Showing 1 words to 3000 words out of 68987 words
[11/19, 10:00 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ
*HAƊIYAR GATARI*
1
©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
Alhamdulillah!!, Ina Ƙara Miƙa Godiyata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Yadda na fara rubuta
wannan sabon Littafi Lafiya, ina roƙon Allah ya bani ikon kammala shi Lafiya.
Bayan *SAWUN KEKE* Ga wani Sabon Salo, Sabon Tsari, Ina Fatan za ku bi ni a sannu
domin jin Abinda ke Ƙunshe a cikin wannan Littafi Me Suna *HAƊIYAR GATARI* Kai tsaye Ba
lallai ku fahimci me Sunan yake nufi ba, amma indai kun yi haƙurin Bibiya Za ku Fahimta.
Ina Gaisuwa
Takun nan ce dai *INDO*......
Marubuciyar
WATA HANYA
DOGON YARO
IDO HUƊU
SAWUN KEKE
TAJMAHAAL
A JINI ƊAYA
SIRRIN ƘETA
AAMINAT (Bazawara)
Da sauransu.......................
10/11/2023
Bismillahirrahmanirrahim.
Sassanyar waƙa gami da hayaniya da iface-ifacen Ƴan Matasan Samari gami da Shewar Ƴan
Mata ga kuma Surutan MC ke tashi ta ko'ina a cikin Ɗan Madaidaicin Hall ɗin, wanda ya
sha Ado da kwalliya da ƙawa ta ko'ina. Duk da ƙarami ne amma sai Masu abin ne kaɗai ke
iya yin shagali a cikinsa. Kai tsaye dai za a iya sanya shi cikin Jerin Abubuwan da ake kira
SAI KA KAI SHEGE.......
Casu gami da shaye-shayen Lemuka da ciye-ciye iri daban-daban ake yi. Kusan kowane
Saurayi da Budurwarsa a wajen, in ma bai zo da tashi ba zai samu Abokiya.
Cikin farin ciki da kwanciyar hankali Kowa ke gudanar da shagalinsa.
Ihun MC ne ya karaɗe Kunnuwan duk ilahirin Mutanen dake wajen, cike da karaɗi da
ƙarawa al'amari Ƙawa yake cewa "Don Allah duk wanda ya san ya zo Taya Irfan Mohammad
Murna ne ya yi shiru kuma ya zubawa Ƙofar shigowa wannan haɗaɗɗen wuri ido, domin ganin
Da wane Salo Babban Abokin Birthday Boy zai shigo!!!!!, sannan Duk wanda yake son jin
kowanene Wannan Babban Aboki da muke ta jiran Shigowarsa ya ɗaga hannu." Cikin
sauri gami da shauki mafi rinjaye Mutanen wurin suka ɗaga hannu.
MC ya sa dariya yana cewa "Wallahi Sai kun biya wani abu zan gaya muku!!, in ba haka ba
kuma zan hana Abokin Birthday Boy ɗin shigowa, Ina son a kece raini tsakanin Mata da Maza
don haka ga inda Mata za su juye Jakarsu ga Inda Maza za su juye tasu." ya faɗa yana
nuna masa wasu Ƴan ƙananun Tebura dake kusa da inda yake tsaye yana zubo maganar. Shiru ba wanda ya fara zuwa hakan ya sa MC ƙara cewa "Yau dai za mu gani Mata ne
Jaruman ko Maza; Maza kar ku bari Mata su kayar da ku don wallahi suna fara fitowa kun faɗi
warwas!!!!" ya ƙarasa maganar yana dariyar shakiyanci da Yaudara.
Jin haka ya sa aka fara tsere tare da gudun wuce tsara a tsakankaninsu, cikin Lokaci kaɗan
suka tara masa kuɗaɗe Mazan kuwa sabida Burga har da masu ajiye watch ɗinsu kuma
suka ce in Matan sun isa su saka, Su ma Matan da yake sun ƙagara su ga shigowarsa
wasu tuni suka cire layukansu suka ajiye wayoyinsu. Kasancewar Mafi yawancinsu Ƴaƴan Masu Kuɗi ne ko damuwa akan hakan ba su yi ba.
