Showing 1 words to 3000 words out of 52375 words
ο»Ώ*KISHIYA KO BAIWA???.*
(TRUE LIFE STORY)
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa~_
*_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*
```Labari me cike da tsantsar soyyayya cin amana,ban tausayi,zalunci sarkakiya,se kunbiyoni acikin wannan labarin nawa zakuji yanda zata kasance inafatan zakubiyoni danjin wannan labari mecike da ilimantar nishadantarwa uwa uba fadakarwa.```
```Banyarda wani ko wata yasauya min labarina takowacce siga ba batare da izinina ba aikata hakan babban kuskurene. Wannan labarin yafaru agaske abinda akacanza kadan ne anma baki 'dayan labarin gaskiyace
_Bismillahir rahmanir rahim_
*PAGE 1&2*ποΈ
___________________________________πKe karamar karuwa,yar talakawa,dangin matsiyata,Wanda basugaji abin alkhairi arayuwarsuba dangin jaraba 'yar anace yar masu jaraba da 'kwalafaci,wlh karki sake kiran wayar mijina inba hakaba wallahi,wallahi,wallahi, rantsuwa uku ki kasake kuskuren kiran wayar mijina sena cimiki mutunci shegiya matsiya ciya karuwa.
"Cikin sanyin muryan ta tace dan Allah aunty kiyi hakuri bansan yana gidaba da bazan kiraba bare har in bata miki rai,kuma miss call dinsa nagani shiyasa nakira anma Allah yahuci zuciyarki tunda kiran danayi ya bata miki rai takarashe cikin rawan murya irin na wanda ke gab da zubda hawaye.Wani dogon tsaki taja tace munafukar banza kawai annamimiya niba aunty ki bace kije can kinemi aunty banason kalen dangi da Neman gindin zama"tana gama fa'din haka takashe layin,tare da zama abakin tangamemen gadonta,Wanda yacinye rabin dakin,kafa 'daya tadaura akan daya tana girgiza wa tare da hura kofofin hancinta kamar Wanda iska kemata wari.
"Wani kyakykyawan matashine me yabude wata kofa yafito da'alama toilet ne,a'kalla shekarunsa zasukai arba'in anma baza kafahimci hakanba saboda hutu da naira dasuka zauna masa,yanada matsakaicin tsawo,da faffa'dan kirji na kiran jarumtaka,bakine,irin black beauty nan yanada madai-daitan idanu da kwantaccen sajen daya kawata kyawun fuskarsa,sekuma gemun daya ajje Wanda yasake fitar da ainihin kyawun fuskarsa tare da dimple daya lotsa agefen sajen dake kwance luf luf afuskarsa.Gabanta yakara so ya tsugunna da towel daure akugunsa Wanda bewuce gwiwarsaba,akan gwiwoyinsa ya tsugunna yana kare wa fuskarta kallo daya ke Iya hango damuwa bayyane aciki" Cikin daddda'dan muryarsa me tafiya da imanin kowace diya mace,yace what's wrong with you my Queen??kuka tafashe dashi tare da rungume sa tace,honey shin menayiwa wannan baiwar Allah datakeso ta musgunawa rayuwata?me natsare mata arayuwar duniya daya zamto batada buri se son ganin bayan farin ciki na dakuma jin dadina,aganina niyakamata inyi kishi da ita,bawai ita tayi daniba!? anma narasa mena tsare mata datake neman addaban rayuwata da munanan kalamai masu zafi azuciyar duk Wanda akayimasu"akan wakike magana??ya tambayeta da alama be fahimci inda maganarta ta tadosaba dan haka yayi gaggawar katseta"Sake marerece murya tayi tace wace kuwa inba matar dazaka auraba kullum cikin cimin mutunci da zagar min da iyayen take, atake ya'daure fuska yace wani abin yafaru??Cikin sheshe'kan kuka