Showing 1 words to 3000 words out of 24530 words
Chapter 1 - Ba Sonta nake ba ( Tausayinta nake ) By UBEERA.pdf
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
HOME OF QUALITIES WRT ASS....
_Bisimillahi Rahamanir Rahim_
001
*KANO STATE*
_CITY STAR HOTEL_
Da sauri ta sunkuya tana mai dafe tarin takardun dasuka watse zuwa ƙasa wanda hakan yayi
dai dai da shima sanda yakai nashi hannun zuwa ƙasan cikin rashin sa'a kuma hannunsu ya
sarƙe dana juna atake anan taji wani baƙon yanayi ajikinta mai wuyar ta fassara shi.
Saɓanin shi dayay saurin ɗauke hannunsa daga saman nata gefe guda kuma yana jefa mata
kallon raini da ƙasƙanci.
Sam bata lura da hakan ba face ƙarasa tattare mai takaddun nashi datai tana sakin wani irin
lallausan murmushi.
Hannunta har yanzu rawa yake sakama kon baƙon lamarin daya faru agareta yanzu.
Seda ta kammala tattara mai sannan ta ɗago fuskarta cike da murmushi mai ƙayatarwa ta dube
shi da matsakaitan idanunta.
Wanda kallo guda tayi masa takasa cigaba da kallon nashi murya na rawa kamar zatai kuka ta
furta!
"Afuwan yallaɓai ban kula ba"
Tafaɗa tana mai janyo maganar da kyar tsintar kanta tayi dajin wata irin wawiyar faɗuwar gaba
marar misali acikin kirjinta zuciyarta kuma kamar zata fasa kirjinta ta faɗo dan tsabar rawan data
keyi.
Bai amshi takaddun ba kuma bai dena kallonta ta ƙasan idanunshi ba yarinyace wadda batafi
shekaru goma sha takwas ba sanye take cikin ɗamammun kaya waɗanda suka bayyana baiwar
kyan surar da Allah ya bata gawani dogon gashi data zubo dashi har gaba da dokin wuyanta
kallo ɗaya yayi mata yagane ainihin itan wacece. Tayi mai kama da karuwa marar aji kokuma tantiriyar ƴar iska marar aji! Abin da ya faɗi kenan
aranshi yana mai lumshe kyawawan idanunshi.
Totaly batafi sa'ar ƴar ƙaramar ƙanwarshi ba to mai yasa zata ɓata rayuwarta ta nakasa kanta.
"Yallaɓai ka amsa hannuna"
Taja maganar cikin ƙosawa.
Tana mai tsareshi da nata idanun wannan lokacin ta ɗan ƙare mai kallo kaɗan.
Ataƙaice Shiɗin dogon namijine ƙaƙƙarfa baƙi mai ɗauke da manyan idanu da yalwatacciyar
gira kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin jerin maza masu aji tare da izza da taƙama uwa
uba kuma hutu gayu da ƴaƴan banki sun sami muhalli atare dashi.
Har yanzu hannunshi na naɗe a saman kirjinshi idanunshi lumshe wanda shi kallonta yake
batare data farga da hakan ba.
"A'a ya subuhanallahi A'A yana ga baka ƙarasa ciki ba"
Maganar wani magidancin farin namiji daya karaso wajansu yanzu wanda hakan yasanya
yarinyar zube mai takaddun ajikinsa ta ƙara gaba cikin sauri tabar wajan.
Cikin sauri yarinyar take sauka ƙasa har tana haɗawa da ɗan gudu kafin ta fita compound na
hotel ɗin wata baƙar mota ta buɗe da sauri ta shiga taja murfin tana maida numfashi.
"Ke Ummul lafiya naga duk babu nutsuwa atare dake kodai...?"
Bata bar wadda ke mazaunin drivern tai magana ba tai saurin tarar numfashinta.
"Ameera ja mota mutafi yau nai gamo da ƙaddarata"
Wadda ta kira da ameerah itake mazaunin driver wadda daga gani zata girmewa ummul da
sauri tai revars haɗi da nufar gate ta fita a hotel ɗin baki ɗaya.
