Showing 1 words to 992 words out of 992 words
Chapter 1 - A idon mai kallo ne Book Complete Hausa Novels by Mansur Usman Sufi .txt
...A IDON MAI KALLO NE
BABI NA ƊAYA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Sadaukarwa ne ga
NANA A'ISHAH BUNU BARNO
Gaba ɗaya jama'ar dake harabar gidan zoo (Namun Daji) ɗin tsoro da firgici mai tsanani ne ya bayyana a kan fuskokin su, sakamakon sautin ƙarar da ya yi bayyana dake barazanar kurumtar da jin su,
Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un tsirarun wasu daga jama'ar ke furtawa,
Wani kyakkyawa matashi sanye cikin shigar kalaman irin ta malam Bahaushe, hannunshi na hagu riƙe da bindiga, cikin yanayin tashin hankali tare da marairaicewa yake magana
" Wallahi ba ni na harbi HUSNA ba a cikin shirin kwaikwayo ne, kuma kuma duk kun shaida cewa bindigar da aka bani bata gaske ba ce", ya ƙare maganar shi yana juya bindigar dake hannunshi,
Wasu Kyawawan 'yan mata su biyu waɗanda da alamu suna da kusanci matuƙa da wacce ake magana akai suka tsugunna a ƙasa suna riƙe hannun HUSNA dake kwance cikin jini male-male hawaye na zuba daga idanuwansu cikin tashin hankali tamkar fitar rai ce ta gabato masu,
"Ki tashi HUSNA kada ki mutu don Allah mun shiga uku mun lalace ta ya za a ce gaske ne daga shirin fim".
"Wanda ya mutu ai ba zai taɓa dawowa ba ina amfanin kira gare shi"
Sautin muryar wata jami'ar lafiya da ke tsaye daf! Da su ɗauke da kayan gwaje-gwaje ta yi dirar mikiya a kunnuwansu.
Director Haidar kuwa ya dora hannu aka ya yi yana faɗin "Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un wane ne irin bala'ine haka, Anwar mene ne abin da ka aikata daga wasan kwaikwayo sai ka kashe Jaruma HUSNA, ka san kuwa musibar da ka je fa mu a ciki, ka san wane ne mahaifin HUSNA"
Hawayen da suka wanke mashi fuska sune suka ƙatse furucin shi,
Sautin kururuwar matocin 'yan sanda ne suka mamaye wajen,
Al'amarin da ya ƙara firgita Jarumi Anwar da Director har da ma sauran masu ruwa da tsaki a shirya wasan kwaikwayon mai taken BA ZAN MUTU BA..
Anwar faɗuwa ƙasa ya yi yana kurma ihu jikin shi na ƙyama, cikin ƙanƙanin lokaci tufafin dake suka suturce mutumtakasar shi suka jiƙe sharkab da gumi tamkar wanda ruwan sama ya yi masa dukan tsiya,
"Kada ku ƙyale wani ya tsere a cikin su ku tabbatar kun kama kowa dake da ruwa da tsaki a shirya fim ɗin,
Sautin Muryar D.P.O ta daki dodon kunnenshi,
Inna lillahi Kawai ya cigaba da faɗa,
Cikin ƙanƙanin lokaci 'yan sanda duk sun tusa ƙeyar duk mashirya shirin har ma waɗanda ba ruwa na azal ta biyo ta kansu,
A gefe guda kuma an ɗauki gawar HUSNA an saka a mota,
"Malam tashi mu tafi".
Wani sankacecen baƙin kurtun ɗan sanda ya faɗi yana cakumar hannayen shi ya sanya mashi ankwa,
"Ranka ya daɗe wallahi ban kashe HUSNA ba ka duba bindigar da Director ya ba ni ta ƙarya ce Kum...
"Bincike ne zai tabbatar da hakan"
Ɗan sandan ya katse shi yana daka masa tsawa shiga mota mu tafi, ya hankaɗa cikin motar jami'ai shi ma ya shiga ya ja murfi ya rufe.
"Dama Ƙarshen masu lalata tarbiyyar yaranmu kenan da sunan gyara ina amfanin waɗannan fina-finai da ke koyar da mashaya,
Sautin muryar wani dattijo dake cikin jama'ar dake harabar gidan zoo ɗin kenan ta daki a kunnuwan Anwar lokacin da hawaye ke kwaranya daga idanuwanshi.
***
Sautin dariyar ta shi wacce ta fi kama da haushin kare ta yi matuƙar razana Hajiya zinaru, amma saboda da ƙi-fa-ɗi irin ta hamshaƙan mata masu ji da kan su, sai dake ta sunkuiyar da kai ƙasa.
"Hajiya dole abin da muka faɗa maki haka ake buƙata da kan ki muke so ki je ki tono sabon ƙabari da mamacin cikin shi bai kwana ɗaya a barzahu ba, ki ciro likkafani dake jikin shi ki kawo gare mu, sannan za mu samu nasarar kammala maki duk wani aiki na ki ina fatan kin fahimta".
Tsoro ya sake kama zuciyarta, ita da saboda tsoron mutawa ko layin da aka yi rasuwa ba ta iya huce sai an yi sadakar bakwai jama'a sun watse, ta ya za ta iya shiga har maƙwabarta ta tona ƙabari ta ciro likkafani, sai ta yi ajiyar zuciya daga can ta ɗago kanta ta ce
"Na ji dukkan abin da ka ce ya jikan KA CI DUBU... Zan yi komai yadda ka umarce ni matsawar buƙata ta zata biya raina ne kaɗai ba zan iya bayar wa ba amma da na tabbatar cewa BA ZAN MUTU BA.. da zan iya bayar da shi, ai masu iya magana na cewa ranar cikar buri rai ba a bakin kamai ya ke ba, ina amfanin baɗi babu rai,
Hahhhhh! Hahhhhh! Shi yasa muke bukatar aiki da ke saboda tsoro yana fusata Sha ji ni da Ɗan tsito.
"Yanzu zan koma sai ka na dawo gare ka".
Sai ta miƙe tsaye ta kama tafiya da baya tana ficewa daga bukkar sai ta durfafi wata ƙorama mai tattare da duhuwa,
Duk da matuƙar duhun da ya mamaye sararin samaniya bai hana bayyana surar Hajiya zinaru ba,
Launin fatarta kalar coka-cola ce ma'abociyar dara-daran idanuwa farare masu matuƙar kwarjini, hancinta dogo ne mai lankwasa gwanin ban sha'awa, bakin madaidaici ne mai ɗauke da jajayen laɓɓa, ƙirjinta a cike yake a tsaye ƙyam, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba,
Komai hassadar mutum dole ya tabbatarwa kanshi cewa hajiya zinaru kyakkyawa ce ta bugawa a jarida.
Tun da ta fara tafiya a dajin babu alamun tsoro a tattare da fuskarta, tabbas masu iya magana sun gaskiya da suka ce biyan buƙata ya fi dogon buri.
Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari mai cike da sarƙaƙiya da cakwakiya,
Daga Alƙalamin
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan yaƙi
08137237071
Comments
Share