Showing 1 words to 2409 words out of 2409 words

Chapter 1 - LABARIN SARKIN NOMA DA 'YA'YANSA, magana Gari ce .pdf

LABARIN SARKIN NOMA DA 'YA'YANSA

Littafi: MAGANA JARICE 2
Mawallafi: ABUBAKAR IMAM

A cikin lokacin jahiliyya akwai wani manomi wai shi Dan’ani, yana da ’ya’ya uku maza. Babban
ana ce masa Jimrau, mai bi masa Kosau, dan karamin kuwa Nomau. Da suka isa mutane sai
ya tara su, ya ce, “Yanzu ni kun ga na tsufa, saboda haka na yarda muku kowa ya shiga
duniya ya kama sana’ar da ya ga za ta fisshe shi. Yau kun ga daya ga watan Salla Babba, na
sallame ku. Badi kuma daya ga wannan wata, in Allah ya sa muna numfashi, ina so duk ku taru
nan, mu ga abin da sana’ar kowa ta ba shi. Na gafarta muku duniya da lahira. Allah kuwa ya
gama fuskokimmu da alheri.”

Yara suka je suka roki gafara ga uwayensu, suka fita, ba su san inda za su ba. Suna fita kofar
gari, sai suka kai ga wata magama hudu nan kofar garin. Wata hanya ta nufi .gabas, wata ta
nufi arewa, wata ta nufi kudu, ta yamma kuwa ita ce wadda su ke bisa, watau mai shiga gari.

Da suka isa wurin, sai Jimrau ya ce wa kannensa, “Mu tsaya nan, kowa ya kama hanyarsa . In
ranan nan kuma ta kewayo badi, in da rai, ko ina mutum ya ke ya yi kokari walima ta yi masa
nan, mu koma ga baba gaba daya yadda muka fito.”

Saura suka ce, “Allah dai ya ba mu rai da lafiya!” Suka yi sallama da juna suka rabu, ko wanne
na hawaye.

Nomau ya kama hanyar da ta nufi arewa. Kwanci tashi , yana cikin tafiya sai
shawarce-shawarce ya ke yi, bai san sana’ar da zai fada ba. Ya yi shawarar noma, ya ga in
don noma da bai tsaya gida ya yi ba? Ya watsad da wannan. Ya yi shawarar saka, ya ga
ba ya iya jure wa taurin gindi. Ya ce kida, ya ga ba ya iya haushi. Ya ce jaura, ya ga ba ya
iya kwana layi. Kai , ko wace sana’a ya kawo a ransa in ya ga wani abin da ya yi mata cikas
sai ya watsar, ya gaji ya ce, “Kai, duk sana’ar da ta fara taron gabana, ita zan kama.”

Yana cikin tafiya, ya kai tsakiyar dajin nan, sai ya ga hadari ya kama ka’in da na’in, ya rasa inda
zai shiga ya fake. Yana ’yan dube-dube ko ya sami wani dan kogo, sai ya ga wata ’yar
hanya, ya bita yana cewa, “In ka ga hanya dai, in ba ta kai gida ba, ta kai rafi.”

Yana cikin tafiya, can gabannin tasowar ruwa sai ya kai wani dan gida shi kadai kwal cikin daji.
Ya isa, ya yi sallama, sai wata tsohuwa ta fito, ta ce masa, “Kai samari, makuwa ka yi? Hala ba
ka San İnda ka zo ba ne. Nan gidan barayi ne. Kama gabanka tun da girma da arziki, kafin su
dawo.”
Nomau ya ce, “In kama gabana in je ina cikin wannan ruwa? Da in tafi wani naman daji ya
cimye ni a banza, ai gwamma in tsaya nan ’yan’uwana mutane su kashe ni. Ko ba kome, in sun
kashe ni lalle sa rufe ni, ko don kada in yi musu wari.”

Tsohuwa ta ce, “To, ga zaure nan, zauna.” Nomau ya shiga zaure ya harde. Yana nari zaune
jim, sai ya ji tim tim tim, barayin nan sun dawo. Ga su katta su goma sha hudu ribda-ribda. Da
suka gan shi sai babban ya ce, “Kai samari, daga ina?” Zai amsa musu, tsohuwa ta tsattsare ta
gaya musu abin da ta gaya masa da isowarsa, da kuma shi abin da ya ce. Suka sake
tambayarsa dalilin zuwansa nan, ya kwashe duk ya gaya musu, har da yadda hanya ta kawo
shi nan.

Babban ya ce, “Tun da ya ke haka ne, ba mu cutarka. Gobe sai mu sa ka hanya ka yi gaba.”

Nomau ya ce, “In dai ba kun ki yarda da ni ba, nan na ke so in zauna tare da ku. Da ma na ce
sana’ar da na fara samu, ita zan bi. Tun da ko sata ta fara bayyana gare ni, ita zan yi. Da ma
baba ya ce kome mu ka so mu yi.”

