Showing 6001 words to 9000 words out of 24835 words

Chapter 3 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

6002

ce kawai ya bar shi za ta sayi maganin zazzaɓin, suka yi sallama, saboda ba ya son jan magana.


Suna gama wayar ta tuna jiya Alhaji ya ce da kuɗi a ledar nan da ya ba ta, sai ta ɗakko ta dudduba, ba ta ga alamar kuɗi ba, sai ta raya ko mantawa ya yi bai saka ba, ta san halin gidansu da sata, amma yanzun ba ta kawo wata ce ta ɗauka ba, to idan ma ɗaukar aka yi, ita yanzu ba ta su take yi ba, ta koma ta kwanta.




Wajen azhar tana zaune tana cin abincin da ƙanwar Mama ta kawo mata, sai ga Isa ya zo da leda har da ruwa wai zai saka mata, Baba yana ƙofar gida Isa ya gaishe su, ya shige, don haka ya biyo bayansa, daidai sanda Nuratu ta fito tsakar gida.


Baba ya ce"Kai yaro lafiya wajen wa ka zo?"


Ya ce"Baba aiko ni aka yi zan duba Nuratu".


Baba ya ce"Ikon Allah! Kai kuwa yaro wane hamshaƙin ne ya aiko ka?"


Ya ce"Abdul ne saurayinta".


Baba ya ce"Ka ce dai tsohon saurayinta, to wuce ba ta buƙata, sannan ka faɗa masa kar ma ya sake asarar kuɗinsa a kan matar da ba ta shi ba, ni na riga na ba da ƴata ga wanda ya dace, lokaci kawai muke jira, ba don mutuwar nan ba ma, da a cikin satin nan za a tsayar da rana".


"Ok" Isa ya faɗa yana juyawa ya fice daga gidan.


Nuratu da duk ranta ya gama ɓaci, ta ce"Haba Baba..."


Ya ce"Buhun ubanki! Ba ki da lafiya shi ne ba ki faɗa mini ba? Duk duniya yanzu kina da wanda ya fi ni ne?"


Ya ja tsaki, ya ciro waya, ya yi danne-danne ya kara a kunne, can ya washe baki ya ce"Wa alaikumus sallam, Alhaji ina kwana?"


Alhaji dake zaune tare da matarsa tana zuba masa abinci ya amsa da"Lafiya lau Baba, ya ƙarin haƙuri?"


Baba ya ce"Da godiya. Wallahi Alhaji dama mutumiyar taka ce dama babu lafiya, wallahi zazzaɓi jiya ba mu yi bacci ba, shi ne na ce to bari a sanar maka..."


Alhaji ya ce"Subhanallah! Bari yanzu zan aiko sai a ɗauke ta a kai ta asibiti".


Daga nan sai Baba ya dinga jera godiya, har yana rusunawa kamar yana gabansa.


Ya kalli Nuratu ya ce"Tafi ki shirya, zai aiko a kai ki asibiti yanzu, ai ke dai Allah Ya dubi maraicinki da ya kawo miki wannan bawan Allah mai karamci".


Nuratu da ta shiga tashin hankali, ta marairaice ta ce"Baba ɗan zazzaɓi ne fa, ni ba sai mun je asibiti ba".


Baba ya ce"Ai ke shashasha ce, har ki samu mau jiɓantar lamarinki amma ki tsaya shashanci, maza shirya".


Ta shiga ɗaki, ta zauna, sai ta fara hawaye, ta san manyan asibitocin nan da ƙirƙire-ƙirƙire, tsoronta ɗaya kar a ce za a yi mata wani gwajin da zai fallasa sirrinta.


Babu jimawa Baba ya shigo ya ce ta fito su tafi, yayarta Rahma ƴar Mama Karime tana tsakar gida Baba ya ce"Ke Ramatu wuce ki raka su".


Har da saurinta ta sako hijjabi, suka fita, Nuratu tana jin kamar ta ce ba za ta je ba.


Har da buɗe mata murfin motar, ta shiga ya ja suka ɗauki hanya. Dab da asibitin ta ga wani babban chamest, ta ce"Bawan Allah kawai ka tsaya ka siya mini magani a nan, ba dole sai an je asibiti ba".


