Showing 1 words to 3000 words out of 19186 words
Chapter 1 - Zuciar Mutum Book 2 Complete Hausa Novels By Takori.txt
[9/15, 2:47 PM] Asmau: ZUCIYAR MUTUM…….
…….BIRNIN SA……
2
Yau yana ofis ayyuka sun kacame masa, sakatariyarshi ta sanar da shi yana da baquwa. Ya dube ta ya ce, “kin ganni dai damn too busy...... ba zan iya ganin kowa ba, tana iya dawowa gobe idan ta matsu”.
Ta fita ta shaidawa baquwa. Ta sake dawowa ta sanar da shi cewa,
“Ta ce kwarai take son ganin ka a yau”.
Ya yi mamaki don kuwa bai fiye yin baki mata ba. Ba tare da ya tambayi ko wace ce ba ya yi mata umarnin ta shigo da ita.
Farida Alqasim, ta bayyana a ofishin, cikin kwalliyar ‘cotton lace’ fari sol mai ban sha’awa. Ta yane kanta da dan share-sharen gyale kalar adon leshin jikinta.
Duk inda ake neman kyakkyawar mace choculate colour to Farida ta kai, har ta so ta wuce. Tana taku dai-dai cikin tsinin takalminta.
Lumsassun idanunshi ya sanya mata har ta yiwa kanta matsuguni a kujerar da ke fuskantar shi. Dan siririn bakinta dauke da lallausar murmushi a sanda take zama.
Ta ce, “Kana mamakin ganina ko?”
Ya lumshe ido ya bude ya ce, “Dole in yi mamaki, ashe talaka na ganin ku?”
Dariya ta yi, “Abdulhakim ke nan, long time!”
Ya ce, “Farida-Farida-Farida! Ya ya a kai kika tuna dani?”
Ta ce, “Mance mutum irinka ba abu ne mai sauki ba”.
Hararar ta ya yi, amma sai ta dauka irin kallon da yake mata a baya ne. Sun dade suna kallon juna, kowanne da abin da yake tunawa.
Shi yana tuna dacin soyayyarta daya dandana ya gode Allah. Ita kuma tana tuna lokuta mafi muhimmanci a gareta, wato lokacin tarayyarsu tun a jami’ar Nsukka.
Ta tabbata mahaifinta ya cuceta, tunda gata nan tana ta bokon banda Alhazan birni har yanzu ba wani kwakkwaran mashinshini. Ko da yake ba mashinshinin ne babu ba, nagartacce na kwarai kamar Abdulhakim ne babu, duk sai Suger Daddies irin wadanda Babanta ke so ta aura kenan.
Wanda shi ma a yanzu ya zo yana nadama. Ya so ya nemi Abdulhakim don ya ba shi hakuri inda ya ji daga majiya mai tushe cewa tun a lokacin ya yi aure da ‘yar aminin mahaifinsa.
Haduwarshi da Farida ta faro ne a jami’ar Ahmadu Bello, suna karanta kwas daya. Sai dai yana gaba da ita da shekaru biyu. Ita kadai ce mace cikin masu yin wannan course din a ajinsu. Don haka Abdulhakim ya ga karfin halinta, kuma ta birge shi. Don yana son mutum mai karfin zuciya a karatu mai wahala .
Sun fara gaisawa ne ta dalilin abokinshi Nura Sule, wanda ya kasance aboki ga yayan ita Farida Mohammed Alqasim. Cikin dan lokaci soyayyar junansu ta kamasu, musamman da ta fara neman shi da ya fahimtar da ita abubuwan da suka shige mata duhu. Ta gane Abdulhakim qwaro ne a kan fanninsa da ya yiwa sauran ‘yan ajinsu fintinkau saboda dinbin fasaha da basirar da Allah ya bashi.
Lokacin da Abdulhakim ya kammala karatu, Farida tana shekararta ta uku, duk da haka basu rabu ba suna tare a waya kullum, sannan in ta zo week end gida Kaduna da yake ‘yan Kaduna ne yana zuwa har ta koma.
Daga baya ne su Farida suka koma Abuja, lokacin da babanta ya samu hayewa kujerar Senator na Southern Kaduna. Har zuwa lokacin da Farida ta kare karatu, ta gabatarwa da iyayenta Abdulhakim a matsayin mijin da ta zaba.
Budar bakin mahaifinta sai cewa ya yi,
“Mene matsayin ubanshi?”