tace kawai dan takira wayar ka nadauka nace,da ita kana toilet shine tafara zagina tare da fadamun bakaken maganganu haddacewa wai ban isa in hanata shigowa cikin Gidan nanba inde malamai nanan kota wani hali se tashigo kuma ta fitar dani"afusace yasanya hannunsa gefen beside drawer yadauki hadadditar wayarsa kiran iPhone 11 yayi Dearing, number second wife,tsaki yayi tare da wurgi da wuyar jin switch off se huci yake yana taunar lips dinsa nakasa.Lallausan tafin hannunsa yasanya abayanta yana
bubbuga alamar rarrashi,cikin sweet voice dinsa yace am so sorry my Queen nakira wayarta switch off anma,zandau mataki dan ba zanyi tolerating din nonses din nanba bata isa tarenakiba in kyaleta"peck tabashi akuncinsa tace thanks Honey that's why nake alfahari dakai nasan bazakataba bari wata ta wulakantani ba"murmushi yayi tare da janyeta ajikinsa yace u deserve more.mikewa yayi yabude sif din kayansa, masha Allah kamar wani shagon seda kayan saboda yawansu kowani kalan kaya da bangarensa,wani farin gezna me kyan gaske yadauko tare da yasanya wa anyimasa dinkin zamani irin na matasan dakeji da naira dakuma sji,kayan bakaramin sake fitar da ainihin kyawunsa yayi na,turarukansa masu dadin kamshi yafeshe jikinsa dasu tare da taje lallausan sumar kansa Wanda kesheki da yalki,fitowa parlour yayi yana zabga kamshi tamkar wanda akayi barin tulare ajikinsa.
Dawani irin sauri,Nadiya tatashi tarungumesa,tana me sake manne kanta afaffadan kirjinsa tare da shakar kamahinsa,cikin kissa tace honey kakulamin da kanka jinake kamar inbika domin banason wasu sakarkari sukallamin kai nafiso dagani se kanwata zakuga wannan wankan"murmushi yayi yalakace mata hanci yana jin kaunarta nasake ratsa duk wani lungu dasako dake ajikinsa,saketa yayi yace my Queen karnayi letti sena dawo"yana gama fadin haka yajanyeta daga jikinsa tare da yafice wa,da kallo tabisa haryafice kana tana jin son sa nabin kowani lungu da sako najikinta"Direct inda yake parking Din motocinsa yanufa wata 'bakar mota me kyawun gaske ya shiga,Cikin motar na fidda wani sanyayyan 'kamshi me dadin gaske,key yayi wa motar tare da Hong dasauri gateman yawangale masa gate yacinna hancin motarsa yafice daga Cikin katafaren Gidan sa....
"Switch off din wayar tayi tare da ha'da kai da gwiwa tafashe da wani irin kuka mutsuma zuciya ba Kalmar datake furtawa face innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,wai shin wannan wace irin masiface?,wani irin rayuwane wannan?,shin me wannan baiwar Allah tamaida ta??shin talauci haukane?ta tambayi kanta cikin 'kunar zuciya, hakika datana da yadda zata gujewa wannan auren toh ba shakka data guje masa sede kash!!bakin alkalami yariga da ya bushe yau saura sati daya adaura aurenta da Ahmad Ajmi"Wanda tunda ga yanzu take Iya hango kalubalen dazata fuskanta agidan sa"Kuka tasake fashewa akaro na biyu me tsuma zuciyar duk wani mai tausayi cikin gunjin kuka tace ya Allah karka jarabcemu da abinda bazamu iyaba ya Allah kakawomin sauki acikin rayuwata Ya Allah idan wannan auren alkhairi ne Allah katabbatar idan kuma babu alkhairi ya Allah kasauya min damafi alkhairi ya Allah kawargazar inde babu alkhairi acinsa...
