Showing 1 words to 3000 words out of 25209 words
Chapter 1 - RAYUWAR MAKARANTA FREE BOOK BY ZAHRA ROYAL.txt
*RAYUWAR MAKARANTA*
*© Zahra Royal Star*
THRILLER
*K'AUYEN RIMAYE, GOVERNMENT SECONDARY SCHOOL RIMAYE KATSINA STATES NIGERIA.*
"Hauwa! na ce ki duk'a k'asa ko?"
Kallonsa ta d'anyi tana tab'e baki cike da jin tsanar Mlm Aliyun, tabi shi da harara k'asa-k'asa.
A hankali tayi k'asa, tasa gwaiwowinta a k'asan.
Muryarsa cike da b'acin rai ya kai dubansa ga D'alibansa y'an mata dake wajan, K'awayen Hauwa ya ce "kuma ku duk'a k'asa marassa jin kawaii"
K'unk'uni suka kama yi kamar baza su duk'a ba, sai kuma suka kai kasa kamar yacce Hauwa tayi, sun kai su had'u.
Ya dube su yana d'aga wata y'ar k'aramar waya dake rik'e a hannunsa.
Kamin a hankali ya ce "wacece mai wayar nan a cikinku?, wato an hana zuwa da kowacce waya, amma tsabar bakwai jin magana shine aka kama ke Hauwa da ita kina jin wak'a Mlm na cikin aji?, an tabbayeki kin ce wai ba taki ba ce, ta uban wacece to?".
Murgud'a baki Hauwa tayi kanta a k'asa tana jin zuciyarta na bak'i tsabar yadda sauran Malamai ke binsu da kallo wa'inda ke cikin Office d'in.
A hankali kamar bata son magana ta ce "eh Mlm ba tawa ba ce ta wata Aunty na ce, ta ban ajiya"
Zai sake magana Malama Rahma ta shigo Office d'in.
Kamar kullum taci uban gayu na kece raini sai k'amshi ke tashi a jikinta, wani matsiyacin leshi tasa wadda yaji d'inkin gayu mai tsadar gaske, ta yafa wani mayafi wadda yayi dai-dai da kalar leshin.
A hankali take taku dai-dai tana wata yanga kai kace bata son taka k'asa ne.
Gaba d'aya Malaman dake a wajan, sai kallo ya koma kanta bakinsu kamar zai tsage, kowa sai binta yake da sannu da zuwa, Kai ka ce zata raba masu Lada ne idan sunce sannu d'in.
Itama cike da yanga take amsawa tana washe baki.
Su Hauwa dake d'uke a k'asa wani kalar kallo na tsana suke bin Mlm Rahma dashi, kai daka kalli yanayin irin kallon da suke jefa mata zaka san na tsantsar tsana ne.
Zama Mlm Rahma tayi akan wani table tana ba wasu al'majirai umarnin cewa.
"Kuje ku shigo da kululin nan gaba d'aya please, sai ku aje su a inda ya dace"
Amsawa sukai suka juya.
Mlm Aliyu dake ta jefanta da murmushi ya ce
"Ohh Hajiya yauma abincin akayo mana, ai kina taimakon mu da kike mana abincin saidawar nan, dama sai mun fita cikin gari muke samu muci"
Murmushi ta sakar masa wadda yaji kamar ya tashi ya taka rawa tsabar farin ciki.
Ta ce "kai kam Mlm Aliyu kullum saika mai-maita wannan maganar, ai shi yasa domin ku nake yi, harma da d'aliban wadda yaji zai iya saya"
Tab'e baki Hauwa tayi, ta tsaki wani tsaki wadda yajawo hankali jama'ar wajan.
"Wannan sakarkarun miye suke a nan kuma?"
Mlm Rahma ta fad'a tana nuna su Hauwa.
Hauwa ta had'e wani miyau ji take kamar ta shak'o wuyan Mlm Rahma.
"Wallahi fa wai waya ce suka zo da ita shine na taho dasu nan"
Cewar Mlm Aliyu.
Kallon banza ta jefa ma su Hauwa tana sake cewa "to miye kuke jira dasu ku amshe wayar mana ku yanke masu hukunci dai-dai da abunda suka aikata. Wai tsayama wayar wace a cikinsu a nan?"
Mlm Aliyu ya ce "waifa duk abun nan wayar y'ar uwar Hauwa ce ta bata ita wai, kinji shashanci tana babba"
"Ohhhoo wannan yarinyar wai wacce ke SS3"
Mlm Rahma ta tabbaya Kai tsaye.
