Showing 1 words to 2937 words out of 2937 words
Chapter 1 - GAMUWAR KOSAU DA JIMRAU DA NOMAU Na Abubakar Imam.pdf
GAMUWAR KOSAU DA JIMRAU DA NOMAU
Cigaban labarin sarkin Noma da 'ya'yansa III
Littafi: Magana Jarice 2
Mawallafi: Margayi Alhaji Abubakar Imam
Ranar daya ga watan Sallah Babba, watau ran da Sarkin Noma yace wa ’ya’yan nan nasa su
komo gida, sai su duka ga su sun taru a magama hudu da suka yi alkawari. Jimrau ya fara
zuwa, ya sauke kayan jakunansa a wata inuwa, ya yi musu tabaibayi suna kiwo, shi kuwa ya
sami wuri ya hakince bisa wundi.
Yana nan zaune sai ya hango wani tafe yana cin ingarma. Da ya matsa. sai ya ga ashe Kosau
ne, ya kama masa ya sauka, suka zauna suna gaisawa. Ga mutanen gari suna kallo, sun qi
shiga don sun yi alkawari in da rai duk su taru tukuna sa’an nan su shiga.
Suna nan sai suka hango wani tafe, daga shi sai lage, ga wata umara ya sa6o yana tafe yana
waqe-waqe. Da ya matso sai suka ga ashe kanensu ne Nomau. Ya zo ya zauna, suka gaisa da
’yan’uwansa. Jimrau ya dube shi, ya ce, “An yi maka fashi ne a hanya?”
Nomau ya ce, “Fashi? Ni ba wanda ya yi mini fashi. Me ka gani?”
Jimrau ya ce, “Ba kome.” Ya bude kayansa ya dauko ’yar madaka, aikin nan har ga shafi, ya ba
shi ya ce ya sa su shiga gari.
Nomau ya ce, “Ai! Ni ka raina abin da na samu ne? To, mu tafi, ni ban raina ba, na gode Allah.
Dauki rigarka, ni abin da na samo ya ishe ni.” Ya dauki rigarsa ya mayar kyankyandi. Suka
shirya suka shiga gari gaba daya yadda suka fita.
Da ma ran nan ubansu ya sa an share gidansa, an yi abinci, don yana tsammani lalle ko ba su
dawo duka ba, wani daga cikinsu ya dawo. Yana nan zaune, yana duban hanya. Can sai ga su
gaba daya. Sarkin noma ya tashi ya rasa inda zai sa kansa don murna. Aka yi ta kinkimar kayan
Jimrau ana shiga da su. Aka kama wa Kosau ya sauka. Yara suka shiga gida, kowa ya tarad da
uwarsa, suka yi ta murna.
Da aka qare murna, mutane suka tsagaita da zuwa, sai Sarkin Noma ya kira su a turaka, yana
tambayarsu labarin yadda kowa ya yi da sana’ar da ya bi. Aka fara kan Jimrau, don shi ne
babba. Ya kwashe labarin dan yaron nan da ya yi wa bauta, da labarin kyanwar da ya ba shi,
da abin da ya gudana tsakaninsa da dodanniya duk ya fada wa ubansa da ’yan’uwansa. Suka yi
ta tu’ajjibi.
Da gari ya waye kuma Sarkin Noma ya sake tara su, Kosau ya ba da labarin abin da ya auku
tsakaninsa da Sarkin Noma, da yadda ya zabi sa’ar da Malam Lamiri ya ba shi, har ya zo ya
sami Maikoma, dan sun nan da ’yan’uwansa suka bubbuge suka sa cikin akwati suka kai cikin
kogon kuka. Ya kuma ba da labarin yadda Maikoma ya taimake shi aljana ta ba shi zobe. Ya
bayyana musu amfanin zoben nan duka. Nan da nan, don ya gwada musu abin da ya ce
gaskiya ne, ya dubi ubansa ya ce, “Me ka ke so, Baba, nan duniya duka yanzu ka gan shi.”
Sarkin noma ya ce, “Ina son nama soyayye.” Kosau ya dubi Jimrau ya ce, “Kai me ka ke so?”
Jimrau ya ce, “Kujerar zinariya.”
Ya ce wa Nomau, “Kai fa?” Nomau ya ce, “Layar zana.”
Sarkin noma ya harare shi, ya ce, “Kai, kowa na tambayar abin kirki, kai sai ka ce wani abu wai
layar zana? Sata za ka yi?”
Nomau ya ee, “Sai dai kada a kara. Na ce ko abin da ke ran kowa ya fadi? To, ni abin da ke
raina ke nan.” Sarkin noma bai gane ba, ya kyale.
