Showing 1 words to 3000 words out of 61103 words

Chapter 1 - MARAINIYA CE​ (1 to End) Complete by Anty Ruky ( Maman Abduljalal.)-.txt

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)


WHATSAPP NO:
+2347039625239
👛👒MARIYA👒👛
1.
By Anty Ruky ( Mmn Abduljalal.)




Bismillahir rahmanirraheem


Tafe take da uniform din makaranta sanye a jikinta da jakar makarantarta rataye a bayanta ,tana waka " oh teacher let me go the time is over" wan an sun saba muddin lokaci yayi haka sukeyi a makarantarsu har a ta she su a makaranta.


Tana cikin tafiyar ne ta hango wani Dan saurayi yana tura barrow , saida ta tsaya tayi ready na gudu sai tace Na ta'ala mai bakin taba romo.yi yai kamar bai jita ba ta kuma fada saiko ya sakin barrown ya yunkura Ai ko arce tana dariya, shima dariyar yakeyi don inda sabo ta saba duk inda ta gansa sai ta tsokaleshi.


Saida tayi nisa ta tsaya ta ci gaba da tafiya tana haki can ta hango wata yarinya tana dauke da tiren talla , daga murya tayi tace A,i mai kafan gula , juyowa A,i tayi da sauri suna hada ido saiko tai mata gwalo, kwafa A,i tayi tace wallahi MARIYA randa na kama ki zaki ubanki, mariya tace back dai ubana saidai naki ta murguda baki tayi wucewarta. Sa,a da take kallonta tace ke Mariya bakya ji yanzu A,i ta kamaki zaki Iya da itane kina karama dake sai son tsokanar manya, tace eh din ke kuma ina ruwanki kanki kamar kankana, ta murguda baki tayi wucewarta.


This just the begining . watch out for the next episode.



In dedication to Halima Auwal.




08161594233 for cmmt.
👛👒MARIYA👒👛


2.


By Anty Ruky( Mmn Abduljll)




Tana isa kofar gida taga mota a kofar , tsayawa tayi ta rike baki oh yau su kawu na birni an zo Kenan, sai kuma ta shiga a sukwane .


Tana shiga kakarta wacce take kira Nenne ta dankara mata harara saiko tayi saurin juyawa.


Assalamu alaikum, tayi sallama , a tare suka amsa mata tare da bakon ,murmushi tayi tare da cewa Nenneres me nawani hada fiska.


An hada fiskar Ai na hanaki shigowa ba sallama amma bakya ji . yi hakuri yar tsohuwa, naga mota ne a kofar gida shine sauri don nasan kawu Na ne yazo.


To bashi bane sai yanzu da kalli bakon wadda ya kura mata idanu tunda ta shi go.kyakkyawan saurayi ne baki irin mai shining dinnan mai dan matsaikaicin tsawo da jiki.


Sannu da zuwa tace mas a , yawwa sannu ya amsa gaisheshi tayi ta shige daki.


Sai da ta tube kayan makaranta ta saka na gida tukun ta fito , Nenne ina abincina. Baki San inda yake bane kike tambaya?


Nenne Na gajine Dan mikomin. Bazan miko ba ja' ira ba dole ki gaji kina tafe kina tsokana. Zaro idanu tayi ni din inna ?


A a ba ke ba nice Mara kunya yo Ai karya namiki ko. Dariya ta kwashe da shi tace Nenneres.


Shiga kitchen tayi taje ta dauko flask Na abincinta tana fadin me kika dafa ne Nenne. Nenne dake tadi da bakon ta tayi banza da ita.


Bude flask din tayi aiko ta fasa ihun kuka Nenne me haka. Fitowa nenne me ya faru Mariya. Naga two miya zoborodo .to me bazaki ci bane? Idan na ci me zanci da daddare ? Me kuwa ban da shi din .Tabb wlh saidai ki ban kudi nasai shinkafa dawake ko alele a gidan uwale.
👛👒MARIYA👒👛

4.


Tashi maza kiyi sallah ki rakashi ya gaida yakumbon Ku.to tace tare da mikewa.


