Showing 21001 words to 24000 words out of 24835 words

Chapter 8 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

6006

hana ta dinga biyoka"


Da sauri ya ce"Hakane, hakane wallahi wannnan duk halina ne, amma na tuba yanzu".


Ta ce"Sannan sai ka yi wata ba ka kira ta ba, to idan ba ka buƙatar mace mu za mu turo maka aljana shafumuleratu, ta shafeka".


Da sauri ya ce"Ku yi haƙuri don Allah! Wallahi zan gyara zan daina".


Ta ce"Kenan da kana sane? Matan waje kake bi ko?"


Ya ce"A'a wallahi ba na bin kowa, basir ne da ni".


Ta ce"Mun ba ka wata ɗaya ka nemi magani!" .


Ya ce"To, zan nema, gobe zan siyo".


Ta ce"Ina kuɗin auren da ka fara tarawa? Yanzu sun kai nawa?" Ta tambaya, don a cikin satin ta ji wata ƴar'uwarsu ta ce kuɗin aure ma zai kai.


Ya ce"Dubu hamsin ne dama za a kai ranar Lahadi, amma yanzu idan kun ce na fasa shikenan".


Ta ce"Ba mu ce ba, amma wannan kuɗin ka ɗauke su ka ba wa matarka ta sayi underwears da kayan kwalliya, kuma ka ba ta haƙuri ku gyara zaman aurenku, sannan daga yau kullum za mu na kawo maka ziyara, idan muka zo muka ganka kana bacci kai kaɗai, sai dai ka farka ka ganka sansanin karuwan aljanu, daga yau ka kira matarka ku dinga kwana tare, ko ba ka ji ba!?"


Ta ƙarasa da daka masa tsawa, wanda da ace a nutse yake ma tsaf zai iya gano muryarta. Amma da yake ba ya cikin hayyacinsa da sauri ya ce"Na ji, wallahi na ji, kuma zan yi duk yadda kuka ce".


Ta ce"Idan ka yi haka ka taimaki kanka, daga gobe mu fara ganin canji".


Ya ce"To, to,na gode". Ta buga ƙofar da ƙarfi, Nura ya kwanta ya lulluɓa yana ta salati. Da yake shi bacci ba a cin bashin shi, haka Nura ya dinga kokowa da shi, har dai ya samu wahalallen bacci ya kwashe shi, sau biyu yana mafarkin aljanu, sai ya farka a razane ya cigaba da addu'a.


Yana jin kiran sallar asuba ya fito, ya yi alwala ya tafi masallaci, da ya dawo ɗakin Hasana ya wuce, ya shiga ya zauna a kujera ya yi shiru, ta gama azkar ɗinta, ta tashi ta fita don kunna wuta, da ta ɗota ta dawo ɗakin ta zauna ta ce"Baban Salim lafiya kuwa?Na ga ka fito da asubar nan".


Ya sauke numfashi ya ce"Babu komai yanayi ne kawai".


Can ya nisa ya ce"Dama ina son mu yi magana ne mai muhimmanci".


A zuciyarta ta ce"An zo wajen".


Ya ce"Ina so mu haɗu mu gyara rayuwar aurenmu ne dama,duk abubuwan da nake yi miki zan daina in sha Allah! Ke ma sai ki ɗan gyara wasu abun, ki guji ɓata mini rai, ina so mu samu zaman lafiya".


Hasana ta ce"To Alhamdulillah! Ni dama baban Salim ai tun tuni nake so mu yi irin wannan zaman, kai ne ka ƙi fahimtata, in sha Allah ni ma zan dinga kiyayewa".


Ya ce"To, me da me ma kika ci mini za ki siya kwanaki?"


Ta ce"Ban ce zan sayi komai ba".


Ya ce"A'a kin ce za ki canza underwears mana".


Ta ce"Ai ka ce ba ta shi ake yi ba".


Ya ce"Kuma yanzu ba gyara zama ake yi ba? Anjima zan ciro kuɗi na ba ki, sai ki siyo duk abin da kike buƙata".


Ta ce"To na gode, Allah Ya saka".


Ko amin ya kasa cewa don takaicin fitar da kuɗin yake yi. Haka kuwa aka yi, ya je ya ciro kuɗi, sai ga dubu hamsin kash ya kawowa Hasana, ta nuna farincikinta sosai kuwa, shi kuma jiki a mace, ta ce"Ni akwai wata hoda da Husaina take nema, ta ce za ta turo maka hotonta ta whatsApp".