Kosau ya murza zobensa, sai suka ga aljani ya zo gabansa ya tsaya, ya ce, “Allah ya ba ka
nasara, fadi naka, aikatawa tamu.”
Kosau ya ce, “Ina so yanzu ka kawo mana nama soyayye da kujerar zinariya in tana
samuwa, da layar zana. Kana da ita?”
Aljanni ya ce, “An gama, ba abin da ba na iya kawo maka, sai abin da babu shi a duniya.” Sai
ya bace. Sarkin Noma ya bude ido suna tsammani dabo Kosau ya koyo, ba kome ba. Suna
nan sai ga aljani ya dawo da dukan abin nan da aka aike shi. Nomau ya sa hannu ya dauki laya
ya sa aljihu.
Ko da Jimrau ya kware kujerar zinariyan nan, sai suka ga wuri ya haske. Suka kewaye ta suna
al’ajibi. Kosau ya ce wa Jimrau, “Ga ta, in kana iya zama kanta.”
Jimrau ya ce, “Don Allah rufa mini asiri, kada ka sa a yanka ni. Ai ko Sarkin Sirika, wanda
Alhaji Imam ya ba da labarinsa cikin Ruwan Bagaja, ba ya kwanta a wannan kujera ba.” Jimrau
ya sa aljani ya dauke ta bakinsa qanen kafarsa ya mayar. Sarkin Noma ya sa hannu suka ci
abinci da ’ya’yansa, suka watse.
Kashegari kuma suka sake taruwa, Sarkin Noma ya dubi Nomau, ya ce, “in ta bi daga daga na
qurya ka sha kashi. Dan autana, kai wace sana’a ka bi? Ban ga alamar ka zo da kome ba.”
Nomau ya ce, “Ni ko gani na ke tafiyata duk ta fi tasu sa’a, sai dai ni abin da na samo ya sha
bâmban da nasu. Wannan ko ba kome ba ne, da ma an ce kowa da kiwon da ya karbe shi,
makwabcin mai akuya ya sayi kura.”
Sarkin noma ya ce, “Hakanan ne, kai ko wace sana’a ka yi?
Kuma me ka samo?”
Nomau ya ce, “Ni sana’ar da na koyo ba cinikin raggo ba ce.
Ni ilmi na koyo da wayo.”
Sarkin Noma ya dafa kansa, ya ce, “Hakika ka koyo babban abu. Wane fanni ka dauka na
ilmi? Furu’a ka koyo, ko Tasrifi, ko Lugga, ko Nahawu?”
Nomau ya ce, "Kada in wahal da kai, baba, ni ban koyo daya daga cikin wadannan fannoni ba.
Ni, sata na koyo. Na ko sami nasara har an nada ni Sarkin Barayi.”
Sarkin Noma ya ce, “Sata!! Wa iyazu billahi! Allah ya kiyashe mu da wannan sana’a da ka koyo.
Wane 6atan basira ya kai ka wannan aiki?”
Nomau ya ce, “Ina laifina cikin wannan abu? Ka yarda mana kowa ya bi sana’ar da ya ke so. To,
ni ko sata na ga ta fi riba, shi ya sa na dauke ta.” Ya kwaşhe abin da ya faru duka tsakaninsa da
barayin ya fadi.
Sauran ’yan uwansa suka yı ta yi masa shewa, suna cewa ba su sake zama da shi. Uban ya cc,
“Lalle kuna da gaskiya. In ka ga mai arziki na zama gida da barawo, ai ka san ana zaman
karya, bakauye ya zo birni ya tambayi masussuka an ce babu.”
’Yan’uwan suka ce sai a kore shi, ko kuwa uban ya gaya wa Sarki a daure shi. Sarkin Noma ya
ce, “To, yaya za a yi haka, mutum ya soki cikinsa ya yi kirari?” Ya dubi Nomau, ya yi salati, ya
ce, “Ka dai zama mana dungu, a bar ka ana kyamarka, a yanke ba a samun sabo.”
Nomau ya ce, “A’a, baba! Na ga za ka kai ga yi mini baki, ka sa in lalace ba da alhakina ba.
Yadda ka sawa kowa albarka nima sai ka sa mini, don sa’ad da za mu rabu ba ka ce mana ban
da sata ba, cewa ka yi sana’ar da mutum ya ke so ya bi.”
Sarkin Noma ya rasa ta cewa. Ya yafe wa Nomau, suka zauna hakanan da shi kan dole.
’Yan’uwan sai dariyarsu su keyi, suna zunde, ko ina ya ratsa suna cewa,. “Ko can ma in ka
bibiya shege ne, ba dan’uwammu ba ne.”
