Showing 1 words to 3000 words out of 22403 words

Chapter 1 - SARAUNIYAR KYAU Takun Tsakiya FREE PAGE'S BY Nanah KD.txt

Nana Kd   

14 Jan 2025

1751


*🔥 SARAUNIYAR KYAU 🔥*
_-_👑ƚαƙυɳ ƚʂαƙιყα👑_-_



_-_ҽρ.1_5






*بسم الله الرحمن الرحيم*






*MALAM AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT*










Daga yadda gaba ɗaya mutanen dake cikin filin hawa da saukar jirgin, suka bada hankulan su akan kallon ta, hakan zai tabbatar muku da cewa lallai takai a kalle ta.


Wasu kai tsaye zasu kira ta da suna *SARAUNIYAR KYAU* ta duniya koma fiye da hakan idan akwai.






Ɗoss, Ɗosss


Haka sautin takalman da ƙafafuwan ta suke ciki yake tashi a wurin, kai daga Kallon ta sannan ka kalla shigar tsadaddun kayan jikin ta, zaka tabbatar da cewa lallai ba ƙana nan ƙuɗaɗe aka kashe akan ta ba. Ko nace ake kashewa.




Matashiyar budurwar ba zata haure shekaru Ashirin ba a duniya.




Za'a iya cewa Princess Gown ne jikin ta, duba da yadda doguwar gown ɗin ta sauka ma ta har ƙasan gwawowin ta, daga ƙirjinta zuwa ƙasa na gown ɗin a buɗe yake, ma'ana dai a tsage wurin yake.
Golding color ce gown ɗin. Ƙafafuwan ta rufe cikin wasu tsadaddun takalma Strappy Heels, kanta kuwa da gashin yake a waje, kuma a baje, an gyara shi in Blonde wavy hair, launin gashin nata dark brown, Kyakkyawa fuskarta wada ce da make-up na nunawa, gaba ɗaya jikin ta indai wuri ne da za'a saka abin ado tofa akwai, kama daga kunnen ta, yatsun ta, wuyan ta, babu inda ba'ayi ado da gold ba, sheƙi kawai take yi kamar zinariya.








Ƙari sawa tayi wurin Ƴan matan su uku da suke matsayin manyan ƙawaye a gare ta. Kuma tamkar ƴan uwa.


Ibtihaaj ƴar asalin ƙasar Austaraliya mazauniyar Dubai, mabiyiya Addinin Buddha ita da mahaifan ta, sai Ansha, haifaffiyar Najeriya, girman Turai, ta kasance banasariya ce, sannan sai Aahila ƴar ƙasar Malaysia.


Dukkannin su tare suka taso, abin nufi su ɗin ƙawaye ne tundaga primary school da suka yi tare a ƙasar Amurika har zuwa secondary, lokacin shiga University ne ma ƙawancen nasu yaja baya sakamakon ko wacce su abin da take karanta daban, sannan ra'ayin su yasha banban ta wasu fanin.




Sun ɗauki tsawon shekaru biyu basu haɗu da junan su ba, sakamakon yanayin karatun ko wannensu, sai yanzu Ubangiji ya ƙaddara sake haɗuwar su, dalilin Birthday Party na Ansha da mahaifan ta suka shirya ma ta a ƙasa Nijeriya, wanda shi ne zuwa ƙasar na farko da kowannen su tayi harda Ansha da take haifaffiyar ƙasar.


Cike da farin ciki kyakkyawar budurwar cikon ta huɗun su da sai yanzu ta samo ta shigo ƙasar ta rungumo su duka cike da murna na sake ganin juna da suka yi.


"Samiupter D'Souza, ashe zamu sake haɗu wa dama, nayi tunanin shikenan tun da kika koma India mun rabu har abada, sai gashi sanadin Birthday na mun sake haɗu wa gaskiya nayi farin ciki sosai, da hakan ta kasance."




Murmushi budurwar da Ansha ta kira da Samiupter D'Souza tayi tana gyara salon riƙon da tayiwa akwatin dake hannunta, zatayi magana wayar Ansha tayi ƙarar shigowar kira.


"Oh Pappa ne yake kirana guy's mu tafi kawai lokacin fara shagali ya yi, jiran zuwan ki Samiupter shi ne ya saka ma ban yanka cake ba, amma tun da gaki kin hallara muje kawai, daga baya zamu tattauna akan bayan rabuwa da."




Motar su mai tsadar gaske suka shiga gaba ɗaya su huɗun, Aahila ce take Driving nasu, sannan suka bar Airport ɗin.