Sai da MC ya ce ya dakatar sannan suka dena Wasan kece raini.... "Dariya ya saka yana
cewa ba shakka wannan Babban baƙo namu me farin jini ne domin kuwa Mata sun yi da
gaske sun kayar da Maza sabida son ganinsa!!!" Tafi akasa gami da shewa tuni wurin ya
ƙara karaɗewa, Wasu daga cikin Mazan suna cewa an yi musu maguɗi, shi kuwa MC hakan
ƙara ziga shi ya yi, sabida Magana Tamkar zai tashi sama.
"To!!! to!!!! DJ yana Godiya yana ƙarawa!!; yanzu dai kowa ya saurara domin jin sunan
haɗaɗɗen Abokin wannan Chocolate ɗin Birthday Boy namu!!" sai da surutan nasu ya lafa
sannan ya ci gaba da cewa "1 - 2 - 3 ALIYU ALMUSTAPA NAIRA!!!!! Muna yi maka Barka
da zuwa wannan waje!!!!" Tafi suka sake sanyawa gami da ihu, lokaci guda Salon wajen
ya ƙara canjawa, da yawa daga cikin Ƴan Mata iyayi da kwainanensu sai da ya canja, duk
suka zubawa Hanya ido cike da Ƙaguwa, kowacce ta ƙwallafa rai akan jan ra'ayinsa.
Sanye take cikin wata fitinanniyar Gown wadda ta kama jikinta tsam-tsam, ta sha Make-up
kamar ba gobe, ta yi bala'in kyau, duk wanda ya kalleta sai ya ƙara, ga eyelashes ɗinnan
zaya-zaya sun ƙara mata kyau da armashi, ta baya kuwa haɗaɗɗen kitson Ƙarinta ya bazu
akan bayanta zuwa kafaɗunta. Waige-waige take yi tamkar me neman wani abun, karaf idanunta suka sauka akan wani da
ke tsugunne gaban wata Haɗaɗɗiyar Mota me Numfashi yana ɗan tattaɓa tayoyinta.
Da sauri ta ƙarasa wajen gami da yi masa sallama tare da Addu'ar Allah ya sa Direba ne, da
sauri ya juyo yana tsitstsilla ido kamar Munafuki, cikin yanayinta na jijji da kai da ɗagawa ta
ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan ta ce "Daga ina do Allah??, wannan Motar Me gidanka
ce??" Jin tambayar tata ta sa shi washe baki sannan ya bata amsa, "A'a Hajjaju, daga wata
Unguwa nake wai ita Ɗorayi." "To gayyatarka aka yi wajen Birthday ɗin??" da sauri ya girgiza
kai yana cewa "Wace ni??, a'a kawai dai na ga an yi posting ne a Facebook ana gayyatar
kowa shine na garzayo in sha 5 alive in tafi, Allah ya sa ma sun yi mana Ƴar garau-garau ɗin
da zamu afa." dogon tsaki ta ja gami da binsa da wani kallo wanda ya fi kama da na ƙyama
sannan ta ce "Menene garau-garau kuma??" tuntsirewa ya yi da dariya yana cewa "Ai Hajjaju
ku manya ne ba lallai ku santa ba, wani Abinci ne namu na Hausawa." Tsaki ta ƙara yi a karo
na ba adadi sannan ta ce "Kai nan har wani Bahaushe ne?? ni ai kama kake yi mini da irin
Fataken nan, yaya ake kiran Yarensu ma??, irin waɗanda za ka ga suna aikin Gadi a Manyan
Gidaje" cikin sauri ya ce "Buzaye?? yo ai Ranki-yadaɗe baki faɗi ba, na ji an ce Kakan
Kakana asalinsa Buzu ne, amma dai tinda ban iya kowane Yare ba barni a Bahaushen
kawai." ɗan numfashi ta ja kafin ta ce "Za ka yi min aiki in biyaka??" Da sauri ya ce "Haba
Hajiya indai za ki bani na cin Taliyar Yara ai ba matsala zan yi." Murmushin samun nasara ta
yi kafin ta ce "Dama PA ɗina ne na aikeshi wani wajen, to ba na son Yawo ni kaɗai shine nake
so ka tsaya a matsayin PA ɗina a wannan wajen, Bayan Mun fito zan biyaka, amma fa za ka
dinga yi mini ladabi sosai sannan kai za ka riƙe mini jakata." leƙewa ya yi ya ƙara gano Jakar
tata, ba laifi da ɗan girmanta, jinjina kai ya yi yana ƙara faɗaɗa fara'arsa ya ce "Na Amince
Ranki-yadaɗe, Muje kawai kina tafiya ina take miki baya, ba ki da matsala." ta yi wani yauƙi
gami da cewa "Okay, amma in ba ka yi abinda ya kamata ba ba zan biya da yawa ba ko kuma
ka rasa ko ficika." "Me zai hana yin aiki tuƙuru ma Hajiya ai kin wuce nan a wajena, ni a kullum
ma in za ki mayar da ni Ɗan Aikinki indai za ki biya na Amince." Murmusawa ta yi kana ta
miƙa masa jakar tana cewa "Yaya sunanka ne??" "Ali Haidara" ya faɗa yana ƙara washe
haƙora kamar me tallan makilin, yana karɓa ta yi gaba ba tare da ta ce komai akan sunan
nashi ba; da sauri ya dakatar da ita da cewa "Hajjaju don Allah jirani, kin san mu Buzaye sai
da rawani." gaba ta yi tana cewa "Ina ɗan can wurin maza ka zo ka sameni."
