Showing 1 words to 987 words out of 987 words
Chapter 1 - FARISATUL ANSARI Pages littafin Yaki .pdf
FARISATUL ANSARI. Page 15
NA
MANU FAGGE
Gawurtaccen sadaukin da ke filin dagar sai dawur-dawur yake kamar zai ci babu, yana jiran mai
karar kwana. Ya fara zabgawa kansa kirari tare da sarkinsa. Cikin kirarinsa yana aibata Gimbiya
Farisatul Ansari, sannan ya ce yau a garin babu maza ko sai mata ne. Wannan furuci ya fusata
Wantaru da Mantaru. Hakan yasa Mantaru ya dira a filin daga a sukwane don fuskantar wannan
gawurtaccen sadauki.
Sadaukin ya bushe da dariya wacce sai da ta haifar da 'yar karamar guguwa sannan ya ce da
Mantaru, "Shekaru goma da suka wuce na kashe ubanka. Yau gashi zan kashe dansa. Wannan
babbar sa'a ce gare ni! Amma kai daya tilo kamin kadan, zan fi so na hada da dan uwanka, in
murkushe ku gaba daya. Yau zan yi gagarumin aiki domin Sarkina, yau ce ranar da zan zama
‘yan tacce a gare shi."
Wannan furuci ya kara fusata Wantaru, shi ma ya shigo filin daga a sukwane. Wantaru da
Mantaru suka ja tunga domin gwabzawa da wannan gabjejan sadauki. Alkalin dambe ya buga
gangar fafatawa. Wantaru da Mantaru suka yi masa dirar mikiya da fushi, da niyyar su yi masa
zuwa daya. Amma sai ya yarda al’amudin da ke hannunsa, suna zuwa suka buga tsalle kansa
da nufin fille masa kai. Amma sai suka sari kwalkwalin da ke kansa, wanda yasa takubbansu
suka karye saboda karfin sarar da suka yi da kuma karfin da kwalkwalin ke da shi.
Cikin bacin rai, basamammen jarumin sadauki ya cafke su duka biyun, ya rinka musu dukan na
fi ƙarfin ka, yana daga su sama yana mammakawa su da kasa. Ya bisu da duka har kasa. Cikin
kankanin lokaci ya galabaita su, ya hada musu jini da majina da hannu, ba tare da makami ba.
Suna kwance a kasa kamar matattu. Sadaukin ya daga kansa sama, ya fara zabgawa kansa
kirari. Yana cikin kirarinsa, Wantaru, yana kwance yana nishi, ya zaro wata karamar wuka daga
gefen banten sa, cikin azama ya daba masa a cinyar hagu, ya zare, ya kara daba masa.
Sadaukin ya yi kururuwa saboda zafin da ya ji, ya zare wukar daga jikinsa, ya wurgar, a fusace
ya dauki al'amudinsa, ya kai wa Wantaru mugun duka, amma Wantaru ya zille, alamudin ya
daki wani ginshikin gini dake wajen, sai ginin ya tarwatse, sadaukin ya sake kokarin kai masa
duka, Wantaru ya kauce, al'amudin ya makale a cikin surkukin ginin, ya kasa zaro shi, kawai sai
ya zare takobbinsa, a lokacin shima Mantaru ya mike, aka jefa musu wasu takubba daga waje,
suka cafe, suka sake kai masa farmaki da dakakkiyar. Shi ma ya nufo su cikin bacin rai.
Sanuwar fafatawa aka soma kowa yana gunji da kururuwa, kura ta turnike gurin har ba a ganin
kowa, sai dai jin karar takubba da fallatsar jini.
Wantaru da Mantaru sun yi masa munanan sara, amma duk da haka ya sake galabaitar da su,
Shima ya musu munanan sara har suka daina motsi, daga nan ya janyo kafafunsu ya daure da
sirdin dokinsa. Ya kara zabgawa kansa kirari tare da yabon Sarkinsa. A cikin kirarin ya sake
aibata Gimbiya Farisatul Ansari, tabbas hakan ya fusata ta matuka. Da ace tana da dama a
matsayinta na sarauniya da zata iya shiga gasar, da kuwa ta halaka wannan sadaukin – ganin
irin fafatawarta da na gani a Kogon Dutsen Matsafi, amma ba ta da wannan dama.
Bayan da sadaukin ya daure kafafun Wantaru da Mantaru, har ya yi niyyar tafiya, sai girman kai
da karfin sadaukantaka suka turnuke shi, ya dawo ya kara kirari, ya ce duk wanda ya isa daga
cikin mutanen Gimbiya ya fito ya wakilci Wantaru da Mantaru. Sai duk mutanen Gimbiya suka
duƙar da kawunansu kasa. Saboda babu wanda ke da ƙarfin guiwar fuskantar sa, sai dai mai
karar kwana.
Ni kuma, ganin yadda ya ci gaba da aibata Gimbiya a gaban mutanenta, sai abin ya konamin
rai. Na tuna bambancin da ke tsakanina da su: kawai tashi nayi daga inda nake zaune, na ratso
cikin dandazon jama’a na shigo filin daga. Sadaukin ya dubeni, ya bushe da dariya, ya ce: "Kai
wane ne? Daga ina kake da har kake da karfin guiwar fafatawa da ni?" Sai ya jefomin takobinsa
yace na dauka na farmake shi. Na tsugunna zan dauka, amma na kasa dagata saboda nauyin
takobbin nasa, Ya sake bushewa da dariya har da tsugunnawa. Sai na dauki takobin Mantaru
da ke yashe gefe, na ja tunga. Shi kuma yana kallona yana dariya. Ni kuma nayi amfani da
wannan dama, cikin zafin nama na debi ƙasa na watsa masa a ido. Tuni dariyarsa ta koma ihu,
yana murza idanuwansa. Kafin ya dawo hayyacinsa, na sare masa kai da takobi. Wurin ya
dauki shewa da kururuwar murna! Na daga kan sadaukin, na dubi inda Gimbiya Farisatul Ansari
ke zaune, na jinjina mata kan. Tuni alkalin wasa ya bai wa Gimbiya nasarar gasar.
Guri ya rude da sowa. Sarkin wancan garin da sadaukin ya fito ya tashi cikin kunar rai saboda
wannan mummunan rashin nasara da kuma rasa jaruminsa. Mu kuma aka rankaya da mu cikin
gari ana kade-kade da bushe-bushe don taya Gimbiya murnar wannan nasara, karo na farko da
ta samu damar yin aure ga duk wanda ta so.
Bayan mun taho, Farisatul Ansari kallona kawai take tana mamaki, da murmushi ba tare da ta
ce komai ba, har muka karasa cikin gari muka wuce fada. Daga nan kuma aka wuce da su
Wantaru da Mantaru wurin magani.
Bayan anyi bukukuwa da shagali a kofar masaraita na tsajon kwana uku, saboda murna,
sannan kowa ya kama gabansa.
Haka na share kwanaki a wannan alƙarya, duk wata matsala da ta kunno kai muna samun
nasara a kanta, ga wata soyayya mai karfi da FARISATUL ANSARI ke nunamin, ni kuma akoda
yaushe tunanina gida.
AREWA Novels