Showing 18001 words to 21000 words out of 24835 words

Chapter 7 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

6004

jama'a, ana ta zagina a gari saboda wannan halin naka na son mata, wai da me na rage ka ne don Allah? Ka sanar da ni matsalata sai na gyara..." Ta fashe da kuka.


Duk da jikinsa ya ɗan yi sanyi, amma ya danne bai nuna ba, ya ma tashi ya bar mata ɗakin, shi dai bai ga wata matsala ba saboda yana kula mata, ai namiji mijin mace huɗu ne, yana da ra'ayi da burin auren mata huɗu idan har ya samu dama, saboda haka ba ta isa ta hana shi ba.


Daga baya ta yanke hukuncin jan hankalinsa don ta gane wace kalar mu'amula yake yi da mata a wayar? Sai ta saka Husainarta ta aiko mata d sabon layi, saboda akwai ƙanin mijinta wanda yake siyarwa, ta saka a wayarta, ta saita sabon whatsApp da shi, ta nemi lambar Nura ta yi masa sallama, ya amsa suka gaisa, ya ce bai gane mai magana ba, a rubuce ta ce"E dama ba ka san ni ba ai, yanzu dai nake ganin lokaci ya yi da ya kamata ka san ni, saboda ka daɗe kana azabtar da zuciyata da soyayyarka, burina ko yaya ne na samu matsuguni a zuciyarka, wanda za ka dinga tuna ni ko da sau ɗaya ne a sati".


Sai ya tura stikar murmushi, ya ce"Ikon Allah! Da farko dai ya sunanki?"


Ta ce"Sunana Suhaila, kuma a kasuwa nake ganinka, wallahi kana burge ni sosai, na daɗe da samun lambarka, amma sai na yi ta jujjuya ta, na kasa yi maka magana, saboda a zotona za ka yi wulaƙanci duba da ganin yadda ka haɗun nan kake da aji, na ji an ce ma mata ba sa gabanka, shi ne nake ta fargaba".


Nura ya yi murmushi ya ce"Wannan dalilin ai ba shi zai saka mutum ya yi wulaƙanci ba, sai dau idan dama can halinsa ne, ita mace ai ba abar wulaƙantawa ba ce, mace abar riritawa ce da tarairaya, kuna buƙatar kula ta kowane fanni, wannan shi ne burin da na ci a kan matar da zan aura har tsufanmu".


Ta ce"Kenan yanzu ba ka da aure? Zan so a ce ni ce zan samu wannan kulawar".


Ya ce"Ina da aure har da yara, sai dai wancen burin nawa yana neman zaɓa tarihi, saboda wata kidahumar mace Allah Ya haɗa ni da ita, wallahi sam ba ta san kanta ba, ballantana ta san mijinta".


Kalmar kidahuma ta daki zuciyar Hasana ba kaɗan ba, nan take ranta ya yi baƙi, sai ta ji kamar ta yi voice ta faɗa masa ita ce, sai dai kuma ba wannan gaɓar take nema ba, don haka ta daure zuciyarta suka cigaba, ta ce"Ikon Allah! Yanzu duk wannan haɗuwar taka ba ka yi dacen mace ba? Amma ai kai ya kamata ka canza ta, ka mayar da ita yadda kake so ku zauna".


Wannan karon voice ya yo, yana ƴar dariya ya ce"Malama Suhaila kenan, wato ba ki san wace ce matata ba, shiyasa kike zaton za ta canza hali, yanzu haka zancen da nake yi miki fa kin gan ni kwance a ɗakina ni kaɗai, na kasa bacci saboda tsananin buƙatarta nake, amma na kirata ta ƙi zuwa, yanzu ya dace a ce mace ta dinga nisa da ɗakin mijinta wai sai sanda ya kira ta?"


Hasana ta daskare da mamaki, sai ta kasa riƙe hawayenta, ashe dama haka Nura yake tona wa aurensu asiri? Kuma ma duk bin ta yake yi da sharri, indai har wacce ta fara yi masa magana yau bai santa ba, bai san inda take ba, zai saki jiki ya dinga tsara mata wannan ƙaryar, to ina ga wacce ya saba da ita har ma yake zuwa gidansu? Yanzu haka yake faɗawa Ramla ma? Tabbas dole ta raina ta.


