Showing 12001 words to 15000 words out of 24835 words

Chapter 5 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

6003

fita, ya kira ta, ya nuna mata kujera ta zauna, ya ce"Ya kuke da shi?"


Ta ce"Yayana ne".


Ya ce"To indai da gaske kike son taimakonsa, ai kina da abin da za ki taimake da shi" Ya ƙarasa yana yi mata kallon ƴan bariki.


Ta ce"Inda ina da shi, da ban zo neman alfarmar nan ba".


Ya ce"Idan har za ki amince mu tsallaka wancen hotel ɗin na kusa da mu, cikin mintuna za ki taimaki yayanki".


Gabanta ya faɗi, ta ce"Amma sai wannan kaɗai?"


Ya ce"E, idan kin duba ai ba wani abu ba ne mai wahala, saboda idan ya tafi zai yi miki alheri fiye da yadda kika yi masa, ƙila ma idan aurenki ya zo shi ne zai yi miki kayan ɗaki, sannan kamar kin taimaki iyayenki ne".


Ta ce"Zan yi shawara".


Ya ce"No, ki je kawai, na faɗa miki yau ne last".


Ya ɗauki waya ya yi danne-danne ya kara a kunne, ya ce"Wannan list ɗin ku cire sunan Abdulmalik Ibrahim, zan tura muku sunan da za ku saka a kai".


Hawaye ya zubo mata, ta ce"Don Allah Oga ka taimake mu, zan dinga kawo maka kuɗin a hankali".


Ya ce"Ki je kawai, ba shi da rabon tafiyar".


Ta tuna wane ne Abdul da yadda yake ƙaunarta, sai ta ga ya cancanci har sadaukarwar rayuwa ta yi masa, don haka ta ce ta amince, nan take suka fita, suka je Nuratu ta miƙa kanta, babu shawara babu tunanin ta tafka kuskure, ta manta wane ne namiji, ba ta tunanin ba kowane zai iya yi maka halakci har ƙarshen rayuwarku ba.


Shigowar Nawwara ce ta katse mata tunani, ta kai hannu ta share hawayen fuskarta, Nawwara ta ce"Ki fito falo yana jiranki, fita zai yi".


Ta tashi ta bi bayanta. Ta zauna kanta a ƙasa, Kabir ya ce"Nuratu me ya kawo ki? Ni ma gobe nake shirin tafiya gaisuwar fa, aiki ne ya yi mini yawa".


Sai ta fara kuka, Nawwara ta ce"Ɗan'uwanki ne, tun da kika zo wajen shi na tabbata kina da yaƙinin samun sassaucin damuwarki, saboda haka bai kamata ki ɓoye masa komai ba" Sai ta tashi ta shiga ɗakinta, don ta ba su waje.


Nuratu ta kasa faɗa masa komai, sai kuka da ya ci ƙarfinta, ƙarshe ya ɗauki waya ya kira Babanta, wanda ke a matsayin ƙanin uba a wajen shi, wato dai ɗan wa da ɗan ƙani suke da Nuratu, amma Allah Ya haɗa jininsu sosai, har ma ya so ta koma gidansa da ya yi aure, sai Mama ta hana, sai dai ta je hutu ta kwana biyu ta dawo gida.


Suka gaisa da Baba, ya ƙara yi masa gaisuwa, sannan ya faɗa masa ga Nuratu ta zo tana kuka, ta ƙi faɗar komai.


Baba da yake kwance a ɗakinsa abun duniya ya ishe shi, ya miƙe zaune yana cewa"Alhamdulillah! Gidanka ta zo ashe?"


Ya ce"E ga ta nan".


Nan Baba ya kwashe komai ya faɗa masa, Kabir ya yi mamaki sosai, saboda duk cikin ƴan gidansu ya fi ganin nutsuwarta, ya shiga yi mata faɗa, tana ta kuka, ƙarshe ya tambaye ta wane ne ya yi mata haka? Nan ma dai ta ƙi faɗa, don takaici ko sallama bai yi wa matarsa ba ya fice daga gidan, a waje Baba ya sake kiransa ya ce lallai-lallai gobe ya sako Nuratu a mota su dawo, ya ce masa da kansa ma zai kawo ta.