Jitayi andafa kafa'darta tana juyawa taga mahaifiyarta,rungume ta tayi tanajan zuciya,cikin sanyin muryan ta tace dan Allah Ummi afasa wannan auren!! wallahi bansan wace irin rayuwa zanfuskanta agidan Ahmad ba, matarsa batasona tatsaneni,Ummi bakiji irin zagin cin mutum data yimin ba hadda yimin gorin talauci shin mumu kabaiwa kanmu talauci ne takarashe tana jan zuciya.Rungume ta mahaifiyarta tayi cike da tausayinta tace insha Allah ba'abinda zefaru se alkhairi ki kwantar da hankali ki,kinji kidinga addu'a komai ze zo da sauki sannan inaso duk maganan data fada miki ki kyaleta da halayyarta,ganin baki shiga Gidan bane anma da zaran kin shiga zaku zama daya duk wannan abin zewuce" kai tagyada mata alamar "toh" batare datace komai ba,Wayar ta dake yashe agefe inda takashe Ummi tasanya hannu tadauka takunna,matashi" kamar jira'ake takunna kira yashigo.
Mika mata wayar Ummi tayi,ahankali tasanya hannu takar'ba tayi picking tare da sallama"batare daya amsa sallamarba yace kisameni awaje ,yana gama fadin haka yakashe wayar yana huci tamkar namijin zaki...
Dan Allah inkun karanta kuyi shearing dinsaππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»ππ»
1/1/2021
_VOTE_ β
_COMMENT_
_And_
_SHARE_
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
*PAGE 3&4*ποΈ
________________________πDafa kafa'darta mahaifiyar ta,tayi tace lafiya kuwa Suky naga duk kin ru'de ko wani abin ne??,Cikin rawan murya tace Ahmad ne yace insameshi yana waje yazo kuma besanar dani cewa ze zoba!!'dan murmushi Ummi tayi tace kuma shine abin damuwa ko Ahmad din bakon kine??maza tashi kije kiji menene karkibarsa yana jira??"Amsawa tayi jiki asanyaye tare da mikewa Ahankali,hijab dinta dake kan kofa tajanyo tasanya tafito cikin gida,'yan biki dasuka fara taruwa se tsokanarta suke suna cewa Amarya bata lefi kota kashe 'dan masu gida!!Murmushin kawai tayi batare da tace dasu komai ba tayi hanyar fita.
'daya daga cikinsu ce mesuna Aunty Aliyah tace ke Suky ina zaki? kose kike kimayar mana da aiki baya bance dake karkisake fitaba harse ankaiki kokuma sokike rana ya ko'dar dake bayan kuma kinsan nafada miki gyaran jiki beson fita rana ta'fada adan kausashe??Cikin sanyin muryanta tace aunty ba dadewa zanyiba yanzu zandawo sa'ko zan amso,tana gama fadin haka tafice batare dajiran jin abinda zasuceba"Kai kawai wacce takira da Aunty tagirgiza kana tacigaba da abinda take.
Cikin nutsuwa tasanya hannu tabude kofar gidan nasu tare da nufar inda yake parking motarsa aduk sanda yazo."tun fitowarta yake kare mata kallo tunda ga fuskarta dake 'dauke da dara-daran idanu dakuma 'karamin bakinta me dauke da pink lips harzuwa manyan hips dinta dasuka bayyana,acikin hijab suna juyawa tamkar da gangan take juyasu,sanye take cikin wani long hijab red color Wanda ya amshi fuskarta duk da hijab din babbane hakan be hana surarta bayya"duk da kasancewar fuskarta ba kwalliya hakan behana ainihin kyawun fuskar ta bayyana ba.
knocking din glass din motar tayi tare da gyara tsayuwarta,yadauki kusan 1mint kafin yadanna lock din yabude mata"hannu tasanya tabude tare da shiga idanu ta lumshe saboda sanyin AC da kamshin da daddadan turarukansa"Shima anasa bangaren idanu ya lumshe yana shash'kan daddan kamshin humran datake domin bakaramin gyara akemataba, fuskarta yakurawa idanu ko kyaftawa bayayi yana kallon baiwar kyau da Allah yaimata.
