Showing 1 words to 3000 words out of 146840 words

Chapter 1 - SOORAJ COMPLETE Book Writing By Fatima Sardauna.pdf

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

             *SOORAJ*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

*(�SPECIAL THANKS TO HAJIYA FATIMA MOMYN NIGER�)*


*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

     
           *CHAPTER 1*

*SOORAJ*

Tsugune yake akan ƙafafunsa, kansa na kallon ƙasa, yayinda  kyawawan idanunsa suke
alumshe,  jama'a ne cike awajen, sai hayaniya suke, fuskar kowa ɗauke take da  farinciki,
banda wani mutum ɗaya, shima ɗin baƙin ciki  da damuwarsa basu bayyana akan fuskarsa ba,
amma tabbas zuciyarsa nacikin matsanancin damuwa.
Sake matse ƴan saffa saffan  idanunsa yayi da ƙarfi, jiyake kansa na juyawa, zuciyarsa nayi
masa wani irin tuƙuƙi,  sosai hayaniyar jama'an dake wajen ke hautsina masa ƙwaƙwalwa, sam
shiba mutum bane mai son yawan hayaniya, aduk sanda hayaniya yayi yawa awajen da yake,
to ciwon kai ne ke kamasa mai tsanani, yanzu haka shikaÉ—ai yasan abunda yakeji, jiyake kamar
ya buɗe bakinsa ya kwarara ihu, koda zaiji sauƙin abun da yakeji.

"ALHAMDULILLAH AURE YA ÆŠAURU YAU ASABAR AN ÆŠAURA AUREN SOORAJ MAI
NASARA DA AMARYARSA AISHATU KABEER MUNA TAYA ANGO MURNA!!!"  abunda wani
maroƙi keta faɗa kenan cikin ɗaga murya.

Wannan maganan da maroƙin keyi shiyayi sanadiyar dawo da SOORAJ dake tsugune cikin
hayyacinsa,   wani yawu mai ɗaci ya haɗiya, lokaci guda idanunsa suka rikiɗe suka zama
jajaye, ƙoƙarin tashi tsaye yasomayi. Da sauri wani kyakkywan matashi dake gefensa yariƙe
hanunsa, cikin murya ƙasa ƙasa yace "Please SOORAJ karkayi haka mana, acikin jama'a fa
muke, kuma kasan tunda mukazo nan idanun jama'a akan mu yake"

Tsuka wanda aka ƙira da Sooraj yayi, tare da fusge hanunsa daga riƙon da wannan ɗin yayi
masa, kallonsa yamayar ga Abbansa, karab idanunsu suka sauƙa akan najuna, da sauri Sooraj
yayi ƙasa da kansa. 

A hankali Tururuwan jama'ar da suka taru a ƙofar gidan Alhaji Kabeer suka soma raguwa, kowa
na ƙoƙarin kama gabansa,    ganin haka yasa Sooraj miƙewa tsaye yasoma nufar inda motarsa
take, ko É—aga kansa baiyiba balle har wasu daga cikin mutanen da sukayi ragowa su fahimci
wani irin yanayi yake ciki.   Hanunsa yaɗaura akan murfin motar zai buɗe, yaji muryar  MAS'UD
ta daki dodon kunnensa.

"Inazakaje?" abunda Mas'ud yatambaya kenan.

Juyowa Sooraj yayi ya watsawa Mas'ud harara, ransa amatuƙar ɓace yake, wani irin haushin
Mas'ud ɗin yakeji, gani yake komai daya faru hadda sa hanun Mas'ud ɗin aciki,  takaici ne
yasake turnuƙe zuciyarsa,  sai kawai yasaki tsuka yabuɗe motarsa yashige, Mas'ud na ƙoƙarin
zagayawa gefen mai zaman banza yashiga, Sooraj yayiwa motar key, aguje yafigeta haÉ—e da
turbuɗawa Mas'ud dakuma sauran jama'an dake kusa dasu ƙura.  Hakan yasa kowa yabisa da
kallo, ciki kuwa hadda Abbansa dake can gefe suna ganawa da Baban Amarya.

