Showing 1 words to 1082 words out of 1082 words
Chapter 1 - Tarihin Shehu Usman Dan Fodiyo Da Jihadinshi.docx
Assalamu Alaikum
Jamaar wannan Zaure ina Neman Taimakon a yi mini Karin haske game sahihanci ko rashin sahihancin *TARIHIN DAN FODIO* dake a kasa👇
An haifi Usmanu dan Hodiyo a kasar hausa cikin yankin Gobir a wani gari da ake kira Marata a kusa da Birnin Kwanni ranar wata lahadi ta karshen watan safar, shekarar 1168 hijiriyya (wajajen 1759 miladiyya). misali shekara dari biyu da sittin da suka wuce kenan.
Ɗanfodiyo yayi karatu ga malamai masu yawa a kasar hausa, yayi karatun Alkurani a gaban mahaifinsa, ya koyi ilimin fikihu bisa mazhabar Imamuna Maliku ɗan Anas a gaban Malan Abdurrahman ɗan Hamadi, ya koyi karatun littafin ishiriniya da wasu littattafan addini a gaban malan Usmanu Bakabe, Haka kuma ya koyi karatun littafin Muhtassar daga kawunsa mallam Bibnoduwa.
Baya da haka, Usmanu ya zauna a hannun Sanannen Malamin nan na ƙasar Hausa wato Malan Jibrilla (wanda ta hanyar sa alaƙa ta ƙullu tsakanin Ɗanfodiyo da Malan Bakatsine) yana ɗaukar karatu. Lokacin da malan Jibrilla yayi niyar zuwa Hajji, ya biya ta Agadez, sannan ya mika Usmanu Ɗanfodiyo ga mahaifinsa shikuma ya wuce aikin Hajji.
Usmanu Ya fara karantarwa a garin “Degel” inda mahaifin shi yakezaune lokacin yana ɗan kimanin shekara 35.
Wata rana sai ya tafi Birnin Alkalawa babbar Alkarya inda Sarkin Gobir Bawa JanGwarzo don ya nemi Iznin yin wa’azi cikin garuruwa. A lokacin kasar Hausa akwai tsarin da malami baya fara wa’azi sai ya chancanta, sai ilimin sa yakai na ya fara wa’azi.
Malaman fada suka yi mishi wata tambaya suka umarce shi da yaje ya ƙaro ilimi daga nan yazo musu da amsa.Kimanin Shekara ɗaya Ɗanfodiyo bai samo amsa ba, sai malamman suka sanar dashi amsa.
Jangwarzo ya bashi iznin yin wa’azi cikin garuruwa harma ya haɗa shi da ɗanshi “Muhammadu Yumfa”, Ance ta dalilin Yumfa Ɗanfodiyo ya samu karɓuwa a ƙasar Hausa (Duk garin da yaje wa’azi al’umma da yawa suna taruwa).
Bayan da Usmanu ya samo inzinin yin wa’azi daga Alkalawa, sai ya Shiga cikin garuruwan Zamfarawa. Ya shekara Kamar biyar yana wa’azi ya zauna kamar su Dauran (cikin kasar Zurmi) Da Faru (Cikin kasar Maradun).
Wata shekara Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo yasa a tara duk malaman da ke cikin kasar hausa ranar bikin Sallah. Ance malamai kamar kimanin dubu suka taru A cinkin su Akwai Malan Usmanu Danfodio.
Sarkin Gobir Ya yi wa malaman kyautar kudi da tufafi, yaba Ɗan fodiyo dukiya mai yawa, Ɗan fdiyo ya roƙi alfarmar ayiwa mutanen gidan yari afuwa a saukaka haraji, da makamantan su, Bawa Janwarzo ya yarda da duk abubuwan da Shehu ya bida.
Bayan dawowar Ɗanfodiyo daga wannan kira na Sarkin Gobir, ya ci gaba da yawon wa’azi. Ya tafi kasar Kabi (Sarkin kabi yayi mishi tarba ta musamman), har ya isa llo, daga nan ya ketare gulbin Kwara ya dakata nan yana wa’azi, (Saboda nan ne iyakar kasar hausa). Sannan ya dawo ya yi kudu har ya isa kasar Zoma da Zugu (Wajen Gumi).
Lokacin da Allah ya karɓi ran Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo sai aka ba ɗan’uwansa Yakuba sarauta, bai daɗe ƙwarai ba ya rasu, sai aka ba Aliyu Nafata, Bayan rasuwar Aliyu Nafata Ɗan fodiyo ya goyi bayan a naɗa wa Yunfa sarauta a lokacin an ce Yumfa yana kan bitar littafin Mukhtasar ne a gaban shi.