Mlm Saminu dake kusa da ita shima ya hamshe da cewa
"Kware fa ita ce, ai nasan yarinyar ba ita ce wacce kullum take tara maza a bakin wonder kujerar da take zama, but idan aure take so ke kece ayi mata mana, tazo tana tara mana Maza bata da aiki sai haka"
Wani tuk'uk'in bak'in ciki ne ya turnuk'e Hauwa kallon Mlm Saminu take, yauce ta k'ara jin tsanar wani Mlm bayan Mlm Aliyu da Mlm Rahma.
Can suka ji muryar Mlm Rahma na cewa "to sakarci kenan ma, idan son maza zatai danmi yasa ta fara karatu, su sanar da iyayanta aure take so mana"
Kamin su sake magana Hauwa tsabar b'acin rai ta kalli Mlm Aliyu tana k'ok'arin magana ya rigata da cewa.
"Zaku iya tashi kuje sai wayar nan tayi sati kamin na baku ita. Wai ku bakwai jin wahalar rik'e k'aramar waya ne?".
Banza Hauwa tayi masa tana tashi harta juya baya kawai taji muryar Mlm Rahma akanta.
"Kee tsaya na ce"
Juyowa gaba d'aya Hauwa tayi tana duban Mlm Rahma data taso inda suke.
Kallonta tayi kallo irin na rainin wayo da wulakanci kamin ta ce
"Kee ban hana yo acuci Maza a school d'in nan ba?".
Hauwa kallon takaici take bin Mlm Rahma dashi, kamin a hankali ta kai hannunta ta tab'a k'eyarta dake d'aure da gashi babu abunda tasa ta d'aure shi bare tayi acuci Maza dashi, tsabar gashin ne kawai tasa ta nannad'e shine sai ya bada kamar tayi acuci Maza.
Ganin rainin wayon yarinyar yayi yawa Mlm Rahma zatai magana rai a b'ace Hauwa ta rigata cewa
"Ni ai ba acuci Maza nayi ba"
Tana gama fad'ar haka zata juya domin barin wajan taji Mlm Rahma ta kamo mata Hijab, da k'arfi har Hijabin na shak'e mata wuya.
Dawowa baya tayi taga-taga kamar zata fad'i Mlm Rahma na cewa
"Keee dan Ubanki har ni zanyi magana ban gama ba ki wani juya ki tafi?, tsabar dama kun raina mutane. Ki cire acucin nan na ce idan ba haka ba kuma inci Ubanki a nan wajan hmmmmm"
Ko ci kanki Hauwa bata ce ba, kawai ta tsaya ne tana kallonta, Mlm Rahma kuma har yanzu tana rik'e da bak'in Hijabinta.
Ganin yarinyar fa y'ar rainin wayo ce ta gidan gaba, yasa Mlm Rahma cike da son yarfa ta da son ci mata mutumci kawai Hauwa batai tsammani ba batai zato ba taji an jawo mata Hijab da mugun k'arfi wadda yasa gaba d'aya Hijab d'in daga kanta ta zame. Gashin kanta ne ya bayyana ta yadda mutanan dake wajan suka zaro ido waje, hatta su Atu K'awayen Hauwa ido suka zaro suna bin Uban gashin Hauwa da kallo, domin duk abotarsu basu tab'a ganin gashin Hauwa a waje ba sai yau. Tsananin yawansa harya zarce yadda basa zato, gashin kan nata har sai da ya sakko k'unk'uminta, yana niyar tab'o mazaunanta, gashi bak'ik'k'irin ga sulb'i kamar irin na k'asar Indiar nan.
Wani kalar Mayan kallo Malaman dake wajan suke bin Hauwa dashi.
Ita ko Mlm Rahma cike da tsananin hassada dajin haushi, inama ace batai haka ba, gashi duk taja hankalin Malamai sun koma akan y'ar k'ank'anuwar yarinya, ga wata irin tsanar yarinyar daya k'ara cika mata zuciya, bata tab'a tunanin haka zata gani a gashin nata ba, ai tayi zaton bai wuce iya k'eyarta ba, tayi mata hakan ne domin ayi mata dariya kuma ta yarfu a gaban samarin Malaman dake a cikin Office d'in.
Ita ko Hauwa kallon Mlm Rahma take cike jin haushi tsantsarsa, sai wani murmushin gefen baki data sakarma Mlm Rahma wadda ta gansa Kuma ta shak'a.
Tsabar ta k'ara jan hankalin Malaman Hauwa ta wani juya gashin har tashi sama yake fuskarta ta k'ara fitowa kyakykyawa da ita dama gata da hasken fata irin hasken nan na Fulanin asali. Tasa hannunta ta d'aure gashin nata ta maida abunta cikin Hijab, k'asa-k'asa yadda Mlm Rahma zataji ta take cewa.