Inayini tace dashi cikin sanyin muryanta,kanta akasa kasancewar bata Iya juran kallon kwayar idanunsa masu dauke da wasu magic"amsawa yayi yana me dago fuskarta da lallausan tafin hannunsa me dauke da zara zaran Yatsu,sake lumshe idanunta tayi akaro nabiyu masu dauke da zara zaran eyelashes tamkar nakanti tasanya,dan bazata Iya juran kallon sexy eyes dinsa ba.
Murmushin gefen baki yayi Wanda ya lotsar da dimple dinsa kunyar Sukainat nasake dulmiyar dashi acikin kogin kaunarta,arayuwarsa yana matukar son mace mekunya"cikin sexy voice dinsa yace da ita meyesa bakya kallon idananu?murmushin dake karawa fuskarta kyau tayi tare da juya manyan idanunta masu haske tace dashi hakade kakegani.
Martanin murmushin yamayar mata tare dacewa hmm zakiyi bayani ne, yace da ita yana gyara nutsuwarsa da'alama magana me muhimmanci ze fada"ganin yanda ya tattara nutsuwarsa baki daya ne yasanyata sunkuyar dakai dan tafahimci magana me muhimmanci zeyi da ita.
Cikin kakkausan murya yakira sunan ta tare da maida hankalinsa kacokam kanta"dara daran idanunta masu sake dulmiyar dashi cikin kogin kaunar ta dago tare da watsasu cikin nasa tare da 'amsa wa"Kauda kai yayi domin bayason kallon yayi tasiri agaresa soyake ya hukun tata abisa lefinta,meyesa kike aikata abinda Sam bedace dakeba??,meyesa kikeson ciwa Nadiya mutunci tare da tozar tata?,meyesa kikeson tayarmin da hankali?,a gaskiya bazan boye mikiba bawai dan rashin kyautatawa ko zaman lafiya bane zesanyani inkara aure kawai sedan raya sunnan manzon Allah (S.A.W)saboda haka ina horinki da kisanyawa zuciyarki salama acikin zaman takewar dazakuyi da nadiya domin bazan lamunci tashin hankali da rashin girmamawa atsakaninku ba Nadiya itace matata tafarko sannan duk wata biyayya da mace yakamata tayiwa mijin ta tanamin saboda haka inaso kigirmamata,se itama tagirmamaki kibata darajanta amatsayinta Na Uwar gida na kuma Uwar 'ya'yana.
Hawayen dake kokarin zubowa daga idanunta tayi saurin mayarwa cikin rawan murya tace Inaso kafin kayanke hukunci akan duk wata magana da'aka fada maka katsaya kayi bincike, bawai kayanke hukunci akan bangare daya ba batare da kaji daga daya bangaren ba,Nasani Nadiya matarkace sannan ni ban isa in shiga tsakanin kuba,kuma dama bance rashin biyayya bane zesa ka aureni,anma ina me baka hakuri inhar kalamaina sunyi maka zafi"insha Allah hakan bazesake faruwa ba tace dashi hawayen datake kokarin boyewa yazuba arayuwarta ta tsani aiyamata kazafin abinda batayiba"lumshe idanunsa yayi domin baya kaunar ganin hawayenta,cikin sanyin Murya yace haba Sukainat meye abin kuka dan Na fada miki gaskiya, kokecefa amatsayin matata bazanso wacce zan auro taci miki mutinciba kokuma tarenaki toh ke meyesa kikeson rainata?? Bayan kuma nasan hakan ba halayyar kibane.