Ta share hawaye ta ɗauki wayar, sai ta ga ya turo mata stika, tana buɗewa ta ga mace ce da namiji rungume da juna suna bacci, ta daure ta rubuta masa"To ko ni ɗin na zo na taya ka baccin?"


Ya tura mata dariya ya ce"Da gaske ba za ki ji tsorona ba?"


Ta ce"To tsoron me?"


Ya ce"Ai za ki zo ne matsayin mai ɗebe mini kewa".


Ta ce"Hmm, za ka same ni fiye da matarka, kwatanta mini gidan naka yanzu zan zo".


Ya ce"Ki dai gwada ta waya don na yarda idan kin zo ɗin za ki iya taɓuka abun arziƙi".


Sai ya turo mata wani vedio, tana buɗewa, ta yi saurin kifa wayar, ganin blue film ne ƙarara, ta dinfa maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!", ta kashe wayar duka ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ta samu kanta da fashewa da kuka, ashe irin mijin da take aure kenan?


A daren nan da ƙyar bacci ya ɗauke ta, da safe har ta makara, sai da ya tashe ta, har da faɗansa yana cewa"Wannan wani sabon salon ne kuma salon yara su makara?"


"Ba ni da lafiya ne" Abin da ta ce kenan kawai, wani irin mugun haushinsa take ji, ji take kamar ta kama shi ta shaƙe, ta tambaye shi me yasa yake zaune da ita ba zai sake ta ba? Ta je ta kunna wuta, sai dai tunawa da kalmar kidahuma ya sa ta fara hawaye, idan ya tashi wulaƙancinsa har jaka yana ce mata, amma a jiya fa wata yake faɗawa ita kidahuma ce, tabbas ta san duk wacce zai auro nan gaba ba za ta kalle ta da mutunci ba.


"Kukan me kike yi?" Ya tambaye ta yana yamutsa fuska.


Ta ce"Na ce maka ba ni da lafiya".


Ya ce"To Allah Ya sawaƙe, sai ki yi ƙoƙari ki dafa shayi, bari na siyo biredi".


Ya fita, ta bi bayansa da kallo, tana tuna wannan ƙazamin vedion, wa ya san adadin matan da ya turawa shi? Wa ya san adadin yawansu a wayarsu, lallai wata wayar za ta iya yi wa mutum jagora zuwa jahannama, haka ta dafa shayin, suka karya, ta shirya yara, tana yin komai a sanyaye, yana taɓa aljihunsa ya ce"Ga shi ba ni da kuɗi da kin tafi asibiti".


Ta ce"Ciwon kai ne, zan sha magani yanzu".


Ya ce"Allah Ya sawaƙe ya fice".


Wajen ƙarfe goma ta kunna data, ta gan shi online, zuciyarta tana ba ta shawarar ta ajiye layin nan, tun da har ta san wane ne mijinta, ta samu abin da take so, wani ɓangare na zuciyar kuwa zugata yake yi, a kan ta cigaba don ta gano iya waya abun nashi ya tsaya ko zai yarda su haɗu a zahiri? Ta fi yarda da wannan don haka ta yi masa sallama, sai da ma ya duba chart ɗin baya har farko, sannan ya tuna ta, saboda yawan matan da yake chart da su, ya amsa ya ce"Matsoraciya jiya sai kika gudu ko?"


Ta ce"La ba fa guduwa na yi ba, wayar ce ta mutu, caji ya ƙare, ban ma kai ga ganin me ka turo ba".


Ya ce"Kin bar ni da kewarki, har da mafarkinki na yi".


Ta ce"Daga haɗuwa?"


Ya ce"Ai haɗuwar ce ta yi daɗi shiyasa, yau za ki rage mini dar ko?"


Ta ce"Me zai hana? Ni fa da gaske nake, ka ga ni ban saba ta waya ba, a ina za mu haɗu?"


Sai ya tura mata dariya ya ce"Kamar gaske".


Ta ce"Tun da ba ka shirya ba shikenan mu bar zancen".


Ya ce"Wai ke ba kya yin voice note?"


Ta ce"Ai ni kurma ce, ba na magana kuma ba na jin komai".


Ya tura stikar dariya ya ce"Ban yarda ba, sai ranar da na ganki a zahiri".


Ta ce"To yaushe zan zo taya ka kwana?"


Ya ce"Yau".


