Showing 1 words to 3000 words out of 77506 words
Chapter 1 - DR HAJAR BOOK COMPLETE DOCUMENT BY DIJA WAZIRI .pdf
[18/12 7:31 pm] Dija Waziri:
DOCTOR HAJAR
GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Mai kowa mai komai muna neman gafaransa. Ya
Allah ka azurta mana tsoranka wanda zai iya hana mu sab'a maka. Ina kodiya a gareka Allah
daka bani ikon fara wannan littafi lfy Allah kasa na kareshi lfy Allah ka bani daman isar da
sak'on da nakeson isarwa ga Al'umma Allah kasa kuma ya amfanesu Allah ka ganar damu
abunda bamu ganeba Allah karabamu da sharrin duk wani me sharri Allah ka biya mana
buk'atunmu ......
*TSOKACI*
Wannan labarin ba gsky bane be faruba k'irk'iranshi nayi kawai don nisha d'antar da masu
karatu ,Allah ka bani ikon isar da sak'on da nake fatan ze amfaneku insha Allah duk wani
wanda ze karanta labarin don haka ina rokon yan uwana da duk yanda kukaga littafin ya
kasance karku ce komai cox haka na riga na tsara...
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan Littafin gareki yar uwata HAJARA HUM'D BUBA Allah ubangiji ya cika
miki burinki Allah yaji k'an mahaifinki yasa haske kabarinshi Allah ya Albarkaci ruyuwanki Allah
ya rayaki muga har auren ki ,Ameen......
KUNA RAINA YAN MUTUNCI
Neeratluv my Besty
jannat (k'awar arziki)
My zee yabour
First lady
Husna Bauchi
Zara Bukar
Mss Xoxo
Yar ficika
Sajna
Aisha Abbakar
Khadija Candy
Maryam S Bello
Anty Khadee
Mummy Sultan
Maman ihsan
Beebei dee
Zara B-B
Action baby
Ayusha Ilyasu
Da sauran wanda ban lissafoba duk kuna raina ina muku fatan Alkairi Allah ya k'ara muku
basira da, daukaka Allah ya rabaku da sharrin mak'iya
Ban manta dakuba yan group d'ina (D&W Novels) Nagode ,da irin son da kuke nuna min Allah
ya barmu tare ya k'ara had'a kanmu, ya biya muku buk'atunku Ameen...
LITTAFIN MARUBUCIYAR
FANSA (RIVENG)
BURIN MINAL
NADIYA
ZURI'A D'AYA
K'IYAYYAR NAMIJI
KANO
"Kaga Malam pls live me alon na fad'a maka wai ana soyayya dolene? Kafa takura ma rayuwa
ta".
"Baiwar Allah don girman Allah kiyi hak'uri ko sunanki ki fad'a min pls I'm begging u," sai kuma
kayi ae, khadija zomu tafi " kije ina zuwa" khadija ta fad'a ranta 'a b'ace ...
Wucewa tayi tabar khadija wurin kallon mutumin khadija tayi tace "bawan Allah kayi hakuri da
'akwai dalilin dayasa kaga tak'i sauraron ka 'amma kar kayi fushi insha 'Allah zan shawo maka
,kanta ga number na, za muyi waya dakai duk yanda mukayi da ita"..
"Ok na gode (god bless you) " murmushi khadija tayi tace "Ameen sai anjima", har zata wuce ya
tsaidata da cewa , pls baki fad'an sunan kiba da kuma sunan k'awar taki "ohhh sorry sunana
khadija ita kuma Hajo " wow ashe sunan mamana gareta", Allah sarki tow barin wuce kar tayi ta
jirana " ok tow thank you very much Nana Khadija am captain murad by the way" ur wlcm
captain sunan babana gareka so bazan iya fad'a ba" Allah sarki ,kice zaki dinga gaisheni har
k'asa kenan duk sanda muka hadu" murmush tayi tace "maizai hana barin tafi kar tayi ta jirana"
ok tow ki gaida mun ita kow bye"....
Tawuce ta , tafi da Sauri don tasan ba k'aramin aikin Hajara bane tatafi ta barta..
"Dallah yar rainin wayo kin sani sai jiranki nake , kuma kinsan nace miki zan d'auki Jawahir a
school" fuskar Khadija 'a d'aure tace sorry tow muje"..