Sake goge kwallan fuskarta tayi tace bakomai Insha Allah hakan bazesake faruwaba"kai yajinjina cike da jin dadin kalaman yace Allah yaimiki albarka"ameen ta'amsa tare dacewa zan Iya tafiya??kai ya gyada mata alamar "eh"begaji da kallon taba sede beson takurama ta" hannu tasanya tabude motar tafice,da kallo yabita komai na sukainat dinsa da banne harseda yadena hangota kafin, yatada motar yatafi yanamejin zafin hawayen datake zubarwa, anma yazama dole ya nuna mata kuskurenta,dakuma muhimmancin Nadiya awajensa domin bazeso awulakan tamasa itaba domin tanada wani matsayi na musamman azuciyarsa"Rurin da wayarsa keyi shiya katse masa tunanin dayake...My queen shine sunan dake yawo akan screen din,rage gudun motar yayi tare da banna bluetooth akunnensa yayi picking din call din,sheshekar kukanta ne yafara yiwa dodon kunnensa sallama,lafiya?,meyesa meki?,me'akayi miki?,duk alokaci daya yajero mata wa'annan tambayoyi"Cikin muryan kuka tace nagaji,nagaji,hakuri na yakare wannan shine karo nafarko kuma na karshe da wannan yarinyar zatasake kirana tacimin mutuncin inkyaleta,bawai dantafi karfina bane yasa nake kyaleta a'a sedan inatayaka son duk wani abu dakakeso haka zalika inatayaka 'kin duk wani Abu dakake 'ki, anma tunda ita batason haka za'ayi irin yanda takeso zan nuna mata nima nasan salon rashin mutunci dakuma tashin hankali kala-kala tanagama fadin haka tafashe da kukan kissa,tace aikishi ba haukabane ta nagama fadin haka takashe wayar.
Da kallo yabi wayar yanajin zuciyarsa na kuna yarasa yazeyi da wa'annan Matsalolin tunkafin ayi aure irin wannan abin nafaruwa inakuma ga anyi auren,Shin duk maganar daya fadawa Sukainat batajiba kenan?ya tambayi kansa "tabbas zedauki mataki akan Sukainat domin ya tabbatar fadan daya matane yasanyata sake kiran Nadiya tai mata diban albarka,dole yaiwa tufkar hanci danbaze lamunci tashin hankali acikin gidansa ba da wannan tunanin yatafi.....
Tana kashe wayar tafashe da dariya tare da mikawa hema hannu sukatafa cikin dariyar mugunta tace wlh yarinyar nan seta gwammaci zaman prison dazaman cikin gidan Ahmad,domin Ahmad nawane ni kadai kuma danni akayishi danhaka banga wacce ta isa tashigo min gida ba,idan 'ya'ya yakeso karyadamu zancika masa gida dasu anma bawai inbari yayi aureba.
Dariyar mugunta hema tafashe dashi tace kinyimin dede tunda shegiyar tanace setashigo kibarta tashigo anma karkiraga mata"Mufy dake gefe tace Momy karkidamu wlh inde ta auri Dady semun yimata duka ko tafiya baza ta iyaba kuma mudinga yimata rashin kunya _(Mamaki ne yakamani ganin duka duka shekarun yarinyar bewuce 7-8 take irin wannan maganan)_ Cike da jin dadi Nadiya tashafa kanta tace shiyasa nakeji dake mufy kinatayani son duk wani Abu danake so,tun kina karama kinsan kishin uwarki nasan bazakibari araina niba"Allah yaimiki albarka yabaki"ameen mufy ta amsa tana dariya,hema ma dariya tayi tace aikuwa kinji dadi kinsamu yara masu tayaki kishi yanda zakuji dadin con ubanta....
Sukainat Na shiga cikin gida direct dakin Ummi tanufa kasancewar batason kowa ya fahimci halin datake ciki"sede tamakara kallo daya aunty Aliya taimata ta hango damuwa karara bayyane afuskarta,hakan yasanya ta mike tare da bin bayanta Har cikin dakin Ummi,kasancewar ta mace mai saurin fahimta.