Ya ɗan yi jim, sannan ya ce"To Hajiya ai ni umarni nake bi, sai dai na tambayi Alhajin, duk yadda ya ce".


Ta ce"To ka faɗa masa jikin da sauƙi sosai, magani ma ya isa".


Ya faka motar, ya ɗakko waya ya kira Alhaji, ya yi masa bayanin da Nuratu ta yi, Alhaji ya ce kawai ya wuce su tafi asibiti, idan ma maganin ne su ba ta a can".


Ba ta sake cewa komai ba, har suka ƙarasa asibitin. Tun kafin zu je Alhaji ya yi magana da likita, don haka kai tsaye direban ya rakata inda ya kwatanta masa, ta zauna a kujera sai raba ido take yi, hannunta yana dafe da mararta ta cikin hijjabi, gani take kamar likitan yana kallonta zai gane tana da cikin. Ya tambaye ta me yake damunta? Ta ce"Zazzaɓi ne kawai kuma ya riga ma ya sauka tun a hanya".


Ya ce"Ma sha Allah! Amma Alhaji ya ce ko abinci ba kya ci, ya ce a saka miki ruwa saboda ki samu ƙarfin jikinki, sannan zazzaɓin ƙila malaria ce, za mu yi miki gwaji mu gani".


Ƙirjinta yana ta dukan uku-uku ta ce"Likita, ni fa ina jin ƙarfin jikina, kawai ku ba ni magani ya isa".


Likita ya yi murmushi, don ya sabada mara lafiya mai gardama, ya ce"Ki yi haƙuri Hajiya, a yi miki yadda ya dace kawai".


Ya tura su wani ɗakin, wajen wata nurse, ita ta ɗibi jininta, sannan aka saka mata ruwa ta kwanta gabanta yana ta faɗuwa, tana ayyana ƙila yau ce ranar ƙarshe cikin ranakun farincikinta na gidan duniya.


A ɓangaren likita bayan sun fita sai ga kiran Hajiya Laila, uwar gidan Alhaji, suka gaisa ta ce"Doctor yarinyar da aka kawo daga wajenmu me yake damunta?"


Ya ce"Yanzu dai za a duba, zazzaɓi ne take yi, sai rashin ƙarfin jiki, an tafi saka mata ruwa".


Ta ce"Ok, don Allah kar ka bari ta tafi, sai ka samu adireshinta ko lambar waya, ka ajiye mini account deteils ɗinka".


Ya ce"An gama Hajiya godiya nake". Suka ajiye waya.




08028966015
[11/20, 9:35 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY




PAGE 4




Sakamako yana fitowa likitan Hajiya Kubra ya fara kira, ya sanar mata yarinyar ciki ne da ita na sati tara, sai kuma malaria. Hajiyar ta yi murmushi ta ce"Idan ka tashi sanar masa ka ƙara da cewar tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki". Likita ya amsa, amma a zuciyarsa yana ta auna yiwuwar hakan, domin babban laifi ne, har a cikin aikinsu, sannan yana gudun Alhaji ya bincika ya gane ba haka ba ne.


Har allurar bacci Alhaji ya sa aka yi mata, don ta samu hutu, ba ta san tsayin lokacin da ta ɗauka tana bacci ba, ta dai farka ne kawai ta ga Mama Karime zaune a kan sallaya, gefen gadon da take kwance, gabanta ya faɗi, ta tashi zaune, har an cire ƙarin ruwan, Mama Karime ta ce"Sannu Nuratu kin tashi?"


Sai ta kasa amsawa, kallonta dai take yi, tana son karantar fuskarta, don ta samu wani haske a kan zargin da take yi na fallasar sirrinta, sai dai ba ta ga komai a fuskar Mama ba, ta ce"Mama ba su sallame ni ba?"


Ta taɓe baki ta ce"Jira suke ki tashi, amma ke wannan gadon asibitin ai a yanzu sai ya fi yi miki daɗi fiye da gidanku".


Gabanta ya faɗi, tana rabon ido ta ce"Mama saboda me?"


Ta ce"Saboda cikin jikinki, da ƙyar aka fitar da babanki daga asibitin nan, don cewa ya yi sai ya kashe ki, da tuni sai dai ki farka ki ji ana man Rabbuka?"


