Showing 6001 words to 7784 words out of 7784 words
Chapter 3 - MAKARANTAR KWANA FREE BOOK, Na Mujaheedah Matar Malam Ammyn khausar.pdf
shigowa yayi tareda banko k'ofar da
k'arfi idanuwansa A juye ga Alama dai buge yake yawo shaye shayensa kamar yarda ya Saba,
Mik'ewa tsaye tayi tana zubda hawaye had'ida cewa"dama Kai mashayi ne Shafiq Kuma
mazina ci Ashe yaudara ta kayi na Aure na? Wallahi kacuceni ka zalunceni bazan tab'a yafe
maka ba Kuma sai..,"
Wanketa da kyawawan Maruka har sau uku yayi Yana fad'in," ke Dan ubanki Ni...Zaki... Kira...
Mazina..ci? Ai..kuwa.. zakiga zinar yau.,"
Bata Ankara ba Kawai ya zare belt's d'insa ya hauta da duka ba k'atk'au tawa ihu take bamai
taimakonta saida yamata lilis sannan ba Imani ya Afka mata, Ranar taci wuya wuya iya wuya
Kuka Tasha har hawayenta Suka k'afe saida wahala ta sumar da ita ba tausayi Kuma bayan
yabiya buk'atar sa ya d'auko ruwa masu mugun sanyi A firij ya watsamata A firgece ta farka
tana D'an ihu da y'ar muryarta Domin harta shak'e Saboda wahala, Yana tangad'i Yana
masifa"dama ke ba cikakkiyar macce bace Ashe? Ke karuwa ce Kikasa na Aureki? Amanda
yazo bakinsa ne Dik yawanke mata jiki da Aman giyar Mai masifar wari,
Kuka take Sosai Bata ko iya motsi tana BAK'INCIKI Dana nadamar rayuwarta gaba d'aya gashi
ba gari d'aya suke da iyayenta ba Balantana takoma gida,
Saida ya Gama Amansa Tass kanta bako Imani sannan yabar wurin Yana cewa "idan nadawo
Baki gyaramun palourna ba wallahi sainayi miki Abunda yafi Wannan karuwar banza
kawa".............
_BASEERATA ITACE ARZIKINA _
WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
*MAKARANTAR KWANA☄️*
*FREE BOOK*
_(BOARDING SCHOOL)_
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR ..._
```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar
namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book,
(6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9)
Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12)
Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN
ZEEYAT PAID BOOK........ And others,. now MAKARANTAR KWANA FREE BOOK.....
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar ```
*Page 95 to 100*
_FINAL! FINAL!! FINAL!!! PAGE_
*MONDAY 9/1/2023 JANUAR*
```Alhamdulillah, Ina godiya ga Allah daya sake bani dama da ikon Fara Wannan littafin
lafiya dama kammala shi lafiya A yau Alhmdllh, Ina godiya ga wad'an da suka nunamin soyayya
ga Wannan littafin wad'an da kemun magana private dama group Dana WhatsApp zuwa
Facebook, inagodiya Alhmdllh Allah yabamu ikon d'aukar darusuka masu kyau dake ciki kuma
Allah kabamu ikon nisantar marasa kyau Alhmdllh Ina godiya ga Allah Kuma Ina godiya gareku
duka MASOYANA............```
Da k'yar tasamu da rarrafe taje toilet A wahalce tagasa kanta tana kuka da nadamar
Shiga *MAKARANTAR KWANA* gabaki d'aya Dan gani take Ayanzu inda Bata Shiga
*MAKARANTAR KWANA* ba da Wannan bala'i bazai faru da itaba, Kuka tasake tafashe Dashi
tana Dana sanin walak'anta Samarin da tayi Abaya Tabbas ba babban bala'i irin
*MAKARANTAR KWANA* data Shiga data sani data d'auke shawarar Mama,
Zaune yake A gafen gado kansa na Sara masa Wai yau shine zai Aure macce Wadda ba
virgin ba me hakan ke nufi,
Sope ce tafito toilet tana tsane kanta da towels kallonsa tayi ganin kamar Yana tinani tazauna
gegensa tana fad'in "Masoyi meke damunka haka kake wannan tunanin,"?
