Showing 9001 words to 12000 words out of 24835 words

Chapter 4 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

6005

ɗakin?"


Gwab! Hasana ta buge bakin yaron, tana cewa"Ban hana ka saka mana baki a magana ba? Waye sa'anka a nan?"


Sai kuwa Nura ya hartsuƙo kamar zai dake ta, yana cewa"Kar ki sake ki ƙara dukan shi, saboda ya tambaye ni? Da ke yake? Ba ki iya komai ba sai shirme!".


Ya tashi yana ɗaukar mukullin babur ɗinsa ya fice zuwa tsakar gida, yana kiran Salim ɗin, ya je ya buɗe masa ɗakin suka shiga, sai da ta ga za su yi lattin islamiyya sannan ta leƙa tana cewa"Ku zo ku tafi makaranta".


Salim Ya noƙe kafaɗa yana cewa"Daddy ni yau ba sai na je ba".


Hasana ta ce"A kan me? Ai kuwa ya zama dole ka je!".


Nura ya ce"Ƙyale shi, ƙila ya gaji ne".


Ta juya ta koma ɗaki, tana jin sanda suka fita, ya siyo musu biskit ya dawo da su, tana zaune ranta a ɓace, saboda ta gaji da yadda yake ɗaurewa yaran akan rashin son karatun addini, ya ce"Ki biya musu karatun, tun da ba su samu zuwa ba".


Ko kallonsa ba ta yi ba, ya fice daga gidan. Ta ja kunnen yaron ta murɗe tana cewa"Idan ka girma za ka gane ba gata yake yi maka ba!".


Ƙarfe sha biyu na dare, Hasana ta kasa bacci, tana tunanin me Nura yake yi a halin yanzu? Ya yi bacci, ko yana ta waya da ƴan mata? Tunanin ya kasa barinta, don haka ta tashi, ta saka hijjabi, ta buɗe ƙofa a hankali ta fito, ta je daidai windon ɗakin ta leƙa, ta kuwa hango shi zaune ya yi ɗaiɗai a kan katifa, yana ta danna waya, wani abu ya zo ya dunƙule mata ƙirji, kamar ta buga masa ƙofar, sai kuma ta ga me ma za ta ce masa? Ta daɗe tana kallonsa ba tare da ya sani ba, sannan ta juya ta koma ɗaki, ta kwanta, sai ta ji ɗakin ma yau ya mata girma, gadon ya yi mata faɗi, duk da dama yawancin daren da bacci suke raya shi, amma duk ranar da ba ya nan tana jin babu daɗi.




08028966015
[11/20, 3:36 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee


PAGE 5




Washegari da safe Hasana ta gama haɗa abun karyawa, tana shirya yaran, Nura ya shigo yana cewa"Ki je ki gyara mini ɗakina".


Ta yi kamar ba ta ji shi ba, ya sake cewa"Hasana magana fa nake yi".


Ta ce"Ni fa wannan raba ɗakin ba lallai ya zama maslaha ga rayuwar aurenmu ba, saboda haka ya kamata a sake sabon tsari".


Ya tsaya yana kallon ta da mugun mamaki, ita kuwa da ba kallon shi take yi ba, ballantana ta lura da yanayinsa, ta cigaba da faɗin"A gaskiya sai dai ni ma na koma can ɗin, idan saboda Aiman ne, ni zan dinga yin shimfiɗata a ƙasan katifar mu kwanta".


Takaici ya ma hana shi tsayawa jayayya da ita, dogon tsaki kawai ya ja, ya ce"Allah Ya raba mu da jahilci".


Ta ce"Ni ce jahilar!?"


"Duk yadda kika ɗauka haka nake nufi!" Ya faɗa yana jan kwanon abincinsa.


Ta shige ɗaki ta yi zaune a bakin gado, ta rasa ta hanyar da za ta bi ta daƙile wannan sabuwar badaƙalar da yake son ƙullawa, sam ba ta yarda da shi ba, ta san bayan uzurin da ya kawo mata, dole yana da wata manufa ta raba ɗakin nan da ya yi.