Ana nan, ran nan sai Jimrau ya ga wata 'yar Sarkin gari ya ko makale wa uban ba wadda ya ke
so sai ita. Abinka da ’yan uwa, ashe kuma Kosau ya gan ta, shi kuma ya nace wa uban sai a
nema masa ita, kome aka ce ya yi dominta. Da Nomau bai sa baki ba, sai ya ce a ransa, Ya
kamata ni ma in sa hancina wurin neman yarinyan nan. Na san halin ’yan uba, in sun ga na
kyale sai su mai da ni talaka, wai don ba ni da wuri ne.” Sai ya ce wa Sarkin Noma lalle shi ma
ita za a nema masa.
Da Sarkin Noma ya ji maganar Nomau sai ya ce, “Ai, mai rai ba ya rasa motsi. ln ba haka ba, ka
ji ’yan uwanka masu kudi na tsoron zuwa yin magana, balle kai mai taqama da sata? Sai ka ce
Akware!”
Nomau ya ce, “Tun da dai kai ka haife ni, ba shege ne ni ba, in ji yadda ka aikatawa saura
lalle ka aikata mini.” Yara fa gaba daya suka tasar wa uban lalle sai ya nema musu ’yar
Sarkin gari.
Sarkin Noma ya ce, “Wadansunku sai su dangana abarwa guda, in yi kasada in tafi in yi masa
magana.” Yara kowa ya tsaya shi dai ba ya iya kyalewa, sai fa karfinsa ya kare dole. Suka
tilasta wa uban dai, har ya tafi ga Sarki ya fadi sakonsu gaba daya. Sarki zai sa a lallasa
Sarkin Noma don wannan rashin hankali da ya yi, Waziri ya ce “Allah ya ba ka nasara, wanda
ya ce yana son gama zumunci da kai ai ba makiyinka ba ne. Mutane kuma sun ce, “In kiji
makaho ya ce mu yi wasan jefe-jefe ya taka dutse.”
Sarki ya ce “Wannan jawabi naka mai yiwuwa ne, Waziri?
Amma me kaga ya fı muyi?
Waziri ya ce, “Sai a tambaye shi abin da ko wanne daga cikin ’ya'yan nan nasa ya taka da ya yi
wannan magana, domin lalle ruwa ba ya tsami banza. In an sami abin da kowa ya ke takama da
shi, sai a jarraba shi ta hanyar da abin da aka san ba ya yiwuwa. Ka ga da dai dai sai a yi musu
kora da hali wadda ta fi kora da kara.” Sarki ya ce, “Wannan magana taka ba ja.” Yasa baki ya
kira Sarkin tsoma (domin da Waziri zai yi magana ya kori mutane ne). Da Sarkin Noma ya
shigo, Sarki ya tambaye shi abin da ’ya ’yansa suka taka, da suka kasa neman daidai da
su sai suka tinkari ’yarsa su yi kasayya.
Sarkin Noma ya ce, “Ba abin da babban ya taka sai kudi. Ka ji an ce yaro da gari abokin tafiyar
manya. Ma bi masa kuwa duniyan nan kome aka sa shi yana iya yinsa. Karamin kuwa Allah ya
ba ka nasara, ka yi mini gafara, da ya je yawon duniya sata ya koyo, har Sarkin Barayi ya ci don
shahara.
Waziri ya ce, “Ba ka ji ba, yanzu, Allah ya ba ka nasara, ai ka ga sai a yanka wa kowa sadakin
da zai iya ta hanyar gwanintarsa.
Sarki ya ce, ‘Wannan batu farilla, Waziri.” Ya dubi Sarkin Noma yana dan murmushi, ya ce,
"Jeka, gaya wa babban dan nan naka sadakin ’yata jaka goma ne, ya kawo maza a yi shirin
aure.” Sarkin Noma ya ruga ya gaya wa Jimrau. Ba a tashi daga fadanci ba sai ga su ya aiko
Sarkin Noma ya kawo ya ba Waziri, Waziri ya ba Sarki.
Sarki ya dubi Waziri, ya ce, “A’a! Waziri, ga shi sun kawo, yaya ke nan?”
Waziri ya ce, “Allah ya ba ka nasara, talakan da ya ba da sadakin jaka goma ai ba a kiransa
talaka. Wannan fa ai a yi da shi. Da ma ba a ce ’ya’yan Sarki ba su auren tajirai ba. Saura abin
da za a yi sai a sa wa sauran abin da ba shi yiwuwa, don hankalimmu ya koma ga wannan shi
kadai. Da mun sani ma, da jaka ashirin muka sa sadakin ’yarka.”