Gabansa ya faɗi tunawa da whatsApp ɗin, ya ce"Ta tura miki kawai ki nuna mini, ni na daina chart".


Ta ce"Ikon Allah, saboda me?"


Ya ce"Ba komai kawai na gaji ne".


Har zai fita ya dawo ya miƙa mata mukullin ɗakinsa ya ce"Yawwa daga yau ki dinga kwana a ɗakina, babu amfanin raba ɗaki yanzu, tun da mun fahimci juna".


Hasana ta ce"Oh! Baban Salim kana ta kashe ni da mamaki fa, ina godiya".


Ya ce"Ki godewa Allah kawai".


Ya fice, babu jimawa ya dawo da tarkacen magani, ya ce"Ungo wannan maganin basir ne ki dafa mini".


Ta karɓa tana daurewa saboda dariyar da ta zo mata, ita da ya ce basir ne da shi ta yi zaton ma ƙarya yake yi, kenan ya san da cutar amma ya ƙi neman magani, sai da ya ji uwar bari.


Ta ce"Baban Salim basir ne ya same ka?"


Ya ce"E" Ya fice ba tare da ya jira ta ce wani abu ba.


Ta dafa magani, da ya dawo da daddare ya kafa kai ya kwankwaɗa, ana idar da sallar isha'i ma ya dawo, ta kuwa ci kwalliyarta, cikin rigar bacci, tana ta jan shi da fita yana mazewa, da yaran suka yi bacci, sai ta ɗauki Aiman suka tafi ɗakinsa, shi dai addu'a ya yi ya kwanta, saboda baccin da yake idonsa, ita kuwa sai da ta yi kallo sannan ta kwanta, suka kwana lafiya ƙalau.




LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL!
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay bank




08028966015
[11/25, 8:33 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)




https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY




Marubuciyar
Wani auren
Iya ruwa
Da walakin...
Wutar ƙaiƙayi
Matar shige
Alhakin so
Mataccen buri
Mukullin nadama
Akwai ragi ga wanda ya sayi littafaina guda biyu ko fiye da hakan
08028966015


PAGE 11




Washegari misalin ƙarfe goma Nuratu ta haɗa duka kayanta a akwati, ta yi sallama da ƴan gida, Baba ya zaunar da ita ya ce"To Nuratu, kin ga dai duk wanda ya janyo ka jikinsa shi ba maƙiyinka ba ne ba, saboda haka dole ki bi umarnin Kabiru shi da matarsa, yi na yi, bari na bari, kar ki sake na ji an kawo wani ƙorafi a kanki, wallahi sai na saɓa miki, kuma sai dai ki nemi inda za ki zauna, ba dai gidan nan ba, ba zai taɓa yiwuwa na aurar da ƴa kuma ta zauna min a gida ba, ban da kin zaɓawa kanki haka ai da tuni kin auri mutumin arziƙi kina can ɗakinki hankali kwance, yanzu kuwa sai ki yi ta zama, ƙila ma har ki tsofe a gida bai dawo ƙasar ba, Allah Ya kyauta!" Kalaman da suka raba ta da Baba kenan, saboda haka ta tafi jiki a mace.


Ana kiraye-kirayen sallar azhar Nuratu ta sauka a gidan Kabir, lokacin ba ya gida, Nawwara ta tare ta da murnarta tana cewa"Babbar baƙuwa ta ƙaraso, kodayake ma yanzu kin zama ƴar gida, sannu da zuwa".


Ta ce"Yawwa Anti na gode".


Ta yi wanka ta yi sallah, tana cikin cin abinci sai ga kiran Kabir, ta ɗauka ta gaishe shi, ya ce"Kin raho?"


Ta ce"Ai har na ƙaraso ma".


Ya ce"Ma sha Allah!".


Bayan ta gama ta fito falo, suna ta fira da Nawwara, nan take faɗa mata ta samu aikin koyarwa a wata primary, tana zuwa kullum daga ƙarfe bakwai zuwa ƙarfe biyu, Nuratu ta taya ta murna, Nawwara ta ce"Kin ga yanzu ke kaɗai za mu dinga bari a gidan kenan, sai na dawo".