Ta ce, “Alkali ne”.
Ya ce,
“Shi kuma yaron aikin me yake?”
Ta ce, “Bai dade da samun aiki da ‘Julius Barger’ ba”.
Senator Alqasim ya yi tsaki ya ce, “Kin gane ko Farida? Bana son ki da auren kananan mutane, ke kadai ce ‘ya mace cikin ‘ya’yana, ina sonki da auren da za ki huta ba in daure akuyar ta dawo tana ci min danga ba.
Don haka ba zan karbi maganar wannan yaron ba, ki ci gaba da karatunki har Allah ya kawo miki daidai ke”.
Farida ta rasa inda za ta sa kanta, don hakika tana son Abdulhakim dinta, shi din take so ba wai abin hannunshi ba.
Ta yi kuka ta yi roqon duniya amma Sanata Alqasim ya ki. Don haka da aka kawo kayan auren Abdulhakim a take ya juyar dasu da abinsu, wanda kuma hakan ya fusata Alkali Khalil Ribadu, ya nemawa Abdulhakim aurena. Duk abubuwan da suka biyo baya kun ji su.
Masoya kam Farida ta gansu kala-kala, sai dai duk ba irin wadanda take so ba. Sai zabin babanta wanda ita kuma ta ki yarda.
Ta fara karatun masters a jami’ar Ahmadu Bello, a halin yanzu ta kammala sai rubutun project take.
Mahaifin Farida shi da kanshi ya zauna ya yi tunani ya gane bai kyauta ba, ya yarda Farida ba za ta taba son kowa ba bayan Abdulhakim Ribadu. Rashin aurenta ya dame shi. Don auren da yayi mata da abokinsa bata dade ba ta kashe auren ta fito. Don haka ne ya soma neman inda zai ga Abdulhakim, a lokacin aka sanar da shi ba ya kasar yana Beirut kuma ya yi aure.
Ya yi kiran Farida ya ce ya amince mata ta nemi Abdulhakim su sasanta in har ya amince zai aure ta, ko da a ta biyu ne ya amince.
Farida ta rasa inda za ta sa kanta don farin ciki, gani take kamar har ta auri Abdulhakim ta gama, don ta san Abdulhakim din ba zai taba iya daina sonta ba, ko da kuwa a ce mata goma ya aura kuwa, balle mace daya.
Don haka ne yau tayo tattaki har Lagos ta cimma shi a ofis. Abdulhakim ya canza, ya kara gigita ta.
Ofishinsa kadai abin kallo ne, balle shi mamallakin ofishin, wanda ya yi wani irin lallausan kyau hade da murjewa tabbacin ilimi da naira sun zauna da gindinsu.
Yana sanye da baqaqen ‘suit’ wadanda ya matse wuyansa da ruwan tokar tie mai santsi, kafafunshi cikin bakin rufaffen cover kirar Italy ya tara lallausar suma a kanshi.
Idan ka yi mishi kallo daya ba za ka so ka dauke idonka ba. Haduwarshi ta kai inda kowacce lafiyayyar diya mace ke buri duk kyau, nasaba da iliminta. Har ta ji ta raina kanta. Da duk abinda take taqama da shi.
Sai dai hakan ba ya nufin za ta kasa isar da saqon da ya taso da ita gari ya gari tun daga Abuja har Lagos. Da ganin shi ka ga daya daga cikin ‘yan gatan ma’aikatan ‘Julius Berger’ tsantsa. Wadanda ke daga gaba-gaba, ake kuma matukar ji da su.
Ganin ta yi shiru tana tunani sai ya kawar da shirun ta hanyar cewa,
“Ya ya Farida meye labari? Ya ya Mohammed? Kuma ya ya maigidanki?”
Ta daga fararen idanunta ta kalle shi, amma ta kasa jurewa, sabida yadda gabadaya Abdulhakim din ya canza mata, da tsabar kwarjinin da yayi mata, babu wannan lallausar kallon da yake yi mata a da cikin fararen kwayan idanunsa.
Gwiwoyinta suka yi sanyi, ta sunkuyar da kai idanunta cike da qwalla, ta samu kanta da yanka karya ba tare data shirya ba.
“Ban yi aure ba”.
Cikin mamaki ya dube ta amma sai ya boye mamakin nashi. Ta kara da cewa,
“Mohammed ya yi aure yana N.N.P.C na nan Lagos, a hidansa na sauka, shi ma yana tambayarka, ya yi takaicin rashin aurenmu.