Barayi suka ce, “Ka iya sata? Bafa sana’ar raggo ba ce, ba ko ta ’ya ’yan kirki ba ce, ba ta
kuma masu tausayi da jinqai bu ce, ba ko ta masu gudun azaba ba ce. Sana’a ce ta taba6bu
wadânda Shaidan ya mallaki zuciyarsu. In kana iyawa, to, kome ya faru gare ka duniya da
lahira kada ka yi kuka da dayammu.”
Nomau ya ce ai ubansa ya ce ko wace sana’a ya ke so ya yi. barayi suka dauke shi kamar
yaronsu. Ko yaushe inda za suyi sata duk sai su je da shi. Sannu sannu har shi ma ya zama
gwani. Suna nan, ka san sata ba ciniki ba ne, ran nan sai rana ta baci wa Sarkinsu, ya taryi
wani Buzu wanda ya fi shi karfi, wai shi yana takama ba abin da ke sonsa.
Buzu ya zare wuka ya daka wa Sarkin Barayi, wuka ta karye uku. Sarkin barayi ya zaburam
masa, Buzu ya zare takobi ya cira zai dauke kansa, ruwan takobi ya fadi can gefe daya
kyangyaran.

Da Buzu ya ga ya yi amfani da makaman da ke gare shi, duka ba wanda ya yi, sai ya ce, “Hi
namiji, galla in ka ci maganin karfe, ka ci na karfi ne?” Sai ya tube, suka rifta da kokawa. Buzu
ya fi Sarkin 6arayi karfi fat. Ya dauke shi ya yi koli-koli da shi, ya buga Qasa ya haye, ya take
hannuwan, ya kama kan kafiri ya murde, ya wuce ya bar shi nan matacce.
Da ’yan’uwan suka komo ma6oyarsu, suka yi jiran Sarki ba su ga ya dawo ba, sai suka bi sau.
Suna zuwa sai suka tarad da shi kwance matacce. Suka kinkima suka kai gida suka binne,
suna cewa, “Yau rana ta haci wa ’yam maza.” Ba wanda ya sake ko tuna shi, balle ya yi masa
kuka. Da ma duk taron sakarai ne kira mini shashasha, in ka ga barkatai ku taho tare.
Ko da gari ya waye sai suka shiga shawarar wanda za su wa sabon Sarki. Kowa ya ce shi za a
ba. Daga nan sai tsohuwan nan ta ce, “Ai wannan ba abin zafi ciki. Sai ku fita, duk mai jin kansa
ku sami wani abu ku gwada. Wanda aka ga dabararsa ta cancanta a ba shi, a ba shi.”

Barayin suka ce, “I, ai ko kina da gaskiya.” Suka yi shiri kamar wadansu mutanen kirki,
suka fita suka nufi gari. Suka je bakin kasuwa suka zauna. Suna nan zaune, sai ga wani mutum
ya fito da jakar kudi a hannu ya nufi gidansa. Babbansu ya dubi ’yan’uwansa, ya ce, “Wanda

duk ya sace jakar kudin nan yanzu da rana, ba da ya ko kashe mutumin nan ba, kun san ya
isa a yi masa Sarkin Barayi?”

Wani nan ciki ya ce, “Wannan ai ba ko ja. Ban da aljanni wa zai iya raba mutumin nan da
jakan nan yanzu da rana qiri-qiri?” Ya dubi saura ya ce, “Ko kuwa da magagaci?"

Saura suka ce, “Don dai taqamar sai da rai, mutum zai sa kansa a wahaia haka a
banza?”

Nomau ya ce, “Ni zan yi kokari. Da rashin tayi a kan bar araha.” Ya tashi ya bi mutumin tinkis
tinkis har gida. Ya sami wuri ya make, yana kallon mutumin nan.

Ko da mutumin ya kai kofar ‹bakinsa, sai ya ajiye jaka daga waje cus, ya ce wa matar ta kai
masa ruwa bayan daki zai ta6a. Ta debi ruwa ta bi shi da shi bayan daki. Sai Nomau ya zo nan
da nan ya sure jaka ya gudu. Ya kai wa ’yan’uwansa, ya ce, “Ga ta, da ma wuyar wuri ba
mu zo ba.” Yagaya musu yadda ya yi duka.
Barayi suka dubi jaka, suka yi ta al’ajibi. Daga nan sai wani mai tsananin hassada a cikinsu
ya ce, “Af, wannan ai ba ka yi kome ba, domin yanzu matar na can zai yi ta dukanta ya ce ita
ta dauke. in dai ka yi dabarar da ka ku6utad da matan nan daga zargi, sa’an nan kuma ka dawo
da jakar, ba ja kai ne Sarkimmu.”
Saura suka ce, “Gaskiya ne, gaskiya ne.”