"Hunmm wani Basma zata cuta Ashe ba virgin bace karuwa ce Banfa sameta A macce ba,"
"Hunmmmm kaima dai kanada son Jan zance to bari na gayamaka Abunda baka saniba
Basma dai ba karuwa bace Kawai ita y'ar less ce lesbian take macce da macce"
Mik'ewa tsaye yayi cikin tsananin mamaki da tsoron maganar yake fad'in "Matar tawa take
lesbian, innalillahi wa'inna ilaihin raju'un, Wannan ba Komai bane face shairin *MAKARANTAR
KWANA*"
"Hunm nadai gayama gaskiya, kaga katashi kamai dani gida,"
wani yanayi yakeji narashin jind'ad'i baiyi magana ba mik'ewa kawai yayi, tabi bayansa
motarsa ya fisge bayan tashiga A fusace yaja motar ransa sai suya yake masa wai matarsa y'ar
lesbian ce wannan wane irin bala'in rayuwa ne? Ya farmasa haka?
"Subhanallah Shafiq katafi sannu kada ka salwantar da rayuwar mu mana"
Ko kallanta baiyi ba Balantana ya saurare metake fad'a ko gabansa baya gani shik'ad'ai yasan
bak'in cikin da yakeji
Rawar motar tafara Kan titin tana neman k'wace Masa dik iya k'okarin sa naganin ya tsaida
motar Amma yakasa
Sope sai ihu take,
Jikake gafffffff motar tadake wani k'aton icce, kansa ya dake sitarin motar,
Sope kuwa ganin motar na rawa yasa tabud'e Anata wayon Wai tafice kada hatsarin ya faru
da ita,
Cikin Rashin sa'a k'atuwar mota tazo bazato ba tsammani kawai saitabi takanta take kanta ya
watse Awurin jini yatsartu Sosai, mutanen gurin duk sun rud'e sunshiga tashin hankali
sakamakon ganin wannan hatsarin, wasu cikin sauri Suka nufe motar suka ciro Shafiq yajima
da Suma,
Asibiti Aka wuce dashi inda Sope kuwa sai tattara sauran Naman jikinta Akayi bako neman y'an
uwanta suka Mata sallah,
Direct Emagency Akashiga dashi likitoci da dama Suka rufu kansa, bincike Akayi har Akasamu
number Ahlinsa Aka buga Aka fad'a musu, take sukazo
Anan Ake sanar musu cewar yasami matsalar huhu saboda shan giya sannan kansa ya daku
zaid'au dogon lokaci Yana jinya Kuma yasami karaya A k'afarsa ta haku da hannunsa nadama,
"Innalillahi Alhaji munshiga uku"
"Kinshiga uku dai dik waya ba yaron Nan hanyar lalacewa dika kece nayita fad'a Amma sam
Baki saurara ta ko kibari shi ya d'auke fad'ana Amma Ina ke gaki wayayya Kuma Dole sai yaron
yayi Karatu A *MAKARANTAR KWANA* Ai ga irin ta nan, yanzu matarsa yakamata muje
mud'auko"
Baijira Ansartaba yafice Asibitin,
************
Yunwa da tsakanin Azabar duka da k'asanta kemata yasa take Kuka da k'yar tad'an mike
Amma takasa tsayuwa da rarrafe tafito waje garin saukowa Kan steps d'in tahard'e Kawai
tafad'o k'asa jikake kaf kaf kaf kanta sai bibbigewa take Koda yakawo k'asa harta jima da Suma,
****************
"Nifa hankalina ya kasa kwanciya tinda Akakai Basma Ace bawani labari gaskiya yau katashi
muje"
"Ni kaina hankalina ya kasa kwanciya Amma nasan Inada Akace sunkoma tashi muje mana"
Kusan Atare suka shigo gidan bayan sungaisa
Ganinta A yashe sukayi Bata numfashi ga jini natabin fuskarta,
Salati mama tasa had'ida kamata bawani b'ata Lokaci Aka wuce da ita Asibiti, bayan gama
dubata likita yake fad'a musu Anmata f'yad'e ne,
"F'yad'e??"