Tunda suka fara tafiya babu wanda yawa wani magana cikin su, Hajar ta fahimci khadee
haushinta ,take ji , murmushi tayi tace "Khadee wai yanaga sai wani 6ata rai kike?".
"Hmmm Hajar kenan ba dole na 6ata rai ba wlh abunda kike baya dacewa sam" rayuwan
duniya tana kunshe da abubuwa da yawa, na d'aya farin ciki, bak'in ciki, haduwa, rabuwa
,samu, rashi lafiya, ciwo,mutuwa, Annabi ya horemu da muyi hakuri da duk wanda mukayi karo
dashi domin ba zai dauwama ba, zai wuce.
Amma ke sam kink'i mance abun daya riga ya wuce she karu biyar da suka wuce, haba Hajar
wlh kiwa kanki fad'a, shi kenan haka zak k'are rayuwanki bazakiyi aure ba 'ina gudun ranar da
Jawahir zata buk'aci ki ,kaita gurin mahaifinta, mezaki ce mata ?wacce amsar kike da ita da zaki
fad'a mata? I hope kin tanadesu?".
"Hmmm Khadee wlh bazan ta6a iya mancewa da abun daya faru ba 'a kullum na kalli Jawahir
sabo yake zamamin Khadee namiji bad'an goyo bane Bazan kuma yarda dawani d'anamiji a
rayuwata ba, namiji mugune Allah ya isa min"ta k'arashe tana kuka ,
Kiyi hakuri Hajar nasan abune mai wuyar mancewa a gareki bake kad'ai ba har muma bazamu
mance ba Amma idan kinyi la'akari bafa duka maza bane masu mugun hali kuma keba yarinya
bace yanzu Dr Hajar"...
"Duk nayarda da abunda kika fad'a Khadee Amma mubar zance kawai, don kina tayar min da
ciwan dake damun zuciyata ne kawai". da haka suka isa school d'in su Jawahir suka d'auko ta
sannan suka d'auki hanyar d'anladi nasidi
A hotoro Dr Hajar ta ajje Khadee ita kuma suka, k'arasa cikin estate d'in Ibrahim kunya wani
k'aton gida suka shiga mention wanda ya gaji da haduwa daga gete din gidan, anrubuta wlcm to
Doctor galadanci house da wani abu me kelli...
Cikin gidan kuwa abun kallone don komai da tsari aka yishi ginin gidan sama ne, wanda 'akwai
wurin da zaka iya ganin mutanen waje wurin da glass akayi shi, wasu furanine a zagaye a gidan
masu bada wani kamshi me kwantar da hankali cen gefe guda kuwa wurin shak'atawa ne
wanda yasha kujeru na alfarma sai kuma wurin parking spaces wato gurin (ajje motoce) motoci
guda bakwaine a gidan ferari da BMW lemozin CRV Lombagini Land rovar sai 406 wanda ake
kai yara school...
Daga ,gefe guda kuwa akwai k'aton masalaci had'ade ,sai kuma d'akin me gadi kusa da get din
gidan ,get din kofee brow ne me remot da an danna ze bud'e kansa, sai kuma k'asan gidan
dayasha intalock masu kyau kalan ja da ruwan toka,
Karnuka ne kwance wurin guda shida masu kama dana surawa sai harkan gabansu suke kala
kala...