Haka suka gama karyawa suka fita tare da yaran, ya kulle ɗakinsa yana mamakin sabon hali na raini da take son tsiro da shi a zaman nasu. Da azhar da ya ɗakko su daga makaranta, yana shigowa fuska a murtuke, ya ɗauki tsintsiya ya share ɗakin, sannan ya haɗa ruwan mopping, har ya fara zuciya ta ciyo shi, shaiɗan ya yi zuga, ya fito a fusace, tana cirewa yaran unifom ya ce"Ke Hasana wai me kike nufi ne? Ɗan iska kika mayar da ni ko yaya?"


Ta ce"Kamar ya?"


Ya ce"Ta ya za a ce ga ki a gida ni zan share ɗakina? Mene ne amfaninki!?"


Ta ce"Ka fi kowa sanin amfanina".


Ya ce"Ki je ki gyara mini ɗaki Malama, ku mata sam ba ku da tunani wallahi, ba dole ma mutum ya ƙara aure ba? Hmm Allah dai ya hore, zan huce takaici tabbas".


Hasana ta yi murmushin takaici ta ce"Ai wallahi ni na fi so ma ka ƙara auren, ta nan za ka san haƙurin da nake yi da kai".


Ya ce"Ki kwantar da hankalinki, ai in sha Allah aski ya zo gaban goshi, wallahi da wannan siyayyar da na yi, kuɗin aure zan kai, to kawai na fi so lissafin komai ya tafi daidai shiyasa na jinkirta, amma kar ki damu indai aure ne dole zan yi shi".


Ta ce"Allah Ya nuna mana".


Ya yi ƙwafa, ta fice ta shiga ɗakin, ta ga wayarsa a kan katifa, ta raya ƙila mantawa ya yi, ta yi saurin ɗauka, sai dai da pasaword kuma ba ta san mene ne ba, ta yi ƙwafa ta ajiye ta, ta gama gyara ɗakin ta fito.


Ta same shi a falo ta ce"Yanzu haka za mu dinga ganinka kai kana yin kallonka mu ko oho?"


Ya ce"Tun da haka kika zaɓa ba!Na gaji da kai gyaran kayan kallo wallahi".


Amir ya ce"Don Allah Daddy a gyara mana".


Salim ya ce"To ai sai mu dinga yi a ɗakin Daddyn".


Bai ce komai ba, ta kawo musu abincin rana suka fara ci, Nura ya yi kamar cokali uku ya taɓe baki ya ce"Abinci ma ba za a nutsu a yi shi ba, Allah Ya kyauta".


Hasana ta yi kamar ba ta ji shi ba, don ita ma ta san gishirin ya yi yawa, ta manta shaf ta zuba, dab da za ta gama girkin ta ƙara zubawa, don haka ba ta da ta cewa. Ya sake tsaki ya ce"Wannan abincin dai ci kar ka mutu kawai, an zabga wa mutane gishiri a abinci" Ya sake tsaki.


A fusace ya ce"Ina ta magana...!"


Ta ce"To me kake so na ce? Ku maza dama haka kuke, sai mace ta yi daidai sau dubu, ba za ku tabe ta ba, amma idan ta yi ba daidai ba sau ɗaya sai kun yi ƙorafi, hannuna ne ya kufce na saka da yawa".


Ya ce"Hmm! Gaskiya na yarda, duk wanda ya mutu da mace ɗaya shi ya ga ƙarshen wulaƙanci, gida biyu maganin gobara, Allah dai Ya kai damo ga harawa!".


Ba ta sake bi ta kansa ba, har ya gama ya fice.


Yau da daddare da wuri ya dawo, hakan ya sa Hasana ta raya a ranta ƙila yau ɗin ya kira ta, amma sai ta ji shiru, don ko leƙo su ma bai yi ba, tana jin lokacin da ya saka sakata a ɗakin, bayan ya gama uzururrukansa, kamar awa ɗaya a tsakani ta tashi ta sakko daga gadon, ta kalli agogo, sai yanzu goma ta yi, ta manta rabon da ya dawo gida kafin ƙarfe goma, sai dai idan ana tsananin sanyi, ko kuma da damuna. Ta saka hijjabi, ta fito a hankali kamar jiya, ta leƙa ta windo, ta ga ɗakin da hasken tv ga kuma sauti alamar ya kunna kallo, amma yana kwance a katifa waya kare a kunnensa ga murmushi shimfiɗe a fuskarsa, da alama yana cike da shauƙi, takaici ya rufe ta, duk abin da Nura yake yi mata na ɓacin rai, har yanzu tana ƙaunarsa, soyayya ce aka sha ta nuna wa sa'a kafin aurensu.