Haka ta wuni a ɗaki, duk yadda ta so Abdul ya fahimce ta abu ya ci tura, babu kalar bayanin da ba ta yi masa ba, amma yanzu ya ma daina duba saƙon, kuma yana online.


Shi kuwa a ɓangarensa shi kaɗai ya san halin da zuciyarsa take ciki, yana da matuƙar kishi, musamman a kan Nuratu da ya yanke a ransa da ita kaɗai zai rayu, ya kasa ganin da gaske halakci ta yi masa, ballantana ya yi mata sassauci a hukunci, abu ɗaya kawai yake yawo a kansa, Nuratu ta yi masa butulci, kuma zuciyarta ba mai kyau ba ce, yana tunanin da aurensu ma za ta iya aikata hakan, da sunan taimako.


Amma ta duniya za ta kalle shi da iyayensa, idan aka ji domin shi ta aikata? Saboda haka zai yanke wani hukunci, zai aure ta na ɗan lokaci, daga nan duk wanda zai ji tarihinta a bazawara zai santa, kenan ba za ta samu wata matsala ba a duk yadda mijin da za ta rayu da shi ya same ta.


Ya kira mahaifiyarsa a waya, ya tausasa murya, ya fara roƙonta yafiya, ya yi mata shimfiɗar ƙaddara, sannan ya faɗa mata kafin ya tafi shaiɗan ya shiga tsakaninsu da Nuratu, har ma tana da cikinsa, mahaifiyarsa ta shiga tashin hankali sosai, ta san idan ta sanarwa mahaifinsa zai iya ƙarasawa, don haka ta faɗawa ɗan'uwansa, wanda yake waliyin Abdul ɗin, duk faɗan da aka yi wa Abdul ya yi haƙuri ya jure, a ganinsa wannan ne halakcin da zai yi wa Nuratu kawai, ya rama wa kura aniyarta.


Haka ƙanin babansa ya je wajen Baba da daddare ya faɗa masa halin da ake ciki, Baba ya dinga sababi, don dama Abdul ɗin kaɗai ya zarga, tun da ba ta kula kowa bayan shi, nan ya rarrashe shi, ya ce Abdul zai turo sadaki a ɗaura auren cikin satin nan, idan ya dawo sai ta tare, nan Baba ya ce bai yarda ba, su je kawai Allah Ya isa, amma ita Allah Ya rufa mata asiri, tana da miji.


Washegari Kabir ya saka Nuratu a gaba suka dawo, nan suka zauna da Baba a gabanta yake sanar masa Abdul ne ya yi mata ciki, kuma ya ce zai aure ta. Ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, sai ta rasa farinciki take ciki, ko akasinsa? Ashe Abdul zai jiɓanci lamarin nan, har ya amsa laifin da ba nashi ba? Ta babbata ita da Abdul ruhi ɗaya ne a gangar jiki biyu, ashe ya nuna fushi ne kawai saboda ya hora ta, sai ta ji kamar ta fita daga duka damuwar ma.


Kabir ya ce"To Baba ai ta kwana gidan sauƙi, dama wanda ya dama kunun ai shi ya kamata ya shanye, kuma suna son junansu, tun da ta ga za ta iya jiransa sanda ya bushi iska ya dawo sai su tare".


Baba Ya ce"Ai ba a nan gizo ke saƙar ba!". Nan ya ba shi labarin Alhaji Hashimu, ya ɗora da faɗin"Ka ga shi ya ji ya gani, sannan babba ne mai hankali, ba kamar Abdul ba da ƙuruciya, bar ganin shi ya yi aika-aikar, tsaf zai wulaƙantata a hakan hakan, shi kuwa wannan mai rufin asiri ne, wulaƙanci mai kuɗi ya fi na talaka sassauci a zuciya, ko banza dai a gidansa za ta fi ƙarfin komai, sannan yanzu ta riga ta san daɗin namiji, ba lallai ta nutsu ba, ƙila ta cigaba da shashancinta shi yana can, tana kwasar zunubi, kuma ni ina ma zargin tilas za a yi masa, idan ya ƙi dawowa ya zan yi da ita?"