A yau na zo ne Abdul musamman don in baka hakuri, in kuma isar da saqon Daddyna na cewa ya gane ya yi kuskure mu dawo da soyayyarmu, don tunda aka yi haka ban kara sauraren kowanne namiji ba. Ka yi hakuri Abdul, Daddy ya yi nadama ka yi hakuri mu yi aure......”. Sai hawaye sharr-sharr.
Bai katseta ba har sai da ta gama. Sai dai zuciyarshi ta sosu da kukan da take yi, ba ya son ganin mace na kuka, musamman a dalilinsa.
Ya ciri tissue guda uku ya mika mata, ya ce,
“Share hawayen”.
Ta karba tana sharewa. A ranshi yana fadin rashin aurena da ke Farida rahama ne a gareni, alheri ne mai dimbin yawa, don hakan ne ya yi sanadin da na samu matar Abdulhakim wanda har yau ban qosa da tarin kuruciyarta ba.
Ya bude murya sosai ya ce,
“Farida kina da labarin na yi aure?”
Ta daga kai ba tare da ta hada ido da shi ba.
Ya ce, “To kin shirya zama da talaka mai mata ne?”
Furucin ya taba zuciyarta sosai, don haka ba ta ba shi amsa ba.
Ya kura ma hoton matar Abdulhakim dake cikin wani dan kyakkyawan frame ido dake kan teburin shi, sai murmushi take cikin uniform dinta. Shi ma murmushin ya yi mata kamar tana kallon shi, rabon shi da ita yau kwanaki biyar, yana tunanin nan ba da jimawa ba zai canza akalar rayuwarsu zuwa irin ta kowadanne ma’aurata na hakika, don in bai manta ba Abbanta ya gaya mishi watan Aprilu mai kamawa Sakinah za ta cika shekaru goma sha biyar. Wanda shi ne target point dinsa na mika mata akalar rayuwar shi.
To kuma sai ga Faridah, wadda har gobe akwai birbishin sonta a zuciyarshi, don tana burge shi saboda hazaqa da jarumtakarta a fannin karatu. Tana ba shi sha’awa don ta san kanta, ta san yadda za ta nuna mashi soyayya mai tsabta ba ta sakarci ba, wai don ta yi zurfin karatu. A kamile take, cike da aji da sanyin zuciya, yadda ya san ba zai sha wahalar lankwasa ta ba duk tarin ilmin ta.
Ganin ta yi shiru ya sake cewa, “Ina da mata Farida. Shekaru biyu da rabi kenan da aurenmu. Na dauki al’amari na dake a qaddara ban kullaci kowa ba. I hold nothing against you dear....... balle kuma Babanki wanda ke da iko da damar zaba miki mijin da ya dace dake.
Zan iya auren ki a matsayin mace ta biyu Farida, domin har gobe ina sonki. Sai dai bana jin iyayena za su kuma yin murna da maganar ki, domin mahaifina ranshi ya baci sosai. Don haka ki bani lokaci in yi tunani, ki yarda har gobe ban daina tuna ki ba, da lokutanmu na baya”.
Ta yi ajiyar zuciya mai karfi irin ta samun salama a zuci, ruhi da gangar jiki. Ko da wannan ta tsira ta gode, ta yarda Abdulhakim bai manta da ita da soyayyarta ba.
Ta ce, “Kamar kwanaki nawa zan baka? Don am eager in san matsayina”.
Ya yi murmushi sosai yana tunanin yadda za su kwashe da Matar-Abdulhakim in ya ce zai kara aure, don ta sha fadi mishi ba ta so tunda kananan shekarunta, balle yanzu da ta fara mallakar hankalin kanta.
Ya ce, “Ki bani kwanaki bakwai, insha Allahu za ki ji komai, in yin yin, in barin barin. Ki gai da Mohammed”.
Suka yi musayar lambar waya ya rakota har inda ta adana motarta. Ya dade tsaye a wurin yana tunani, daga baya ya koma ofis.
Ganin tunanin ya dame shi ya tattara komai ya yi gida. Don ya kasa hattama aikin. Tausayin Farida fal ranshi, ya kuma yarda da soyayyar da take yi mishi ne ta hanata aure har zuwa wannan lokacin.
Ya yi wanka ya zuba shirt da wandon DKNY ya kwanta cikin resting dake falonshi, Kukun shi Alfa na shirya mishi abinci a tebir. Shi kuma yana ta ansa call a wayoyinshi.