Ta gama yankewa a zuciyarta sai ta hana shi sukuni, don haka ta koma ta wajen ƙofar ta fara ƙwanƙwasawa. Nura da ya nutsa a kofin soyayya da wata wacce ya yi mata laƙabi da baba Leemat, sosai ya yi mamakin wannan bugun ƙofar, da ya dawo sai da ya duba ƙofar Hasana ya ga a rufe, kuma ya santa da baccin wuri, ya ce da baba Leemat yana zuwa, ya katse kiran yana haɗe gira ya ce"Wace?"


Ta ce"Ni ce".


Ya zo ta buɗe yana cewa"To ya aka yi, ni har na fara bacci ma?"


Za ta kutsa kai ciki, ya ɗan tare yana cewa"Wai mene ne?"


Ta ce"Akwai wani film da nake kallo a bollywod, shi ne na ce tun da akwai wuta ga ka, ka dawo da wuri bari na zo na ci albarkacin turakar Oga". Ta ƙarasa da murmushi.


Sai ya matsa ta shige ta zauna, ta canza tasha, amma gabaɗaya hankalinta yana kanshi, wayarsa tana ta kawo haske ya ƙi ɗauka, can dai ya tashi ya fice daga ɗakin, ya tura ƙofar ɗakinta a hankali ya shiga, ya haska ya ga Aiman ya baje yana ta baccin shi, ya ji fanka, ya kai hannu ya fara jijjiga shi, yaro kuwa ya fara mutsu-mutsu, sai ya tashe shi ya zaunar, ai kuwa ya fara ƙananun kuka, ya yi saurin ficewa daga ɗakin.


Ya koma nashi ɗakin yana cewa"Na ji kamar kukan Aiman".


Ita ma ta jiyo sama-sama, don haka ta tashi, ta ce"Bari na ɗakko shi".


Ya ce"Ina? Kin ga Malama ki yi kwanciyarki kawai, saboda ni ma bacci nake ji".


Tana fita ya mayar da sakata.



*********


Baba ransa ya kai maƙurar ɓaci, ya kai ya kawo a tsakar gida rungume da hannuwa a bayansa, ya ma kasa cewa komai. Can Mama Karime ta ce"Malam ba fa shiru za ka yi, kamata ya yi a bi sahunta tun kafin ta yi nisa".


Sai kuwa ya zaburo kamar mai jira, ya ce"To a gidan uban wa zan nemo ta? Ni dai na san abu ɗaya, yanzu Nuratu baƙinciki da hassada kawai take yi mini, wallahi saboda ta hango ɗan abin da zan samu a jikinta shiyasa ta yi mini haka, amma babu komai". Ya shige ɗakinsa.


Ita kuwa Nuratu motarsu tana harbawa titi, ita ma ta harba duniyar tunanin makomarta, sam ba ta hango haske a gobenta, ta san babu ta yadda za a yi Abdul ya karɓi uzurinta, fatanta ya yarda da ita ko da ba zai aure ta ba, ita ta yarda ta sadaukar da mutuncinta don farincikinsa. Sai dai idan bai aure ta ba, wa zai aure ta ya kalleta da mutunci? Gani take shi ma Alhaji Hashimu da ya yi alƙawarin aurenta ya yi maganga ne kawai a cikin mayen giyar so, bayan auren ba lallai ya riƙe ta da daraja ba, sannan yana da mata har uku da yaran da ba ta san adadinsu ba, ta tabbata wasu sun girme mata, yanzu ya za ta yi idan suka ji ta yi ciki a waje kafin auren? Anya gori zai bar ta ta zauna lafiya?