Sheshsheƙan kuka ne ketashi acikin ɗan madaidaicin ɗakin, wata yarinyace rakuɓe ajikin
bango, ta takure kanta waje ɗaya, daga yanda take sauƙe ajiyar zuciya akai akai zai tabbatar
maka da cewa kuka taci ta ƙoshi son ranta,   idanunta da suka kaɗa sukai jajur ta buɗe haɗe da
kai kallonta sama.   "YA ALLAH!" abun da ta ambata kenan cikin wata irin raunanniyar murya,
dake cikin halin matsanancin naiman taimako,   tabbas ta yarda cewa idan Ƴa Mace tarasa Uwa
to tarasa babban gata aduniya, Uwa itace komai itace ginshiƙin rayuwa, kamar yanda ruwa
keda matuƙar amfani aduniya, haka uwa take awajen kowani ƴa/ɗa, ayanda take da ƙananun
shekaru, tunaninta da hankalinta basukai É—aukar wasu matsalolinba, amma saboda halin
rayuwa duk tazama wani iri, rayuwarta duhu ne, rayuwarta ƙunci ne, HASKE take nema akoda
yaushe, da fata dakuma burin wani wanda zai taimaka mata.

"Dan Ubanki wai maikikeyi acikin ɗakinnan ne? baƙar munafuƙa, Allah dai yayi wadaranki
ZIYADA natsani waƴannan halayyartaki, muguwa mai baƙar zuciya, zaki fitone kosai nashigo
cikin ɗakin nayi ƙasa ƙasa dake!?"   faɗan wata mata dake tsaye abakin ƙofar ɗakin da yarinyar
ke ciki, matar tacika fam sai jijjiga ƙugu take.
Jinmuryan Inna Ma'u acikin dodon kunnuwanta baƙaramin tsoritata yayiba, jikinta na rawa tanufi
hanyar fita daga É—akin.

Tana fitowa Inna Ma'u ta bita da wani irin kallo. 
  "Wallahi natsaneki Ziyada, natsani koda jin sunanki ne, adole nake rayuwa dake acikin
gidannan, keda uwarki kun riga da kunzamemin JARABA, Æ´an iska masu fararen fuska!" Inna
Ma'u tafaÉ—i haka cike da takaicin Ziyada.

Itadai Yarinyar da ake ƙira da sunan ZIYADA shiru tayi tare da sunne kanta ƙasa,  ƙirjinta kuwa
jitake kamar zaiyo tsalle yafito waje sarai tasan wacece Inna Ma'u, yanzu zata kuma sake
jibganta fiye da wanda tayi mata ɗazu.  

"Ungo wannan naira ishirin ɗin kije maza ki ɗauko min niƙa na, kuma wallahi idan kika sake baki
dawo da wuri ba, yau saina ƙona wannan ɗan iskan fuskan naki, mai zubin mayu"  Inna Ma'u
tafaɗi haka tana mai sanya hanunta ta  mangare Ziyada harsai dakanta ya bugu da bango, 
sosai taji zafin bugewa dakuma mangareta da Inna Ma'u tayi, amma babu halin tayi kuka, naira
ishirin É—in ta amsa, cikin yanayinta mai sanyi tanufi hanyar ficewa daga gidan.
Tana ficewa Inna Ma'u tayi ƙwafa haɗe da cewa.
"Wallahi bazaki ƙara min cikakken sati biyu agidannan ba, ko kasheki ne ma gwamma nayi na
huta, komai na mayyar uwarki kin kwashe"....