Daga nan sai Nomau ya dauki jaka ya korna. Ya tafi har kofar zauren mutumin nan ya shiga, ya
tsaya yana saurare, sai ya ji mutumin nan na ta zagin matar, yana cewa lalle ta nuna masa inda
ta kai, in ba haka ba ko yanzu su gamu.

Da Nomau ya ji haka sai ya yi sallama, mai gida ya fito yana zage-zage. Ko da ya zo zaure,
sai ga jâkar kudi hannun Nomau. Ya bude ido yana duba, sai Nomau ya ce’ “Mutumin da ka
zauna rumfarsa a kasuwa ya aiko ni, ya ce wai in kawo maka jakan nan taka da ka manta a
rumfa. Ya ce in gaya maka ya kamata ka riqa lura da kudi, ba dukan mutane a ke amincewa
da su ba. Da sun fada mugun hannu ai da sun 6ata ke nan.”

Mutumin ya bushe da dariya, ya yi ajiyar zuciya, ya ce. “Gaskiyarsa.” Ya mika hannu zai
karba, yana cewa, “Bari in je in kawo maka tukwici.”

Sai Nomau ya ki mika masa, ya ce, “Ina fa zan ba ka, a zo a ce ban kawo ba? Ko kuwa a ce
na kwance na diba. Yanzu ba abin da ya fi sai ka shiga ka yiwo mini ’yar wasika Shaida, ka zo
ka kidaya, in sun cika ka ba ni wasikar in kai masa.”

Mai gida ya ce, “Gaskiyarka, amma ’ya’yan kirki irinku ai ba a zarginsu ga wannan. Tsaya dai
mu yi yadda ka ce.” Ya ruga gida ya dauko tawada da takarda, sai Nomau ya fice da jaka.

Ashe sauran barayin sun biyo, don su ji yadda zai yi, kada ya yi musu karyar ya je. Da suka ga
ya fito suka tare shi, suna yabonsa a kan wannan hikima. Suka nufi gidansu, suka yi masa
Sarkin Barayi.

Da mai gida ya fito bai ga Nomau ba, sai ya ruga kasuwa ya tarad da mai rumfar da ya zauna,
ya ce, “Yaron da ka aiko da jakar kudina da na manta a nan ya kai mini. Na ce ya mika mini, ya
ce ba ya ba ni sai na yi masa takardar shaida ya kawo maka. Na shiga gida dauko takarda da
tawada, na fito ban gan shi ba. Ko ya yi gajin haquri ne ya dawo?”
Mai rumfa ya ce, “Ni ban aiki kowa ya kai maka kudi ba. Wane kudi ma za a kai maka? Da
jakarka a hannu ka rabu da nan.”

Maigida ya ce, “Ni ma fa da kamar haka na gani.”

Mutanen rumfar suka ce, “ Kai, nemi taimakon aljannu, su suka sace maka kudi suna son
zauta ka! Watakila da ma kudin ba na sosai ba ne, irin wadanda aljannun ke kawo wa mutane
ne. Ka ko san irin wadannan kudi, ko ka same su sa gudu su koma ga mai su na asali.”

Mai gida ya ce, “Lalle hakanan ne.” Ya nufi gidan wani malami aka yi masa laya, don kada ya
motsu.

Suna nan, ran nan Sarkin Barayi Nomau, ya yi kamar wata goma tare da harayin nan, suka
hana mutanen karkaran nan sakat da sata. Da abin ya yi yawa, Sarki ya yi bincike ya sami
labarin inda su ke, sai ya yi shirin yaki cif, aka dakaki ma6oyarsu da dare. Dakaru suka kewaye,
aka sa wa gidan wuta. Barayi suka yiwo waje, aka bi su kama kama, aka bubbuge aka daure.
Sarkin 6arayi Nomau kuwa, da ya sami wata 'yar kafa ya 6alla da gudu, ku tara, ku tara, ya yı
musu fintinkau, wani Dogari mai kili ya sake shi ya bi shi, ya sa doki ya banke shi. Ja'irin naka
sai ya yi laya, aka nemehi qasa ko bisa, ya sulale yayi tafiyarsa yana haki, ko riga bai tsira da
ita ba, daga shi sai bante da mayafin da ya kwanta da su. Dama dami ya fadi kan kaba, lokacin
tafiyarsa gida ya yi, saboda haka ya sami ’yar sanda ya tasar wa garinsu. Ga shi nan tik ba
sutura, ba ko abin sayen tuwo a hanya. Saboda haka gogan naka sai ya riqa fizge. in ya tarad
da maciya sai ya tsaya, ya ce a sa mai abinci na taro ko na kwabo biyu. Da ya ci ya koshi sai yu
tashi ya dauki sandarsa ya sa6a, zai wuce. In mai tuwo ta tambaye shi kudi sai ya zura a guje,
ya ce, “Biyo ni ki karba!” Kama kama ya tsere. Haka ya yi ta yi har ya isa.

ZAMUCI GABA…

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login