"Uhum wani ko ya d'auka gashin kowama kamar nashi ne?, gashi kamar hamtar d'an iska.........
_____________________
RAYUWAR MAKARANTA. Hmm idan na ce rayuwar makaranta kowacce rayuwa akwai kalar nata k'alubalen, akwai darasi a rayuwar makaranta akwai rayuwar da ake gudanarwa a cikinta wacce baka tab'a mantawa rayuwace mai tsayawa a zuciya, labarin RAYUWAR MAKARANTA ya k'unshi b'angarori da dama, Malama da d'alibai na fuskartar k'alubale, shin wane irin k'alubale ne?, bare akace maka rayuwar secondry wacce d'alibai basu da y'ancin kansu, haka ma Malamai na fuskantar rashin kunya ga d'aliban, shin a tsakaninsu suwa keda laifi?, suwa ke janyo hakan?, ga Malaman ne?, ko ko d'aliban ne?, akwai shiga rai a wannan labarin. Bazance komai ba kai dai mai karantawa kawai ka biyo ni, kasan mai karatu bana rubuta labarin banza wadda baida fad'akarwa da shiga rai, masoya kune zaku bada shaidar Hakan.
Find out in RAYUWAR MAKARANTA (LOVE STORY).
RAYUWAR MAKARANTA zai fara zuwa maku a sabuwar shekara 2025 insha Allahu.
#Zahra Royal Star
#Bakatsiniya
#Rayuwar Makaranta
#Hauwa
#Atu
#Aunty Sa'adha
#Mlm Rahma
#Mlm Fiddausi
#Mlm Aliyu
#Mlm Bahari
#Mlm Muhammad
#Abdallah
*RAYUWAR MAKARANTA*
*©Zahra Royal Star*
*GOVERNMENT SECONDARY SCHOOL RIMAYE KATSINA STATES NIGERIA*
Page 1
A hankali take tafiya tana yi tana kallon shataletalen dogowar hanyar data mik'e wacce zata kaita zuwa school, da a yau zata fara zuwanta, tun bayan gama primarynta. A hankali ta saki wani k'aramin tsaki tana jin haushin Day d'in da aka sata, taso akaita boding school ba wai Day ba, gashi ba k'aramar tafiya suke sha ba kamin su iso school d'in, saboda tayi nesa daga cikin garin nasu, a can k'arshen gari kana gaf fita garin school d'in take. Da yawan d'alibai Maza da Mata wasu a k'asa suke zuwa, wasu kuwa akan Keke suke tahowa, wasu idan y'an gata ne har cikin mota ake kawo su, gashi duk tafiyar daka sha idan kazo k'arfe takwas ta gota, koda da ace da minti biyar tofa saika sha dukan makara.
Juyowa tayi jin an dafa ta ana cewa
"Hauwa please ki tak'o k'afa dan Allah, kinga na gabanmu har sunyi nisa, ina hangen wa'inda suke gaf shiga school d'in kamar sun had'a da d'an gudu, yanzu haka an fara bugun makara ne please musa k'afa muma ko mun isa, kin san bana son abunda zai tab'a min jiki bare duka"
Tsaki Hauwa ta kuma bugawa tana tab'e baki tana cewa
"Ke ni fa babu gudun da zanyi wallahi Atu, idan ke zaki iya to Bismillah, haka kawai nifa shi yasa nasu a kaini makarantar kwana wallahi ba wai wannan Day d'in banzar ba"
Ta idasa maganar had'e da sakin wani tsakin.
Kallonta Atu ta d'anyi tana tafiya da sauri har yanzu, tasa hannunta na dama ta kamo hannun Hauwar tana janta sosai yadda tafiyar taso zata zo d'aya domin taga Hauwa bafa saurin zatai ba, idan ta biye tata tofa yau sai sunsha jifgar makara.
"Da alama Hauwa har yanzu baki san micece makarantar kwana ba, ke miye ake a Day school, ai in gaya miki mugunta da bugu da komai ba na kalar azaba tofa tana Makarantar kwana, dan haka banga laifin Abbanki ba daya ce kinyi k'arama ma da kaiki Makarantar kwana, gara a nan idan yaso kika k'ara girma a sadda zamu kai SS 1 mun wuce Boding school d'in"
Murgud'a baki Hauwa tayi tana fisge hanunta tana cewa
"Kinga cika ni, ai gashi nan ma har sun fara Taran makarar, kuma tunda na shigo Day d'in nan kin san Allah bazanyi wata Boding school ba kuma.....
