wato su yayah basa gajia da fira,Dariya suka sa dukkan su."
"Sallama da juna sukayi da zummar gobe zasu hadou Islamiyya,Tunda qannan su sun saka masu ido,Kowacce hanyar gidan su tabi itada qananta da yake layin gidajen su ya bambanta sai dai duk a unguwa d'aya ne."
"Ko da su yaseera suka dawo gida sun sami yayansu yaseer ya dawo daga makaranta,Ai kuwa murna aka shiga yi,Musamman Abdul da akayiwa tsaraba da yawa,Yaseera kayan kwalliya da hijab aka saya mata."
"Nan take ta fada kichen umma ta samu tana sanwar rana,zage hannu tayi ta tayata,bayan sun gama dan wake da zobou tayiwa yayanta domin shi yaya yaseer yafiso,dan kawai ta faranta masa yadda yayi musu abin alheri."
********************
"Tunda aka kai amarya Asma'u agidan mallam kalle kullum cikin masifa da rashin mutunci take,Allah ya jarabci Alh.kalle da ciwon son Asma'u Wanda ya haifar masa da jin tsoronta."
"Kusan kwanaki hud'u da auren su amma har yau Asma'u bata bashi dama ya dama ba kamar kowane Ango."
"Gidan Babban gidane mai dauke da ciki da falo hud'u na matan gidan,Uwargidan sa uwani,sai mai binta sahura,saina Asma'u,dayan arufe yake ba kowa,sannan dakin yammata biyu da filin gida, sai turakar mai gidan,,shimaa babban falone,da daki da bayi."A harabar gidan akwai dakunan yara maza uku,da wurin ajiye motoci,duk gidan tayal ne,an fenti shi da farin fenti,har qatoun get din gidan."
"Dakin Asma'u an gyare shi tsaf,ansa mata gadon jan katako,kalar jinin kare,da madubi,da wadirof,afalo ko kananan kujeru ne saiti daya,suma kalar kayan dakinta da labule."Alh.kalle shi yayi gadara ya sanya mata talabijin da bidiyo duk gidan dakinta ake kallo,saboda ba mai kayan sai ita,da sashen Alhajin kuma shi idan yasa ba mai shiga yayi kallon."
"Yadda Asma'u tayi tsammani agidan ba haka bane,domin kowa tsoronta yake ita kuma sai rashin mutunci takeyi."
"Batasan cewa Alhaji yayiwa matansa da yaransa kashedin kwarai akanta ba!."Shiyasa kowa ya zuba mata ido sai yadda taga dama."
"Tun a kasuwa Alh.Kalle ya kudurta aiwatar da kudirin sa ayau,shiyasa ana tashi kasuwa yadawo gida tun wuri."Asma'u ko tun safe suke Abu daya wato kallo ita da larai da Jummai yayan Alhaji da bazasu wuce sa arta ba,A yanzu sune manyan abokanta agidan,shiyasa ta daina yiwa uwani da sahura rainin wayo daman can da mama take kiransu."Tana zaune lafiya da su sai kurciya take zubawa agidan da hauka duk da Alhajin ya saketa dan har girki batayi sai dai taci ta kwanta acewarta bata iya ba,kuma ko ta iya bazata yiwa katti da yawa abinci ba!''
"Da misalin 12 na dare Alh.Kalle ya fad'a dakin Asmau da yake yanada mukulayen dakinta,shiyasa bai samu matsala awurin budesu ba!"Kwance ya sameta rashe-rashe akan gado,Baccinta takeyi cikin nutsuwa,Tasbaha ce rike a hannunta ga alamu tana janta ne bacci barawo ya saceta,Sam Asma'u bata bar addininta ba!Bata wasa da lokacin ibada,tarbiyarta ce,kawai tayi watsi da ita,saboda *AUREN DOLE* shiyasa take rashin mutunci kamar ba ita ba!"
"Ba kunya bare tsoron Allah Alh.kalle ya farma Asma'u,Warin 'ya'yansa mai karamcin shekaru."
"Tashin hankali marar misaltuwa tasamu kanta aciki,kusan sati d'aya ana jinyarta!"Tayi kuka harta godewa Allah,kishiyoyinta ke kula da ita tare da bata baki,akan tumasancin da mijinsu yayi mata,Batayi mamaki ba!Saboda daman can jahili ne!shiyasa ya nuna mata karfi!"
"Lami mahaifiyar Asma'u da gwaggo usaina sun zo da kansu har gidan,sun duba yarsu,ran su yabaci matuka!"sai dai hakuri suka ba Asmaun!!"Wacce banda kuka da cewa ita bazata zauna ba!zata bisu ba abinda take fadi!"
