Showing 1 words to 3000 words out of 27403 words

Chapter 1 - ABDULFATAH by Fatima S Umar Jajira.txt

ABDULFATAH
by Fateemah S Umar Jajira




PAGE 1-2




A hankali take saukowa daga benan har ta k'araso cikin falon zama ta yi kusa da shi ta na ya mutsa fuska ta ce


"Morning my choice."


Yana mata kalon tuhuma ya ce


"Morning ya gajiyar ki ta jiya?"


Baki ta tab'e ta ce


"Ba gajiya na yi sauki."


Murmushi ya sakar mata ya ce


"Okay ya kamata ki tashi mu yi bearkfast sai ki koma ki k'ara hutawa ko."




Tana yatsina fuska ta ce


"Ka ga my Choice ni fa na yi bearkfast d'ina tun ba ka dawo daga kiran Abba ba, kai dai ka je ka yi na ka."




Girgiza kai ya yi ya mik'e ya haura darning table d'in ya fara tsiyaya tea a cup ya k'ara suger san nan ya d'auki spoon yana tonawa,
Satar kalon ta yake yi, tun da ya tashi tana rike da waya tana dannawa,
Kad'an ya sha tea d'in ya mik'e yana cewa


"To My zan wuce office."


Kalon sama da k'asa ta masa ta ce


"Office fa ka ce My Choice tun yau zaka fara fita na ga yau 2days ke nan da kawo ni gidan nan amma za ka ce za ka fita wani office."




Murmushi ya yi cikin rarrashi ya ce


"Ayya! hakuri za ki yi My ina da marasa lafiya da yawa da suke buk'atar kulawata, in sha Allah zuwa 2:00pm zan dawo gida."




Ya k'arasa maganar yana kamo hannun ta da fuskar tausayi


"To na ji amma kar ka huce two d'in don Allah"


Kai ya gyada mata ya ce


"In sha Allah"


Mik'ewa ta yi ta rakoshi har waje hannun sa na cikin nata har ya shiga motar sa sannan ya sake ta ya ce


"Ki kulamin da kanki My."


"Kai ma haka."


Ya tada motar ya fice daga gidan tana d'aga masa hannu har ya fice sannan ta koma cikin gidan,



Sama ta haura ta shiga d'akinta ta zauna gefan gado ya d'auki wayarta ta kira wata number,
Bugu d'aya zuwa biyu aka d'auka daga can b'angaran a kace


"Hello! kawata ya kike? Ya Amarci?"


Lokaci d'aya ta jero mata tambayoyi,


Murmushi Mufida ta yi ta ce


"Amarci lafiya lau k'awata mutumin ki harda rawar kai da yi mun sannu."


Dariya sosai Nuratu ta yi ta ce


"Ai wallahi Mufida ba k'aramin tada mun da hankali wannan mijin na ki ya yi ba, na d'auka duk shirin da muka yi a banza zai tashi tun da kika ce mun Doctor ne."




Murmushi Mufida ta yi ta ce


"Haba Nuratu duk shirin da Malam Tanimu ya mana zai tashi a banza ne?"


"Hhhhhh haka ne fa k'awata ba shi ya yi kan saba dan haka sai yadda muka yi da shi"




"Ashe kin gane k'awata"




"Yauwa tun da yanzu mun gama da page d'in maganar mijinki to yanzu ya maganar Alhaji Sani kin san fa dan kin yi aure ba yana nufin kun rabu ba kuma kin san idan Alhaji Sani ya san kin yi aure sunanki sorry ko?"




Ajiyar zuciya Mufida ta yi ta ce


"Gaskiya ne na san rashin hakuri irin na Alhaji Sani yanzu ya san na yi aure sai ya kashe auran kuma asirina zai tonu a gurin ABDULFATAH dan haka zan ji da shi"


"Yauwa k'awata"


Nan Nuratu ta ringa ba wa k'awarta ta shawara yadda za ta yi da Alhaji Sani,
Har suka yi salama Mufida ta ajiye wayar.