Titi tahau tare da kunna redion motar.
Seda suka bar arean sannan Ameera dai ta kuma juyowa ta dubi ummul ɗin haɗi da ce mata.
"Ina mukai can ko nan?"
Lumshe idanu ummul tayi tare da cewa.
"muje rufaida ki mana order babu wani target yau kam mu tara gobe insha Allahu"
Tafaɗa har yanzu kirjinta bai dena rawa ba wanda tun haɗuwarta da A'A kamar yadda taji ɗayan
ya faɗi ta tsinci kanta tare da hakan.
Gangara motar ameera tayi zuwa Rufaida fita tayi zuwa cikin wajan ta siyo musu ta dawo har
lokacin idanun ummul suna lumshe haka ameera taja motar tare da ɗaukar hanyarsu kai tsaye
hotoro ta nufa da motar tafe da ƙwarewa.
"Ameera yau naso shiga cikin gari amman hakan baze samu ba"
Tafaɗa tana mai cije lips ɗinta ameera batai magana ba sabida wayarta datai ringing ɗauka tai
tana magana cike da barikanci still idanunta yana bisa kwalta.
Hotoro tsamiyar boka dai dai rakat ameera tasha kwana layi na uku ta shiga wanda yake tsit
babu alamun jama'a awajan.
Abakin wani dogon gate ta tsaya tare da kashe motar ta ɗauki ledar data siyo musu rufaidan
tayi waje itama ummul cike da sanyi ta balle nata murfin ta fita.
Gate ɗin suka karasa ameera taja kofar ta shiga itama ummul taja ta shiga ciki wanda tundaga
farkon gidan har zuwa ciki matane zaune wasu na lido wasu na karta wasu tabar sigarice
agabansu wasu kuma shisha gefe ɗaya kuma dogayen ɗakuna ne masu layi layi kallo ɗaya
zakama gidan kasan gidane na karuwai amman na haya. Kowani ɗaki akwai number ajikinsa hakan yasa ameera nufar ɗaki mai lamba ta hamsin ta buɗe
da key suka shiga ita da ummul.
Ɗakine madaidaici domin babu tarkacen komai aciki daga gado se wadrobe na kaya se gas
karami da frij babu toilet sabida gaba ɗaya bayi yana can waje kowa da kowa shiga yake.
Ameera ta aje ledar tare da faɗawa gado tana furta.
"washh kawata yaufa naci ubana na gurzu babu karya komai na jikina ciwo yake lallai Alhaji
motar daya bani ba abanza ba"
Murmushi ummul tai kafin tayi magana wata mace kakkaura baƙa ta shigo ɗakin nasu.
"Yau akwai gayu zasu zo da daddare acikinku idan da wadda bata da M point sedai magana
domin babbar fita ce"
Ummul batai magana ba sema tashin datai zuwa gaban wadrobe tana kokarin ɗaukar zani ta
ɗaura Ameera ce ta kada baki tace.
"nikam yau naci azaba sedai ummul"
Tafaɗa tana mai kallon ummul dake tube kaya tare da zira hijab akan zanin data daura.
"Nima bana jin fita yau bana jin daɗi sam"
Murmushi matar tayi tare da cewa.
"Haba keko ina hasko alkairi atare da fitar nan taki gaskiya kiɗan daure sabida sunfi son irinku
ƴan yara shakaf sekinfi kawo light"
Tafaɗa tana mai kashe idanu irin na ƴan duniya.
Rabeta ummul tai haɗi da ɗaukar boket tabar ɗakin.
Da kallo ameera da matar suka bita.
"Rabu da ita Anty ladi lafiya lau muka fita amman duk tai wani iri kamar wadda akama sukuwa"
Ameera ta faɗa tana dariyar iskanci.
Taɓe baki anty ladi tai tare da cewa.
"Ki shawo kanta ami sabida wannan fitar mai lasisi ce ok sena jiki yadda kukai"
Tafaɗa haɗi da ficewa daga ɗakin gaba ɗaya.