Ta ce"Za kuwa ka gan ni, da gaske fa".


Ya yi dariya.


Ta ce"Zan zo ƙarfe sha ɗaya daidai, saboda haka ka koma gidanka da wuri yau".


Ya ce"Allah Ya kawo ki, zan shirya miki abubuwan mamaki kuwa".


Daga haka ta kashe data, ta tashi ta ɗora girki, a ranta tana ayyana tabbas yau ɗin kuwa za ta je, ta fito masa a mutum, don ya san ta gane badaƙalar da yake yi a wayarsa. Da ya zo cin abincin rana ba ta nuna komai ba, sai dai sam ba ta da walwala, da daddare yana dawowa ya gama komai ya shiga ɗakinsa, ta kunna data, ta ga saƙonsa ya shigo, yana ce mata"Kyaun alƙawari dai a cika, yana jiranta".


Ta ce"Ka tashi ka buɗe ƙofa yanzu za ka ji na turo na shigo".


Ya ce"Na buɗe".


Ta ce"Ba ka buɗe ba, ina kallonka fa, kana kwance a katifa da gajeren wando bulu".


Ya yi ƴar dariya ce"Kuma wallahi kin canka".


Ta ce"Na ce fa ina kallonka, yanzu na ƙaraso ƙofar ɗakin zan ƙwanƙwasa, ka buɗe, amma don Allah ko a yaya ka gan ni kar ka ji tsorona, wallahi ni mai sonka ce".


Ya ce"Kai Suhaila kenan".


Hasana ta buɗe ƙofarta a hankali, ta fito, ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Nura da ƙarfi, gabansa ya faɗi rass, ya ce"Wane ne?"


Ta tsaya da bugun ta rubuta masa cewar"Ni ce mana, ya kake haka, ko na shigo ta saman ɗakin?" Sannan ta cigaba da bugawa.


Nura bai san sanda ya yi wulli da wayar ba, ya fara karanto duk addu'ar da ta zo bakinsa, ya yaye zanin gadon da aka shimfiɗa a katifa ya lulluɓa, yana ta addu'o'i.




LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL! ZA KU IYA FARA BIYAN KUƊINKU TUN YANZU TA NAN


8028966015
Sadiya Abdulrazak opay bank


Sahaidar biya ta nan
08028966015
[11/24, 1:16 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY


PAGE 10




Jin shiru ya sa Hasana ta leƙa shi ta windo, nan ta hango shi ya naniƙe bango kamar ƙadangare, dariya ta zo mata, amma ta daure ta riƙe ta, ta matse murya tare da dakushe ta tamkar ta tsohuwar da ta gaji da duniya ta ce"Kai yaro kai fa ka ce kyaun alƙawari a cika, mu ba ma karya alƙwari, kai yaro yanzu za mu ɗage ka, kai da katifar mun kai ka tsakiyar sansanin karuwan aljanu, zan nuna musu masoyina, a can za mu rage dare na zo maka a matsayin matarka kamar yadda ka ce".


Wani irin hautsinawa kayan cikinsa suka fara yi, ya yi adungure ya diro daga katifar, ya buɗe sif ɗinsa ya shige lokar ƙasa yana tsananta addu'arsa.


Hasana ta sake cewa"Sakan ɗaya na ba ka, ka fito daga sif ɗin nan idan ba haka ba, zan rufe ta da mukullin garƙam na kakana na goma sha tara, babu wanda ya isa ya buɗe sai bayan shekara ɗari da saba'in".


Kafin ta rufe baki, sai ga shi ya faɗo daga ciki kamar an jefo shi, ya kalli gabas da yamma, ya fashe da kuka yana cewa"Na tuba, wallahi na tuba don Allah ki yi haƙuri?"


Ta ce"Me ka yi kake tuba?"


Ya ce"Ni ɗan iska ne wallahi, amma daga yau na daina ba zan ƙara ba".


Ta saki wata muguwar dariya ta ce"Yanzu kana nufin ka haƙura da rage daren?"


Da sauri ya ce"E wallahi, dama ƙarya nake yi, ban san ma yanda ake rage daren ba, ki yafe ni".


Ta ce"Ni sunana Aljana Salsabilatul-silsilatul-sakafilatul-salwaisus, ya na ce sunana?"