"Innallihi, Hauwa mun shiga uku, kinga dukan da suke yi kuwa, ki gani wayyo Allah"
Atu ta katse maganar da Hauwa keyi mata, had'e da nuna mata yadda suke dukan d'alibai duk wadda ya k'araso yanzu.
Tsaki Hauwa tayi tana kallon dai-dai bakin inda ake taran makarar, ga Siniyoyi nan manyan school d'in y'an SS3 suna tare duk wadda ya shigo yanzu bugu suke na Innallihi, ba tausayawa, wasu an sasu tsallan kwad'i wasu shara suke a house d'insu. School d'in ta cika tayi maki's amma duk da haka idan ka waiga baya wasu ne ke k'ara tahowa, idan ka dubesu da yawa hankalisu a tashe yake, bare sabbin zuwa, wa'inda suka giga kuwa irin y'an SS2 haka ko a jikinsu, domin ana bugunsu suke tashi su kakkab'e jikinsu, su tafi wasu harda tsakin tsaki.
Atu ta kalli Hauwa tana had'iyar miyau tana cewa
"Kefa dama ba tsoron bulala kike ba, duk ke kika ja min, Allah daga yau bazan sake jiranki ba, tahowa ta zan rink'a yi, yanzu gashi kinja mana, ni gaskiya sai dai nayi tsallan kwad'o bazan bari a duke ni ba, ko kuma a sani wankin toilet"
Ta idasa maganar tana zare ido saboda sun kusa k'araso inda ake bugun makarar, ganin yadda suke hantarar d'alibai had'e da mugun dukan da suke ma Yara, gyeza ce suke sawa mai kauri ga tsawo suke bugun da ita, nanfa hankalin Atu ya sake tashi.
Tana gani da Siniyoyi y'an SS3 sun iso koda sun makara wuce kawai suke abunsu, wani ma a nan zai tsaya ya amshi bulala ayi taran makarar dashi.
Hauwa ta dubi Atu tana cewa
"Allah ya kiyaye ni da wankin toilet daga zuwa na school d'in nan, kin san babu abunda zai hana aljanu shiga jikinka idan kana zuwa toilet d'in makaranta, garama kiyi shara ko su bige ki, amma karki sake a saki wankin toilet ko a saki tsallan kwad'o na gaya miki, tunda ke matsoraciya ce, daki tsaya ayi miki bulalar tafi "
Hauwa ta idasa maganar tana k'arasawa dai-dai inda wani Siniyo yake yana bugun wasu, ana gama masu ta duk'a ya fara zafga mata bulala, wani bugu daya kai mata saida da runtse idonta da k'arfi saboda taji bugun har tsakiyar bayanta.
Yana gama mata ta tashi idonta sunyi jawur ji take kamar ta shak'e masa wuya shi kam bai ma san tana yi ba, jifgar wasu kawai yake idonsa a rufe.
Tashi kawai Hauwa tayi tana kallon Atu da aka sasu tsallan kwad'o abunda take mata gudu kenan.
Wani dogon tsaki ta ja wadda yasa wata y'ar SS3 ta juyo tana dubanta, a wulakanci take kallonta tana cewa
"Kee tsaya"
Tsayawa Hauwa tayi gabanta na d'an fad'uwa.
Dakewa tayi tana kallonta itama, ganin irin duban da take mata
Can ta ce
"Ubanwa kike ma tsaki a nan wajan dan Ubanki?"
Wani abu mai d'aci Hauwa ta had'i a mak'oshinta jin yadda ta zagar mata uba cikin isgilanci Kuma"
Saukar maganarta ta k'ara ji tana sake cewa
"Ba magana nake miki ba, kun raina mutane ke y'ar k'arama dake duka ba yau ne kuka baro primary ba, to bari kiji na gaya miki a nan ba'a mana haka, uban mutum zamuci wallahi, dan har yanzu yarintar primary bata sake ku ba, duk'a na ce dan Ubanki"
Kowa na wajan kallonsu yake amma babu wadda yayi gigin mata magana, a yadda take zagin Hauwa son ranta.
Hatta Malamai suna zuwa su wuce amma ko a jikinsu daga ganin alama ma suke ba Siniyas d'in Okay d'in cin uban yaro ko waye shi.
Tana k'arasowa gaban Hauwa ta amshi bulala ta fara jifgar Hauwa baji ba gani dan har hijab d'in Hauwa na dagewa sama amma haka ta rink'a bugunta kamar ta sami Jaka.