Ya yi kiran Abdallah ya ce,
“Ko za ka iya zuwa nan Lagos muyi wata shawara?”
Ya ce, “Gaskiya bani da sararin aiki, mu hadu dai next week a gida. In ce ko lafiya?”
“Lafiya sai alheri, sai mun hadu dai”.
Yana kashe wayar kirana na shigowa, ya kashe ya kirani da tashi wayar.
“Ya ya aka yi matas?’
Murmushi na yi kamar yadda na tabbatar shi ma murmushin yake yi.
“Za ka zo Friday?”
“A’a, sai upper week”.
Kamar na yi kuka, na ce,
“Amma me ya sa Mijin-Sakinah?”
“Common matas! Aiyuka ne sunyi yawa, ki yi hakuri, ki yi min uzuri kin ji babyna?”
Na kyalkyale da dariya,
“Nice ma babynka?”
Ya ce, “Ke baby ce man kamar teddy, ko in siyo miki teddy ne? Jiya na gansu bula-bula a wani boutique”.
Na ce, “Don Allah ina so”.
Ya ce, “Na yi alqawari zan kawo teddy”.
Ranar yau na dawo gida dauke da matsananciyar yunwa, abin haushi na samu Sabuwa ba ta nan ta barwa mai gadinmu Buzu sallahun wai ta je can gidanmu duba jikin Yaya Suwaiba.
Na cillar da jakar na tube socks da sandal suma na yi wurgi dasu na fada kicin. Na bude firji duk lemukan sun kare, sai ruwa mai sanyi na daddaka.
Na soma tunanin abin da zan dafa wanda ba zai dauki lokaci ba. Don haka na dauko Indomie guda biyu na soma soyawa tare da kwai.
Ban ji takun mutum ba sai wani abu mai laushi na ji yana zungurina. A razane na juyo na yi arba da dindimemiyar ‘teddy bear pink’ mai shegen kyau.
Na yi tsalle na rungume shi, shi ma ya makaleni muna kyalkyala dariya. Na ce,
“Amma ka yi min bazata mijin sakina, kai da ka ce sai upper week?”
Ya rausayar da kai yana ta kallona da wani irin sassanyan murmushi a fuskarsa, ya ce,
“To ya zan yi? Tunanin Sakinata ya hanani aikin, dole in zo in ganta in ina son kwanciyar hankalina”.
Dukkanmu bamu ankara ba, sai kauri muka ji yana tashi a gidan. Da gudu na yi kan girkina, na tadda Indomie na da kwai sun kone qurmus. Shi kansa frying-fan din ya yi bakikkirin.
Kamar inyi kuka don haushi, sai kuwa ga kukan ya zo, amma ba mai sauti ba. Na kashe gass din na sauke ina share hawaye. Tsaye ya yi a bakin kofar ya ce, “Kukan na mene ne?”
Na ce, “Bayan girkin da na sha wahala na yi ya kone?”
Dariya ya yi, ya karaso ya kama hannuna ya rike cikin nasa.
“Konewar girkin laifin wanene? Cewa nake laifi na ne? Sai yaushe za ki girma ne matar Abdulhakim? Ki daina yin abubuwa irin na su Nazir mana? Da abin da ya isa, da wanda bai isa ba ki dinga zubar min da tears dina”.
Ya fada yana share min hawayen da hankicinsa.
“Kada ki yi fushi, ki dafa wani, nima ki dafa dani ina jin yunwa”. Na ce,
“To”.
Cikin minti ashirin na kammala muka zauna a tsakiyar falo ba bisa tebir ba, ya nado taliyar a fork (cokali mai yatsu) ya ce,
“Bude bakin”.
Na bude ya saka mini na cinye, ya sake kawo min wata lomar na karba, sai nima na debo da nawa cokalin na ba shi. Yana murmushi ya amsa.
Haka muka ci abincin har muka qoshi. Na kwashe kayan na kai kicin. Ya yi kwance cikin doguwar leather da suka yiwa dakin kawanya ya ce,
“ Bani labari me da me ya faru in my absence this week?”
Na ce, “Abubuwa da yawa, munje ‘quizz’ Queen Amina College Kaduna da motar makaranta, kuma school dinmu ne ta dau kofin”.
Ya ce, “Weldone! A kan me aka yi quizz din?”