Nuratu ta ce"Ai babu komai, Allah Ya taimaka".


Nawwara ba ta taɓa haihuwa ba, saboda tana da matsala a mahaifarta, suna zaune lafiya da Kabir, kuma tsawon shekarun da suka yi bai damu da matsalar rashin haihuwarta ba, mafi yawan lokuta ma shi ne yake nuna mata muhimmancin yarda da ƙaddara, yana kyautata mata da ba ta kulawa daidai gwargwado, sai dai akwai wata ɓoyayyiyar hallayarsa wacce hankalinta bai kai kanta ba, ballantana ta yi nazari, ba ta taɓa sanin Kabir mane min mata ba ne, saboda yana yin komai cikin tsari, sannan ba mai tsananin da za ta yi saurin ganewa yake yi ba. Sau uku tana ɗakko wata yarinyar cikin ƴan'uwanta, domin ta zauna a gidan ko za ta samu ta rage kewar zaman kaɗaici, sai yaran sun zo suna murnar zaman gidan, daga ƙarshe sai su rikiɗe su ce su ba za su zauna ba, duka su ukun ba ta gano dalilin barin su gidan ba, Kabir ba ya iya ɗauke kansa a kan mace, ƙananun yaran nan su uku duk ya gwada masa halinsa, amma bai samu cikar muradinsa ba, wannan halin nashi ne yake korar su daga gidan, dangi duk an sani, ana kallonta a fanko, domin har mahaifiyarta ta sani, amma ta ƙi faɗa mata, kuma ta hana a faɗa mata, sai dai ta taka mata burki a kan sake ɗaukar wata yarinya da sunan riƙewa, ta ɓoye mata ne saboda ta zauna lafiya da mijinta, sai dai tana yawan yi masa addu'ar shiriya, saboda Kabir yana da kirki, yana girmama murane, wannan halin ne kawai matsalarsa.


Da daddare bayan ya dawo sun gaisa da Nuratu, ya tambaye ta ta taho da kayan lefenta? Nan ta sanar masa ai bai yi mata lefe ba, sai kuwa ya hau faɗa yana cewa"Me yake nufi kenan? Wannan fa ya samu dama da yawa wallahi, ga cutarwar da ya yi miki kuma saboda samun sake lefe ma ba zai yi ba? Ki ba ni lambarsa".


Gabanta ya faɗi, saboda ba ta so wani ya gano Abdul shi kansa ba son auren yake yi ba, ta sunkuyar da kai ta ce"Yaya ba haka ba ne, ka san bai daɗe da tafiya ba, duka wata biyu kenan, yanzu ma albashin wannan watan ne fa ya ba da sadakin, ya ce gaba zai yi mini lefen".


Ya taɓe baki ya ce"Allah Ya kyauta, wannan auren amma sam inda an bi shawarata da an bar shi".


Nawwara ta ce"A'a ka daina cewa haka Honey, tun da suna son junansu komai zai daidaita".


Ya ce"Tashi mu je na samo miki kaya, na san nakin duk tsofaffi ne".


Nawwara ta ce"Mu je na raka ku, dama ina son siyan wani curry".


Ya ce"A'a rubuta mata dai ta ɗakko miki, kullum sai kin fita ko gajiya ba kya yi?"


Ganin ta canza fuska kamar ba ta ji daɗi ba, ya yi murmushi ya ce"Ke wai ba ki gane me nake nufi ba ne? Ni dai ki tafi ki yi wannan shirin naki mai gigita ni, kawai ina dawowa na gan ki a turaka, ya fi miki wannan fitar".


Ta yi murmushi tana faɗawa Nuratu sunan curryn, suka tafi tana cewa sai sun dawo.


A hanya yake ce mata"Yanzu ke Nuratu kina tunanin nan da shekara nawa mijinki zai dawo?"


Ta ce"E to, da zai tafi cewa ya yi shekara biyu zai yi, yanzu tun da an yi auren ƙila ma ba zai kai hakan ba".


Ya yi murmushi ya ce"Kuma ke za ki iya riƙe kanki har tsawon shekara biyun?"


Ta ce"To Yaya ka ce zan zauna a gidanka ai, idan ma an kwana biyu zan iya komawa gidan yayan babata, sun ce na koma can, sai na jira sanda zai dawo, idan kuma babu dama sai na fara wata sana'ar na dinga yi wa kaina komai".