Tun da *ABDULFATAH* ya fita yake aikin tunani, har ga Allah bai yarda da Mufida ba amma ya rasa me yasa ya kasa d'aukan mataki a kanta amma duk ya ji ta fita a ransa tun da ta kasa rike mutuncin kanta,


Haka yaringa tunane-tunane har ya k'araso Asibitin wadda aka rubuta
*ABDULFATAH* *HOSPITAL*


Me gad'i ne ya bud'e masa kofa ya shiga, fitowa ya yi ya na nufi cikin Asibitin, gai da shi aka rin ka yi har ya k'arasa office d'in sa,






Shiga ya yi ya sa key ya kulle ya zauna akan kujerarsa ya kifa kansa a table d'in gaban sa,




Ya jima a haka ya ji ana buga k'ofar, tsaki yaja ya mik'e ya zare key d'in sannan ya ba ta izinin shigowa, ganin wadda ta shigo ba k'aramin b'aci ransa ya yi ba,




Budurwace da bazata haura shekara 18 ba sanye take da kaya farare na nurses




Kanta a k'asa jikinta na rawa ta ce


"Barka da safiya Sir! da fatan ka tashi lafiya?"


Ta k'ara maganar tana d'agowa ta kalle shi, ganin irin mugun kalon dayake jifan ta da shi ya sa ta k'ara tsorata,


Cikin fushi Abdulfatah ya ce


"Sau nawa zan fad'a miki idan na zo kar ki bari naga wannan bak'ar fuskar ta ki, naga alama aikin Hospital d'in nan ya fara isarki shiyasa kike k'etare umarnina."




Kai ta girgiza muryarta na rawa ta ce


"Ba haka bane sister Hauwa ce bata zoba shine Doctor Rukayya ta ce nazo na fad'a maka akwai matar da kasawa rana zaka mata CS sai kuma ka shiga hidimar biki to matar tazo tun shekaran jiya kuma ta ce a nesa ta ke shiyasa zata koma gida ba zata jira ka dawo aiki."




Harara ya watsa mata ya ce


"Yaushe gidadancin ki ya fara shafar na kusa da ke, meyasa Doctor Rukayya bazata kirani a waya ta sanar da ni ba ko ita da Doctor Nasir su mata CS d'in har sai an jira na dawo? yanzu ida ban dawo yau ba fa? kuma matar wani abu ya sameta fa? ki je ki ce ta zo ina kiranta kuma wallahi kika bari na k'ara ganin wannan bak'ar fuskar ta ki hmmm ki kuka da kanki."




Ko bari ba ta yi ya gama maganar ba ta fice daga office d'in tana haki
Ya bita da harara ya tsaki.




Islam na fita ta sanar da Doctor Rukayya sakon Doctor Abdul ta d'auki kayata ta fice daga Hospital d'in gaba d'aya.








*Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karantawa* *zasu* *biya* #200 *kacal*
*Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167




COMMENTS
AND
SHARE








by
*XAHRA*







*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 3-4






_____________ Gida ta nufa ranta a dagule, idan da mutumin da ta tsana a duniya to Dr Abdul ne ji take kamar ta kasheshi tahuta da muguwar tsanar da ya mata tarasa me ta tsare masa a rayuwa da ya tsaneta haka,






Abunda bata sani ba shi Abdulfatah bak'ar maca ce bayaso a rayuwar sa dan cewa yayi daya auri bak'a gara ya mutu a aure, shiyasa ya auro Mufida sabuda Mufida farace k'all,




Shi Abdul ya d'auka farin Allah da Annabi ne baisan na kanti bane, shiya yake mugun son Mufida wai a cewarsa farar wace itace mace bak'a kuma muna mata.




Haka Islam ta koma gida ranta a b'ace, a tsakar gida ta zube tana cika tana batsewa,
Ummi ce ta fito daga kitchen tana kallon ta ta ce


"Lafiya kuwa uwata naga kin dawo yanzu? keda yau aikin safiya kika tafi."




Hawaye Islam ta share ta ce


"Gaskiya Ummi na gaji da wannan shegen aikin, daga yau ba kuma zuwa zanyi ba ai talauci ba hauka bane"


Nunfashi Ummi ta sauke cikin rarrashi ta ce


"Haba uwata haba mamana ki dena iskanta aikin da muke cin abunci dashi kiyi hakuri wata rana sailabar."




"Amma Ummi dan kana cin abunci a k'ark'ashin mutum saiya ringa wulak'an ta ka, shima fa Allah ne ya bashi ba wayansa ko dabarar sa ba."


"Hakane uwata amma wasu basa fahimtar hakan, idai akan likitan kune in sha Allah wata rana zaizo har gaban ki ya duk'a ya baki hakuri kuma zaizo neman wata aifarma a gurin ki da yardar Allah."