Kabir ya ce"To gaskiya da wannan ma, indai shi Alhajin ya ji ya gani, ina ga gara ma kawai ta aure shi ɗin, shi Abdul mu bi shi da Allah Ya isa kawai".


Baba ya ce"Yawwa ɗan gari, ashe ka gane".


Nan suka gargaɗe ta akan kar ta sake ta amsa auren Abdul, wanda ta kalli maganar a wani abu da ba zai taɓa yiwuwa ba, domin tana ganin indai har sun yarda Abdul ne ya yi aika-aikar kuma suka zargi zai iya wulaƙantata bayan aure, to shi Alhajin waliyyi ne da zai ƙyale ta? Ta saka a ranta ba ta da mijin da ya fi Yaya Abdul ɗinta.






08028966015
[11/21, 6:01 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)




https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY





PAGE 7




Yau kuwa kafin Nura ya dawo Hasana ta ci kwalliyarta, wata ƙaramar rigar bacci da ta daɗe ba ta saka ba, ita ta ɗakko ta saka, ta fesa turare, ta zauna tana jiran dawowarsa. Yana dawowa ya shiga wanka, kafin ya fito ta tafi ɗakin nasa ta haye katifa ta zauna, har da kunna kallo, ya fito daga wanka yana tura ƙofar ɗakin ya ganta zaune tana yi masa murmushi, ya haɗe rai ya ce"Lafiya?"


Ta ce"Lafiya ƙalau, an dawo lafiya?"


"Ƙalau" Ya amsa a daƙile.


Ta ce"Dama fira na zo taya ka, na ga ka dawo da wuri, ga wannan ɗan abun taɓawa ne".


Ta ƙarasa tana miƙa masa ɗan kwano mai ɗauke da ilokar da ta yi da rana. Ya yi tsaki ya ce"To wace irin fira cikin daren nan?"


Ta ce"Fira dai irin wacce kake yi a majalisa, na yi zaton ka fara dawowa da wuri ne saboda ka ba ni lokacina, mu dinga fira muna tattaunawa game da rayuwarmu da ta ƴaƴanmu bakiɗaya".


Takaici ya ishe shi, shi kam ashe ya gudu bai tsira ba, yanzu haka daga wajen ƙawarta Ramla yake, kuma sun yi da ita za su yi vedio call su sha fira, sai ga shi ta kwaso jiki wai ta zo su yi fira, ya saka kaya ya nemi waje ya kwanta, ta ce"Baban Salim, ba ka sha ilokar ba".


Ya ce"Ki ajiye zan sha".


Ta ce"Ni kuwa Baban Salim sai na ga malaman makarantar yaran nan kamar sun fara shirme, sai a kwana uku ba a ba su home work ba".


Ya yi kamar bai ji ta ba, ta ce"Ni dai kamar na je na ji dalili, saboda...."


A fusace ya katse ta da faɗin"To tashi ki tafi! Wannan wace irin takura ce haka, na dawo gida kaina yana ciwo ba za ki bar ni na huta ba, wannan ai masifa ce! Ka ware ɗakin ma ba ka tsira ba!".


Ranta ya ɓaci, ta ce"Allah Ya huci zuciyarka, ni dai ban ga abun faɗa a nan ba". Ta tashi ta fice ta janyo masa ƙofar.


Ya je ya saka sakata, yana tsaki, a ransa yana ayyana sai fa ya taka mata burki a kan shigo masa ɗaki.


Hasana ta zauna a kujerar falonta, tana tunanin yadda za ta yi, har ga Allah ba ta son mijinta ya zama ɗaya cikin masu lalata tarbiyyar yaran jama'a ta waya, ta taɓa ganin chart ɗin banza sau ɗaya a wayarsa, har ta kasa shiru ta tare shi da maganar, ya yi mata kaca-kaca, daga nan ya saka key a wayar yake kuma taka-tsan-tsan da ita, tun daga nan take zarginsa, ko don yawan son matansa dama dole ta kasa yarda da shi, ta san sarai bai daina chart ɗin banzan ba, ballantana yanzu da ya ware ɗakinsa zai ci karensa babu babbaka, sai a ce mace ba ta jan mijinta a jiki, shiyasa yake yi da wasu matan ta waya, to idan da ba ta ja shi a jiki ba, yanzu ta yunƙuro za ta gyara zaman, don kayan baccinta da ta daina sakawa duk ta fito da su, kuma ya ƙi ya ba ta dama.


