Showing 9001 words to 10473 words out of 10473 words
Chapter 4 - TATSUBA 7 Book Origal by Madakin Gini .pdf
har zaka iya aikata hakan to
tabbas dan da ka haifa da kanka ma zaka iya kasheshi !!
.
Koda gama aiyana hakan sai hawaye ya zubo wa sarki shardas a karo na biyu ya kishingida
akan shimfidarsa ya lumshe idanunsa domin yayi barci amma sai barcin ya gagara.
.
A takaice dai yadda yaga rana haka yaga dare da asubar fari boka nata faman shara barci
abinsa sai sarki shardas yaji yana sha awar ya shiga daji yayi farauta ko ya harbo wani tsuntsu
ko kuma ya samo musu dabbar da zasu yi kalaci da ita saboda ya gaji da cin irin abincinsu na
guzuri wanda suka tanada, ba tare dasarki shardas ya tashi bokansa daga barcinsa ba sai ya
mike tsaye ya dauki damararsa ya daura ya gyara zaman takobinsa a cikin kufenta sannan ya
dauko kuttun kibiyoyinsa ya sakashi a kafadarsa ya rike sandar bakan a hannunsa yana gama
wannan shiri sai ya fice daga cikin wannan kogon dutse da suka kwana yana sanda don kada
ma boka labarusa ya farka daga barcin ya hanashi fita wannan farauta, nan da nan sarki
shardas ya kutsa cikin dajin yayi nisa cikinsa yana ta dube dube leke leke da neme neme sama
da kasa gabas da yamma kudu da arewa a cikin kowanne sako kwari da tudu har cikin ramuka
sarkakiya da duhuwoyi amma ko gafiya bai gani ba bare ya sami abin farauta har tsawon sa'a
guda
Al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan nan har tsoro ya dan darsu a cikin zuciyarsa
yace ya za ayi ace duk girman wannan daji da kuma tarin ni'imar dake cikinsa amma ace babu
dabbobi dake rayuwa a cikinsa?
.Tsatsuba Na 2 Littattafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/gini |
https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-2-littattafin-yaki-na.html
Ko dai wata annoba ce ta kashesu gaba dayansu a lokaci guda ? Idan hakane kuwa ai
yakamata ace annobar ta bar gawar koda daya ne daga cikinsu, koda sarki shardas ya gama
aiyana hakan a cikin zuciyarsa sai yaji wata irin iska mai karfin gaske ta giftashi ta samansa,
cikin hanzari ya daga kansa sama domin yaga ko menene ya gifta din kawai sai yaga ashe wata
jibgegiyar halitta ce mai manyan fuka fuki amma saboda tsananin karfin gudunta ya kasa gane
ko dabba ce ko aljan ko kuma tsuntsu domin kafin giftawar ido halittar ta bace a cikin sararin
samaniya cikin matukar karfin hali sarki shardas ya yunkura da nufin ya tashi sama da karfin
sihirinsa na tsafi amma sai yaji ya kasa tashi saman al amarin da yai matukar razanashi kenan
kuma yai matukar bashi mamaki saboda wannan shine karo na farko a rayuwarsa da ya taba
jarraba amfani da karfin sihirinsa na tsafi yaki yayi tasiri amma da yake shi sarki shardas mutun
ne wanda bai san tsoro ba kuma yana da dakakkiyar zuciya sai kawai ya falfala da masifaffen
gudu yabi bangaren da wannan jibgegiyar halitta tabi, sai da ya shafe sa a guda yana gudu
yana daga kansa sama ko zai hango halittar kuma yana duba kasa ko zai ga alamun sawunta
idan ta sauko kasan amma bai gani ba, kwatsam yana cikin falfala wannan azababben gudu da
dube duben halittar nan ko sawunta kawai sai ganin wani katon kogi yayi a gabansa saura kiris
ma ya fada cikinsa yayi turjiyar bazata ba a bakin gabarsa cikin tsananin sauri da zafin nama,
tsayuwarsa a gaban kogin keda wuya sai yaga tsakiyar kogin ya kumburo sama wani abu mai
girman gaske na shirin fitowa daga karkashinsa aikuwa kafin yayi wani yunkuri sai ga wannan
jibgegiyar halittar ta taso izuwa saman kogin ta dora kafafunta guda hudu a samansa tamkar
kasa ta taka ita dai wannan halitta mutum bai isa yace ga abin da take kama dashi ba ita ba
tsuntsuwa ba, ita ba dabba ba, kuma ba aljana ba tana da tsananin muni gami da matukar
kwarjini da ban tsoro kawai sai halittar ta juyo da kanta ta kurawa sarki shardas idanu ba tare da
tayi wani yunkuri ba koda ganin hakan sai sarki shardas ya durfafi halittar har sai da yaje dab
da ita sannan ya dubeta ba tare da nuna alamun wani tsoro ba yace yake wannan halitta waye
kai kuma menene dalilin da yasa kaine kadai halittar dake rayuwa a cikin wannan daji mai tarin
ni'imomi haka ?
