Showing 1 words to 3000 words out of 135428 words
Chapter 1 - NOOR IMAN(Complete) BY GUREENJO.pdf
í žíľNOOR IMANí žíľ
*Fatima Muhammad Gurin*
    â˘Gureenjo6763 on Wattpadâ˘
*'Yar mutan Adamawa*
í ˝í˛ŤANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
         *01*
Tafiya kawai nakeyi sam ban san inda nake jefa kafana ba bare na kula da hanya, hawaye
kawai ke kwaranya daga cikin kurmin idona zuwa kan kumatu na.
Tsananin damuwan da nake ciki be sa na kula da kan hanya na jefa kaina ba seda naji wani
wawan bugu yayinda students na arean suka saki salati wasu na ihu, runtse kyawawan idanuna
kanana nayi cikin jin zafin bugun tun daga kafana har tsakiyar kwakwalwana amma ko kad'an
zafin be kai na zuciyata ba.
A hankali na waiga na kurawa bakar meserati wadda gabad'ayanshi baki ne har glasses d'in ido
don ganin ko ze fito ya bani hakuri amma ko motsi kofan motar be yi ba bare ayi alamun
bud'ewa.
Mikewa nayi na d'ingisa kafana da nasan yayi mugun buguwa na koma gefe na zauna, wasu na
min sannu wasu kuma cewa suke Allah ya kara dama yarinyan kullum tana tafiya kaman
mahaukaciya sam bata da hankali a kanta me makon a kaita psychiatric amma an kawo ta nan
makaranta ko me zata d'auka oho.
Kuma runtse ido na nayi ba su kad'ai ba duk inda zan gilma sau d'aya sau biyu zasu ce psycho
ce ni ba wai dan wai yanayin shigar jikina ba, a'a tsantsar rashin natsuwa da damuwan dake
d'auke a yanayina da fuskana ke sa su zaton haka duk da sanyi na a abubuwa dayawa.
Karan wucewar motar da speed shi ya dawo dani daga duniyar tunani na, kafana na riqe da
zarazaran yatsotsin hannuna na dinga matsawa har naji dama dama amma na tabbatar akwai
matsala jin irin azabar dake shigana.
Agogon dake d'aure a tsintsiyar hannuna na kalla 7:50 ajiyar zuciya na sauke kan na mike na ci
gaba da tafiya a hankali Ina d'ingisa kafan na nufi auditorium sbd achan nake da lectures karfe
takwas gashi yanzu 7:50.
Ban isa auditorium ba se takwas da kusan mintuna takwas hall d'in tsit kaman anyi ruwa an
d'auke a hankali na tura kofan na shiga bakina d'auke da sallaman da iyakarshi pink lips d'ina a
hankali na ci gaba da takawa da nufin karasawa ciki In samu wurin zama.
Seda nayi tsakiyar hall d'in kan naji an ce "who the heck did yhu think yhu are!!! Will you get out
of my class jor" sam muryanshi bata da hayaniya dukda tsawa yayi ba don microphone da yake
amfani da ita ba ko rabin ajin baza su ji tsawar nashi ba bare lectures d'inshi.
Juyawa nayi na mishi kallo d'aya yayinda shi kuwa idonshi ke kan damin lecture note d'in
hannunshi.
'Fa tabarakallahu ahsanul khalki' na furta akan lips dina ban kara gangancin kallonshi ba na
juya na fita a sanyaye still cikin d'ingishi kujeru irin na zaman d'alibai dake gaban hall d'in na
samu na zauna Ina sauke ajiyar zuciya.
A rayuwana ban ta'ba ganin namiji me irin kyaunshi a fili ba sede a tv, tv d'inma se tashoshin
larabawa ko indiyawa kwata kwata ban san yadda zan fasalta kyaun shi ba sede na san yana
da bala'e'en kyau ga fari me d'aukan hankali.