Nan Nura ya ruɗe ya fara jero baragada, S kawai kake ji tana tashi, ga shi kuma yana kuka".


Hasana ta kasa daurewa ta yi nesa da ɗakin, ta yi dariya a ciki-ciki, sannan ta daidaita kanta ta dawo ta sake buga ƙofar, ya zabura, yana ba da haƙuri, ta ce"Yi min shiru, munafukin banza!" Daidai nan kuma ta fara jiyo kukan Aiman.


Ta ce"Ka ci sa'a, yau muna da mitin namu na ƙungiyar karuwai, amma ka sani zan dawo gobe domin mu tattauna game da ƙuntatawar da kake yi wa matarka, da sharrin da kake yi mata, sannan duk chart ɗin cikin wayarka ka tabbata ka goge su, ka goge whatsApp ɗin duka mun haramta maka shi har abada, tun da tarbiyyar yaran mutane kake ɓatawa".


Ya ce"To zan goge, na ma goge wallahi, ni da charting har abada Kaka".


Ta ce"Kai yaro, bar ganin muryata haka kake ce mini Kaka, ni matashiyar aljana ce, shekaruna ɗari uku da ashirin da uku, kawai ina yi maka kalar muryar da kunnenka zai iya ɗauka ne".


Ya ce"To na gode, na gode".


Ta ce"Gobe zan dawo mu tattauna, sannan duk wanda ka ba wa labari, to ka tabbata ka furta kalamanka na ƙarshe kenan, domin daga ranar zan fansar da harshenka ga saurayina, ba za ka sake magana da bakinka ba. Yanzu ka tashi ka yi ta tsallen kwaɗo har sai gari ya waye, idan ka fito kafin kiran sallar asuba, sai dai ka ga kanka a tsakiyar barikin aljanu".


Ta leƙa ta windo ta gan shi yana ta tsallen kwaɗon har da kama kunnensa kamar a makaranta, ta buga ƙofar ɗakin da ƙarfi, Nura don tsoro har sai da ya faɗi, sannan ya tashi ya cigaba da yi, ta yi wani irin abu da muryarta, sannan ta tafi cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ɗakinta, ta shiga, ta hau gadon ta ɗauki Aiman, ta fashe da dariya, ashe ita tana da maganin Nura ta tsaya take ta shaƙar takaici? Har ta fara hasashen azabar da za ta ba shi gobe, tabbas sai ta huce takaicinta. Haka ta kwanta bacci ranta fes.


A ɓangaren Nura kuwa, ya kai awa biyu yana ta tsallen kwaɗo, yana yi yana addu'a, ya gaji matuƙa, amma tsoro ya hana shi tsayawa, ƙarshe dai da abun ya ishe shi, sai ya yi shahada ya daina yi, ya rarrafa ya kunna kayan kallo, ya nemo tashar da ake yin karatun Qur'ani, ya manta rabon da ya saurari Qur'ani sai yanzu da yake neman tsira, ya zauna yana bin karatun duk da ma bai iya surar ba, a haka har asuba ta yi, bai runtsa ba. Yana jin fitowar Hasana za ta yi alwala, amma tsoro ya hana shi fitowa, ya ce"Hasana!"


Ta amsa tana tahowa ɗakin.


Ya ce"Don Allah samo mini buta da roba mai faɗi haka, alwala zan yi, ki haɗo da fo ma".


Ta ce"Subhanallah! Baban Salim karyewa ka yi ne?"


Ya ce"Dalla idan ba za ki kawo mini ba ki faɗa mini!".


Ta ce"A'a ni ba ni da fon da ƙato zai hau, ga dai buta nan" Ta miƙa masa butar hannunta da roba ta fice.


Can dai ya yi shahada ya fito, ya yi alwala ya tafi masallaci, sai da gari ya waye sosai sannan ya dawo, yanzu tsoron ɗakin yake ji, wayarsa kuwa bai kula ta ba, sai da suka gama cin abinci, gabansa yana faɗuwa ya ɗauka, ya goge whatsApp ɗin duka, ya saka a aljihu ya fita, a kasuwa ma jikinsa duk a sanyeye, haka ya dawo cin abincin rana Hasana tana lura da yanayinsa, da zai fita ya ce"Yau kar ki rufe ƙofar nan, a nan zan kwana".


Ta ce"A nan za ka kwana kuma? Kai kuwa me ya yi zafi?"