Ta jima tana wannan tunanin sannan ta tashi ta sake fita cikin sanɗa, ta leƙa shi ta windo, ta hango shi, zaune yana kallon waya yana magana fuskarsa ɗauke da murmushi, ta koma ɗaki ta ɗakko panadol da ruwa a kofi, ta je ta fara ƙwanƙwasawa. Nura yana jin daɗin firarsa, ga iloka yana rakawa da ita kawai ya ji bugun ƙofa, sai da ya zabura, sannan ya ce wa Ramla yana zuwa.


Ya tashi ya je ya buɗe yana cewa"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Hasana kaina fa ciwo yake yi, na samu bacci da ƙyar kin tashe ni".


Ta ce"Dama magani na ga ya dace na kawo maka".


Ya karɓa, ya mayar da ƙofar ya rufe, ta koma ɗaki ta yi addu'a ta kwanta, tana jin zafi a zuciyarta. Da asuba ta idar da sallah ta ɗan kunna data, kamar an yi mata umarni ta shiga status ɗin Ramla, ta ga ta saka "Jama'a namiji ya ware turakarsa fa duniya ne, mace tana can sake da baki tana yawun bacci, shi yana caskalewa" Ta haɗa da emojin dariya.


A na gaba kuma ta saka"Auren mijin wata akwai lada".


Nan take Hasana ta ji ta tsargu, kamar ta wuce sai kuma ta kasa, ta dawo ta ba ta amsa a kai, ta ce mata"Ƴan'mata kenan, ku dai dinga tuna yadda ake caskalewar da ku, an caskale da na gidan fiye da haka, kuma kar lokacinku ya zo ku yi mamaki" Ta haɗa mata da dariya.


A na biyun kuma da ta ce auren mijin wata da lada, ta ba ta amsa da "Musamman mai cefane da nama".


Wajen azhar da Ramla ta duba saƙon, ta ce mata"Ke dai ƙawata ku riƙe mazajenku da kyau, amma tabbas duk wanda ya kawo kanshi wajena sai na tatike shi".


Hasana ta ce"Ku dai bi a hankali, wani sai bayan auren za ki san ko wane ne".


Daga haka suka taɓa fira, aka bar wannan zancen.


Da rana yana cin abinci ta ce"Don Allah baban Salim kayan kwalliya nake so, hodata ta kusa ƙarewa, ina son siyan humra ma, kuma underwears ɗina duk sun tsufa".


Ya ce"Mata kenan, ku fa babu ruwanku da halin da ake ciki, a nemo a ba ku kawai, ana ta abinci ke kina ta wasu tarkacen da ba su zama dole ba".


Ta ce"Hmm! Ai tarkacen ne yake kwasarku ku je ku dinga rawar ƙafa a wajen matan waje, waɗanda ba kyau suka fi ni ba, na ji an ce ma an ce har wannan mai awarar ta bakin kasuwa ita ma son ta kake yi, wannan dai zubar da aji ne wallahi, ka rasa wa za ka so wannan kucakar? Wannan uban kurkur ɗin ne fa ya kwashe ka, amma ka faɗo wallahi".


Ya ture abincin yana nuna ta da yatsa ya ce"Ke ya ishe ki haka! Saboda tsabar raini ni za ki saka a gaba da zancen banza sai ka ce wani ɗanki? Ba mai awara kaɗai ba har mai dankali ma son ta nake, wannan mai gurasar ma yau zan je wajenta, ko za ki hana?"


Ya tashi yana cewa"Kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, ina da kuɗin auren, kuma Allah Ya ba ni damar ƙarawa za ki hana ne? Idan na ga dama ma mai ƙosai zan auro wallahi, ta zo kuma idan kika yi wasa ta fi fada a wajena!".


Ta ce"Au kai har wata fada ce da kai?"


Ya ce"Da babu da ba a biyo ni da ilokar toshiyar baki ba".Ya fice daga gidan, yana ayyana dole ma fa ya tattara ƙaryar nan ya tsayar da mace ɗaya ya aura.