Samiupter D'Souza dai ta kasance haifaffiyar Amurka ce, sai dai dangin mahaifiyar ta a India suke kuma ƴan ƙasar ne, yau ga Samiupter D'Souza a Najeriya, ƙasar da bata taɓa zuwa ba, sannan kuma gaba ɗaya Ahalin ta babu wanda yasan tazo ƙasar domin Birthday Party.🩸








*MENENE ZAI FARU GABA?.*😏










*ABUJA*
*NAJERIYA*






A kalla takai mintuna goma da parking motar, a cikin gidan ƙanwar ta Sailuba.






Ƙafarta ɗaya ta fara fitowa da ita, bayan wani lokaci kuma ta fito gaba ɗayan ta daga cikin motar, kai tsaye babban palon ta nufa.








Sallama ɗauke a bakinta ta ƙari sa shiga cikin palon.


*Fadeelah*
Yau bata da lecture saboda haka, tana zaune a palon tana kallon wani Turkish drama.




"Wa alaikumus-salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu."




Ta amsa sallamar da taji tare da juyawa don ganin mai yin sallamar.




Tsakanin tashin ta daga inda take har ƙari sawar da tayi wurin baƙuwar tasu, ta tarbota da farin ciki bayyane saman fuskarta, ta gaisheta ta, ta amsa, taje kitchen ta samo ma ta abin taɓa wa, ta kawo ma ta, cikin girmamawa, har fitowar mahaifiyar su, Hajiya Sailuba daga Bedroom ɗin ta, da shigewa Bedroom da suka yi, su barta anan palon.




Duka lamarin ya faru ne fuskar Fadeelah wadace da murmushin farin ciki da jindaɗi.


Tana matuƙar girmama Momy Rafi'at sosai, a sakamakon buri da take dashi, sannan tasan muddun ba tayi ma Momy Rafi'at biyayya tun yanzu ba, tofa hakan zai iya hana burin nata cika.




*A TUNANIN TA*












Burin tayi ta kammala kallon da take yi domin zuwa Gidan Uncle Mai Kyau, don ganin Yaya Maleek da ake faɗa ma ta ya dawo gida.




Sai kuma gashi Momy Rafi'at tazo gidan wurin Hajiya, hakan kuma ya yi ma ta daidai.




Ba tare da wani ɓata lokaci ba, da shigar Momyn nasu da kuma Momy Rafi'at Bedroom, ita ma ta miƙe ta nufa Bedroom na ta domin ta yanke zata bi Momyn ne kawai zuwa gidan Uncle Mai Kyau ɗin.


Kayan ta kala goma ta saka cikin akwatin ta sannan ta haɗa da duk wani abu da zata buƙata, tayi wanka tayi make-up ta shirya ta zauna gefan gado tana jirar fitowar Hajiya Rafi'at.










*KANO*
*NAJERIYA*




Da sauri tayi reverse da motar cikin tsananin tashin hankali yayin da ta ɗa go kanta a hankali don ganin ta kaɓe wani ko wata. Don kuwa yadda taja baya da motar da kuma yadda taji ta burge wani abu, tunaninta bata yake yi ka karɓe wani.








"Afeefah kina lafiya kuwa, dawo back seat kawai, bari ni karɓa tukin naga kamar bakya hayyacin ki, gashi zaki saka muyu accident a titi."






"Kafin nan mu fara duba motar da ta bige, wata ƙila ma tayi musu ɓarna."


Cewar Mah'eesha tana kallon Lailah wacca tayi wa Afeefah maganar cike kulawa.




Fitowa suka yi daga motar bayan Afeefah tayi parking a gefe, domin kuwa a titi suke.


"Kuyi haƙuri fa, mun kusa muyi muku ɓarna a mota, sorry Afeefah ɗin ce sai a hankali kuma take tuƙi our apologize."




Mah'eesha ce da tare da Lailah suke wannan maganar wa Ƴan matan da Afeefah ta bugewa mota.




"Oh nothing, ae bata mana ɓarna ba, babu komai fa."




"Yauwa Sister mun gode sosai."


Lailah ta amsa wa ɗaya daga cikin ƴan matan wacca ta basu amsa.


Yayin da idanunta suke a kan su duka, sai dai ɗaya take yiwa kallon sa ni.




Komawa mota sukayi sannan Afeefah wacca bata fito ba, ta matsa gefe Lailah ta zauna a mazaunin driver sannan ta ja motar kai tsaye har Gidan Yaya Shahid dan nan suka nufa dama su uku ne, ita Lailah ɗin sai Afeefah da kuma Mah'eesha, Deejarh taso ta bisu amma ciwon mara da take yi yasa Afeefah ta ce ta zauna a gida kawai.