Sarki ya ce, ” Kai dai kuma yi shiru.” Ya dubi Sarkin Noma, ya ce, “Ka je ka gaya wa ma bi
wa wannan, wanda ya ce kome aka sa shi ya yi, kafin gobe war haka ya gina mini gida mai
tsawo taki metan, fadi taki dari, tsawon katangar ya zama ta wuce hangen ko wane mai
ingarma. Ya gama zauruka goma sha biyu wadanda za a wuce kafin a kai cikin gidan. A ciki
kuma ya gina dakuna hudu, ‘turakata guda, duk kuwa dakuna da zaurukan nan a yi musu
daurin guga. A cika su kuma da katifu, da kilisai, da dangogin kayan qawa iri iri.”
Sarkin Noma ya yi kasake, don ya ji abin kamar ba shi yiwuwa. Ya sallami Sarki dai, ya tashi ya
tafi ya tarad da kosau, ya gaya masa abin nan da ya faru duka. hosau ya ce, “Ba kome, Allah
ya gyara.” Ya murza zobensa, nan da nan aljani ya fito, ya nuna masa inda Sarki ya ce a
gina gida kafin safe, da irin fasalin da ya ce yana so duka. Ya tambayi aljanin in ya iya
taimakonsa, don Sarki ya yi alkawari wannan shi ne zaı zama sadakin ’yarsa da ya ke so.
Aljani ya ce, ‘Wannan har wani aiki ne? Tun da ka mulki zoben nan, ka tabbata rai
kadai ne ba ka da ikon sa ni in hura.”
Sai ya bace
Sarki kuwa na can da Wazirinsa, suna dariya suna cewa, "Ka ga wannan shi mun rabu da
shi!” Da lokacin tashi fadanci ya yi, suka watse.
Ko da gari ya waye Sarki ya farka ya leqa ta taga, sai ga gidan gingirin kamar daga sama. Bai
ko tsaya wanke ido ba, sai ya tashi ya nufi can, ya shiga ya yi ta yawo ciki yana ta
kakabi. Gidan dai ga shi na kasa ne, amma sai ka ce na siminti ne. Zaurukan nan ko wanne ya
shiga sai ya tarad da karaga da shimfidu da kayan qawa iri iri, in ya wuce su sai ya isa
barga ya tarar da dawaki ’yan Azbin firda-firda suna harbin iska. Da ya shiga turakar
gidan, kallo ya yi kai. Ga barori da kuyangi sai kai da kawowa su ke ciki. Ko wane dakin
kwana ya shiga in ya ga gadaje da kilisai da katifu da shinfidu iri iri sai ya yi tsammani ya fi na
baya da ya fito kyau. Kayan da ya gani a wannan daki kuwa, in ya shiga mai bi masa ba su
zai tarar ba. Kai, wani al’amarin ya fi gaban a bayyana. Da yaga haka, ya aika Waziri ya
zo ya taya shi kakabi.
Suna nan sun kasa fitowa don sha’awa, sai ga Sarkin Noma ya shiga. Ya durkusa ya gaida
Sarki, ya ce, “Ga gidan nan ya ce a gaya maka an gama. Ya yi yadda ka ke so?”
Sarki sai tafa hannu kawai, Waziri ya ce wa Sarkin Noma, “Je ka, ka ce masa ya qayatad da mu
ainun.” Sarkin Noma ya fita.
Sarki ya ce wa Waziri, “To, qaqa tsara qaqa, yanzu kuma me za mu yi? Wannan dai lalle yana
sha’ani da rauhanai ne.”
Waziri ya ce, “Ai ba sai an fadi ba. Abin da ya fi yanzu sai mu ba autansu nasa abin da zai yi na
wajen sana’arsa ta sata, don ya kasa, mu debe shi mu san da wadannan mu ke yi. Don fa ko
kura ta tsufa ai ta san ta fi qarfin kare ya zangure ta. Haka kuma ko ’yarmu ta lalace ta fi gaban
a aura wa Sarkin Barayi.”
Sarki ya ce, “Haba, a ma fara? Allah ya sawwaqe. In Allah ya kai mu gobe muna rayayyu, sai
in aika Sarkin Noma ya zo tare da autan nan nasa Sarkin 6arayi, mu ga abin da ya ke qobobo
da shi.”
Waziri ya ce, “Allah ya daukake ka, hakanan ne. Yau cikin dare sai mu tuna abubuwa masu
wuya wadanda za mu ba shi ya sata.” Ya durkusa, ya ce wa Sarki, “Na bar ka lafiya.” Ya nufi
gidansa.
Zamuci gaba JARABAWAR DA AKAYIWA SARKIN BARAYI NOMAU