Ido Islam ta zaro ta ce


"Ummi kinsan halin wannan mutun kuwa?"


"Ban saniba Mamana amma yardar Allah na ce kuma kinsan lamarin Uban giji ya huca nan."




Ajiyar zuciya Islam ta sauke ta ce


"Hakane Ummi lamarin Uban giji yahuce nan dan nima ikonsa ne ya kaini matakin dana ke ciki a yanzu."


Haka Ummi ta zauna ta ringa tausar Islam tana bata baki har har Islam ta saki ranta ta manta da batun wani Dr Abdul ta cigaba da harkokin gabanta ranta fari k'all.




Sai yamma Abdul ya koma gida tun daga waje yake jin k'arar kid'a yana tashi kuma bana hankali ba,
Da sauri ya shiga gidan ya tadda Mufida a falo kure kid'a sai rawa ta keyi tana d'aukar Video,




Kayan jikin ta ya kala ya ga rigace iya guwa sai wando da kad'an ya huce rogar,


Sarai Mufida taga shi gowar sa amma ta share sa,
Sai da ta gama video sannan ta juyo tana murmushi ta ce


"Harka dawo k'arfe biyu ko?"




Harara ya watsa mata ya haye sama ya barta,
Itama da Harara ta rakashi ta cigaba da rawar ta.




Ya jima a zaune a d'aki yana takaicin abunda Mufida ta masa, ya dawo daga office mai makwan ta masa sannu da zuwa saita bige da tuhumar sa,




Tsaki yaja sabuda yadda yaji yinwa tana kwakular sa.




Wayar shi ya zaro a aljihu ya kirata ya ce tazo, yana kashe wayar ya bud'e data ya shiga WhatsApp,


Status ya fara dubawa da Status d'in Mufida ya yi karo ashe duk videos da pics d'in da tayi posting ta ringayi, jikin Abdul ne ya d'auki rawa sabuda Allah ya zuba masa kishi a rawuyarsa,




Ko salama babu Mufida ta shiga d'akin zama tayi kusa dashi ta ce


"Gani My Choice."


Shiru ya yi na d'an lokaci kad'an kafin ya ce


"A gidan ku ba'a koya miki bawa miji abunci ba in ya dawo?"


Ido ta zaro ta ce


"Abunci fa ka ce? Kana nufin ni zan girka na baka?"


Kalon mamaki Abdul yake mata,


Tayi murmushin rainin hankali ta ce


"Tun huri ma ka nemi wadda zata ringa dafa ma abunci dan ni ba......!"




Tsawar da Abdulfatah ya daka mata ne tasa ta had'iye sauran maganar dake bakinta, cikin d'aga murya ya ce


"Wallahi ki tashi ki dafa mun abunda zanci tun ranki bai baci ba"


Baki ta turo gaba ta kunkuni ta tashi ta fita.




Wayar da ta manta yakan gadon ya d'auka ya bud'e ya shiga WhatsApp d'in ta,
Comments d'in mutane ya ringa gani akan pics d'in data d'ora wasu suna Amarya tayi kyau harda maganar daba ta dace ba kuma yawanci duk maza ne abokan charting.




Bata jima ba ta dawo d'auke da plet a hannun ta ajiye masa tayi, ya kali filet d'in,




Kwai ta soya fari fattt dashi ko albasa babu sai k'arni ya keyi.




D'agowa ya yi ya kaleta ta had'e rai ta ce


"Nifa shi kad'ai na iya soyawa."


Takaici da bakin ciki yasa Abdul kasa cewa komai sai tsaki da ya yi ya mik'e ya fice abun sa.




Sarah ce ta shigo da salama Ammi ta amsa ta zauna kusa da Ummi ta ce


"Ammi kinsan me?"


"To uwar kawo k'ara me akayi?"


"Baki ta turo ta ce ba wannan Yaya Abdussamad d'in nan bane na gama girki na ya kwashe ya cinye d'an kad'an ya bar mun."


"To yanzu tunda ya bar miki ragowa mene na kawo k'ara ba Yayanki bane?"


"To amma Ammi....!"




"Nifa kin ta kuramun tashi ki bani guru."




Mik'ewa Sarah tayi zata fita Ammi ta ce


"In anjima ki kiramun Abdulfatah kice Abban su ya ce Jibi zai je ya d'auko Maman Kaduna."