"Amma kashedin Baba mallam, Gwaggo ta tuna mata!"Wanda yayi sanadiyar katse mata hanzari!"Kuka ta cigaba da yi tamkar ranta zai fita!"A haka suka lallabata suka koma gida rai ba dadi musamman mahaifiyarta lami!!"
"Zama ta cigaba da yi agidan Alh.kalle zaman bakin ciki da ganin azaba domin da girkinta da na kishiyoyinta duk Alhaji farmata yakeyi ya mayarda ita kamar wata baiwarsa akullum cikin kuka take!tare da dinbim da nasani akan zaman da tayi ta zuba ido har igiyoyin *AUREN DOLE* suka rataya awuyanta!"
***************Najibullah,Ya dawo gida lafiya,kuma kwas din da yaje madina yayi nasara domin yadawo gida Nigeria da sakamako mai kyau."
"Mahaifinsa malam Usman,Babban Alaramma ne,yanada ilimi sosai yanada mata biyu,Hajiya Rabi'a da Hawwa suna zaune lafiya,sai yaran sa biyar Najibullah ne babba,sai Rahma,da Sudais dukkansu yayan Hajiya Rabi ne,Sai Nabeela da Khadija yayan Hjia Hawwa."Suna zaune lafiya cikin karamci da son junansu,haka kan yaran ahade yake suna da ilimi da tarbiya mai kyau."
"Najibullah matashi ne kyakkyawa wanda mata keta kai kawo akansa,Allah yayi masa baiwar kira'ah kamar sheik sudaisi idan yana karatu.Gashi da dimbin Ilimi bayada makosa ko daya iyayensa na alfahari da shi kwarai da gaske."
"Da dadewa mahsifinsa ya sanarda shi zancen aurensa da yaseera,sai dai shi ya amsa masu domin kawai bin umurnin iyaye,Amna aganinsa yafi son zabin sa, ba hadin iyaye ba!"Kasancewar bai taba haduwa ita ba,akan tana makaranta har yayi tafiya,shiyasa Mallam usman ya kirashi tare da bashi umurnin,ya tafi gidam malam Aminu ya ga yaseera wato matar da zai aura nan da wata d'aya."
"A zuciyar Najibullah mamaki da tunanin wannan aure nasu yakeyi shin *AUREN SO NE!KO KUWA AUREN DOLE* ne za'ayi musu."Amma afili da ladabi ya amsawa mahaifinsa da in shaa Allah zai tafi bayan magrib,godiya yayi masa tare da sanya masa albarka."
"Murmushin jin dadi najib yayi kana yabar falon mahaifin nasa cike da zancen zuci,"Da tunani wannan wace irin mata ce!?Shin tayi dai-dai da ra'ayinsa,irin kalar macen da yakeso ce!?"Oho dai ido kannan kai..."Inji Nabeela Dikko
"Kofar gidan,Ya tsaya yana nazarin ta ina zai fara,Sai kawai ga Abdul Raheem riqe da leda a hannu ga alama daga ake yafito,Fuskarsa a sake yace,Abdul ne ko?"
"Abdul da ya kada fadarsa daya a bakin get din gidan,ya waigo kasancewar bai lura da Nabullah ba.."
"Da sauri ya karaso wurinsa ya gaida shi aladabce..."
"Amsa masa Najib yayi saboda daman sun san juna,Domin yaseer mutumensa ne."
"Abdul,"Ya ce "Yaya Najibullah ne!"Hannu ya bashi sukayi musabaha..."Ya ce Yaya,kayi hakuri ban ganka bane,Saukar yaushe!"Andawo lafiya!?Ya hanya!?"
"Murmushi yayi sosai,Sannan yace"Duk lafiya qlaw,Shekaranjiya na dawo."Inji Najibullah."
"Masha Allah,Abdul yace Allah ya taimaka."
"Ameen,Abdul,Am nace yaseera fa tana ciki,"Najibullah ya ce"da Abdul."
"Eh,Yaya Yaseera tana nan.''Abdul ya ba shi amsa."
"Yawwa Dan Allah kayi min magana da ita,"
"To Yaya bismillah mu shiga daga ciki,Bayan Abdul din Najibullah ya bi,har babban falon Abbu,Ruwan faro,da lemu Abdul ya ajiye wa Najibullah,tare da Kofi sannan yace Yaya ga ruwa bara na kirata,Ledojin sa ya dauka ya fice daga falon."