Bayan ta idar da sallah suka kama hanya Nenne sai mun dawo .yawwa mariyatul kibdiyya kada ayi halin dai. Kai Nenne har wani hali dani. Oho ni kuje kada yai dare a hanya.


Suna tafiya tana zuba mishi surutu shi dai sauraranta kawai yake . can ta hango wata tana tsaye da saurayinta tayi murmushi tace ya Salim zo mubi nan .


Shiko da bai San kan gariba sai binta yake.said a suka iso dab dasu tace Mara kunya dai baiji dadiba hmmm.


Yarinyar ta kalle ta .ke kuma da wa kike Mariya. Tace da irin ' yan iskan mata masu tsayawa da samari a kan hanya.ke Mariya ki kiyayeni Mara kunyar banza. Tace mariyoo tare da murguda baki.


Salim dai mamaki ya isheshi .Ashe haka yarinyannan take da tsokana ya fada a zuciyarshi.


Kiyi hakuri yan mata yace bayan ya kamo hannun Mariya wuce muje ya mata tsawa sai da suka danyi nisa kadan ta tintsire da dariya har da rike ciki.


Meye kuma yace tare da kallonta. Wlh ba nan bane hanya mun baro hanyar a baya. Da mamaki ya kalleta .kamar ya? Ya fada tare da daure fiska.ta wani marairaice tayi fiskan tausayi. Dama ganin su laminde ne yasa nace mu biyo nan.


Jan ta tai da karfi c' mon my frnd wuce muje ko in Zane ki yanzunnan. To ya Salim karya ni zakayi.oh on Niki wuce nikam.


Ya Salim sake min hannu kada a ganmu ace nima bani da kunya ina barin saurayi yana riken hannu.


Waye saurayin? Kai man kumama a islamiyyanmu ance hakan haramunne.to ai ni yayakine.
Nidai cika min hannu ka wani rikeni sai kace wasu ' yan iska.


Ikon Allah yace aranshi a fili kuma sai yace to naji. Class nawa kikace kike? " class six" tace dashi. Yayi. Kyau aranshi kuma yana tunanin yarinyar da Zara koma tayi karatu zaifi. Dan wayonta yai yawa.




In dedication to ummu A' isha.


Luv u all.
👛👒MARIYA👒👛


5.


By Anty Ruky ( Mmn Abduljll.)




Jama'a kuxo mu d'unguma muje ta'axiya gurin iyalan marigayi Ramadan (SAMAREEN BANA) Na Rahamat Nalele sanadiyar wuta data lamusheshi wajen kokarin ceto matarsa masoyiyarsa, Allah yaji k'anka RAMADAN senior😭😭😭.


Aikinki na kyau Anty Hajjo. Allah ya sa ki gama lafiya. Thumb up my sister👍?



Tunani yake da zata samu tayi karatu a birni da zata fi haka sosae Dan tana da wayo.


A haka yai ta hakuri da shirme da tsokananta har suka je suka dawo.


Bayan yayi sallah 'n la' asar ne yai haramar tafiya. Nenne ta bashi tsarabar kayan miya irinsu kuka, kubewa, barkono da dai saurans
u.


Suka rako shi kofar gida nan ne Mariya take ce masa ya gaida mata mami , ya Sadiq da kuma ya sagir, sai kuma Hafsa.


Dariya yai yace fa' izar fa, turo baki tai tace " to ni ina ruwa na da ita.
Shigewa cikin motar yai tare da cewa tsakaninku ne wannan.


A kwana a tashi ba wuya. Mariya ta rubuta exam Na common entrance .saura jiran certificate.


Sai dai halinta na tsokana har yanzu sai abinda ya karu. Nenne tayi fadan har ta gaji.


Yau ma kamar kullum ta je aika tana dawowa gida tahadu wata tana wucewa. Tsayawa tayi tana kare mata kallo kafin daga ta karkace ta fara rera mata waka.
" ahayye Atika mai hannun gula , kanwan Bawuro mai kafan gula .addan Kaltume mai idon kule.


Aiko Atika ta biyo ta a guje ita ma ta ruga sai gida .


Nenne Na yanke farcen ta sai ji tayi an shigo mata a guje kamar za a fado kanta.