Da isarsu gidan mai gadi ya buɗe musu gate ta shiga ciki, ta daidai ta parking, sannan suka fiffito a tare suka nufa palon gidan.








Kwankwasa ƙofar palon Mah'eesha tayi tana ƙara wa cikin ƙunƙuni, dama tasan indai wannan baƙar Aeezath ɗin ce sai ta shanya su, sannan zata buɗe ƙofar.




"Au dama haka kuke ma ta idan kun zo ke nan. No wonder take muku abin da take yi, don ko ni ce dai dai Abin da tayi zanyi fa."




Afeefah ce take wannan maganar a yayin da take kallon Mah'eesha ɗin.




"Me kike nufi da wannan maganar Afeefah ban gane ba, menene nayi ɗin?, nasan dai iya knocking nayi kuma taƙi tazo ta buɗe dama haka ta saba halinta ne."




"Bafa halin ta ba, fisabilillah yanzu da ƙari sowar mu nan bakin ƙofar, ko fa mintuna biyu bamu yi ba, amma harkin fusata saboda batazo ta buɗe ƙofa ba, kiyi ma ta uzuri mana, kika sani ko tana kitchen ne ko kuma tana sama, kodai tana wani abun?, Gaskiya Mah'eesha a wasu abubuwan da kuke faɗin tana muku, kuma harda laifin ku fa, duk kun bi kun tsaneta haba."




Iya kar gaskiyar ta Afeefah take faɗa wa Mah'eesha haka ɗin, domin kuwa ta fara fahimtar abubuwa da yawa akan su duka, daga ita Aeezath ɗin wacca ko taɓa haɗuwa ita Afeefah ɗin bata yi ba, sakamakon lokacin da aka yi auren Yaya Shahid ɗin bata ƙasar, shekaru biyu baya, tana India wajen jinya, kuma sannan ba'a ƙasar ya zauna da matar tasa ba, ko watanni huɗu basu yi da dawowa Nigeria ba, tsakanin jiya da yau ta fahimci wasu daga cikin halin rashin kirkin da su Mah'eesha ɗin suka ce matar Yayan nasu Aeezath take nuna musu, su suke ja ma kansu, domin idan ta duba da labarin da Haseeya ta basu jiya da dare na cewa wata ƙawar Mah'eesha ɗin taso Yaya Shahid sosai, amma yaƙi aurenta ya aura Aeezath.
Idan ta cinka a iya tunanin ta saboda Yaya Shahid ɗin yaƙi auren ƙawar ita Mah'eesha ɗin ce shiyasa ta tsana matar da ya aura Aeezath.




Shiru Mah'eesha tayi bata ce da Afeefah ɗin komai ba, sai dai tunani take a zuciyarta ko shin Aeezath ta taɓa musu wani abu da basu ji daɗi ba, wanda kuma basu suka jama kansu ba, bata taɓa musu kallon rashin kirki ba, har sai sun fara ma ta tukunna take biye musu.




Buɗe baki Lailah tayi zatayi magana, sai dai maganar cak ta tsaya a bakinta sakamakon ganin mutumin da ya buɗe musu ƙofar palon da tayi. Dogo murɗaɗɗe dashi kuma Kyakkyawa mai kama da Uncle Sagir sanye da normal singlet da wanda 3 quarter.






Kawar da idanunta tayi daga Kallon sa yayin da a bakinta take furta kalmar gaisuwa garesa, suma su Afeefah suna gaishe sa.


Bai amsa musu ba ya basu hanya suka shiga ciki, sannan ya mayar da ƙofar ya rufe yana mara musu baya.


Saman haɗaɗɗun kujerun palon suka zazzauna suna kuma gaishe dashi, sai da ya zauna saman kujerar Dining da yake sannan ya amsa musu yana haɗawa da tambayar ya ya suke.




Cike jindaɗi Afeefah ta amsa masa tana haɗawa da masa tambayar.




"Muna lafiya lau, Yaya Shahid hala dai Anty Aeezath ɗin ba nan ne?."


"Masha Allah, wai Darling tana kitchen qiwa ne ya hanata tashi tun safe sai yanzu wuraren ƙarfe sha biyu take haɗa mana breakfast, duk ta bar muku ni da yunwa."


"Lallai anty Aeezath ta cancanci tuhuma tunda har tabar mana Yaya Shahid guda da yunwa har sha biyu, bari na bita kitchen ɗin sai naji dalili."