Ya ce"Nuratu kenan, ni fa ba wannan riƙe kan nake nufi ba, ai bai kamata mace ta dinga ciyar da kanta ba, ballanatana ma irinki wacce ta haɗa komai da najimi zai so".


Ya gangara gefen titi ya faka motar ya kashe ta, ta kalle shi da alamar tambayar dalilin tsayawar, sai ya kafe ta da kallon da ya saka ta tsarguwa da kuma faɗuwar gaba, ta kau da kai daga kallon shi, a bazata ta ji hannunsa a kan nata, ta kalle shi da sauri, sannan ta kalli hannun nashi, a hankali ta zare hannunta, don ba ta manta wane ne shi ba a wajenta, shi ba muharraminta ba ne, ko ba ta da aure haramun ya taɓa ko da hannunta ne, ta ce"Yaya mene ne?"


Ya ce"Wato Nuratu akwai maganar da nake son mu yi da ke mai muhimmanci, shiyasa na nemi mu fita mu biyu".


Ta yi shiru tana sauraronsa.


Ya ɗan yi shiru yana jujjuya kalaman da zai furta, sannan ya ga kunyar mara kunya ai asara ce, don haka ya fara magana kai tsaye"Nuratu wani auren ana yin shi ne kawai saboda rufin asiri da neman kamala a idon jama'a, kin gan ni a haka kamar ina samun cikakkiyar nutsuwa da matata, amma a baɗini ba haka abun yake ba, wallahi Nawwara sam ba ta san zaman aure ba, don dai ina da haƙuri ne kawai shiyasa har muka kai haka, dama can maleji nake yi, ballantana kuma yanzu da ta fara fita koyarwar nan, idan ta dawo ta yi girki dare ya yi, da na matso kusa da ita za ta fara ƙorafi, tana cewa ita fa duk a gajiye take, cikin kwanakin nan lamarin ya dame ni, ina tsoron na kasa jurewa. Nuraru na san a yanzu kin riga kin san maza, wannan mara kirkin mijin naki ya cuce ki, ya lasa miki zuma a baki".


Ta dai yi shiru tana so ta ji ƙarshen zancen, ta gama sakankancewa so yake ya saka ta, ta nemi saki a wajen Abdul, don ta samu wanda zai aure ta su yi rayuwa mai inganci, sai dai tana nazarin me yasa zai sanar da ita matsalar iyalinsa?


Kabir ya cigaba da faɗin"Nuratu ke ƙanwata ce, na san ba za ki kasa taimakona ba, wannan alaƙar da nake son mu ƙulla ni da ke sunanta taimakon juna, domin za mu dinga yin abin da Hausawa suke cewa ban gishiri, na ba ka manda".


"Yaya alaƙa?" Ta tambaya da mamaki.


Ya ce"Alaƙa mai ƙarfi ma kuwa, ina roƙon wannan alfarmar a wajenki Nuratu, mu dinga ragewa junanmu zafi, tun da ke kin saba da maza kuma yanzu babu damar samun su, ni kuma ga yanayin matata, kin ga ke ƙanwata ce, kuma matar aure, babu wanda zai kawo wani tunani mara kyau a kanmu, amma ya kike gani?"


Ƙwalla ta cika idonta taff, ta ma rasa me za ta ce, gabaɗaya ya ɗaure ta da jijiyoyin jikinta.


Ya ce"Na yi miki alƙawarin duk watan duniyar nan zan dinga ƙirga dubu ashirin ina ba ki, na tabbata kafin mijinki ya dawo kin haɗa kuɗin kayan ɗaki, kin ga ba ganewa zai yi ba, tun da dama can ya gama lalube ki, ya kike gani?"


Tuni hawaye suka wanke mata fuska, ta rasa wane irin zamani ake ciki wanda mutane ba sa jin tsoron Allah, ba sa yin taimako domin Allah, indai wanda ke da matsayin ɗan'uwanta na jini zai so lalata rayuwarta to ina ga Agent wanda ba su haɗa komai ba? Tambaya take yi wa kanta wai meyasa maza suka mayar da kansu tamkar ƴan taure?