Da wannan tunane-tunanen fal zuciyarta aka ƙarasa Kaduna, kowa ya sauka, ta samu babur ya ƙarasa da ita unguwar da za ta je, sai da ta kai ƙofar gidan sannan ta fara fargaba, ta san dai wannan tafiyar ba gudu sunanta ba, don inda ta zo ɗin ba mafaka ba ce ba, kawai ta zo ne saboda ƙwaƙwalwarta ta samu hutu, kuma zuciyar Baba ta yi sanyi, don idan ya tashi yi mata hukunci ta samu sassauci. Ta kai hannu tana ƙwanƙwasa get ɗin gidan, sai da ta buga sau uku, sannan daga ciki aka tambaya waye, ta ɗaga murya ta ce"Ni ce".


Babu jimawa aka buɗe, wata mace ce wacce za ta kai shekara ashirin da bakwai ta buɗe, ta ɗan saki fuska ta ce"Nuratu" Tana kallon tsohuwar akwatinta.


Nuratu ma ta ɗan saki fuska ta ce"Anti Nawwara".


Ta matsa mata, ta shiga jaye da akwatin, Nawwarar ta yi gaba tana binta har zuwa falo, ta zauna, ita kuma ta ƙwala wa mijinta kira"Honey!".


Sai ga shi ya fito, yana gyara agogon hannunsa, ya yi turus ganin Nuratu, da mamaki ya ce"Nuratu, ke ce kuwa?"


Sai idonta ya kawo ruwa, ta ce"Ni ce, Yaya Kabir ina kwana".


Bai amsa gaisuwar ba, ya ce"Amma dai ba lafiya ba ko Nuratu?"


Nawwara ta ce"Ina fa lafiya? Ko sadakar ukun babarta ba a yi ba, ka ga ta yo nan ai ka san akwai matsala".


Ya ce"Mene ne ua faru Nuratu?" Sai ta fashe da kuka.


Nawwara ta ce"A'a yi haƙuri, ta huta tukunna, kafin nan zuciyarta ta yi sanyi ma".


Ta ja hannunta, ta kai ta ɗaki, ta zaunar a bakin katifa, ta koma kitchen ta haɗo mata shayi da biredi, har ma da sauran dankali da suka rage, ta kai mata, ta ce"Maza ki ci".


Dayake gidan ba baƙonta ba ne, sai ta fara tashi ta yi wanka, ta canza kaya, sannan ta ci abincin, ta ɗakko wayarta, ta kunna data, saƙonni suka gama shigowa tass babu na Abdul, hawaye ya sakko mata, ta san yana can cikin ƙunci, ta yi masa sallama a rubuce, ba ya online, babu jimawa kuma ta ga tik biyu, alamar ya hau, ya duba saƙon nata, sai ya fara typing, tana ta fargabar abin da zai rubuto, har ya gama ya turo, "Wannan shi ne sakayyar soyayyata a gare ki ko? Na gode Nuratu, Allah Ya saka da alkhairi". Abin da ya rubuta kenan, sai ya bi bayansa da stika ta namiji yana kuka sosai.


Ita ma kukan ta fara, ta danna viice ta ce"Na san ban cancanci ka saurare ni ba, amma don Allah ka daure ka ji bayanina, ba don halina ba, na yi komai ne saboda cika maka burinka, rayuwarka ta inganta".


Bayan ya saurara ya tura mata emoji na mamaki, ta sake yin voice ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, ka fahimce ni, na fi kowa shiga ƙunci sanadin wannan kuskuren da na yi".


Ta typin ya ce mata"Cikin wane ne? Kar ki ba ni amsar da za ta wuce kalma uku, don ba ni da lokacin sauraron tsarinki".


Sarai ta san halinsa, tun da ya ce haka, idan ta ba shi amsa akasin yadda ya buƙata, zai iya yin blocking ɗinta, don haka ta rubuta masa "Agent ɗin da ya yi maka hanyar tafiyarka ne" Ta tura masa.


Abdul yana karantawa, ƙirjinsa ya doka da ƙarfi, ya fara karanto innlillahi wa inna ilaihi raji'un! Ya fara tunanin yanzu a kan shi ta ba da kanta ga wani banza? Nan ya tuna ranar da yake tunanin abun ya faru, da abokinsa Usman ya ce masa, ya ganta ta fito daga mota tare da Agent ɗin nan, amma Abdul fir ya ce ba ita ba ce, sannan a ranar mutumin ya kira shi ya yi masa alƙawarin tafiya. Ya kashe data yana mamakin irin _zuciyar mace_.