Mikewa tayi tabi bayanta harzuwa dakin Ummi,gefen gado tahango ta zaune, danhaka itama tanufi gefenta tazauna kallon ta aunty Aliya tayi ido cikin Ido tace Suky meke damunki??na fahimci cikin yan kwanakin nan kina cikin damuwa ko auren ne bakyaso??'kwallan datake kokarin boyewa ne su kayi nasaran zubowa cikin rawan murya tace bakomai aunty kawai banjin dadin jikinane!harara Aunty Aliya tamaka Mata tare dacewa ke banson sashanci banza fa bayan ina hango damuwa bayyane afuskarki sannan zakice bakomai,koba ki daukeni matsayin dana daukeki bane suky??,Cikin muryan kuka tace Aunty, matar Ahmad bataso na tatsaneni kullum cikin sharri takeyimin awajen Ahmad kullum cikin yimin sharri da kazafi take,shikuma yaitamin fada yana cewa shi badan rashin zaman lafiya yasa ze aureniba matarsa nayimasa biyayya dan haka nabita danbeson tashin hankali,kuma ko yaushe cikin zagina take tanqcewa muddin nashigo gidanta se prison yafimin kwanciyar hankali takarashe tana fashewa da kuka,kafadarta aunty Aliya tadafa tace shine kekuma kikazauna kike mata kuka??,har ki kesan ya kanki acikin damuwa muddin kikace zakiyiwa kishiya haka kinatare da wahala dan haka tin wuri kinenawa kanki 'yanci muddin kinaso kiyi rayuwar farin ciki agidan mijinki,to karkiraga mata intanuna miki yatsa kikarya inko taso kuyi zaman lafiya toh kuyi,maza kishare hawayenki banson ganin ki cikin damuwa"murmushi tayi tare da share hawayen fuskarta tace nadena Aunty,martanin murmushin Aunty Aliyah tamayar mata tace kokefa..mikewa tayi tafita sukacigaba da sabgoginsu,yayinda Sukainat taji kaso ashirin cikin damuwar ta yaragu....
_VOTE_ β
_COMMENT_
*And*
_SHARE_
*_ESHAA CE~_*π€π»
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
(TRUE LIFE STORY)
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
*PAGE 5&6*ποΈ
________________________πZaune suke a dining area suna dinner,Cike da so da kaunar junansu suke hira,tamkar zasu koma cikin junansu saboda yanda suka mannewa juna."Ahankali Ahmad yamaida kallon sa gareta cikin sweet voice din sa yace my Queen haryanzu baki fada min mekikeso nayi miki Na fadan kishiyaba"murmushin ya'ke tayi tace Honey da kabarshi domin kaga hidin dimu sunyi maka yawa nayafe,'bata fuska yayi yace anma de kinsan hakkin kine ko?,kuma tunda inada halin yi yazama dole nayi miki dabani dashi shine zakice kinyafe dan haka kifadi duk abinda kikeso nayi miki"Shiru tayi kamar me tunanin wani abu,sekuma tace kabani 1million,murmushi yayi yace kintabbata ze isheki?"Kai tagya'da masa alamar eh"tana mejin zuciyarta na kuna tamkar zefashe wai ita Ahmad zeyiwa kishiya,ita Ahmad ze ha'da dawata azuciyarsa,ita Ahmad zerabawa kansa da wata hakika duk wacce tayi gangancin shigowa gidanta seta gwammaci zaman gidan yari akan gidanta setayi rayuwar kunci da bakin ciki acikin Gidan ta.'Karan shigowar massage wayar tane yakatse mata tunanin ta,Hannu tasanya tadauki wayar tare da bude massage din, Alart tagani na 2million daga Ahmad dinta,da murmushi afuskarta tamikewa tabasa peck akuncinsa,thank u so much Honey tace dashi, anma gaskiya kudin sunyi yawa kagafa akwai sauran hidindimu agabanka duk da nasan cewa bawai baka dashi bane anma yakamata inrage maka dawainiya"murmushin jin dadi yayi yanda take tayashi son duk wani abu dayakeso"cikin jin dadi yace kin cancanci fiye da haka my Queen girmankine, inayiwa Allah godiya daya azurtamin ke amatsayin mata burina kuhada kanku da Sukainat kuyi zaman lafiya.
Tamkar yacaka mata mashi akirji haka taji jin