"Laaa Ammi taji sauki Maman?"


"Taji sauki Jiki Alhadulilah."




"Masha Allah, Allah ya k'ara mata lafiya."


"Ameen, amma fa kice wayata ce ta samu matsala shiyasa ban kirashi da kaina ba, karya je ya rufeki da fad'an nasa."




"Lalai kuwa Ammi na dan Yaya Abdul akwai lafiyar fad'a wannan aunty Mufida tana kokari."




Juyawa tayi zata fita suka had'a ido dashi.
Ido Sara ta zaro gabanta yana fad'uwa murya na rawa ta ce ........






*Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal*
*Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167




COMMENTS
AND
SHARE








by
*XAHRA*





*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 5-6






_____________ "Sannu da zuwa Yaya."
Harara ya watsa mata ya huce ta ya shiga ciki,
Gaban Ammi ya je ya zauna yana ce wa


"Ammi ina huni."


"Lafiya lau Abdulfatah ya gidan?"


"Lafiya k'alau Ammi."


"Dama yanzu nake cewa Sarah ta kira ka ta ce maka Abban ku ya ce jibi kaje ka d'ako Maman Kaduna."


"Allah ya kaimu, Ammi dama idan da abunci a zubumin yinwa na keji."


Ya k'arasa maganar yana sosa kai,


Murmushi Ammi ta yi ta kira Sarah,


Shigowa Sarah ta yi ta zauna kusa da Ammin ta ce


"Ammi gani."


"Yayan ki zaki kawowa sauran abuncin naki da kike fad'a akan sa."


Fuska ta marairaice zatayi magana taga Abdulfatah ya rararo ta tai saurin mik'ewa ta fita.




Abunci taje ta zubo masa ta kawo masa ta ajiye ta fice, itama Ammi mik'ewa tayi tabi bayan Sarah.






Saida Abdulfatah ya ci ya koshi sannan ya yiwa Ammi salama ya fice,
Ita kuwa Sara sai wani abuncin ta dafa tana ta mita.






Sai 12:30am Abdulfatah ya koma gida lokacin har Mufida tayi bacci, yaji dadi sosai da yaga tayi bacci sabuda yasan damun sa zatayi.


Wanka shima ya yi ya kwanta.




Washe gari shi ne ya fara tashi a gurguje yayi alwala ya yi salah dan ya makara, har yayi wanka yai shirin office Mufida bata tashi tayi Sallah.




Tashin ta ya farayi yana kiranta


"Mufida."


Mik'a tayi ko salati babu tana hamma ta kalle shi, shima ita yake kallo,
Mik'ewa zaune tayi ta ce


"Ina zakaje da sassafen nan?"


"Hospital zani mana."


"Wai meka keso ka d'aukeni ne Abdulfatah? Jiyama fa haka kace ba jimawa zakayi ba zaka dawo da dare ma har nai bacci baka dawo ba sannan kace yau ma zaka k'ara fita da sassafe."






Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya ce


"Ga kud'i nan akan stool idan kina buk'ata zaki anfani dasu."


Yana gama fad'in haka ya juya ya fice daga d'akin,


Da kalo Mufida ta bishi a ranta tana ayana irin tashin mutuncin da zata masa.




Yau tunda Islam ta shigo Hospital bata bari sun had'u da Abdulfatah ba, har lokacin tashin ta ya yi ta fito domin tafiya gida,




Tana sauka daga bene ne kicin rashin sani ta taka b'awan Banana aikuwa ta zame tayi k'asa zata fad'a, ji tayi ta fad'a jikin mutum k'anshin turaran sa ne ya tabbatar mata da waye,


Ji tayi kamar ta saki fitsari a gurin sabuda tsoro da firgici, shikuwa Abdulfatah cikin fushi ya hankad'eta ta daki ginin gurin,




Saida ta saki k'ara sabuda zafin da taji tana zubar da hawaye,


Kallon tsana Abdulfatah yake jifan ta dashi cikin b'acin rai ya ce


"Kewace irin jaka ce jahila bagidajiya dazaki fad'owa mutane jiki, ko da gidan ku bakuda bene? Koda yake ina matsiyata sukaga arzikin yin bene a gidan su, to inma da gangan kika tab'ani nafi k'arfin ki domin ni ba irin sauran k'azaman 'yan iskan tasha ki bane ki sake tunani yarinya mtsss."