Bugun zuciyarta ya tsananta, tuni tsoro ya dirar mata, ba ta sake shiga tashin hankali ba sai da Mama ta cigaba da faɗin"Babban abun damuwar ma asirinki ya tonu, don na san zuwa yanzu maganar nan ta fantsama cikin gari, tun da a gaban Zainabu aka yi komai".


"Innalillahi! Me ya kawo ta?" Ta tambaya tana sakin kuka.


Mama ta ce"Ta je gida kai miki abinci, aka faɗa mata kina asibiti, dama lokacin babanku ya ce gado aka ba ki, na ce ya kamata na bi ki, shi ne ta ce mu tafi tare, shigowarmu ke da wuya, muka samu ana kokowa da babanki. Nuratu kin ba mu mamaki, ba ki kyautawa Salamatu ba". Ta ƙarasa a raunane.


Ta kifa kai a cinyarta ta rushe da kuka, shikenan asirinta ya tonu, abin da take ta ɓoyewa yau ya fito fili, tunani take yi yanzu ya za ta yi? Wane bayanin za ta yi musu su fahimce ta? Da wane idon za ta kalli Abdul? Sannan idan ta faɗa masa dalilita zai yi mata uzuri kuwa?"


"Ina wayata?" Ta tambayi Mama.


Ta ɗakko ta miƙa mata, ta danna ta ga ƙarfe takwas da rabi na dare, ta sakko daga gadon, ta shiga banɗaki ta yo alwala, ta fara jero salloli, lafin ta idar Mama ta zuba mata abinci, ta miƙa mata tana cewa"Wannan abincin duk Alhaji ne ya aiko miki, wallahi Nuratu kin yi asarar miji kamar shi, don kuwa shi ma zuwa yanzu ya samu labari, ai da mutunci ma, idan wani ne na tabbata korar kare zai sa a yi mana daga asibitin".


Nuratu ta fara cin abincin a hankali, tana hawaye.


Mama ta cigaba"Idan kuma Allah Ya tarfa wa garinmu nono sai ki ga duk da hakan bai janye ba, tun da wasu suna sane ma suke auren karuwa, saboda huce takaici ta wani ɓangaren".


Sosai surutun Mama ya dame ta, saboda tana ruguza mata lissafin da take yi ta tafkawa a zuciyarta. Fatanta dai a ce yau a asibitin za ta kwana, indai lissafin da ta yi yanzu ya tafi daidai, to a tasha za ta kwana, washegari ta bar garin.


Ƙarfe tara da ƴan mintuna, sai ga direban ɗazu da ya kawo su, ya shigo ya ce"Hajiya za mu tafi, in ji Alhaji".


Nuratu ta ce"Sun sallame ni?"


Ya ce"E". Ya kwashi kanukan abinci ya wuce gaba.


Mama ta ce"Sai ki tashi mu wuce, ƙiyamarki ta tsaya cak yau".


Wani sabon kuka ya zo mata, duk nuƙu-nuƙun da ta tsaya yi don Mama ta yi gaba, abun bai yiwu ba, haka ta saka ta a gaba suka shiga mota, a ciki suka tarar da Alhaji Hashimu, sai kunyar duniya ta rufe Nuratu, duk da ba son shi take yi ba, amma ba ta so a ce zai yi mata kallon mara tarbiyya ba, haka motar ta yi tsit har suka ƙarasa gidan.


Baba da abokansa biyu suna zaune a ƙofar gidan, ya taso da sauri ganin motar Alhajin, sai dai Nuratu tana fitowa ya gimtse fuska, yana huci.


Wani mugun haushinta yake ji, gabaɗaya ta canza masa lissafi. Suka shiga daga ciki, a zaune Alhaji ya ce su tsaya, Nuratu za ta wuce ya ce ita ma ta tsaya, ta dawo ta tsugunna kanta a ƙasa tana hawaye.


Baba ya ce"Don Allah Alhaji ka yi haƙuri, wallahi da na san da wannan badaƙalar a jikinta da ban yi maka alƙawari ba, ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba!".


Alhaji ya ce"Na sani, kuma a yadda na samu labarin tarbiyyar Nuratu na san wannan ƙaddara ce, kar ku damu, ni tsakani da Allah nake son yarinyar nan, musamman yanzu da wannan ƙaddarar ta faru da ita, na san rayuwarta za ta iya shiga garari, saboda Baba ni na ji na gani, zan aure ta na kau da ido a kan komai, da an cire cikin shikenan".