Share tunaninshi nayi sbd damuwana ya fi karfin tunanin kyaun wani halitta, ya zanyi da
rayuwana, wai laifin me na aikata da ake hukunta ni da abunda ban san hawanshi ba bare
saukanshi? Why always me? A shekaruna na 23 a duniya nayi aure sau hud'u duk ba wadda na
mishi kyakyawar wattanni biyar.
Yes inada kyau daidai misali amma kyauna ba me d'aukan hankali bane sbd fata me duhun
haske ce dani wato 'chocolate' color ba kallo d'aya zakamin ka fahimci kyaun da surar da Allah
ya bani ba shiyasa tun ina shekaru sha takwas a duniya samari suka min rutututu kowa so yake
ya mallakeni.
Ashe ni kam maza sune kaddarana ganin kullum za'ayi sallama ace ana kiran Noor Iman yasa
baba na yanke shawaran In fidda miji ya min aure.
Dukda bana so sbd Ina matukar son karatu kan aure amma ba yadda na iya kasancewata me
tsananin biyayya yasa na fidda wani saurayina da ya nace min tun Ina jss class ba 'bata lokaci a
randa na cika sha takwas cib a ranar aka d'aura min aure da bello sede abun takaici a ranar da
aka kaini gidanshi a ranar Bello ya dankara min saki har uku ba tare da na san laifi na ba.
Cikin tsananin tashin hankali na dawo gida da safiyar ranan amma se babana da 'yan uwanshi
suka rufu akaina da duka ba tare da sunji ta bakina ba, ba don mama ba 'yaddiko na, wato
kishiyar mahaifiyata' da inaga ban yi rai ba a ranan.
Bakaken maganganun da na sha ko seda nayi dana sanin zuwa na duniya dayawa suna cewa
rashin kai budurcina gidan mijina yasa ya min wannan wulakncin yayinda maganan yayi tasiri
akayi ta yad'ata unguwa da 'yan uwa.
Amma abun takaici ko kallo ban ishi umma na ba, bare sannu ko kuma ta ajiye ni taji damuwa
ta hakan yafi komai yimin ciwo a rayuwa ban san daad'in uwa ba, ban san abinda ake cewa
uwa ba a kaina kam sede Ina ganin yadda take kula da kannena kaman zata maida su ciki.
Abun na min ciwo fiye da tunanin me tunani, mutuwar aurena na farko yayi sanadiyar tashinmu
a rijiyar lemu, muka koma gadon kaya da zama sbd ban isa fita ba haka 'yan gidanmu, Babana
na matukar sona kan faruwan mutuwar aurena na farko, wani irin so yake min da ban san
iyakarshi ba.
Sbd tausayin da nake bashi, komai sede kishiyar uwata ta min, tun Ina karama umma ke
banzantar da ni wai ita alkunyar 'yar fari a yadda baba ya fad'amin kenan amma har yau ban
yarda ba sbd abun yayi yawa.
Ban san kula ba se a wurin mama, ban san yadda ake shagwa'ba a gaban uwa ba se a
gabanta, ban da wadda zan kaiwa kuka na se mama, da farin cikina da bakin cikina duk tare
muke rabawa se ince ta fini shiga damuwa akan mace macen aurena.
Hayaniyar d'alibai masu fitowa daga auditorium hall ya tabbatar min da an gama lectures d'in,
d'ago idon da zanyi se ya fad'a cikin nashi ko second idonshi be yi a kaina ba ya manna bakin
space akan sparkling brown eyes d'inshi tare da nufar motanshi cikin takun isa da kasaita, se a
lokacin na gane ashe wadda ya kad'e ni a hanyar shigowata shine lecturer d'inmu na yau.
Kallonshi nake yadda farinshi ke d'aukan ido ga baki wuluk d'in gashin kanshi dake kwance
lublub har kasan keyanshi se sheki yakeyi, irin gashinne cike da giranshi haka sune gargasan
dake kwance a hannunshi zuwa saman kirjinshi da ya fito kad'an sbd V neck black shirt da ya
saka.