Fitowa tayi ta kama hannun jawahir suka nufi wata kofa me kyau ,dannan bell tayi wata yar
budurwa tazo ta bud'e mata ga dukan 'alamu yar aikin gidan ce , da murmushi ta kar6i jakar
dake hannun Dr Hajar da kuma lunch boxs din dake hannun Jawahir ,
Shiga sukayi suna shiga k'amshin abinci ya daki hancin su , wuri coredor ne haka sai kitchen ta
gefe sai kuma wani k'ofa transperant ana iya ganin nawaje amma nawaje bazai iya ganin na ciki
ba, falow ne wurin yasha royar chairs ruwan madara da goldin masu masifar kyau da laushi cen
gefe guda kuwa daining aire ne shima royal ruwan madara da goldin sai kuna wani drowar da
aka ajje cups dasu madara confals da sauran su zubi da tsarin falon yayi ga wani taf keken tv
tare da stand dinshi na gani a fad'a gefe guda kuma stairs ne me hannun k'arfe yasha carpet
gefen wurin anjera wasu cendulls masu bada wuta different colos sai kuma wani shoglass
wanda yasha humurori da turarukan wuta masu k'amshi
Hawa saman sukayi nan ma wani falow ne wanda taci uwar na k'asa a haduwa ,kujerun ciki
royal ne suma amman ruwan toka hannun kuma sky blue da carpet dinma haka sai santa tabel
kalan jikin hannun kujeran ,sai katon tibin bango wanda sai wane da wane ake ganin irunsu a
gidan su gefe guda kuma wani standard a.c ne, had'ad'e gefe da gefen gurin t.v kuma wasu
manya manyan sufiku ne tare da hufan su,falon ba k'arya yayi k'amshin turaren wutane kawai
ke tashi sai sanyi ac dake bugawa gidan shiru babu hayaniyar kowa sai tv dake aiki sai kuma
na'urorin gidan na more rayuwa ,cikin falon akwai daki daya sai kuma da'an fito akwai dakuna
guda uku daya na kalifa daya na Dr Hajar d'ayan kuma ciki da falo ne shima na 'alfarma shi
kuma na mahaifin sune...
Zama tayi kan lalausar kujeran dake falon tana ,maida numfashi irin ta gaji dinnan, kuma kowa
yaga fuskarta yasan bata, da walwala kuma tana cikin damuwa, "Alawuya ina Mami" ta fad'a
tana cirewa Jawahir doguwar rigan school din ta" tana d'aki bata jima da shigaba yanzu bak'inta
suka tafi" ok maybe ta shiga sallar la'asar ne ,yau me kike dafa mana?" Sakwara miyar igusi sai
kuma marfesun naman kai sai gashe -shen kifi da ,dankali," wow my best food yau zanci abinci
kenan na koshi kin kusa gamawa?" Eh miyar igusi da farfesu suna wuta sakwara da kifi da
dankali kuma nagama su"...
"Yawwa tow kiyi sauri ki gama kafunnan nayi wanka sai naci, yanzu tafi da Jawahir ki hada
mata confax tasha" suna fita Dr Hajar ta fara sana'ar nata wato tunani , har Hajiya ta fito bata
sani ba ,saida ta dafata sannan ta dawo daga duniyar tunani data shiga..
"Wato Mamana ,har yanzu baki dena tunanin nakiba kow? kina so ki sawa kanki hawan jini a
banza .
Hajara!! mun fiki jin d'aci da zafin abundaya faru" a razane Dr Hajar ta dago tana kallon Hajiya
tana hawaye don wannan shine karo na farko data ta6a kiranta da sunan Hajara saboda
mamana take ce mata saka mak'on sunan maman baban su Hajar d'inne..
"Amman mun fawalana Allah tunda munsan k'addara ce zata iya fad'awa kan kowa , tow ke don
meyasa bazaki kar6i k'addarn kiba ? Jarabawa ce Allah yake miki kuma ina miki fatan Allah ya
baki ikon cinye ta.
Manzan Allah ya bamu addu'a yace Wanda ya gamu da wata masifa ko bala'i tow ya dinga
karanta wannan adu'ar insha 'Allah zai samu waraka,
*inna lillahi wa-inna ilayhi raji'oon, allahuma -ajurnee fee museebatee wakhluf Lee khayran
minha.*
Fassara:mu daga Allah muke kuma hak'ika mu ,masu komawa ne zuwa gare shi ya Allah !ka
bani ladan hakurina a kan wannan masifa kuma ka mayar mini da abin da yafi ta alheri..
Kow kuma ki dinga yin wannan addu'ar yayewar baqin ciki.
Wanda ya hadu da bakin ciki ko damuwa aharkan rayuwa ,ana so ya yawaita karanta wannan
addu'ar isha Allahu Allah zai yaye masa dukkan damuwarsa ,kuma zai saukaka masa dukkan
lamarin sa.
*ALLAHUMMA LA SAHLA ILLA MA'A JA'ALTAHU SAHLAN WA'ANTA TA JALUL HAZNA
IDHAA SHI'ITA SAHLAN*..