Suka maimaita kalmar Atare,.
"Eh"
Mahaifin shafiq ne yayi k'arfin halin yimasa bayanin tanada Aure ai,
"Amma wane irin Mara Imani ne Kuka Aura Mata haka? To yayi Rashin Imani kanta kuma ga
Alama yarinyar tana lesbian tasami matsala gaskiya bazata sake samun wani ciki ba Dan
dukanda Akamata da Kuma lesbian d'inda take hakan ne Kuma...."
"Innalillahi kingani ba da y'ata ba y'ar iska bace amma gashi sanadin *MAKARANTAR
KWANA* y'ata tafad'a harkar less innalillahi wa'inna ilaihin raju'un wallahi kacutar dani Alhaji"
Kuka mama tasa Sosai.
"Kunga ba kune k'ad'ai kece cikin wannan bala'in ba na *MAKARANTAR KWANA* mu kanmu
muna ciki saboda D'an mu shaye_shaye zinace zinace Abunda baifara ba dika Silar
*MAKARANTAR KWANA* Saidai mu d'auke hak'uri Kawai"
_BAYAN WASU WATANNI_
Shafiq yasami sauk'i Saidai Ayanzu ya shiryu ya koma shuru shuru Kuma ya neme yafiyar
matarsa da iyayensa, fitowa sukayi waje Dan An sallamesu gaba d'aya,
Hafsat na hanga suna shigowa Asibitin itada mijinta ga ciki jikinta sai shagwab'a take masa,
Da kallo Basma tabisu cikin mamaki Basma tace"Hafsat da gaske kece Kuma Wannan shine
mijin naki,"?
"Wai Basma kece kika dawo haka? Ina karatun ki Ina Kuma mijinki," eh wannan shine mijina
jibril Tahir Auwal Mai gidan kaji wanda kika sani dai Kuma Yanzu haka nazama midwafe Dan
nayi Karatu A Istanbul"
Kuka tafashe dashi tana rok'on yafiya had'ida Bata labarin komai " wallahi Ni Hafsat nayi
Dana sanin Shiga *MAKARANTAR KWANA* A can na gurb'ata tarbiyata na had'u da k'awayen
banza da mazinacin miji Mara tsoron Allah, dukanmu nida shi da sope muna Dana sanin Shiga
*MAKARANTAR KWANA*
"Kiyi hak'uri Basma k'addara ce takan riske kowanne bawa Amma Inafatan hakan Yazama
izina gareku dama wasu y'an baya, bama kune cikin bala'i ba Dan ku Kuna raye koba komai
zaku neme Gafarar Ubangijinku ita zamu tama rok'on Allah yafiya"
Taimako tabasu Sosai inda tawuce Abunta sukuwa ko wanne cike da danasani yawuce suna
kuka had'ida nadamar Shiga *MAKARANTAR KWANA*...............
ALHAMDULILLAH....... Anan nakawo k'arshen wannan littafin nawa maitaken *MAKARANTAR
KWANA* Allah yaban ladan Aikin k'warai danayi ciki Mara kyau kuma Allah ya mun Afuwa.......
_Muna da Rai muke tuba Idan mun mutu ba maganar tuba saidai musha wahala tareda
k'arb'ar Aikin da muka shuka A kabari,. Allah kaha nemu da mugun Aiki Ameen_
*TAKU HAR KULLUM MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR CE*
_BASEEERATA ITACE ARZIKINA _
WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948