Yaja tsaki ya huce ya barta a tsaye tana sharar kwala.
Sauka tayi ta fita daga Asibitin d'an sahu ta tare ta shiga tana faman kuka.




Ta madubi yake kallon ta lokaci zuwa lokaci yana kalon yadda take kuka, gyaran murya ya yi ya ce


"Haba baiwar Allah komai ya sameki kiyi hakuri ki daina irin wannan kukan, Allah madaukakin sarki da kansa yake sanar damu acikin suratul bak'ara aya ta 155 cewa Allah zina iza asabatuhun musubatu, k'alu inalilahi wa'ina ilaihirraji'un, to meyasa zakiyi anfani da fad'ar ubangiji ba koda mutuwa aka miki ki daure kita maimaita inalilahi wa'ina ilaihirraji'un."


D'agowa Islam tayi suka had'a ido da saurayin ta duk'ar dakai a hankali ta furta
"Nagode."


Daga haka bata k'ara magana ba, shikuma sai nasiha yake mata har suka k'arasa gidan su Islam.




Fitowa tayi ta mik'o masa kud'in sa, murmushi ya yi ya ce


"Bazan amshi kud'in ki ba alfarma d'aya zaki mun itace kibani Number ki."


Murmushi Islam ta yi ta ce


"Me zakayi da number ta."


"Sabuda kina buk'atar wanda zai ringa kwantar miki da hankali ni kuma zan iya."


"Hmmm Ummi na zata iya kwantar min da hankali ai ba saika wahalar da kanka ba."




Murmushi ya k'arayi wanda saida fararan hakoran sa suka bayana ya ce


"Duk da haka ki bani dama duk wannan damuwar taki in sha Allah zata ragu."


Duk yadda Islam ta so ya rabu da ita yak'i saida ta bashi number ta ya ce


"Wane suna zansa?"


"Islam."


"Wow nice name suna me ma'ana, nikuma Sahal."


"Masha Allah suna me dad'i."


"Nagode fa."


Ya fad'a yana dariya
Da haka sukayi salama ta shige gida.




Wacece Islam


Islam 'yar salin garin Meduguri ce ba banta da babarta duk 'yan can ne sunada arziki da wadata sai canji gurin aiki ya samu babanta ya dawo Kano da zama nan Sharad'a ya cigaba da zama da matar sa Amina da yaranta biyu Fateemah (Islam) sai Aliyu yanda shine k'arami.




Shekarar su biyu da dawowa Kano Allah ya amshi ran mahaifin su,
Sunyi kukan rashi sosai duk da 'yan uwan Baba sun so tafiya da su Islam amma Ummi ta hana ta ce zata iya rik'e 'ya'yanta, gun kar a kwace mata yara yasa tak'i komawa Meduguri tai zamanta a nan duk da nan sai rufin asirin Allah can kuma da masu taimakon ta amma ta fi son zaman Kano.




Shikuma Asalin Abdulfatah
Baban sa d'an asalin Kano ne amma mahai fiyar 'yar Kaduna ce
Baban su yanada mata biyu Hajiya Khadija (Maman Kaduna) ita ce babba tanada yara uku maza Abdulfatah shine babba sai Abdulmalik sai Abdussamad ita kuma Ammi tana da yara biyu Abdallah da Sarah wadda ita ce autar su


Rashin lafiya da Mama takeyi na Asuma ne yasa dole ta koma Kaduna gurin iyayen ta da zama duk da ba rasa me kula da ita tayi ba amma ita ta buk'aci hakan


Baban su Alhaji Umar yana matuk'ar k'aunar matar sa Khadija sabuda tun bashi da ko sisi take zaune dashi shiyasa duk abunda take so a rayuwar ta komene shi indai bai sab'awa shara'a ba sai yayi mata.




Wannan kenan


Bayan kwana biyu , yau Sunday ba aiki dan haka Abdulfatah ya shirya ya tafi d'ako Mahaifiyar ta su yana zuwa bai ko bari ya zauna ba ya d'ako Mama suka taho gida.




Ita kuwa Mufida dataga yayi asuban ci ya fita kawai takira abokai maza da mata wai zasuyi..................!




*Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal*
*Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167




COMMENTS
AND
SHARE








by
*XAHRA*





Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login