Zazzafar iska ya furzar yana bin bayanta da kallo.
Sai da ya naɗe fuskarsa da kansa ya rage sai idanunsa kaɗai a waje sannan ya bi bayanta.
A tare suka shiga ɗagwas-ɗagwas tana tafe yana binta a baya kamar wani Mijin Ta ce.
Sai suka zama abin kallo kuma abin sha'awa ga Mutane, shi kansa MC sai da ya bata yabo da
jinjina da girmamawa, hakan ya sa kanta ya ƙara huruwa Kamar Balo.
Tinda suka shigo Irfan Mohammad ya zuba musu, ba kowa yake kalla ba face na bayan
nata ita kuwa sam bai ganeta ba ma.
Sai da ta ƙaraso inda yake suka gaisa sannan ta yi masa bayanin itace Leelah Facebook
Friend ɗinsa, na bayanta kuma Body guard ɗinta ne. Tarbar Mutunci da Mutuntawa ya yi
mata gami da yi mata godiya a bisa kyautar da ta bashi, sannan ya sa a rakata waje na
Musamman a kula da ita.
Har zuwa lokacin hankalinsa ya fi karkata kan Body gourd Ɗin nata, hakan kuwa ya sosa
mata rai don so take ta ja ra'ayinsa akan Soyayyarta amma shi yana can yana kallon wani
Gardin Namiji Ɗan Uwansa.
Duk wanda ta haɗu da shi bayan gabatar da kai sai ta gabatar da Body Guard ɗinta.
Bayan sun zauna Ya dubeta kafin ya ce "Amma Hajjaju za ki ƙara min Kuɗi ko??, na ga da
farko PA kika ce mini yanzu kuma kin mayar da ni Body Guard!" tattaɓe baki ta yi a
yanƙwane ta ce "Ka fiye azarɓaɓi, na gaya maka indai kuɗi ne ba ka da matsalarsu." Laƙwas
ya yi yana zazzare ƴan idanunsa a cikin Naɗi.
Shagali aka ci gaba da yi yayin da MC ke ta ɓaɓatun Kiran Abokin Birthday Boy amma shiru
wasu har sun far tunanin ko raina Musu hankali yake yi.
Kallo ne ya koma sama lokacin da wata Ƴar Budurwa me Halittun Indiawa ta doso ciki, sanye
take cikin wata Shegiyar Doguwar riga blous fara tass!!, daga ƙasan rigar a buɗe yake
buzur!! sai sharar ƙasa take yi daga baya, duk da Ɗan Mayafin da ta naɗe kanta da shi sai da
Dogon gashinta dake ta sheƙi da walwali ya bayyana. Cikin nutsuwa da kamala gami da jin kai take takawa, tana yi tana sama da ƙasa da
dara-daran idanunta wanda Allah ya ƙawata mata su da dogayen gargasa. A bayanta Kuwa
wasu daka-daka Ƙartai ne hannayensu riƙe da award wanda ya sha ado irin na Indiawa.
Duk wanda ya kalleta sai ya ƙara ba ma kamar Maza, Manyan Abokan Irfan ne kawai suka
Ganeta ciki kuwa har da shi.
MC Kuwa tuni ya ƙara ruɗa wajen da surutai kamar wanda aka yiwa allurar hauka.
Tattausar ajiyar Zuciya ya sauke wadda ta kusa tawowa da hawayensa, shi dai ya san Ba dai
Abokinsa ya ba shi Kunya ba.