Ina mamakin wannan bawan Allahn anya d'an nijeria ne? Bakaken kananan kayan dake sanye
a jikinshi ya kara fitar da farin fatarshi, kananan maganganun da d'alibai suka fara akanshi ne
yasa ni kauda kaina daga kallonshi na mayar kasa Ina me kokarin sake zundumawa duniyar
tunani na naji an zauna gefe na.
A hankali na waiga se naga wata kyakyawar matashiyar yarinyar da tunda na fara zuwa
makarantan take yawan ce min sannu bayan ita ban ta'ba magana da wani d'an ajinmu ba,
alhalin Ina cikin sati na hud'u kenan da na fara zuwa makarantan ta BUK inda nake karantar
B.sc Ed Biology.
"Sunana Zarah Ahmad Malabo and yhu?" Da kyar na iya yi mata yake don murmushi wahala
yake min nace "Saudah Hafeez ana kirana Noor Iman".
*â˘Assalamu alaikum 'yan uwa ga fah Gureenjoh da sabuwar littafi hope zaku so shi kaman
sauran books d'ina, promise yhu will never regret reading my book, in shaa Allah, comments for
more pagesâ˘*
Â Â Â Â Â Â Â Â Â Â í ˝íś¤Gureenjoí ˝íś¤
í žíľNOOR IMANí žíľ
*Fatima Muhammad Gurin*
â˘Gureenjo6763 on Wattpadâ˘
*`yar mutan Adamawa*
í ˝í˛ŤANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
*02*
âWow nice name, kiyi hakuri fah da abinda Dr. Abdurraheem ya miki haka yake da wulakanci ga
dizgi wai shi In har ya shiga aji to ba me shiga a bayanshi, amma ke baki jima da fara zuwa ba
ko? Gashi an ci rabin semester na san baki yi catching up wasu abubuwan ba, zan dinga koya
miki karki damu daga yau mun zama friendsâ.
Lord!! Wannan bade surutu ba mutum kaman aku, na raya a raina a fili kuwa murmushi na mata
Ina son inyi karatu sossai inga na zama wata a duniyan nan yanzu ban son aure ban son wani
magananshi karatu kawai hakan yasa nake son yin kokarin yaki da zuciyata In kuma kau da
tasiri da maganan mutane ke min inyi karatu tukuru.
Dama asalina me surutu da kazar kazar ce rayuwa ne ya maida ni miskilar karfi da yaji, kallonta
nayi nace âyanzu dâan wannan yaron ne doctor kina nufin ya kammala doctoring degree
dâinshi?â Zarah ta taâbe baki kan tace âkwarai kuwa ke abunki da wadda be yi karatu a nigeria
ba firrrrrr ya tafi ba wani delay balle strike duk degrees dâinshi a kasar waje yayi kuma daban
dabanâ
Jinjina kai nayi don son kawar da magananshi na ce âToh yaushe zaki fara koyamin karatun?â
Tace âduk sadda muke da interval tsakanin lectures se mu dingayi ko In mun gama da wuri
kuma bamu da wani se mu dâan yi kan mu tafiâ wannan karon murmushin da na mata tun daga
cikin zuciyata ya fito, wara brown eyes dâinta kadâan tayi kan itama ta saki murmushi tace âwow I
like your dimple and your wushiryaâ na kuma yin murmushi nace ânice meeting yhu zarahâ.
Tace âsame hereâ hira ta ci gaba damin ni kam se nodding da dâan murmushi tunda na shiga 18
zan iya rantsewa ban taâba mintuna biyu ba tare da damuwa ko tunani ba amma gashi yau
samun mutum a kusa dani kuma me faran faran ya sani sakewa da ita sossai har na manta da
damuwana na wani lokaci.
Eleven nayi muka shiga another lectures na chemistry sossai na maida hankali kuma ba laifi na
fahimta don ni dâin ba laifi me dâan kwakwalwa ce.