Afeefah tayi maganar cikin dariya sannan ta miƙe tsaye bayan ta a je mayafin kanta a saman kujera ta nufa kitchen ɗin.




Murmushi Yaya Shahid ɗin ya yi yana bin bayan Afeefah da kallo, Yarinyar tana burgesa tun daga kan nutsuwar da take dashi, kyawunta, da sauran su, shiyasa ko cikin yaran dangi yafi shiri da ita, daga ita sai Husnee da kuma Zaynerb yake sakarwa fuska, wani lokacin harda Lailah.




"Lailah yakike?, wai da gaske Maleek ya dawo, na fa kasa yarda."


Yaya Shahid ya yi maganar bayan ya mayar da kallon sa akan Lailah da take zaune gefan, Mah'eesha da tayi tsit a palon dan kuwa ba kaɗan ba take tsoron Yayan nasu, domin babu wasa.








"Eh wallahi Yaya Shahid ashe ka sama labari yau ina ga kwanan sa uku ke nan da dawowa fa."


Lailah ta basa amsa tana gyara zamanta cike da son suyi fira dashi.




"Ɗan kwal uba yaji wuya ya dawo, ae naso ace ina nan lokacin da ya dawo da bazan bari Uncle Mai Kyau ya yafe masa da wuri ba Allah kuwa."




Dariya Lailah tayi jin abin da Yaya Shahid ɗin yake faɗa, dama sun saba irin haka da Maleek ɗin domin sa'annin junane su ɗin, duk da dai Yaya Shahid ɗin ya bawa shi Maleek kusan shekara, Yayin da shi kuma Maleek yaba mah'fuz da Yasir shekara da watanni shiyasa duka suke kansu ɗaya, kuma abokai, domin kuwa idan Maleek da Shahid suka haɗu wuri ɗaya rantse wa zaka yi abokan wasa ne, saboda yadda suke abu kamar wasu abokan wasa.




"Huh Yaya Shahid ke nan, ina baka labari sai ma lokacin da Daddy yake cewa bai yadda Yaya Maleek da ya zauna masa a gida ba, har sai ya fito da mata, a lokacin kwatsam yace Husnee yake so, ita kuma tsaban gulma harda wani faɗin zata je tayi shawara, ina faɗa maka ta shige Bedroom ɗina ta sha rawa da waƙa ta fito, tana wani kyaɓe fuska na wai ta ce amince."🤣






Dariya Yaya Shahid yana a je cup of coffee dake hannun sa yace.




"Kaji ƴan rainin hankali dukansu son junan su su ke yi, dama tun kafin yanzu na daɗe da sanin cewa Maleek yana son Husnee, dan haka amfani ya yi da damar sa kawai a ranar ya jefa tsuntsaye biyu da dutse ɗaya, babu komai zai gamu dani, zamu haɗe, Allah ya kaimu nazo Abujan."


Dariya Lailah keyi nan dai suka ci gaba da fira dashi, Mah'eesha tana daga gefe tana ɗan tsoma baki idan an sakata a wani abin.😉






Da sallama ta shiga kitchen ɗin yayin da take hangen matar da ta juya baya tana aiki cikin kitchen ɗin.








"Wa alaikumus-salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu."


"Barka dai Matar Babban dama nazo tayaki aiki ne, Yaya Shahid yace qiwa ya hanaki tashi sai yanzu kike masa breakfast."




Cewar Afeefah bayan Aeezath ɗin ta amsa ma ta sallamar da tayi.


Murmushi tayi tana faɗin "Lallai ma wannan mutumin sai kace bashi ne ya hana ni motsawa ko nan da can ba, shi ne zai wani ce qiwa ya hana ni yi masa breakfast Aikuwa zai gamu dani tabbas."😚


Dariya kawai Afeefah ta kuma yi tana faɗin
"Yaya Shahid ke nan, wato shi ne yazo qiwa ya hanaki ko Humm. Ni bama wannan ba, Matar Yaya ni fa kama kike min da wata ƙawata da muka yi school tare a Jamus gaskiya kuna kama sosai."




"Allah Sarki shin ko dai Adivat kike nufi?." Aeezath ta tambaya tana kallon Afeefah ɗin.


Cike da farin ciki Afeefah ta amsa ma ta da "Eh wallahi sunan ta Adivat school ɗaya muka yi da ita a Jamus, tunda muka rabu, ban sake haɗu wa da ita ba."


"Ayya Aikuwa ta kwana gidan sauƙi domin ƙanwa ta ce uwa ɗaya uba ɗaya muke da ita."