Da sanyi jiki ta ƙarasa gaban famfo ruwa ta tara haɗi da nufar toilet ɗinsu dake tsakiyar
gidan..........
*AYI HAƘURI ABI LABARIN DA YADDA SALON YAZO AUTA 08142105218*
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
HOME OF QUALITIES WRT ASS....
002
Da sanyin jiki take watsa ruwan ajikinta batare data sanya sabulu ko soso ba,har ta kammala ta
ɗauro zani tare da saka hijab a samanta ta ɗauki bokitin datai wankan dashi ta fito zuwa waje.
A bakin famfo ta ɗaura alwala ta wuce ɗakinsu.
Zaune ta tarar da Ameera ta baje Shisha a gabanta tana zuƙa.
Lumshe idanu tayi haɗi da raɓewa ta isa gaban wadrobe ta ɗauki doguwar riga mai sauƙin
nauyi ta sanya ajikinta sallaya ta shinfiɗa ta soma gabatar da sallar la'asar.
Tajima tana addu'a acikin sujjadarta ta ƙarshe kafin ta ɗago tana share hawayenta haɗi da
sallama tai addu'a sosai acikin tafikan hanna yenta, ta shafa batare data zare hijabinta ba, Ta
kwanta a saman sallayar idanunta lumshe tana hasko Kamannin A'A kamar yadda taji abokinshi
ya faɗa.
Hannunta dafe da saitin zuciyarta ita kaɗai tasan mai takeji game dashi.
"Kekam lafiyan ki duk kin sauya kuma ba haka kika tashi ba ko furar rufaidar ma da kikace nayo
miki order baki shaba?"
Ameera ta dafe mata kafaɗa cike da kulawa.
Daga kwancen ta furta magana cikin sanyin jiki kamar ba ita ba.
"Ameera kaina ke ciwo sannan ina son naje city star,naga wannan guy ɗin?"
Da sauri Ami ta zabura tana washe bakinta tare da cewa.
"Kardai Bangis wayyo kice mutumina ya taki sa'a kinsan kwa bai jima da turon sakon kuɗi akan
nasha mai kanki ba"
Ami tafaɗa da saurin ta cike kuma da murna marar iyaka.
Tashi tayi zaune tana girgizama Ameerah kanta.
"Ami bafa bangis ba, wallahi ɗazu naje city star wajan Alhaji mudi kwatsam nazo zan sauka na
haɗu da wani Haɗaɗɗan mutum wanda atake anan naji ya tafi da dukkan tunanina sedai kallo
ɗaya nai masa nasan ba harkarmu guda ba don naga kallon rainin da ƙyamar daya kemin,
Ameera yaya zanyi zuciyar data tashi da tsanar ɗa namiji sabida tabon dayay mata ayau ta afka
ga son wanda bai son tana yi ba ƙilama bazan kuma ganinshi ba har abada"
Tafaɗa tana mai sakin marayan kuka.
Baki da hanci Ameera ta saki yau UMMUL-KHAIRI mai sa maza jinya itake kuka akan wani
namiji? lallai so makahon zuciya ne inji bahaushe.
Cikin tattausan lafazi mai daɗi ameera ta janyota jikinta.
Tana mai share mata hawayenta.
"Dena kuka Ummul babu wani ɗa namiji daze ganki baiji wani abuba idan bai soki dan komai ba
yasoki dan baiwar kyau da sura da Rabbi ya baki ina ji ajikina zaki sami soyayyarshi domin
nasanki babu wasa"
Tafaɗa cike da ƙarfafa gwiwa.
"Baze soni ba kallon tsana yake min ba ajina bane"
Tafaɗa tana wani taɓe baki kamar wata karamar yarinya.
"Dena faɗin haka babu wani ɗa namijin daze fi karfin ɗiya mace muddin tasan lagonshi tofa
magana ta ƙare maza share hawayenki ƴar ƙanwata dena kuka insha Allahu komai zezo mana
cikin matiƙar sauƙi"
Ameera ta faɗa mata hakan cike da kulawa tare da kwantar mata da hankalinta.