Mikewa tayi tare da fadin subhanallahi lafiya?


Atika ce ta mayar mata da duk abinda ya faru tana magana tana haki ga bacin rai karara a idonta.


I
Nenne tayi salati tare da tafa hannu zatayi magana kenan sai suka ji sallama....


Ku biyoni don jin waye mai sallama.


In dedication to ummu A'isha.
👛👒MARIYA👒👛

7


By Anty Rukie (Mmn Abdul)


Kuka ta fashe dashi ita fa lallai ba za ta bisu ba. Lallai wannan shine hausawa suke cewa " sabo turken wawa"


Ita kanta Nenne jin wani iri tayi .anya zata iya rabuwa da Mariya kuwa? Wata zuciyar kuwa tace mata Ai kuwa gwara ki barta taje ta samu ilimi mai nagarta. Kila ma tabar wannan halin Na tsokana ke kuma kin hut a da bada hakuri.


Mariya me yasa baza ki bimu ba cewar kawu. Kawu nidai karatuna ta fada tana zumburo baki.


Karatu wane Iri? Ya tambaya.
Karatun allo kaga saura min surori uku Na sauke Al- qur' ani. Kuma bana so Na bar karatun islamiyya Na.kumama idan Na tafi Nenne ta zauna da wa.


Murmushi kawu yai yace Mariya idan don karatune a can ma zakiyi kuma akwai islamiyya sai a sakaki ciki Ku rika zuwa da su Hafsa.


Zaro idanu tayi yanzu dama akwai islamiyya a birni shine kuma ' yan birni suke rashin kunya?


Dallah Malama ce miki akai ' yan birni jahilaine ko ance miki kowa ma marar kunya ne? Sagir yafada yana zare idanu.


Koda akwai islamiyya amma dai malaman Ku basa muku wa azi yadda namu sukeyi.


Mtseew sageer yaja tsaki. Kanki akeji ke dai kice bakya son zuwa ba ki tsaya kina mana wani Qabli da ba' adin da ba Na sallah ba.


To ba gashi har wani qabli da ba adi kuke dashi wadda ba Na sallah ba mu kuma wlh Na sallah muka sani.


Kawu ne ya katse su da cewa " ya isa haka Mariya je ki shirya mu kama hanya."


Sabon kuka ta fara wadda ya kara kashewa Nenne jiki tace " Ali ina gani a barta ta sauke kafinnan ma taje tayi sallama da ' yan uwanta ko ya ka gani? Ta karishe da tambaya.


To Nenne duk yadda kika ce.ke dai Nenne kice ba kya son rabuwa da Mariya ne kema. Any way rana bata 'karya very soon zata sauke Ai ni zan zo daukanta . Hmm hhhh ranan zanga kukan Nenne ya fada cewar Sadiq yana dariya.


Kaniyarka Sadiq, baza kazo bare ka dami Nenne a banza sadda za a dauko tama baza ka sani ba.


Kyaleshi Safiya zanyi maganinsa ne cewar Nenne ranar da zaizo yana karamar murya in taimakamai a bashi Mariya.


Tabb Allah ya kiyaye cewar mariya. Kyaleta Mariya zo Na tambayeki wani abu cewar Sadiq gudun kada ta ce shi Dan isakane a gaban iyayensa su sa mishi ayar tambaya.


Wai ke meyasa bakya son zuwa birni cewar Sadiq bayan sun fita kofar gida. Kaima ka sani Ai. Hmm saboda mu yan iskako? Ya tambaya tare da riko hannayenta.Ga zahiri ta fada tana kallon hannunta da ya rike .ba a ce muku haramun bane a islamiyyarku. Ta tambayeshi. Murmushi yai tare da cewa yarinya karama dake sai kice zakiyi wa mutane wa' azi.


Fincike hannunta tayi sai kuma yaga ta tsaya tana murmushi yabi inda idonta yake da kallo . kafin ya Ankara sai jin muryarta yayi tana cewa " Rabi' u famfon majina"


Ta juya zata gudu ganin Rabi'u ya juyo.sadiq ya cafkota zonan. A islamiyyarku ance muku tsokana tana kyau ? Eye Na' am tace cikin in ina Dan ita tama manta dashi a wajen.