********


Ta yi wa Abdul saƙo ya kai biyar bai ba ta amsa ba, amma ya saurara, duka haƙuri take ba shi, tare da alƙwarin za ta jira shi ko shekara nawa ne. Da daddare Alhaji Hashimu ya zo, Baba yana rawar jiki ya zo ya kira Nuratu, tana jin haushi a ce wai mahaifinta ne ɗan aiken saurayinta, ta fito suka gaisa, ta sunkuyar da kai, ya ce"Ya ƙarin haƙuri?"


Ya ce"Da godiya".


Ya ce"Ya jikin naki?"


Ta ce"Na warware".


Ya ce"To ma sha Allah!Mun yi magana da Baba, gobe za a kai ki asibiti sai a cire cikin, bayan sadakar arba'in sai a saka rana ko wata biyu ne, zuwa lokacin na kamalla ginin inda zan saka ki".


Ta ce"Amma Alhaji Baba bai yi maka bayani ba?"


Ya ce"Na me?"


Ta ce"Shi saurayin nawa da abun ya faru sanadinsa, ya ce zai aure ni, kuma har an gama magana da Baba".


Ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce"Amma bai faɗa mini ba".


Ta ce"To zai faɗa maka".


Suka yi shiru na ƴan sakanni, sannan ta cigaba"Alhaji na gode da ƙaunarka gare ni, sai dai ina so na faɗa maka ni Abdul shi kaɗai nake so, gaskiya duk wanda ya aure ni ba shi ba, zai iya yin nadama a gaba, saboda ba zai taba samun nutsuwa da ni ba, kai babban mutum ne mai mutunci, kuma kana da ƙima a idona, ba zan so yi maka abin da na tanadarwa namijin da ya yi gangancin aurena ba, saboda haka don Allah Baba ka kama girmanka, kai baban wasu ne, ba zan so yi maka ba daidai ba, tun da ba zan so a yi wa nawa uban ba, na gode sosai Alhaji".


Daga haka ta juya za ta shiga gida, ya ce"Ɗan tsaya Nuratu".


Ta dawo, ya ce"Na ji duk bayaninki, kuma na fahimce ki, ita rayuwar aure ba a yin ta da tilas, kamar yadda kika ce na kama girmana, na kama in sha Allah, dama ni na zo da ƙauna ne, da kuma niyyar taimako duba da ƙaddarar da ta same ki, yanzu zan janye batun soyayya, zan kuma yi wa Baba bayanin da zai fahimta, idan har kina buƙatar wani taimako ƙofa a buɗe take za ki iya tambayata, a matsayina na mai tallafawa marayu. Sannan goben za a je cire cikin" Daga haka ya juya ya fita, ta shiga gida jiki a mace, amma sai ya kasa faɗawa Baba yadda suka yi, saboda ba ya son haɗa ta da mahaifinta.


Washegari da safe direba ya zo ya ɗauke ta, tare da wata yayarta, suka tafi asibiti, gabanta yana ta faɗuwa, tana jin kamar ta gudu, a hannun likitan farko dai ya damƙa ta, da alama shi ɗin amintaccensa ne, shi da kansa ya yi mata allurar zubar da cikin, sannan ya ba ta gado. Bayan ya kammala ya kira Hajiya Kubra a waya ya sanar mata.


Zuwa yamma komai ya kammala, cikin ya fita duka, aka sallame su direba ya mayar da su gida. Tun kafin su ƙarasa likita ya kira Alhaji suka gaisa ya ce"An kammala aikin cikin nasara".


Ya ce"To Alhamdulillah!".


Likita ya ce"Sai dai fa akwai wata matsala".


Ya ce"Ta mene ne?"


Likita ya ce"To ban sani ba ko ka san yarinyar tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki".


Gaban Alhaji ya faɗi, ya kaɗu sosai da jin kalmar nan, ya ce"Ok babu damuwa, na gode".


Ya katse kiran, nan tausayinta ya ƙara kama shi, ya kuma raya a zuciyarsa lallai yaron nan ya cuci Nuratu, ko ta san tana da cutar a jikint? Da ya yi tunanin sanarwa Baba, sai kuma ya ga tun da yaron ne zai aure ta gara ma ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login