MA'ANA:ya Allah babu wani abu sassauka sai dai abinda ka saukaka .kuma kaine idan kaso
kake sanya bakin ciki ya zama abu mai sauki , Aduba SUHIHU IBNI HIBBAN hadisi mai lamba
2,427 IBNUS SUNNEE hadisi na 351 domin k'arin bayani..
"Kuma ki yawaita salatin annabi da karatun Alkur'ani, ya fiye maki wannan tunanin da babu inda
zai kaiki"...
D'agowa tayi tana hawaye tace"nagode Hajiya insha 'Allah zanyi amfani da 'abunda kika fad'a
min".
"Yawwa mamana 'Allah ya miki albarka"..
"Ameen Hajiya barinje na watsa ruwa nazo na ci abinci"..
"Tow sai kin dawo ina takwara ta?" Tana k'asa wurin Alawuyya"..
D'aki tashiga kai d'akinta kawai abun kallo ne pink color ne dakin da fari komai naciki pink and
write ne, kaya tacire ta dauki towel ta shige toilet tayi wanka tayo alola , tana fitowa ta d'auko
wani riga da wando na kanti marasa nauyi tasa wandon skin tait ne baki dogo har k'asa sai riga
ja me hannun bes da hoton mage a gaban rigan wanda 'aka zana da bakin abu doguwa amma
baikai gwaiwa ba kama kanta tayi da ribbon ta d'auki hijab ta ,tada sallar la'asar...
Tana idarwa saiga Alawuyya da Jawahir sun shigo , littafin add'u'oin ta ,ta dauka ta fara karan
tawa, alawuya kuwa toilet suka shiga tayiwa Jawahir wanka ta samata wani doguwar ,riga mara
nauyi mai lk'aramin hannu...
Dr Hajar na idarwa tasa Jawahir a gaba saida tayi bacci sannan ta sauka k'asa doncin abinci,
daining area ta wuce nan tayi karo da mahaifinta doctor galadanci da Mami da Khalifa sunacin
abinci. Da fara'a sanye a fuskarshi yace "mamana dama kin dawo?" itama murmushin tayi tace
yes tun d'azu na dawo " ok amma mum d'inki bata fad'an ba don tsabar son kai ita taganki
amma ni bata sanar dani kin dawo ba" a zolaye yayi maganar yana kallon Hajiya , dake
murmushi kawai tace"tsakanin ku da yarka ai sai kai, nima lokacin da kake bata abu sani nake
ae saidai na ganta dashi "dariya kawai yayi ita kuma ta nemi waje ta zauna ta fara cin abinci.....
*WACECE DR HAJAR DA KUMA 'ASALIN SU*
Dr Hajar yar ce ga Dr Muh'd Tahir Galadanci da hj Asma'u, Dr Galadanci babbab likitane yana
da babbab hospital me suna get well special hospital, Dr Galadanci ba karamin atajirin mutun
bane yana da dukiya me tarin yawa, yana da matarshi ta 'aure guda d'a Hj Asma'u auren
soyayya suka Hj Asma'u yar bokoce sosai Amman bata 'aiki saboda Dr kafun suyi aure ya nuna
mata baya buk'atar tayi wani aiki inde kud'i shi ya d'auki nauyin babu abinda zata nema tarasa
'a gidanshi Hj Asma'u saida ta shekara 3 gidan miji sannan ta samu ciki ta haifo santaleliyar
yarta me kama da maman mijinta sak, Dr Galadanci yayi matuk'ar farin ciki da kyautar da Allah
yayi musu don tunkan yayi aure yake kwad'ayin idan yayi aure Allah yabashi d'iya mace don
yasa, sunan mahaifiyar shi Hajara ,sai kuma 'Allah ya karb'i addu'ar shi, ranar suna yarinya taci
sunanta Hajara, mahaifiyar Dr ta d'auki son duniya ta d'aura wa Hajara haka iyayen tama sunaji
da ita basa k'aunar suganta cikin bak'in ciki duk abunda takeso to shi ake mata, tundaga lokacin
da aka haifi Hajara Dr ya maida sunan hospital dinshi sunan ta, kuma yaci burin saitayi zurfi a
karatunta ta zama babban docton mata hakan yasa ya tsaya mata 'akan karatunta sosai,
Dukda irin sakalcin da suke nuna mata be hanasu bata tarbiyya ba, tun tana jss 3 mahaifinta ya
d'auketa ya kaita chaina 'anan ta k'arasa secondary school d'inta har jami'a, bayan ta gamane
tadawo naija tayi NYC d'inta sannan ta koma london tayi masters d'inta tow daga nan kuma
tafara aiki a hospital d'in mahaifinta, bawai don taso ba taso ace ya barta, tayi Phd kafun ta fara
aiki. Saida ta shekara 13 da haihuwa sannan Hj Asma'u ta sake samun wani cikin ta haifo san
talelen danta beby boy shi kuma yaci sunan mahaifin Hj Asma'u tow tundaga lokacin Allah be
sake basu haihuwa ba..