08028966015
[11/21, 11:35 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY


PAGE 6




Shiru bai ma sake kunna data ba, ballantana ta ji hukuncin da zai yanke, ta sake tura masa saƙo, ta ce"Ka yi haƙuri don Allah, ni ban ce dole sai ka aure ni ba, kawai dai ka yarda ba yaudara ce ta saka na yi haka ba, ba kuma son abin duniya ba, kawai na yi ne saboda na taimake ka".


Ta ajiye wayar tana tuna ranar da ya zo ƙofar gidansu, jikinsa a mace, yana faɗa mata Agent ɗin ya ce yau ce rana ta ƙarshe, idan bai kawo kuɗin nan ba, babu shi a tafiya, sai dai ya sake nema a gaba, abokansa uku duk sun biya, shi ne kaɗai ba shi da shi, ga shi mahaifinsa yana zaune a gida, jinya ta saka shi a gaba, a ƙa'ida ya kamata a ce yana asibiti, amma yanzu yana gida sai maganin Hausa ake ta banka masa. Ya ce"Nuratu macuta sun yi yawa a ƙasar nan, a gabana ya cikewa mata biyu, kuma ina zargin sun ba shi kansu ne, ɗayar ma buduruwa ce, tsananin rayuwa ya sa take son tafiyar, na ga bayan ta fito ta tsaya tana kuka, ita da ya kamata ta yi farinciki, ni kuma da nake namiji kuɗi ne kaɗai zai fitar da ni, na rasa yadda zan yi, ba na so tafiyar nan ta kufce mini, domin na san haka ke ma za ki kufce mini".


Nuratu ta ce"Allah Ya kiyaye, wallahi ba zan taɓa kufce maka ba Yaya Abdul, zan jira har ka samu aiki".


Ya yi guntun murmushi ya ce"Wa ya san nan da shekara nawa za a samu? Ai ni ma ba zan so tauye miki rayuwa ba".


Ta ce"Yanzu babu wata hanyar?"


Ya ce"Ba ni da komai wallahi, kin ga babata duk ta siyar da kayan ɗakinta, akan tafiyar nan idan ba ta yiwu ba akwai damuwa".


Haka suka dinga tattaunawa, ƙarshe da zai tafi ta ce ya ara mata wayarsa za ta yi kallo, dama yana ara mata, don haka ya miƙa mata ya tafi. Ta shiga ɗaki ta yi zaune da wayar tana tunanin mafita, kafin ta bi shawarar zuciyarta ta ɗauki lambar Agent ɗin, shi ne wanda suka yi waya na ƙarshe, ta saka a wayarta, ta danna kira, ya ɗauka suka gaisa, ta ce"Ni ƴar'uwar Abdul ce".


Ya ce"Wane Abdul?"


Ta ce"Abdulmalik, wanda kuka yi waya ɗazu, wanda bai samu ya cika kuɗin tafiyarsa ba".


Ya ce"Ok ya aka yi?"


Ta ce"Dama ina son mu haɗu, akwai alfarmar da zan roƙa idan zai yiwu".


Ya yi mata kwatance, Allah Ya taimake ta Mama ba ta nan don haka ta saka hijjabi ta tafi. A bakin titi ta tsaya, ya turo aka shiga da ita, ta shiga har ofishinsa, ta zauna ta gaishe shi, ta sake yi masa bayanin kanta, sannan ta ɗora da faɗin"Abdul yana cikin matsalar rayuwa, shi ne babba a gidansu, ga mahaifinsa ba shi da lafiya, don Allah ka taimaka masa ya samu tafiyar nan, daga baya sai ya biya ka".


Ya ce"To ƴan'mata ai haka tsarin yake, mu babu ruwanmu da ƙarfin matsalar mutum, kamfani ne, dole yadda aka tsara ake yi".


Ta ce"To amma me zai hana ka ɗauke ni a nan ɗin ko na shara ne, sai ka dinga riƙe albashin nawa da haka har ya biya ka?"


Ya yi ɗan murmushi ya ce"Wannan lokaci ya ƙure masa ai, yau ce kaɗai damarsa, ni kuma ba zan yi masa aiki bashi ba".


Idonta ya kawo ruwa, ta karaya sosai, ta tashi tana cewa"Shikenan na gode".


Har ta kusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login