Ya ɓata rai ya ce"Ban sani ba! Ko ni da gida za ki yi mini iyaka ne?"


Ta ce"A'a, amma dai da mamaki, a ce wai kai da kake kora ta kuma yanzu za ka baro lafiyayyen ɗakinka ka zo nawa, gaskiya da wata a ƙasa".


Ya yi banza da ita, ya fice.


Ana yin sallar isha'i, Hasana ta garƙama sakata a ƙofarta, ƙarfe takwas sai ga shi ya dawo gidan, gabansa yana ta faɗuwa, ya ga abincinsa a ƙofar ɗakinsa, ya je ya fara ƙwanƙwasa ɗakin Hasana tare da kiran sunanta, tana ji ta yi banza da shi, ya dinga bugawa, ƙarshe har Salim da Amir yake kira, ya ji shiru, sai ya kira ta a waya ta ƙi ɗagawa, abun duniya ya ishe shi, shi bai taɓa jin haushin wannan nauyin baccin nata ba kamar yau, ya zauna a tsakar gida duk da gabaɗaya gidan ma tsoro yake ba shi, Hasana ta ɗakko wayarta ta rubuta mata saƙo, ta ce"Ko ka tashi ka shiga ɗakinka mu tattaunawa ko kuma mu yi sama da ƙoƙon kanka yanzu".


Sai da gabansa ya faɗi da ya ji shigowar saƙon, ai kuwa yana karantawa ya tashi a guje ya nufi ɗakin Hasanar yana ta bugawa haɗi da addu'a, Hasana da take ta dariya, ta sake rubuta masa"Muna kallonka kana buga ɗakin baiwar Allah, nan muka aike ka?"


A guje ya je ya buɗe ɗakin nasa ya shiga, yana ta addu'a. Ya tsugunna kamar ɗalibi a gaban Malami, ki mai laifi a gaban jami'an tsaro, ya fara cewa"Don Allah ki yi haƙuri ki yafe ni, wallahi na tuba".


Hasana ta buɗe ɗaki ta fito, karaf a kunnensa, sai kuwa ya daddage yana ƙwala mata kira cikin kuka, "Hasana! Hasana don Allah zo ki cece ni".


Maganarsa ta guntse jin an buga ƙofar ɗakin da mugun ƙarfi, ya yi tsalle ya haye katifa yana "Wa innahu Sulaimanu".


Hasana ta fara irin muryar jiya ta ce"Wato matar taka da kake cuta ita za ta zo ta cece ka ko? To fitsari ta fito, kuma mun juya mata ƙwaƙwalwarta mun mai da ita ɗaki, sai kuma wa za ka kira?"


Da sauri ya ce"Babu, wallahi babu wanda zan kira".


Ta ce"Me yasa kake chart ɗin banza da ƴaƴan mutane?"


Ya ce"Ƙaddara ce, amma na daina wallahi, har abada".


Ta ce"Mun gama da wannan shafin, to me yasa kake ƙuntatawa matarka? Kake zaginta idan ka je zance wajen ƴan'matanka?"


Ya ce"Babu komai wallahi, na daina".


Ta ce"Bayan ƙungiyar karuwan aljanu, ina cikin ƙungiyar masu ladabta bil-adaman da suke ƙuntatawa matansu, saboda haka zan ɗauke ka na kai ka can ofishinmu na aljanu masu kare haƙƙin matan bil-adama! A tarihin sama da shekara dubu, babu bil-adaman da ya shiga ofishinmu ya fito da rai"


Cikin tashin hankali Nura ya fara"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Don girman Allah ku yi haƙuri, wallahi na daina, daga yau ba zan sake yi mata komai ba, zancen ma na daina zuwa".


Ta yi wata dariya ta ce"Muna sane da abubuwan da kake yi mata, ba ka ba ta kayan kwalliya, amma kana ba wa matan waje, kwanaki ta tambaye ka me kake so ta dinga yi don ku zauna lafiya, ka ƙi faɗa mata, ta ce ka ba ta kuɗi ta sayi ƙananun kaya nan ma ka ƙi, haka kawai sai ka fara yi mata masifa, sannan kuma ba ka ba ta ɗan kuɗin kashewa, kuma duk baƙin da ta yi sai ka ce kana son su, hakane? Ka raba ɗaki, ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login