Zaro ido Afeefah tayi tana kuma kallon ta ciki gyaɗa kai take faɗin


"Babu shakka domin kuwa ga alamu nan ya bayyana ɓaro ɓaro kuna kama sosai ita, Allah Sarki ko yanzu tana ina oho."




Afeefah ta ƙarisa maganar nata da alamun tayi kewar ƙawar karatun nata Adivat.




Aeezath tana ɗauraye plate's dake hannunta ta amsa ma ta cewa.


"Ai Adivat yanzu tana can U.s tana karatun ta a can tama kusa kammala, domin ina ga a wannan shekarar zata kammala, kin san karatun likitanci take shiyasa ma ta daɗe bata kammala ba."


Karɓar plate's ɗin Afeefah tayi tana faɗin
"Allah Sarki kice abu ɗaya muke karanta da ita, aikuwa Insha Allah kafin mu koma Abuja zan karɓa lambarta a Wurin ki."


Afeefah tayi maganar tana jere plate's ɗin a wurin da ya kamata sannan ta ci gaba da taya Aeezath ɗin.




"Okay babu damuwa, in ce dai ba yau ne zaku koma na ko?."


Aeezath ta tambaya


"Yau ne anjima ma kuwa, Around 4:30pm Insha Allah mun sauka a Abuja ma."




Afeefah ta bata amsa tana ci gaba da cewa
"Amma Please na tambaye ki mana, wai menene a tsakanin ki dasu Mah'eesha ne haka, na lura sam bakwa shiri fa, ko zan iya sani Please?."


Afeefah ta ƙari sa maganar ne a daidai lokacin da Mah'eesha ta shigo kitchen ɗin, batare da kallon su ba, don taji Abin da Afeefah ta faɗa, ta wuce can ta ɗauki ruwa a fridge sannan ta buɗe gorar ruwan tana sha.


A daidai lokacin kuma Aeezath take bawa Afeefah amsa da cewa


"Kin san a rayuwar nan kowa abin da yaga zai iya yake yi. Ni a tsarina indai mutum ya nuna baya yi na, to nima fita harkar sa nakeyi, na sani ana cewa bani da kirki, sai dai rashin kirki na akan wanda ya gwadamin rashin kyautawa nakeyi, sun nuna ban musu ba, shiyasa na fita harkar su gaba ɗaya, yanzu idan aka min magana ae zan kula Mutum, bazan sha re shi ba, wasu kawai suna wahal da kansu ne akan ga ba dani wallahi."






Gaza haƙuri Mah'eesha tayi sai da ta juya ta kalla Aeezath sannan tayi ma ta tambayar da ta daɗe a zuciyarta tana so tayi ma ta bata sama dama ba, sai wannan lokacin.




"To idan maganar ki haka ne, me saya ranar da muka fara zuwa gidan nan wurin ki ni da Haseeya da Hameeda kika kulasu baki kulani ba?."




Murmushi Aeezath tayi sannan ta bata amsa da faɗin


"Saboda a lokacin na sama labarin kece wacca bakya so na cikin familyn Shahid saboda ya aure ni, bai aura ƙawar ki ba, ko ba haka bane?. Wannan ne yasa bana shiga harkar ki ba komai ba."






Shiru Mah'eesha tayi ba ta ce komai ba, sai zare ido.🙄












*Mrs Mai Kyau*




"Sailuba ke fa nake jira baki ce komai ba tunda na faɗa miki maganar da ta kawoni wurin ki fa?."




Momy Rafi'at tayi maganar tana kallon Ƙanwar nata Hajiya Sailuba domin jin amsar da zata bata akan maganar da tazo ma ta da'ita.




Dogon numfashi Hajiya Sailuba taja tana kallon Yayarnata cikin nazarin maganar da ta faɗa ma ta tun shigowar su Bedroom ɗin.




Sannan ta ce




"Yanzu idan na bari Fadeelah ta aura Maleek kamar yadda ki ka so shin bakya ganin hakan zai iya kawo matsala tsakanin, Yaranki da dangin Mahaifin su, kuma naji kince Maleek ɗin ya riga ya zaɓa wacca zai aura cikin yaran dangi, to menene manufar ki akan cewa kina so ya aura Fadeelah, ni fa gaba ɗaya ban gane inda kika dosa ba Wallahi sam."


Ƙayataccen Murmushi Hajiya Rafi'at tayi tana juya idanunta akan ƙanwar nata Sailuba sannan ta ce






"Ina da dalilai da yawa da yasa nace miki ina so Fadeelah ta aura Maleek, biyu daga ciki kawai zaki iya sani, sune na farko, idan Fadeelah ta aura Maleek

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login