Kamar sokuwa tahau goge hawayen sedai Batajin zata iya kai komai cikin bakinta a halin data
ke ciki a yanzu Seda ameerah taga ta dena kukan sannan ta mike zuwa mazauninta tana
cigaba da zuƙar shishar ta.
**********
Tsaki yaja ƙasa ƙasa tare da tattare takardun nashi masu matiƙar mahimmanci agare shi.
Batare daya yima Abokin nashi magana ba ya wuce Ɗaki mai number ta biyar abin mamaki
ƙofar room ɗin abuɗe take sannan da alamun anyi amfani da ɗakin sedai ba'a ɓata shi ba
sannan ma'aikatan Hotel ɗin basu gyarashi ba da alamun yayi mistake ɗakin daze shigane,
agajiye ya zube takardun dake hannun shi tare da zama akan stool ɗin gefen gadon ɗakin yana
dafe kanshi dake mai ciwo ya gaji over domin tuƙi daga abuja zuwa kano akwai ɗunbin gajiya
wayarsa dake aljihun gaban rigarshi ita ke ringing da lumsassun idanun shi ya ke kallon screen
na wayar bayan ya zarota.
My Baby aka rubuta a saman da wani tsadaddan murmushi ya ɗauka yana karawa a saman
kunnen shi.
Daga cikin wayar.
"Hellow nawan nika ɗai ina ta jera maka kira baka ɗauka ba?"
Daddaɗar muryar matarshi abar sonshi Basmah ita ke dukan cikin dodon kunnen shi.
Miƙa yayi daga zaunan alamun gajiya taci karfinsa alamun bai saba dogon driving ba kana
yace.
"I'm sorry my love ina driving ne ban lura ba yanzun nan na sauka kano ko kayana ma ba'a
kawo min ba"
Yafaɗa cike da nuna mata kulawa.
Shagwaɓe mai tayi tare da cewa.
"Ayyah baby sannu bara na barka hakan amman pls kayi wanka seka sha tea nasan ze rage
maka gajiya"
Tafaɗa kamar zata mai kuka!
Lumshe idanu ya kumayi tare da mannawa wayar hot kiss batare dayay magana ba ya katse
tare da jefa wayar shi tsakiyar gadon.
Da sauri ɗaya daga cikin ma'aikatan Hotel ɗin ya turo ƙofa rissuna wa yayi har ƙasa tare da
cewa.
"Yallaɓai ba nan ne ɗakin dasuka kama maka ba room number 1 ne nan anyi amfani dashi
bamu ma gyara ba no need ka zauna ciki"
Shafa saisayen sumar kanshi yayi.
"No problem kawai a gyaran bathroom nai wanka nan ɗin ma is ok"
Yafaɗa tare da kama yatsun shi yana matsawa suna bada sautin ƙas-ƙas.
Cikin mintuna goma wannan ma'aikacin ya kuma gyara ɗakin ya sauya bedshirt haɗi da gyara
toilet wanda ba'ama ɓata shiba, Bayan ya kammala ya miƙa mai keyn ɗakin haɗi da amsar
nashi wancan ɗin.
Sannan ya juya yana ƙoƙarin fita.
"Dan Allah ga keyn motana ka ɗauko min bags ɗina suna boot in ban takuraka ba"
Haɗaɗɗiyar muryarshi ta karade ɗakin cikin sauri ma'aikacin ya karɓa haɗi da fita mintuna
kaɗan ya dawo mai da jakun kuna guda2 godiya yayi masa haɗi da ɗaukarsu ya fara firfito da
kayan cikinta.
Sosai ya gyara kayanshi tsaf ya fito da system ɗinshi ya jona a caji sannan ya nufi Toilet sedai
tsananin ƙyamƙyami irin nashi ya hanashi shiga sabida bai san adadin mutanan da sukai
amfani dashi ba.
Dafe kanshi yayi yana ta jan tsaki akai akai ahaka ya faɗa bayin amman seda ya kuma
wankewa tass sannan ya iya watsawa jikinsa ruwa........