Maido da kallonta tayi kan sadiq bayan taga Rabi u ya tafi. Tace kai kuma ina ruwanka dani. Allah ya shirye ki yace. Ameen tafada tana murguda baki.hmmm shi abinnnata ma dariya yake bashi.


A haka suka tafi ba tare da ita. Amma saida suka gama magana akan za a zo a dauketa idan lokaci yayi don sun gane inna ma tana tararrabin rabuwa da Mariyanta.


In dedication to Halima Auwal.


08161594233 for comment .


Luv u all.
👛👒MARIYA👒👛
6.


By Anty Rukie.


Juyowa sukai tare da amsa sallamar.


Oyoyo, oyoyo kawu Na birni , fadin Mariya ta ruga a guje ta rungumeshi tana dariya.


Oyoyo mariyan KAWU.sakeshi tayi ta kama mami tana tsalle da murna.


Ke mu baza Ai mana oyoyon bane, Sadiq ne ya fadi haka yana janyota daga jikin mami.


Ni ka sakeni , ta fada. Anki a sakekin cewar Sadiq ,yana leka fiskarta.


Mami kin ganshi ko, ta fada a shagwabe. Juyawan da zatayi sai gani tai ba kowa a wajen. Daga ita sai shine agun.


Ya kikai shiru, ya Sadiq kaga nifa ba marar kunya bace kuma ba 'yar is.. rufe bakinta yai ke, kada ki zageni daga zuwana , wato a takaice dai nine dan iskan. Nidai ban ce ba tace tare da murguda baki.


Karasa shigowa yayi cikin gidan yana Dan murmushi.


Nenne ce take mayar musu labarin tsokanar datai, hakuri suka bawa yarinyar. Kawu ya bata Dari biyu .


Bayan sun gaggaisa ne aka gabatar musu da ruwan sha da kuma abinci.


Bayan sunci sunsha sunyi sallah ne , kawu yake bada shawaran a basu Mariya su tafi da ita.


Toh kasandai bani ke iko da Mariya ba Ali.
Saidai kaje ka tambayi mahaifinta idan ya amince bazan hana ba. To Nenne hakan za ayi.


Ko da yaje ya tambayi mahaifinta saida yayi Jim daga bisani yai ajiyar zuciya tare da cewa ba komai Alh. Allah ya taya riko. Ameen yace sannan sukai sallama da juna.


A gaskiya badan yana kunyan Alh. ba ba abinda zai sa ya amince . in banda saratu ta ki rike masa Mariya me zaisa ya rabu da ita. Abinda mahaifinta mal. Umar yake fada a zuciyarsa kenan bayan rabuwansu da kawu.


Koda kawu ya dawo ya tarar da Mariya tana fita da Al- qur' ni a hannunta zataje je karatu.


Mariya zo tukunna yace mata.


Ya zayyane musu yadda sukai da BABAN Mariya. Ba Mariya ba hatta nenne sai kirjin ta ya bada dam..


Toh fa. Ko ya za a karke?


In dedication to Halima Auwal.
👛👒MARIYA👒👛


8


By Anty Rukie ( Mmn Abduljll)




Cikin ikon Allah Mariya ta sauke Qur'ani . Bayan sati biyu ta karbo sch. Leaving certificate da Kuma testimonial.


A cikin satinne kuma Salim ya zo 'daukanta.
Tasha kuka ba kadanba .


Har suka kama hanya bata daina kukanba.
Yayi rarrashin har ya gaji yai shiru.


Suna cikin tafiya ne sai yaji ta ' daga murya tace Talatu guntuwa .yarinyar ma ta daga murya tace uwarkice guntuwa. Mariya tace uwarki dai.


Kallonta yai da mamaki kamar ba ita take kuka yanzu ba.bai gama tunaniba yaji taci gaba da kukanta .tsaki yayi yaci gaba da tukinsa.


Sun kusa fita Gari yaji tace , Dan Allah ya Salim tsaya nayi sallama da waccar matar. Yai mata banza. Ta kuma cewa dan Allah fa. Ya tsaya yace minti uku kar ki batan lokacin.