Gudu sosai yake tsalawa akan babban titin, saida yayi tafiya mai nisa kafun yayi parking motar
agefen titi, hanunsa yasanya ya bugi steering motar, tare da furzar da iska daga bakinsa,  wata
drawer dake jikin motar yajawo haɗe da ciro goran ruwa, ɓalle murfin goran yayi haɗe da kafa
goran abakinsa, saida yasha ruwan fiye da rabin goran kafun ya É—auke bakin goran daga kan
nasa bakin,   numfashi yake fitarwa ahankali, jiyayi ƙirjinsa yayi masa nauyi,   ɗaga kansa yayi
ya kalli madubin dake cikin motar, da sauri ya kauda kansa gefe, wani irin tsananin tausayin
kansa ne ya kamasa, jiyayi zuciyarsa tayi wani irin karyewa,    kifa kansa yayi ajikin steering
motar, baisan yazaiyi da rayuwarsa ba, baikuma san taya zai fahimtar da iyayensa lalura da
damuwarsa ba, akodayaushe su kansu kawai suka sani, koda sau É—ayane basu bashi dama
yasanar dasu matsalarsa ba, ako da yaushe basu da wata magana saita Aure, burinsu É—aya
shine yayi aure, baruwansu su basu wani damu da sanin shiɗin yayakeba,   ɗago kansa yayi
daga jikin steering motar, idanunsa ne suka sakeyin ja, kamar anwatsamusu garin barkono,  
bayajin cewa zai iya zama da kowace mace aduniyarnan, yanaji ajikinsa cewa shi ba'ayisa don
yayi aure ba,  rayuwarsa cike take da DUHU baisan wani HASKE ba,   "Sai yaushene zasu
fahimci hakan?" yatambayi kansa.  Shiru yayi naɗan wasu mintuna kafun yatada motarsa,
yanzu kam ahankali yake tuƙin motar bakamar ɗazu ba, saidai kuma zuciyarsa cike take da
tarin tunani kala kala lallai dolene zaiyi abun da ya saba, duk da yasan hakan ba daidai bane
kuma ALLAH Ma bayaso, amma baida wani zaɓi da ya wuce haka...


*(Sunan labarinnan SOORAJ shima ƙirƙiransa nayi kamar yanda na ƙirƙiri sauran, kamar yanda
kukasani labarina ina ginashine akan mutum biyu, to wannan labarin ma hakanne, domin akan
SOORAJ da kuma ZIYADA na ginashi, kamar yanda nagina SHU'UMIN NAMIJI akan ZAID da

ZAHRAH,  nakan tsayawa nayi komaina akan daidai, ina iyaka ƙoƙarina wajen ganin nabaku
nishaɗi, nasamu ƙalubale sosai akan Labarin dana gama wato SHU'UMIN NAMIJI duk da
nasan matakin nasara yana tarene da ƙalubale, amma wasu sunta faɗamin maganganu son
ransu so please kuna kiyayewa, bakowacce magana yakamata ace wasunku na furtawa ba,
karku manta magana mai daÉ—i sadaka ce.)*

*VOTE and COMMENT yawan vote da comment yawan typing...�*     *Friday/13 March/2020*
    
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ*


   *Written By*
Phatymasardauna


*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*CHAPTER 2*

Agaban wani tankamemen gate yayi parking motarsa, fitowa yayi daga cikin motar ya nufi Æ´ar
ƙaraman ƙofar dake jikin gate ɗin, ahankali yatura ƙofar yashiga, Manu mai gadi naganinsa ya
kwaso aguje cike da girmamawa yace.
"Ranka ya daɗe barka da zuwa, Ango, Ango kasha ƙamshi...." 

Kallon da yayiwa Manu mai gadine yasa yaja bakinsa yayi shiru, batare daya ƙarasa maganar
dayakeyi ba.

Direct wani dogon gini dake tsakiyan compound É—in gidan yanufa.

Wata Æ´ar dattijuwar mata ce ke zaune acikin katafaren falon, kayane zube agabanta tare da
wasu manyan akwatuna masu kyau da tsada. 