Kabir ya kalli agogo a wayarsa yana cewa"Lokaci yana tafiya, na san maganar tana da nauyi, amma zan ba ki dama ki yi tunani, za ki samu ci da sha, har ma sutura a gidana, babu abin da ba zan yi miki ba, duk abin da kike buƙata kawai ki sanar da ni, sannan wannan ba wani abu ba ne mai wahala, da safe idan ta tafi gantalin koyarwarta, ni kuma sai na dawo gida, kamar ƙarfe goma haka, mu samu ko minti talatin ne".


Ta ce"Yaya Kabir mayar da ni gida".


Ya tashi motar yana cewa"Mu je ki yi siyayyarki, ki zaɓo kayan bacci ma su kyau".


Takaici ya hana ta cewa komai, har suka ƙarasa babban shop ɗin, duk yadda ya yi da ita, fir ta ƙi fitowa daga motar, sai shi ya shiga ya siyo mata kayan, wanda yawanci riga da wando ne da riga da siket na roba, sai atamfofi kala uku, da ƙananun abubuwa, irin su towel, soson wanka, brush, da saitin man shafawa da subulai, haka dai kaya rigijib ya kawo mata, sai ta kasa yi masa godiya tun da zuwa yanzu ta fahimci ba don Allah yake yin komai ba.


Da suka dawo gida sun tarar da Nawwara a falo, ta yi mamakin ganin shi ne ya ruƙo kayan ba Nuratu ba, sannan ba ta ce komai ba, ta wuce ɗaki, shi ma sai da ya ji ƴar fargaba, Nawwara ta ce"Lafiya kuwa, na ga ranta a ɓace?"


Ya ce"Wallahi wani ne ya biyo mu wai yana son ta, na faɗa masa matar aure ce, to shi ne fa a mota har da kukanta, tana cewa ban da ƙaddara da tana tare da mijinta ai da wani bai ganta ba ma, ballantana ya ce yana sonta".


Nawwara ta yi murmushi ta ce"Nuratu kenan, ni dai ban ga abun fushi a nan ba".


Ya ajiye kayan, ta ɗauka ta buɗa tana cewa"An samo curryn?"


Ya ce"To ina ma ta bi ta kan wani curry, lokaci ɗaya fa ta birkice kamar mai aljanu".


Nawwara ta ce"To Allah Ya kyauta". Ta kwashi kayan ta miƙa mata, ta tafi ɗakin mijinta.


Nuratu ta zauna tana ta tunanin mafita, indai wannan manufar ce tabsaka Yaya Kabir ya nemi ta zo ta zauna a gidansa, to kuwa gara ma ta zauna a gidan su Abdul ɗin, ba ta fatan ta sake aikata wani kuskuren a kan wanda ta yi, zina babban bala'i ce, ga shi ta sanadin aikatata sau ɗaya ta shiga masifar da take neman yi wa rayuwarta juyin waina cikin baƙar tanda, lallai gidan Yaya Kabir ba wajen zamanta ba ne, ya zama wajibi ta tattara ta koma inda ta fito.


Bayan ta gama shirin bacci, sai ta ɗauki wayarta, ta kunna data, ta yi wa Abdul sallama ta gaishe shi, sannan ta ce"Na sauka lafiya tun ɗazu, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya".


Yana dubawa sai ta ga ya fara typin, daɗin zai kula ta da kuma fargabar abin da zai rubuto suka dira a zuciyarta lokaci ɗaya, yanzu har tana fargabar jin furucinsa a kanta, saboda ba ya faɗa mata magana mai daɗi.


"Ke da waye yanzu a ɗaki?" Abin da ya rubuto kenan.


Ita ma rubutun ta yi masa ta ce"Ni da kewarka ne, ka san gidan babu yara, ni kaɗai ce a ɗakin da aka sauke ni".


Ya ce"Za ki iya yi mini vedion kanki a halin yanzu?"


Ta ce"Gaskiya ba zai yi ba, saboda wayar babu flash".


Ya ce"To gobe da safe ki yo mini vedion jikinki, ban ce ki saka kaya ba, saboda ina buƙatar ganin halal ɗina ne".


Sai da ta ji gabanta ya faɗi da ta karanta, ta sake maimaita karantawa, ta yi mamaki, tun da ta ga yana ta nuna rashin damuwarsa a kanta, sannan ma ta lura kamar dole ce ta saka ya yarda da aurenta, amma har a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login