Baba ya fara jero godiya har da kukansa, Alhaji yana cewa "Babu komai".


Sannan ya yi wa Nuratu nasiha sosai, tamkar tsakanin uba da ƴarsa, har ta ji a ranta wannan mutumin ƴaƴansa sun yi sa'ar uba, ba kamar ita ba, ya ƙara da roƙon Baba kan kar ya ce zai dake ta, ko wani hukunci, addu'a ita ce kaɗai mafita, daga haka ya tafi, ita ma ta shiga gida, ta saka sakata a ɗaki, duk bugun da Baba ya yi ba ta buɗe masa ba.


Ba ta taɓa zaton mutumin nan zai ce zai aure ta a hakan ba, ta san auren nasa rufin asirinta ne, amma ya za ta yi da soyayyar Abdul ɗinta? Sai ta ɗakko wayarta, ta yi masa sallama ta whatsApp, yana online bai duba ba har tsawon mintuna, sai ta danna voice, sai dai ta kasa cewa komai, har tsawon sakan goma, sai ta sake shi a hakan ya tafi, wannan karon da wuri ya duba, bai ce mata komai ba, ta ajiye wayar ta kwanta.


Can tsakar dare kuma ta tashi ta fara haɗa kayanta a wata tsohuwar akwatin Mama, wanda ta bar mata ita, kayanta ne dama a ciki, ta saka komai ta ajiye ta tsaf, sam ba ta runtsa ba, kiran sallar farko a kunnenta, ta fito a hankali, tana jan akwati ta fice daga gidan a hankali, ta karo ƙofar, ta fara sauri don gudun wani ya biyo bayanta, tafiya mai nisa ta kai ta tasha, ta tarar da tsirarun mutane, ta zauna ta fara hawaye tana fatan Allah Ya sa a karɓe ta a inda za ta je, sannan ta samu buta, ta yi alwala ta yi sallar asuba wanda har an kusa idarwa. Ta faɗawa kwandasta Kaduna za ta je, aka saka ta a motar, ta yi zaune tana jira ta cika, zuciyarta tana ta dukan uku-uku. A daidai lokacin ne kuma Mama Asabe ta leƙa ɗakinta, ta ga ba ta nan, nan ta hau cikiya a tsakar gida, kowa ya fito ana jajantawa.




********


Misalin ƙarfe goma Nura ya kira Hasana a waya, tana ɗagawa ya ce"Ke maza ki buɗe wannan ɗakin ki share shi tass! Gani nan zuwa".


Ta san dai ɗakuna uku ne a gidan, ciki da falon da take ciki, sai kuma falle ɗaya, wanda take saukar baƙinta, da kuma keken ɗinkinta a ciki, ta san shi yake nufi, amma hakan bai hana ta tambayarsa ba"Wane ɗakin?"


Ya ce"Wannan wace irin tambaya ce? Ɗayan ɗakin nan dai, da kike saka shirgi, ba na so na zo na tarar da komai a ciki".


Ta ce"To saboda me? Yanzu ina zan kai keken nawa?"


Ya ce"Wannan kuma ya rage naki, idan za ki kai shi bola zan taya ki". Ya kashe wayar.


Ta zauna tana mamakin me zai saka a cikin ɗakin? Ta san halinsa yanzu sai ya zo ya fara yi mata hayaniya, don haka ta tashi, ta fito da komai, ta share kamar yadda ya ce, ta janyo ƙofar ta koma ɗakinta, can anjima sai ga shi yana shigo da kaya, katifa ce madaidaiciya, da kayan kallo, har da ƙaramin firji, ta cika da mamaki, tana tsaye ya fara shiga da kayan yana ƴar waƙarsa, da alama yana cike da nishaɗi, ganin ko kallo ba ta ishe shi ba, sai ta shige ɗakinta, tana jira ya gama ta ji bayanin da zai yi mata. Ai kuwa yana gamawa ya ƙwala mata kira, ta fito tana amsawa, ya ce"Shigo mana".