Da sallama É—auke abakinsa yashigo cikin falon, amsa masa sallaman matar tayi fuskarta babu
yabo ba fallasa. Baidamu da yanayin yanda yaga fuskarta ba, don yasan dalilin daya sanya tayi
kicin kicin da fuska damace batason bashi, kuma amma duk da haka baijin zaiƙi furta abundake
cikin ranshi.
"Barka da gida Ummu"
Sooraj yafaÉ—i haka bayan yayiwa kansa mazauni akan lallausan carpet É—in da ya mamaye
ƙasan falon.

"Yauwa sannu" Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin tattare kayan dake gabanta.  Shirune yashiga
tsakaninsu, dama shi haka yake idan yayi magana saiyaja wasu mintuna baisake cewa wani
abu ba, bakuma don baida abun cewa ba, a'a haka ya sabarwa kansa.  Ummu kuwa afakaice ta
É—an saci kallonsa, yanda taga fuskarsa ya tabbatar mata da cewa akwai magana abakinsa,
itakuwa bazata so taji komai daga bakinsa ba.   Miƙewa tayi daga zaunen da take, wayarta
taÉ—auka kana ta nufi hanyar da zai sadata da É—akinta.

Ganin da yayi cewa idan yabari tatafi yarasa damansa ne, yasanyashi  gyara zama haɗe da
cewa. "Ummu dama inaso...."

"Banason kacemin komai, ya isa haka, munriga da mungaji da halinka SOORAJ, wallahi kaji na
rantsema awannan karon kasaki matar da muka aura ma, ranka saiyayi mummunan ɓaci,
zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!" Ummu takatseshi ta hanyar faɗan haka
cikin ɓacin rai.
Jajayen idanunsa yaÉ—ago ya watsawa Ummun, itakuwa ko waiwayosa batayiba ta wuce
É—akinta.

Wani irin tsannin baƙinciki ne yasake kawo masa ziyara, babban abun takaicin shine yanda
akaƙi basa dama,  jiyayi kansa na sarawa kamar zai rabe gida biyu,  tashi yayi ya fice daga
cikin falon,  ko iya kallon gabansa bayayi haka yakoma motarsa, kafa kansa yayi ajikin steering
motar, yana fidda numfashi mai zafi,    "Wannan wace irin rayuwace yakeyi? sai yaushene zai
samu sauƙi daga raɗaɗin da yakeji?"  tambayar dayaketa yiwa kansa kenan acikin zuciyarsa. 
Ya kusan mintuna 10 a wajen, kafun ya iya tada motarsa yabar unguwartasu gaba É—aya,
kaitsaye gidansa ya nufa.   

Koda ya isa bedroom ɗinsa kayan dake jikinsa ya cire tare da shigewa cikin bathroom,  wanka
yayi tare da ɗauro alwala kana yafito,  dogon wando na jeans yasanya tare da wata farar
T-shirt, kallon agogo yayi yaga da sauran time kafun aƙira sallan Azahar,   kwanciya yayi akan
makeken gadonsa tare da lumshe gajiyayyun idanunsa.....
***
Idan hankalin Ziyada yayi dubu to atashe yake, domin kuwa tana zuwa injin niƙan tasamu ba'a
niƙawa Inna Ma'u niƙan garin kunun tsamiyanta na gobe ba,  hawayene suka cika idanunta,

yayinda tashiga haɗa mai injin da Allah akan yaniƙa mata sauri take, da ƙyardai tasamu ya
yarda ya niƙa mata.   Tunda ta shawo kwanan ƙofar gidannasu take hango wata yagalgalalliyar
mota, wanda taji tsufa harta gode Allah, cikin yanayinta na sanyi taƙaraso ƙofar gidannasu.

Wani dattijone wanda aƙalla shekarunsa zasukai 60 tsaye ajikin wata ragwaɓaɓɓiyar mota
dagani motar taci wahala, mutumin irin baƙaƙen tsofinnan ne, sannan kuma ko wani gashi
najikinsa yatashi daga baƙi yakoma fari, kai tsaye zaku iya ƙiransa da tsohon najadu, domin
daganin idanunsa zakasan cewa baƙaramin ɗan duniya bane, yanayin yanda yake kallon
Ziyada kamar wani tsohon maye ne yasanya tayi ƙasa da kanta, tashige cikin gida, Murmushi
Tsohon yayi haÉ—e da jijjiga kansa, wani irin daÉ—i yaji aransa alokacin dayaga Ziyada'n.


