Showing 24001 words to 24835 words out of 24835 words

Chapter 9 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

6008

ce yana jin kewarta da ta kai har yana neman ganin ko da hoton jikinta ne?"


Ganin ta duba saƙon ba ta ce komai ba, ya sake rubuto"Ko ba zan samu ba?"


Ta rubuta masa"Allah Ya kai mu goben".


Ta ma rasa ta ina za ta fara wannan abun da ba ta taɓa yi ba, amma ta sani a yanzu Abdul mijinta ne, wannan ba haramci ya nemi ta aikata ba, sai dai tana jin nauyi kuma ta ga abun banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Tana cikin duba saƙonni sai ga saƙon Yaya Kabir ya shigo, stika ce ya turo mata ta mace da namiji rungume da juna, sannan ya yi gajeren rubutu ya ce"Zan kwana da kewarki". Don takaici ba ta san sanda hawaye ya sakko mata ba, ta kashe data ta kwanta tana jin zuciyarta babu daɗi, ga kuma rashin nutsuwa a tare da ita, ta san a yanzu idan ta ce za ta koma gida ba ƙaramin yaƙi ta ɗakko ba tsakaninta da Baba, da haka ta yi bacci kanta a cushe.


Washegari da sassafe ta ji motsin Nawwara, ta fito ta gano ta a kitchen, ta shiga ta gaishe ta, sannan ta fara taya ta aiki, suna gama komai ta koma ɗaki, sanda suka fito karyawa Nawwara ta zo ta kira ta, ta ce"Anti sai anjima zan karya".


Saboda ko ganin Kabir ma ba ta son yi.


Bayan sun gama karyawa Nawwara ta leƙo tana ce mata "Za mu tafi"


Ta ce"To Anti, me za a dafa muku kafin ku dawo?"


Ta ce"Ki dafa duk abin da kike ra'ayi, sai mun dawo".


Ta ce"A dawo lafiya".


Bayan sun tafi, ta fito ta ci abinci, ta yi wanke-wanke, ta share gidan ta gyara komai tsaf, maganar Abdul tana maƙale a zuciyarta, don haka ta tashi ta yi wanka, ba ta ji a zuciyarta za ta iya yin vedion kamar yadda ya ce ba, don haka ta yanke za ta saka rigar bacci, sai kuma ta tuna ba ta da wata rigar bacci, rigunanta marasa nauyi ma duk sun tsufa sun ji jiki, ba za ta iya yi wa miji kwalliya da su ba, ta tsinci kanta da duba ledar kayan da suka siyo jiya, ta kuwa ga kayan bacci kala uku, ciki har da wata riga ta net mara kirki sosai, sai ta saka ta, ta ɗauki kanta a hoto, ta kunna data, da saƙon Kabir ta fara cin karo, da alama tun jiya ya turo, don cewa yake yi"Na zo na taya ki bacci?"


Ta yi tsaki, ta shiga lambar Abdul ta yi sallama ta gaishe shi, sannan ta tura masa hoton da ta ɗauka yanzu, yana dubawa ya ce"Mene ne wannan?"


Ta ce"Ba zan iya yin hoto babu kaya ba".


Ya ce"Amma za ki iya ba wa wanu kanki ai ko? Kuma vedio na ce, sannan ina son ganin fuskarki sosai a vedion".


Ta sauke gwauron numfashi, sai dai ta kasa cire rigar, don a ganinta rigar nan ta jikinta da ita da babu duk ɗaya suke, ta yi vedion a haka da rigar, ta tura masa.


Tana turawa ta ajiye wayar tana jin babu daɗi, duk da ba haramun ba ne, sai can anjima ta ɗauki wayar domin ta ga amsar da ya bayar, ƙirjinta ya yi wata mummunar bugawa ganin kamar mutum biyu ta turawa, da sauri ta kalli lambar Yaya Kabir wanda har saƙon ya nuna blue tik alamar ya gani, ta miƙe tsaye tana ɗora a ka, ita ta ma manta da ana delete saboda yadda kanta ya ɗauki zafi, salati kawai take jerowa, wajen minti biyar kafin ta dawo cikin nutsuwarta, ta zo ta goge da sauri.


Kabir wanda daɗi ya gama rufe shi, don wannan alama ce da take nuna ta gama amsar tayinsa, tuni ya tura shi zuwa laptop ɗinsa don ya more kallo da kyau, saboda haka ko da ya ga ta goge bai wani damu ba, sai ma stikar godiya da ya turo mata.


Shi kuwa Abdul a na shi ɓangaren, yana kallon vedion zuciyarsa tana tafasa, wani kishi ne yake azabtar da zuciyarsa, a fili ya ce"Nuratu in sha Allah wannan vedion sai ya zama silar shigarki ƙunci na har abada, wannan vedion sai ya hana ki zaman aure, sai kin dawwama a gida kin tsufa kin mutu babu aure, babu ɗa babu jika, wannan ce hanya ma fi sauƙi da zan rama cin amanar da kika yi mini" .




LAST FREE PAGES!


To mutanena mu numfasa a nan, ko kun hango girman matsalar da Nuratu ta jefa kanta kuwa? Shin da gaske Abdul zai iya take ƙauna ya aiwatar da furucinsa a kan wacce ya fi so duk duniya, ashe ƙauna tana rikiɗa ta zama ƙiyayya? Yaya Kabir zai yi da wannan vedion? Shin zamanta a gidansa zai yi tsayi ko na ɗan lokaci ne? Na ba ku satar amsa? Nura zai yi ta aure-aure a wannan labarin, amma a ƙarshe ya zamansa da Hasana zai kasance? Akwai tarin ƙadarori a kan Nuratu, ku dai kar ku bari a yi babu ku, da ɗarinki biyar ki sha karatu.


8028966015
Sadiya Abdulrazak opay bank


Shaidar biya ta nan
08028966015

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login