Na ce, “Wadanne abubuwa ne idan anyi eradicating dinsu (kau da su) Nigeria za ta samu ci gaba tsakanin rashin adalcin shuwagabannin mu da hauhawar farashin man fetur?”
Ya gyara kishingidarsa sosai yana dubana, “To ku wanne bangare kuka kare?”
Na ce, “Muna bayan hauhawar farashin man fetur”.
Ya kalle ni sosai ya ce, “Ni kuwa sai na ga adalcin shuwagabannin mu garemu ya fi komai, tunda ba sai ana cikin kwanciyar hankali za a sayi man fetur din ba?”
Na yi murmushi na ce, “Haka ne. Sai dai ka san quiz ba ‘reality’ ke ba da makin ba, a’ah, hujjoji kwarara da points din da ka kawo sune”.
Ya sunkuyo gabana yace, “….Give me a kiss Sakinah….!”.
Na rufe fuska ina murmushi, na kuma zura daki da gudu. Ya biyoni dakin ya ga ina zaro lokas da alama neman wani abu nake.
Ya ce, “Me kike nema?”
Na ce, “Report card dina”.
Na ciro na mika mishi. Ya karba ya duba ya bude min hannunshi, da sassarfa na tafi, sai kuma na kara da gudu-gudu na shige, ya mayar ya rungume yana shafa kwantaccen gashin kaina yana lumshe idanu.
Ya ce, “Sakinah har tsaho kin kara......”
Jin sautin shi da yanayin jikinshi ya sauya sai na yi kokarin zamewa amma na kasa, ya soma kissing dina passionately. Ji na yi nima numfashina yau yana canzawa, yanayin jikina shima na sauyawa, numfashina ya soma fita da sauri da sauri. Zan janye, ya ce, “A’a, Sakinah….. kada ki yimin hakan……?’
Dole na yi hakuri ya cigaba da abin da yake yi. Ganin muna shirin shiga wani ‘limit’ ya janye jikinsa da karfi ya jingina da kofa yana regaining consciousness. Gaba daya a firgice nake, don hakika na tsorata da al’amuran Mijin-Sakinah a yau. Na dauka cinye ni zai yi yadda yake bina da sumba ta ko’ina tamkar namijin Zakin da yunwa ta koro. Saida ya samu nutsuwa ya ce (cikin wata irin lallausar murya),
“Ki yi hakuri, ban sani bane Sakina.... kwanta a gadonki, ki huta, ba zan yi abin da baki so ba, kin yi hakurin?”
Na daga kai. “To kwanta ki huta”.
“Ai lokacin barci bai yi ba”.
“To zo ki yi min tausa?”
Na ce, “To”.
Ya ce, “To bari in yi wanka in zo”.
Kafin ya fito wankan na fiddo mishi riga da wandon barci masu laushi, na feshe su da turaren ‘dior’ (Mid-Night Poison). Ya fito daure da tawul iya kugunshi, na yi saurin kawar da kaina, sakamakon ganin wasu nannadaddun muscles da kwantaccen bakin gashi a kan kirjinshi. Kwarjininshi da zatinshi ya cika dakin.
Na daga kai ina duban Abdulhakim, ina kallon kyautar da Allah ya bani, wani irin abu na tsirgawa yau a zuciyata da gangar jiki na wanda ban taba ji ba. Tsigar jikina na tashi. Ya yi saurin sanya kayanshi yana cewa, “Wannan kallo haka Sakinah?’
Kunya ta kamani, na fice dakin da gudu. Na kwaso manyan teddyn da ya kawo min na yi dakina dasu, na jajjerasu a kan gadona ina ta murmushi.
Shigowa ya yi ya tsaya a kanmu ni da teddyn, ya ce,
“Baki ce kin gode ba”.
Cike da kunya na ce, “Ai kaima ka san na gode”.
Ya ce, “A’a, ni ban san kin gode ba, tunda baki bude baki kin gaya min ba ya ya za ai in sani? Tunda kuwa ni ba Allahn musuru bane?”
Na ce, “To godiya nake Mijin-Sakinah”.
Ya ce, “To, shirya fita zamu yi”.
Na ce, “Zuwa ina?”
Ya ce, “Saloon, bana son ganin wannan gashin a cukurkude himili guda, na fi so in ganshi a kwance yana qyalli kamar na Larabawa”.
Na yi dariya na ce,
“To fita in shirya”.
Ya ce, “Na fita, kada a ce na yi iskanci”.
Na kyalkyale da dariya,