Komawar Dan fodiyo Gudu
Bayan Yunfa ya hau gadon sarauta ya aika ma Malan Abdussalami da ya dawo Alkalawa anyi mishi afuwa, amma sai malan Abdussalami ya ƙi. Wannan ne yasa Yumfa ya aika da Dogarai su Dawo dashi. (Abdussalami yabar Alƙalawa ya koma Gimbana ne saboda rashin jituwar data shiga tsakanin shi da Sarki Nafata).
Dogarai Suna bisa hanyar su ta dawowa daga Gimbana sai Fulani daga Degel (watau garin da Usman Danfodiyo yake) suka abka musu suka Saki Malan Abdussalami.
Labari yazowa Yunfa, yumfa ya damu ƙwarai, har yayi niyyar ya ɗauki matakin korar Fulani da ke Degel.
Jin haka Sai Ɗan fodiyo ya umurci ƴan uwansa da su fice daga wannan gari su koma wani kauye da ake kira Gudu.
Ɗanfodiyo dashi da dukkan Fulani suka tashi daga Degel, suka koma Gudu chan tsakanin kasar Gobir da Kabi.
Sarkin Gobir Muhammadu Yumfa ya Tara malamai ya nemi Shawarar su, ya ce Dani da Malamina wane ne bisa gaskiya? Sai malaman suka ce, “Kai ne bisa ga gaskiya, Hillani Sune bisa ga hanyar da bata daidai ba”.
Fulani sun kafa ƙungiya Bayan komawa Gudu 1802-1803.
A shekarar 1802-1803 Fulani suka koma Gudu suka kafa kungiya suka naɗawa Dan fodiyo matsayin shugaba. Wanda ya fara yin gaisuwa gare shi, shine kanensa, Abdullahi, Sai dan sa Bello, sai abokin sa Umaru Alkammu. Sa’an nan sauran mutane suka biyo baya.
Bayan wannan ne Suka fara yin tanadin kayan faɗa.
Garuruwan da fulani suka fara kaima Hari a kasar Hausa
Bayan kafa kungiya karkashin jagorancin Dan fodiyo, da kaɗan kaɗan fulani suka fara kai hari Birnin Ƙwanni da Matankari kusa da Kalmalo a ƙasar Gobir.
Daga wannan lokaci ne faɗa ya tashi tsakanin Fulani da sarakunan ƙasar hausa tsakanin shekarar 1803-1804.
Usmanu Ɗanfodiyo bai taɓa fita fagen yaƙi ba. Sai dai yana nuna ma Fulani yadda za Su tafiyar da yaƙi.
Dan fodiyo ya aika ma duk mutanen su dake ƙasashen hausa da su yi himma ga yin abun da suka kira Jihadi a wuraren da suke. A wannan rikici fulani sun gayyato sarkin Agadaz da Sarki Agale da maguzawan fulani, da kuma wasu kasashen hausa waɗan da basu iya biyan Haraji.
Fulani Sun ci mafi yawan garuruwan ƙasar Hausa, Suka canza sarakuna Haka kuma suka shinfiɗa mulkin fulani cikin kasar Hausa.
Ɗanfodiyo yace ya ƙaddamar da jihadi ga sarakunan Hausawa ne akan abubuwa kamar haka:
Zaluncin su.
Tsananta Haraji
Mayar da mulki gado da Gudanar dashi ba a kan tsarin musulunci ba.
Bayan mamaye ƙasar Hausa Ɗan fodiyo ya raba ƙasar ga ƴan uwanshi da ƴa6an shi, ya raba tutoci ga Sarakunan daya kafa, ance a lokacinne Ɗanfodiyo yaba Sulaiman dake Kano Takobi da wuƙa da Kundi da kayan faɗa irin na wannan zamani, ya kuma umarce shi da ya yanka duk wanda baiyi biyayya gare shi ba, wannan rashin adalcin ne yasa Abdussalami bagimbane ya nuna damuwar sa daga karshe shima aka ce yabar hanyar Musulunci aka kashe she
Cikin ikon Allah Ɗanfodiyo bayyi nasarar kafa tuta a Kasar Borno da Katsinar maraɗi, da Zazzau Suleja da Birnin Alƙalawa (Babbar
Alƙaryar Ƙasar Hausa ta wancan lokaci ba) saboda jajircewa da sukayi suka kare kansu.
والله
علم