"La'anatu sai yanzu kikaga daman dawowa? halin asaran dai shine bazaki fasa ba?" Inna Ma'u
ta tambayeta.

"Kiyi haƙuri Inna Ma'u, wallahi ba ayi miki niƙan da wuri bane, shine kuma....."

"Da Allah rufemin baki shine kuma me? waye baisan fetsarancinki ba, shashasha kawai, yanzu
da kika ebo ƙafa kika shigo cikin gida, shin bakiga  Tsoho ɗan dashe natsaye a waje yana
jiranki bane?"

Wani irin bugawa ƙirjin Ziyada yakumayi, a tsorace tace
   "Tsoho ɗan dashe kuma?"

"Ƙwarai kuwa, zakije kisamesane ko kuwa saina ɓaɓɓallaki yanzu anan wajen!" Inna Ma'u tafaɗi
haka a hasale.

Jikin Ziyada ne yasoma ɓari amma bata da wani zaɓi daya wuce zuwa tasamu tsohon najadun
dake tsaye a waje yana zaman jiranta.

Tana fitowa daga gida Tsoho ɗan dashe yasaki dariya irinta tsofaffin ƴan duniya.  Kallonsa
yamayar kan ƙirjinta, saida ya haɗiyi wani yawu,    "Ƙaraso mana Amaryata" yafaɗa yana washe
wawagegen bakinsa.  

Kallon tsananin tsana Ziyada tabisa dashi haɗe da soma ƙare masa kallo,  idanunta ta sauƙe
akan jajayen haƙoransa dayaketa washewa, gaba ɗaya bakinsa cike yake da tsakin goro, komai
nasa dagajaja ba kyaun gani, duk da itama acikin dauɗa da ƙazanta take, sannan kuma bata da
wani suturun kirki, amma duk da hakan ƙazancin Tsoho ɗan dashe daban take dana kowa, duk
garin babu wanda baisan wanene Tsoho ɗan dashe ba, tsohone da bai riƙe mutumcin kansa ba,
bashida wani aiki sai lalata yaran jama'a, matansa huÉ—u, kuma acikin garinnasu sosai akeji
dashi, kasancewar yana da shanaye dakuma dabbobi, saboda tsabar duniyanci irin nasa har
mota yake dashi, irin ko ohon motocinnan, nanma ƙaryan raine kawai irin nasa, ko iya tuƙata
baiyiba, akwai wani ɗan ƙullinsa Ɗan liti shike tuƙasa yakaisa duk inda zashi, yanzuma tare

suke.

Saida tagama ƙare masa kallo kafun ta kawar dakanta gefe, wani sabon tsanarsa taji acikin
ranta,  ganin da yayi cewa yarinyar nada taurin kai bazata ƙaraso garesaba yasanyasa soma
takowa zuwa inda take, da sauri taja da baya.   

"Wai Amaryata badai tsorona kikeji ba? ai gwamma kisaki jikinki dani domin ina tabbatar miki da
cewa mako mai zuwa za'a É—aura mana aure dake" Tsoho É—an dashe yafaÉ—i haka yana mai sake
washe ƙaton bakinsa.

Jin ya ambaci kalmar aure yasanya taƙara ja da baya, ganin da tayi kamar baya cikin
hayyacinsa ne yasanya ta juya ta koma gida yana ƙiranta amma ko waiwayosa batayiba, ashe
Inna Ma'u na laɓe tanajinsu, Ziyada nashigowa cikin gida Inna Ma'u ta ɗauketa da wani irin
faskareren mari, cike da takaici tace. "Amma kedai anyi yarinyar banza, ke inbanda hauka har
Tsoho ɗan dashe zaizo miki da maganan aure kinemi wulaƙantasa, to kijini da kyau, ninan
nabada aurenki ga Ɗan dashe, ko kinaso ko bakyaso, munafuka kawai, mai baƙar zuciya da
aniya!"