*DOMIN SHAWARA/ GYRA/SHARHI INA MARABA 08142105218*
_Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin
zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu
lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya
k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar
sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga
sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya
mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da
wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal
zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI
GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah
duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu
'batawa kai lokaci_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!
infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula
mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi
amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_
[8/2, 2:10 PM] ❤️❤️ : *BA SON TA NAKE BA*
{ Tausayi ne }
NA
*AUTAR MANYA*
HOME OF QUALITIES WRT ASS....
003
Ya fito ɗaure da faffaɗan tawul a ƙugunshi tare da ɗan ƙarami a hannunshi yana goge sumar
kanshi dake ɗigar da danshi lemar ruwan wanka a gaban ƙaton dressing mirrow ya tsaya yana
cigaba da tsane jikinshi kasancewar shi mai zafin nama irin na lafiyayyun maza yasa cikin
ƙanƙanin lokaci ya kammala tsane jikin nashi tsaf ya rataye ƙaramin tawul ɗin yana ƙoƙarin
ɗaukar Cream daze shafa wayar shi ta kuma ringing da ɗan sauri ya ƙarasa gabanta ganin.
MY BABY yasa shi sakin wani ƙayataccen murmushin daya ƙara bayyana zatin kyanshi kafin
yay rejecting kana shi ya kirata murya a shagwaɓe take furta.
"My one and only kayi wankan kasha tea ɗin wallahi duk na damu"
Takai maganar cikin salon kirsa.
Har yanzu tsadaddan murmushin nasa bai gushe ba cike da shauki da jin daɗin kulawarta gare
shi ya furta mata.
"yes baby yanzun haka nai wanka tea ɗinne ban shaba shima kuma zan sha dana kammala
shiryawa"
Yafaɗa mata hakan cikin lallausar muryarshi mai kashe jiki.
Tura baki tayi gaba kamar yana ganinta kana ta marai raice kamar wata ƙaramar yarinya.
"Nidai ka kunna data zan kiraka VD call yanzu na shirya ka ta wayan"
Tafaɗa tana wani irin narkar masa da murya wadda tasa sauran kaɗan ya sume a wajan dan
tsabar daɗin muryar tata.
Cikin lafazin so ya furta.
"Not now my baby sabida ina da ayyuka agabana kinga yanzu mutumin dana zo gani ze shigo
mu zauna please ki bari zuwa dare se muyi kafin nan ma kin saka min sleeping dress masu
kyau sena fi kallon ki na more"
Yafaɗi maganar yana wani ɗage gira kamar tana gabanshi.
Cikin barikancin data saba ɗauke mai hankalin sa akan kowa ta soma rera mai kuka! wanda
zahiri na karya ne amman shi bai san hakan ba sema susucewa dayay yana rarrashinta kamar
ze tsaga wayar ya shiga ya kamota ya cigaba da rarrashinta haka yake ji aranshi.
Ta jima tana Hargitsa mai lissafi ta cikin wayar na salon kirsa da shagwaɓa kafin suyi sallama ya
koma bakin gado jagwab ya zauna yana fesar da zazzafar iska, ga wani uban feeling daya ke
ƙoƙarin taso masa.
Hannunshi dafe da tawul ɗinshi ya janyo ƙasan lips ɗinshi da sauri yake tsotsa kamar ya sami
alewa ko kaɗan bai da juriya akan buƙatar shi wannan tasa yaso yazo da Basmah amman fafur
taƙi binshi sabida wurin aikinta.
Ya jima yana kokawa da numfashin sa kafin ya sami dai daiton nutsuwarshi kana ya kuma
ƙoƙarin miƙewa a karo na biyu sedai still ringing na biyu daya kuma shigowa wayarshi shiya
katse masa hanzarin sa.
A ɗan tsorace yake kallon screen ɗin wayar yawani zaro idanunshi waje waɗanda suka ƙara
haska tsantsar kyawun da Allah ya bashi.
Batare daya iya ɗaukar wayar ba