Zaman minti shida yayi yajita shiru. Wai yarinyarnan ina tayi ne? Ya fito daga motar.


Yana fitowa ya hangota da wata mahaukaciya suna ta tikar rawa.ita kuma Mariya tana waka har da tafi.


Sai da yaci dariyarsa sosae sannan ya tsagaita ya doka mata kira.


Ina zuwa Yaya minti biyu tace taci gaba da abinda takeyi. Daure fiska yai tare da cewa " idan kika kuskura nazo Na sameki a wajen mhhhm yai kwafa. Saura minti daya tace dashi. Amma fa yarinyarnan ' yar rainin hankalice. A zuciye ya nufo su ita kuma ta kama buya bayan mahaukaciya.


Bai Ankara yaga mahaukaciya ta nufo shi da sanda. Ai da saurinsa ya juya har yana cin tuntube. Mariya me zatayi ba dariya ba.


Tana ganin ya shige mota ta juyo taci gaba da rawa .Mariya ganin tada motar ta tafi aguje ta je wurin motar . budemin tace tana zumbura baki.

Bude mata kofar yayi yana harararta. Ta shiga ta zauna .suna fara tafiya ta ' bare baki tana kuka. Takaici ne ya ishe shi ya gagara ce mata komai .saida sukayi dan nisa sunfara fita gari ya yi parking a gefen titi. Fita min a mota shegiya fitinanniya. Gyara zamanta tayi ta kara volume din kukanta.way yo Nenne na Nenneres. Saura kadan dariya ta subuce masa.ya maze. Juyawa yai ya karyi bulala, wlh idan baki rufemin bakinnan ba sai Na fasa miki jiknki.


Ganin yadda ya hade raine ya sata yin shiru. Shigowa yai tare da tada mota yana mita shegiya kawar mahaukaciya. Duk kin batan lokaci a shirmen banza.


Basu jima da ci gaba da tafiya ba bacci ya kwashe. Ya juyo ya kalleta yace fitinatu anyi bacci.


Ba ita ta farka ba saida suka iso ya tasheta.


Thanks a lot my lovely fans.


In dedication to Halima Auwal.


Fasaha writers.
👛👒MARIYA👒👛


10-15


By Antie Ruky.




Tunda suka shigo qauyen take jin wani irin nishadi, Allah Allah take su isa gida raga Nennenta. Fahimtar hakanne yasa Sadiq rage tafiya kamar bayaso.


Ya Sadiq me haka, tace dashi.me akayi? Ya tambayeta naga tafiya kakeyi kamar bakaso.


Banza yai da ita.Dan Allah ya sadiq......ke kar fa ki dameni ya katse ta. To azarb'ab'i naga dai mun riga mun iso gari saurin me kike .Fa'iza ce ke wannan maganar.
Ke kuma ina ruwanki dake nayi magana? To Ai kin toshe mana kunne da mita ne.
Kyaleta fa'iza idan ta damen sai in juya. Tabb..tace , sai kuma tayi shiru.


Har suka iso ba Wanda ya kuma magana. Yana kashe motar ta balle murfin motar ta fito zata kwashi gudu kawai taji an cafketa. A fusace ta juyo ta Sadiq ne ya mata wannan aiki. Kwab'a fuska tayi kamar zatayi kuka.


Dan Allah ya Sadiq ka sakeni.anki a sake kin. Ke kin fito birnin ma saikin yi qauyanci.
Zumburo baki tayi .to Ai naga nan gida ne.yai shiru yana kallnta. Da dai taga baiyi niyyan saketan ba sai ta sassauta murya , Dan Allah ya Sadiq Na tuba ba Dan Nina kayi ha....au yau ba rashin kunya Kenan. A a bazan sake ma rashin kunya bama har abada.
Dariya abun ya bashi ita kuma ji take kamar ta mangareshi. Amma ba dama. Ga su Hafsa harsun shige gidan sun rigata ganin Nennenta.
Saboda Neman magana sai ya kama hannayenta duka biyu ya rike yana kallon idonta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login