ASalin su yan Adamawa ne amman suna zaune a garin kano mahaifin Dr ya rasu tun yana ciki
shi kad'ai mamarsa ta haifa, tow tundaga lokacin bata sake aure ba tanan Dr yayi mata gidanta
me kyau tare da masu kula da ita..
Dr Hajar ba fara bace sosai kuma ba bak'a bace, tana da hanci dai-dai misali tana da yalwar
gashin ido dana gira tana da gashi sosai tana da ken jiki dadi Dr Hajar tayi tako ina don zan iya
cewa tacika goman lol tsayawa fasaltata b'ata lokacin me karatu ne
Wannan shine tak'aitaccen labarin Dr Hajar
masu karatu
Hope zaku biyoni don jin cigaban wannan lbrn comments dinku shine k'arfin gwaiwa na
Ya kuke gani acigaba ne koya?
Sai naji daga, gareku zan cigaba......
*DIJA_WAZIRI CE*
[18/12 7:31 pm] Dija Waziri:
DOCTOR HAJAR
*Allah yana jaraftar bawanshi ta kowace hanya don yaga iya k'arfin imanin shi,*
*Dukkan tsanani yana tare da sauk'i ,duk abinda kaga ya sameka na farin ciki kona bak'in ciki
tow ka da'uki hannu ka gode wa 'Allah kuma ka ,kusan cesa ,sosai insha 'Allah zai yaye maka
dukkan damuwar ka*
*idan ka rasa abinka, kada ka rasa hankalinka, damuwa bata maidoda b'atacce ,bata dawoda
matacce, bata hana k'addara yin Aikinta. Barwa Allah duk abinda ya sameka ,sai Allah ya isar
maka duk Al'amuranka*
*nasiha ce Allah yasa mudace*
Dedicated to Sadfa, Faty azland, zara k'awata, ummixey ,kuna raina Allah yabarmu tare
Jannat mungode da soyyar Allah ya biyaki da gidan Aljanna,
Naga sabon buk yanda kika fara lfy Allah ubangiji yasa ki gama lfy, Allah
Yasa mutane su amfana da 'abunda kike son fad'akarwa Ameen
Chapter 2
"Madam dan Allah ki taimaka ki shigar da files d'ina gurin likita d'ana zai mutu, " kinga Malama
na fad'a maki mutane sun rugaki ha'a nifa kin dameni " haba!!, baiwar Allah ke kuwa ki taimaka
mata mana bakiga yanda 'd'an yake burgima kamar zai mutu ba," kaga Baba ,babu ruwan ka
nagafa mutane sun rugata"....
"Tow Allah ya kyauta 'amman gsky inde haka wannan asibitin yake gara mutun yaje na gomnati"
kiyi hakuri Baba na tabata da Dr Hajar me asibitin tana kusa da wlh kunshiga...
Bayan minti 20
Subhannala ya take amai meke damun ta ? Ina nurses d'in suke? wlh tun jiya take fama da
'amai da gudawa shine muka kawota 'tow munyi munyi da masu gurin su shigar damu muga
likita sunk'i "...
"Ya salam jamila "Na'am Doctor " ku tafi dasu x ray aje yai masa maza sai kuzo yaga Doctor
kuma karnaji karna gani ,zanje naga patient d'ina nasan suna jirana "ok ma'am....
Dr Hajar tana wucewa mutanen dake zaune wurin suka fara k'usk'us, "wannan fa itace me
Hospital din bakuga yanda take