Kai Ziyada tashiga jijjigawa lokaci guda kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tayi aƙasa haɗe da
kama ƙafan Inna Ma'u cikin muryan kuka tace.  

"Dan Allah Inna Ma'u kimin rai, karki haÉ—ani da Tsoho É—an dashe, kowa dake garinnan yasan
halinsa ɗan iska ne, kuma ba tsohon kirki bane dan Allah kiyi haƙuri !!"

Ƙafa Inna Ma'u tasanya ta shure Ziyada cike da tsanarta tace "Idan kinga baki auri Ɗan dashe
ba to saidai in mutuwa kikayi, ke ko mutuwa kikayi sai ankai masa gawarki" tanafaÉ—in haka
tazari mayafinta da koyaushe ke akan igiya ta fita zuwa waje.

Kuka Ziyada tasanya haɗe da tashi ta nufi ɗan ƙaramin ɗakinta.  Zama tayi akan tabarma tare
da cusa kanta tsakankanun cinyoyinta kuka tashiga rerawa mai taɓa zuciya, tasan tunda Inna
Ma'u tafaÉ—i haka to sai ta aikata.

Inna Ma'u kuwa koda taje tasamu  tsoho ɗan dashe sosai suka tattauna akan Ziyada, inda
yatada hankalinsa akan cewa shi lallai bayason aja lokacin auren, idan da ta sonsa ne ma shi
koda yau abasa ita, idan yaso daga baya sai a É—aura auren sosai yarinyar tashiga ransa,
musamman daya lura cewa komai nata ɗanyene shakaf, da'alama zai kwashi garaɓasa mai
romo,  kuɗi sosai ya dumbulawa Inna Ma'u ita kuwa sai washe baki take da haka sukayi
sallama..

Saida tayi kuka mai isarta kafun ta fito daga cikin É—akin takama aikace aikacenta daya zame
mata  dole.  

Sallaman Babanta da tajine yasanya taji gabanta ya tsananta bugawa,  muryarta na rawa ta

amsa sallaman nasa.

"Baba Sannu da dawowa!" tafaÉ—a murya a sanyaye.

"Daban dawoba ai da bazaki ganni ba!"  Fari kyakkyawan dattijon da taƙira da sunan Baba
yafaÉ—i haka ahasale.

Cikin sanyi ta sunkuyar da kanta ƙasa, wannan halin shi kullum Babanta ke nuna mata, tun tana
ƙarama harkawo yanzu bata taɓa sanin ya soyayyar mahaifi yake ba, babanta ko kusa dashi
bayaso tazo, tsanar dayake nuna mata haryafi wanda Inna Ma'u ke nuna mata, cigaba tayi da
aikinta, shikuma kai tsaye ya wuce ɗakin Inna Ma'u jikinsa na rawa, gudun kada ta leƙo ta fara
zazzaga masa masifa, don kamar yaron cikinta haka tamaida shi.

***
Bayan yadawo daga sallan Azahar bacci mai nauyine ya É—aukesa, kusan awa uku ya share
yana bacci, kasancewar yau weekend babu aiki.  Ahankali yake buɗe kyawawan idanunsa
masu ɗauke da zara zaran gashi asamansu (Eye lashes)   akan agogon dake saƙale jikin
bangon ɗakin ya sauƙe idanunsa.  3:00 pm daidai yagani, cikin nutsuwa ya zuro ƙafafunsa ƙasa
daga kan gadon,   bathroom yashiga yakumayin wanka tare da ɗauro alwala.

Tsab yagama shirya kansa cikin riga da wando na jeans masu kyaun gaske,  ya feshe jikinsa da
turarukansa masu ƙamshi da kama jiki, combat shoe yasanya aƙafarsa haɗe da ɗaura agogon
Apple a hanunsa na dama, sosai yayi kyau,  ɗago

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login