Sai da wata K'awarta tazo ta amshe bulalar dake hannunta tana cewa
"Haba Lamratu ki barta haka mana, kefa muguwa ce dama wallahi, yara da yawa suna kuka dake idan kika kamasu bakya masu ta sauk'i"
Tsaki Lamratu ta saki tana hararar Hauwa dake d'uke a k'asa tana mata kallon banza.
Ta ce "dalla can tashi ki bar nan wajan, karki sake wani laifi yasa mu k'ara gamo da ke shashanci banza kawai"
Tashi Hauwa tayi idonta sunyi ja sai jan ajiyar zuciya take tana k'ara tausar zuciyarta, da zata biye ta zuciyarta da yanzu wata maganar ake ba wannan ba.
A hankali Lamratu ta juyo wajan Hindatu tana d'an harararta tana cewa
"Kefa shi yasa ba'a son zuwa dake wajan taran makarar nan, miye haka yanzu Fisbilillahi? Karfa kisa Yara su fara raina ni wallahi, domin zaki sa na tsani yaro yayita shan jifgar banza a waje na wallahi, idan bazaki iya gani ba ki zaman ki a class mana please"
Dariya kawai Hindatu ta saki tana cewa
"Kin manta da acan nake zaune kece kika taso ne dole saina raka ki kinyi bugun makara, haka kawai Allah kuna bani haushi wannan muguntar da kuke ma yaran mutane, ku guji ranar da iyayan Yara zasu kawo k'arar ku wallahi"
"Ahaye, yo ai da alama kin manta irin buguwar da mukasha muma ko?, har kin manta irin iftila'in rayuwar da muka shiga a school d'in nan, ai yanzu ma ana masu da sauk'i wallahi, ai yanzu banza suke sha, yo a lokacin mu mun ma isa na gaba da kai yana magana ka kalli tsakiyar idonsa, ranar baka ci ubanka ba harda ma uwar. To dan haka kinga ki barmu muma mu bigi banza dan wallahi saina rama abunda akai mana, duk da nasan bazamu tab'a rama irin abunda akai mana ba, sai dai mu kwatan ta kawai"
Dariya kawai Hindatu tayi tana samun waje ta zauna akan wani dutse tana kallon yadda ake dukan Yara.
"Washhh Allah na wayyo na k'afata"
Cewar Atu tana zama d'aya daga cikin kujerun class d'in nasu bayan an gama aikatuwa an shigo aji, d'alibai sai shigowa suke suna zamun kujerunsu suna zama kamin kuma Malami ya shigo.
D'an matsawa Hauwa tayi har yanzu ranta babu dad'i akan abunda akai masu d'azo ta ce
"Ga waje nan ki zauna na zab'ar mana gaba-gaba bana son zama baya kin sani"
D'an yamutse fuska tayi da kyar ta zauna tana dafe cinyoyinta tana cewa
"Gaskiya dole mu sake waje bana son zama a gaba kin sani nima, saboda komai za'a fara damu za'a fara, ni kuma gaskiya bana so, kina ganin yadda y'an SS3 nan suke bafa mutumci suka cika ba, har cikin aji suke bi su bigi mutum son ransu ko Malami idan anyi masa laifi ya fara daga ta kanmu to bazata sab'o ba gaskiya ki duba magana ta"
"Eh kuma Atu kina da gaskiya fa, tashi mu koma na bayan k'arshe. Amma ma wai miye kiketa yatsine baki kina tafiya a tale da kyar?"
"Hmmm wai kin manta tsallan kwad'o aka sani a wajan taran makara ne?, to shine jikina kemin ciwo fa"
Tashi sukai a tare suna tafiya bayan class d'in domin samun wani wajan zaman, suna tafe Hauwa na tikar dariya tana cewa
"Sai da na gaya miki karki sake a saki tsallan kwad'o, ai gashi nan tukunna ma yarinya saima gobe jikinki yayi tsami Allah ma yasa ki iya tashi goben"
Dai-dai sun iso kujerar baya ta ukun k'arshe suka tsaya, suna duban wasu y'an Yara wa'inda basu kai su ba sun kama kujerar mutum uku ne ko wacce kujera.
Atu ta kalle su tana cewa
"Kai ku tashi daga nan kuje ga wata can ku zauna, daga yau ta zama tamu wannan kujerar"
Wata y'ar figaggiyar yarinyar idonta a tsaye yake ta tashi tana rik'e k'ugunta tana kallon su Hauwa tana cewa
"Tabd'i jam, kamar ya mu tashi mu baku waje?, wannan ai mugunta ce da son kai, mune