"Dakin umma,ya nufa ya bata saqon aikenta,Ya ce "Umma Yaya Najibullah dan gidan Baba Alaramma ne yazo wai in kira masa Yaya Yaseerah,"
"Umma ta ce"To Ashe dan nawa yadawo Hajia Rabi bata sanar min baah."Yanzu kace ya shigo daga ciki kaje ka sanarda ita."
"Abdul ya ce"Umma ya na falon Abbu,Bara na kira yayar,Umma halan sonta yake naga kamar yana jin kunyata..."
"Katse shi umma,tayi tace,bana son gulma Abdul jeka ka tambaye shi!"
"Dariya yayi,yace kai Umma,Sannan yayi hanyar dakin yaseera,Buga kofar yayi har sau biyu,Fitowa tayi sanye da hijab,Ta bude ganin Abdul yasa ta ce"Daman nasan Kaine meye haka kamar zaka balla min kofa!!"Yaseera tace ahasale!"
"Allah ya baki hakuri!"Aikoni akayi kinyi bako yana falon Abbu!"Yana jiranki!"Abdul yace ya juya abinsa saboda da kyar ba'a saida halin ba!Shi da yayarsa."
"Ras!taji gabanta ya fadi to waye!?Ga shi tayi fada da Abdul din ta bare ta tambaye shi."
"Dakinta ta koma,Gyara fuskarta tayi,Hijab ta sanya!Ta fito afalo ta samu Umma ga alama da Abbu take waya domin yayi tafiya,Durkusawa tayi agaban Umma,Domin neman izinin tafiya,Alama umma tayi mata da hannu ta tafi,Duk da taso ta tambayi Umma ko waye!Dan tasan cewa Abdul bazai rasa gayamata ba."Tashi tayi jiki ba sanyi ta nufi falon da sallama kanta sunne."Tafiya take ahankali cike da nutsuwa."
"Amsa mata yayi,tare da dago idonsa gareta,Tozali yayi da kyakkyawar budurwa wankan tarwada,mai zubi da tsarin halitta mai kyau,Duk da hijab ne ajikinta bai hanashi hango cikar sura da halitta mai Jan hankalin mai dubanta ba,"
"Da sanyin murya ta gaida shi,"Saboda irin kallon da yake mata taji wani iri."
"Amsa gaisuwar yayi,Wuri ta samu a kujerar zaman mutim daya shi kuma yana kujerar zaman mutum uku,Nan dai musayar gaisuwa sukayi."
"Ya ce,Nasan baki sanni ba,sunana Najibullah usman."
"Kallon shi tayi taqasan ido,kyakkyawqn matashi ne nan take yayi mata wani kwarjininsa."
"Murmushi tayi tace gaskiya ban gane ba...,Inji yaseeea"
"Ya ce,Kin san kina makaranta,
"Hakane gaskiya"
"Nan ya fada mata duk abinda ke tafe da shi,cikin hikima da iya zance."A zuciyar yaseera wani farinciki taji yadda Iyayenta suka hadata da miji nagari."
"Sun fahimci junansu da yake kowannen su yanada ilimi,sai kakkyawar alaqa ta shiga atsakanin su,Najibullah bai bar gidan ba!Har sai da suka aminta da junansu."
"Asma'u sau uku tana samun ciki yana barewa!Bayan wuya da azabar Alhaji kalle da ta addabi rayuwarta,Ana hakan tasamu wani ciki!"Babu yadda Alhajin baiso azubar da shi ba!"Amma Asmau ta hana saboda tasan irin ciwon da takeji alokacin da take barin da Allah ya kawo da kansa,Bare na likitoci...Dalilin kafiyarsa yasa Alhaji dukanta!"Tare da juya mata baya!Gashi batada halin zuwa gida yaji!domin Baba malam dukan kawo yuka yake mata!"Kwanaki da taje yaji yayi rantsuwa duk tadawo bakin auren lami da yusuf(Iyayenta)Shiyasa take hakuri kullum cikin kuka!"Ga rainon ciki ga hawan jini da ciwon zuciya!"Da ke damunta,babu wata kulawa tsakaninta da Alh.kalle su sahura da uwani ne ke taimakonta."Tuni Alh.kalle yafara kokarin neman aure na hudu banda tasko da wulaqanchi babu abinda matansa ke fuskanta."
"Najibullah da Yaseera sun gina rayuwarsu abisa gaskiya da amana,duk a dalilin yiwa iyayen su biyayya."Shirye shiryen auren su