Karfe dâaya muka fito muna fitowa zarah ta kalleni tace âhar anzo dâaukana muje mu sauke ki a
gida ko Ina Gandun albasa kike kikace?â Kai na gyadâa mata Ina dâan murmushi nace ânop ke
kam yi wucewarki, se in mun hadâu gobeâ na san irin gulman mutane yanzu a fara radâe radâen
na fara bin maza ana saukeni a manyan cars dama yanzu ma ban tsira ba.
Ba yadda zarah batayi ba amma naki haka ta tafi ni kuma na ci gaba da takawa a hankali sbd
kafana da ya dâan suntuma zuwa lokacin, ban wani âbata lokaci ba na tare napep na shige tare
da fadâa mishi inda zani.
Bayan mun iso na sallameshi na fara takawa cikin taka tsantsan kaina a kasa kaman kullum
daga gefe majilisan âyan unguwa ne na samari gaba kadâan kan gidanmu na tsoffi.
Kullum In har zan bi ta wurin na wuce se na zub da kwalla dayake mutuwar aurena har biyu a
unguwan na Gandun albasa ne, âka ganta nan ashawon, ta fito yawon karuwanci da sunan
makarantaâ runtse ido nayi Ina jin zafin sunan amma daga yanzu nayi alqawarin bazan kara yi
musu kuka ba.
Ina jin wani daga ciki yace âwai itace me aure auren?â Wani yace âkwarai kuwa aurenta na farko
sako ta akayi a daren farko sbd bata kai budurcinta baâ da sassarfa na karasa wucewa dukda
zafin da kafana ke yi, haka zuciyata kaman an saka a tukuban tsire.
Ina isa wurin manyan mutanen na duka har kasa na gaidasu suka amsa ba yabo ba fallasa
amma nayi musu farin sani na san ina bada baya zaâa dasa maganata dukda ba koyaushe
sukeyi yadda zanji ba amma sun hana âyaâyansu kap huldâa dani wai zan âbata su.
Ina shiga gida hawayen da nake rikewa ya fara gangara umma ta na tsaye jikin igiya tana
shanya baba zaune a kan taburma kasan bishiyar umbrella (almond) yana shan iska don ya
dena fita majalisa sbd habaice habaice da bakar maganganun da ake yaâba mishi gashi ya ci
alwashin baze taâba chanza wani unguwan ba sbd ni, rijiyar lemo da Gadon kaya sun isa.
âUmma barka da gidaâ da âyauwaâ kawai ta amsa ni ba tare da ta ko kalle ni ba, girgiza kai nayi
inajin hawayena na karuwa na rasa dalilin kasa sabawa da wannan hali na ummana a
shekaruna na 23 a duniya.
Har kasa na duka gefen taburman baba nace âsannu baba Ina yini?â Kau da kaina nayi daga
kallon banzan da yake watsa min Ina jin yadda ya ja dogon tsaki, gwiwa a sage na mike na
karasa kofan mama nayi sallama daga ciki ta amsa ni tana cewa âlale lale âyar albarka barka da
dawowaâ murmushin yake nayi na karasa parlorn na zauna.
Ikhram da ikhlas dake zaune saman kujera suka ce âsannu da dawowa yaya imanâ nace
âyauwaâ mama ce ta fito tana kallona tace ânaga kaman duk kin gaji tashi kije kiyi wanka ki zo
ga abinci nan kizo kiciâ wani yaken nayi Ina mikewa nace âToh mama na godeâ taku dâaya biyu
nayi naji ta saki salati tsayawa nayi na san sbd kafana ne itace kadâai!!
Itace kadâai a duniyata da zata ganni da damuwa ta magance min, ita ce kadâai me sona nan
duniya haka nima Ina sonta har raina sbd son da take min ban damu da kasancewarta kishiyar
uwata ba âna shiga uku Iman me ya samu kafankin?â Na juyo Ina murmushi nace âmama
bugewa nayiâ tace âashsha zo mugaâ wurinta na koma tana gani ta waro ido âmaza juya mu fice
gidan malam iro ya gyara miki daga gani gurdâewa ce ko tsagewar kashiâ.