Ta shiga tana ƙarewa ɗakin kallo, ya ce"To yanzu saurana sif, zan sa a yi mini sif mai biyu ƴar madaidaiciya haka, wacce zan zuba kayana a ciki, kin ga komai na zai zauna lafiya, idan zan fita na rufe ɗakina shikenan".


Da mamaki ta ce"Kamar ya ɗakinka? Au wai nan turaka ce ka ware kenan?"


Ya ce"Ai ya wuce wai, ni na gaji da yadda nake bacci rabi da rabi, yara su hana ni bacci su hana ni sakat, tsakar dare a farka a yi ta kuka, don haka na ware ɗakina".


Hasana ta ce"Baban Salim kenan! Kuma ban da abunka na ga dai yaran nan naka ne, sannan abu ba na farko ba, ba na biyu ba ai ya kamata zuwa yanzu a ce ka saba, kuma ma yanzu don ka yi hakan ai ba shi zai hana ka jin kukan Aiman ba, tun da dai ka san ba zan zo na kwana a nan na baro yaro ƙarami mai shan nono ba, dole da shi zan dinga tahowa".


Nan take fara'ar fuskarsa ta gushe, ya ce"Ki taho ina? Wai kina nufin saboda na ware ɗaki sai ki kwaso jiki ki biyo ni? Kenan ma na gudu ban tsira ba! A'a ba zai yiwu ba, ki yi zamanki da yara, ni duk sanda na buƙace ki zan kira ki, amma gaskiya ba don mu tare mu biyu na ware ɗakina ba".


Ta ce"To shikenan!" Ta juya ta fice, ranta bai so ba, sam ba za ta samu nutsuwa ba, saboda zarginsa da take yi ne zai ƙaru sosai, haka kawai ma tsakar dare farkawa take yi ta ga ba ya ɗakin, sai ta ji shi a tsakar gida yana waya, ko ta gan shi a falo yana vedio call, sai ya ganta ya yi tsaki, ya koma ya kwanta, to ina ga kuma ya ware ɗakinsa shi kaɗai? Tabbas zai ci karensa babu babbaka kenan, ta san ba ta isa ta ja da shi ba, amma kuma za ta yi iya yinta ta saka masa ido, don ganin bai kauce hanya ba, don haka ta ayyana bacci da ido ɗaya ya kama ta.


Haka ya wuni yana shige da fice, ya saita kayan kallo tsaf, dama akwai babbar setilait a tsakar gidan, tun da risibarsu ta lalace take ajiye kawai, bai kai musu gyara ba, yanzu sai ya sa aka saita da sabuwar risibar da ya siyo, firji ma nasu ya lalace bai kai gyaran ba, don ya ce ya gaji da gyarawa suna lalatawa, ita kuma a ganinta tsufa ya yi, tun da tun na aurenta ne, shekararsa takwas kenan.


Ya ɗakko yara daga makaranta, suna zaune suna cin abincin rana, yake cewa"Ma sha Allah! Ɗakina ya haɗu, yanzu mun yi magana da wani kafinta, zuwa jibi sif ɗina za ta zo, sai na samu ɗan kafet, na saka a tsakiyar ɗakin, ina ga ma sai na sayi senta tebur".


Hasana ko kallonsa ba ta yi ba, saboda takaici duk ya ishe ta.


Ya cigaba da cewa"Yadda tsarin gyaran ɗakin zai kasance, da safe idan na gama shiryawa, ina zaune ina karyawa, ke kuma sai ki shiga ki gyara, idan zan fita na rufe abuna, salun-alun karatun yankan jaki".


Har yanzu dai ba ta ce komai ba. Sai ya ajiye kofin hannunsa yana haɗe gira ya ce"Wai ni Hasana me kike nufi ne? Ya ina magana kina manna mini hauka? Ko hassada kike yi da ɗakin nawa?"


Ta ce"Hmm! A kan me zan yi maka hassada? Kawai dai gani na yi tsarin kamar bai yi ba, a ce kana da mata ita tana ɗakinta, kai kana naka, wai sai ranar da ka kira ta? Ka manta sai ka yi wata ba ka kira ni ba?"


Ya ce"To mene ne? Ke ba hutunki ba ne ba ma? Ki sake a ɗakinki, na sake a ɗakina".


Salim Ya ce"Abba wane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login