Showing 1 words to 590 words out of 590 words
Chapter 1 - FARISATUL ANSARI littafin Yaki By Arewa Novels .pdf
FARISATUL ANSARI. page- 16
Na
Manu Fagge
Watarana na dauki littafin The Page na fita rangadi ni kadai akan ingarman doki, nayi nesa da
gari sosai, har takai ga nashiga wani surkiki me tarin bishiyu da duhuwa,kawai sai na hangi
wani zomo fari kyakkyawa, tabbas yayi mutukar birgeni, hakan yasa na sauka daga kan
ingarman dokina da nufin na samu damar kamashi, ai kuwa ya fita da gudu, nima na bishi, ya
shiga nan ya fita nan, amma bandaina bin saba, har yakai ga ya shiga wata kogon wata
katuwar bishiya, ya shige ciki, daga can nesa inda na bar dokina naji sautin haniniyar dokin ya
fita da gudu ya bazama, bansan mai ya gani ba har hankalinsa ya tashi, ya bazama da gudu,
hakan yasa na dawo hayyacina, sannan na dubi kogon bishiyar dake tsaye a gabana, anan
nagane wannan bishiyar duk ta banbanta da sauran bishiyu dake cikin wannan surkikin jeji.
Bishiyar tana dauke da suffar ban tsoro ta yarda ba zan iya siffanta taba, hakan yasa na fara ja
da baya, kawai sai naji na taka wani guri kamar tsohon kabari, kafata guda daya ta zurma ciki,
harta haifar da wata kofa, cikin tsoro na zaro kafata, daga nan kawai wata guguwa naji ta taso
daga saman bishiyar nan tana shiga cikin wannan ramin kabarin da kafata ta haifar da ramin,
iskar tana wani irin kuka na daban, hakan yasa na tsorata naja da baya na labe a bakin wata
bishiya ina kallon me yake faruwa.
Bayan iskar ta gama shigewa saiga kuma wata koriyar iska ta fara fitowa tana taruwa guri
guda, bayan ta gama taruwa iskar ta rikide ta koma siffar wani shigegen aljani mai ban tsoro
kuma mara kyan gani, gashi tsoho tukuf. Tuni na fito daga inda nake boye na zura da gudu,
kawai sai ganinsa nayi ya bayyana gabana yana kyakyata dariya sannan yace, "yaro tunda ka
tononi ka tono masifa ka tono bala'i kuma annoba ga duniya baki daya" cikin rudewa nace
"waye kai kuma me namaka"?
Ya sake bushewa da dariya yana nufoni a sukwane sannan yace, "yau shekarata sama da dubu
uku a wannan wuri, Sarkin aljanu na wancan lokacin ya daureni a wannan wajen da kayi
sanadin fitowa ta, ina daya daga cikin shaidanin aljanu da suka rubuta littafin The Page, a
wancan lokacin, naso na sace littafin na gudu dashi, dan nayi amfani da shi wajen mallakar
duniya, na mulki mutane da aljanu, amma banyi nasara ba, sarkin Aljanu, ya kamani ya daure,
a wannan waje, sannan suka sarrafa littafin ta yadda ido bai isa ya gansa ba, ko ya karanta sai
wasu kebantattun mutane, mutanen da babu wanda ya sansu a duniya, kuma daga baya littafin
ya dawo sarrafa kansa da kansa, nayi ittifakin cewa babu wanda zai iya cetoni daga wannan
azabar daurin da sarkin aljanu yamin sai daya daga cikin wadan nan mutane 'yan baiwa, ni
kuma nayi rantsuwa da wannan bishiya da aka binne ni daf da ita sai na hallaka irin wadan nan
mutane 'yan baiwa duk nisan tsayin zamani". Aljanin yayi wata mika ta gajiya, tare dayin hamma
wata wuta ta fita daga bakinsa, sannan yace, "yaro ka ceceni amma ceton mutuwarka, yi maza
ka mikon littafin The Page kafin na kona ka kazama gawa". Anan na lura shima duk da yana
cikin marubutan littafin a yadda yace, shima baya iya ganinsa, sannan yayo kaina
gadan-gadan yana huci na juya na fita da gudun ceton raina.