Kai tsaye wajen Irfan wanda yake binta da ido ta nufa, sai da ta isa gabansa sannan ta saki
murmushin da ya ƙara bayyanar da ainahin kyaunta, cikin zazzaƙar muryarta ta ce "Ka yi
haƙuri Yayana yana Uzuri ba zai samu zuwa ba." "Ba komai, iya ganinki da na yi ma ai ya
biyani, ki temaka mini ki yiwa kowa bayanin abinda ke faruwa don kuwa duk wurin nan shi ake
jiran gani." nisawa ta yi kafin ta yi magana cikin yanayin shagwaɓa "Ka san ba na son sa idon
Mutane Irfan Bhai" "Na sani temaka mini za ki yi Chotti Bahen" ya yi maganar yana
kwaikwayon tata maganar har da shagwaɓar, dariya ta yi kafin ta ce "To ka rakani sai ka fara
gabatar da ni." amsawa ya yi sannan suka nufi wajen da MC yake.
Leelah da ke tsaye ta riƙe Ƙugu wani baƙin ciki ya tokare mata Zuciya, ita da take shirin
cusawa Irfan Soyayyarta ya ƙi saurararta sai wata me jan kunne. Ali ne ya dubeta kafin ya ce
"Hajjaju a zauna mana" "Kai ba zan zauna ba" ta faɗa a masife, ya yi dariyar Yaro ba Mutum
ba sai ya girma kafin ya ci gaba da sa hankali akan Irfan da Ƴar Indiyarsa. Bayan ta gabatar da Uzurin Yayanta ta bayar da kyauta tana shirin miƙawa MC Microphone
Azaan ya dakatar da ita ta hanyar tare mata hanya yana binta da wani shegen kallo da babu
komai a cikinsa sai zallar ƙwalama gami da iskanci.
"Me ya sa za ki fito a irin wannan daren??, 11:37PM fa ai na ɗauka Mamarki ba ta barinki
gantali yadda kike da tsaurin halin nan." Dakakkun idanunta ta watsa masa kafin ta ce "Ba
ruwan wani da lokacin fita da shigata, bani hanya." "Ba za ki wuce ba har sai kin bani amsar
tambayoyina, ko kuma daga nan in wuce da ke guest house ɗina mu kwana tare.... Tasss!!!!
ta wanke shi da wani kyakkyawan Mari me ratsawa har cikin ƙwaƙwalwa. tuni wurin ya ɗau
ihu da shewa don kuwa abin ya burge Mutane tamkar a film suke kallonsu.
Azaan kuwa jin ana yi masa dariya ya ƙara fusata shi, sauke hannunsa ya yi daga kan
kumatun yana cewa "Ni kika mara???" cikin ɗaga murya ta yadda har Microphone ɗin yana
amsawa ta ce "Na Mareka How dare you!!!!" shu'umin murmushinsa ya saki ba tare da ta
ankare ba sai jinta ta yi a cikin ƙirjinsa ya yi mata wata muguwar matsa, ta buɗe baki za ta yi
magana ya rufe bakin nata da nasa, sai da ya kai a ƙalla 3 minute yana kissing ɗinta sannan
ya saketa yana ƙara wararo mata tsayayyun idanunsa.... ita ma kallonsa take yi ya yinda
Zuciyarta ke wata muguwar tafarfasa...... gefen mayafinta ta sa ta goge bakinta hakan bai
wadatar da ita ba don haka ta taƙarƙare ta ƙwalla ihun cewa "Rochaaaan!!!!!!!!!" Sai da
kowa na wajen ya firgita, aka ƙara zazzaro ido ana kallonsu, Azaan kuwa sai da numfashinsa
ya tsaya na ɗan lokaci kafin ya ci gaba da gudana, Idan ya tsaya jayayya da kansa ma akan
cewar bai tsorata ba ya ɓatawa kansa lokaci, tuni zuciyarsa ta fara bada Darrr!! darr!!!!! tana
tsalle. Ba ihunta ne kawai ya tsorata shi ba jin sunan da ta ambata.............
*PAID BOOK, 300 ONLY*
*INDO*
[11/19, 10:00 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/Ghq9lsJzlnsD0d4jlde7rQ
*HAƊIYAR GATARI*
2
©️
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
*GORGEOUS WRITER'S FORUM*
.........Zuwa yanzu ya gane dole