Baki na turo Ina shirin mata musu har ta shige dâaki tana fitowa ta sani a gaba muka fice zuwa
tsakar gida ta kalli baba tace âmalam yarinyarnan Noor Iman ta samu matsala a kafanta bari
muje gidan malam iro ya duba mataâ bata jira cewar shi ba muka wuce don ta tabbatar ba amsa
ze bata ba inde akan maganan da ya shafeni ne kaman yadda nima na san da hakan.
Muna isa ya tabbatar da gocewar kashi ne a rike ni ya gyara da kuka da komai aka gyara mama
se mita take wai na cika ragwanci, biyanshi tayi muka fito muka dawo gida ina share hawaye,
wanka nayi na shirya cikin riga marar nauyi duk a dâakin mama komai na yake don ban ci
darajar a bani dâaki na ni kadâai kaman sauran âyan matan gidan da yanzu suke gidan
mazajensu ba.
Ido na a lumshe nake taryo rayuwarmu na baya, Malam Musa Muhammad dâan asalin kauyen
wudil ne na nan jahar kano yana da mata dâaya da yara takwas ya jima yana sanaâan driver
kuma har Allah ya karâbi rayuwanshi sanaâanshi kenan, da Sanaâan ya sayi gida anan hayin
rigasa suka dawo nan da zama anan cikin kano gabadâaya yaranshi sukayi karatu
kasancewarshi me son boko, dukda shi be yi ba, baba shine na hudâu a cikin âyaâyanshi yana da
kanne hudâu.
Goggo Kamila, goggo saratu, goggo hindatu, se bappa Audu.
Yayyunshi uku duk maza ne bappa Yusheâu, se bappa Muâazu se bappa samaâila kan baba, duk
mazan sunyi karatu daidai gwargwado iyawar mahaifinsu kan rasuwarshi inda babana yayi
diploma dâinshi a fannin mass com, ya auri ummana (Aisha) ne a chan garin malumfashi na nan
katsina inda ta kasance âya dâaya tilo a wurin iyayenta batayi wani karatun kirki ba iyayenta suka
cireta suka aurar da ita.
A lokacin ya fara aiki a matsayin karamin maâaikaci a gidan rediyon freedom, suna son junansu
don zaman amana da soyayya sukeyi wadda jigonshi ya kasance hakuri, har ummana ta
shekara hudâu bata taâba koda âBatan wata ba, hakan yasa su goggonina da inna mahaifiyar
baba suka matsa ya karo aure yaki sam amma se suka fi karfinshi inda ya auri kanwar matar
bappa yusheâu.
í ˝íś¤Gureenjoí ˝íś¤
í žíľNOOR IMANí žíľ
*Fatima Muhammad Gurin*
        â˘Gureenjo on wattpadâ˘
*'yar mutan Adamawa*
í ˝í˛ŤANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
           *03*
Hadiza wato mama kenan, zuwan mama da kwanaki kad'an ciki ya bayyana a jikin ummana
sossai baba ya d'auki son duniya ya d'aura akan cikin, su inna kam da suka ji labari se kunyan
yadda suka dinga mata ya baibayesu suka dawo suna son cikin suma kaman su janyo ran
haihuwanshi.
Kwarai umma ta wahala a wurin haihuwa na har Allah ya sa ta sauka lafiya inda ta sameni ba
karamin farin ciki su inna da baba sukayi da hakan ba, har mama kaman zata had'iyeni zan iya
cewa son da take min yafi na ummana a ganina fa kenan, aka saka min sunan inna "saudah"
yayinda mama ta saka min inkiya "Noor Iman" shekaruna biyu a duniya ummana ta kara
haihuwa nan ma mace "hafsa" sunan mahaifiyarta ce bata yarda kuma a boye mata suna ba.
Bayan hafsy da shekaru biyu ta haifi Nafeesah daga ita da shekaru biyu ta samu Al'amin se
Ihlam yayinda ikhlas ta kasance auta, har rana yi ta yau mama bata samu haihuwa ba kuma