.
Koda jin wannan tambaya sai halittar ta bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da saukar
kwarankwatsa tayi ta dariyar kamar ba zata daina ba lokaci guda kuma sai ta turbune fuskarta
ta dubi sarki shardas cikin nutsuwa tace
yakai wannan hatsabibin bil adama kayi sani cewa babu wata dabba ko wani kwaro ko mutum
ko aljan da ya isa ya shigo cikin wannan daji har ya rayu na tsawon dakiku dari face ya kasance
mashahurin matsafi abin kwatance don haka nayi maka jinjina kai da bokanka labarusa kafin
halittar ya gama rufe bakinsa tuni sarki shardas ya tari numfashinsa yana mai cewa wane ne kai kuma menene dalilin da yasa wannan daji ya zama daban da kowanne daji dake nahiyar nan.
.
Koda jin wannan tambayoyi sai halittar ta sake bushewa da dariya akaro na biyu sannan tace ni
kaina bansan kaina ba tunda ban san asalina ba amma dai na san na kawo i yanzu babu uwa
babu uba don haka ko suna bani dashi, koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata,
sannan na fusata ya dubi halittar cikin fishi tare da daka mata tsawa yace kada ka raina mini
hankali mana ai ko a ina ka rayu zaka iya sakawa kanka suna ko kuma a saka maka
tunda ba zai taba yiwuwa ba ace ka ray a inda babu aljan ko mutum.
.
Koda jin haka sai halittar tayi murmushi tace yakai wannan sarki kayi sani cewa hakuri na daya
daga cikin tafarkin dake kai mutum izuwa ga nasara bisa abinda yasa a gabansa kai kuwa baka
da hakurin sarki shardas najin haka sai ya kara fusata da fishi mai tsanani ya zare takobinsa ya
dubi halittar cikin fushi yace tabbas bani da hakuri kuma babu wani mahaluki wanda ya taba
gaya mini magana haka cikin gadara kamarka haka kuma babu wani abu da na taba sashi a
gabana ba tare da nayi nasara ba saboda haka kaima sai na jarraba sa a ta akanka domin na
san ko kai waye ne.
.Tsatsuba Na 2 Littattafin Yaki Na Abdulaziz Sani M/gini |
https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/tsatsuba-na-2-littattafin-yaki-na.html
Koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya daka tsalle sama tamkar an harboshi daga cikin
baka yayi sama izuwa kan halittar yakai mata wawan sara a wuya cikin bakin zafin nama halittar
ta sunkuya takobin sarki shardas ta sari iska kafin sarki shardas yayi wani yunkuri tuni halittar ta
maka masa jelarta akan kirjinsa saboda karfin dukan sai da sarki shardas yayi baya a sama
tamkar an janyeshi da majajjawa yaje ya gwara bayansa a jikin wata katuwar bishiya sannan ya
fado kasa tim a cikin matukar galabaice yana kumallon jini ta baki da Hanci kuma ya kasa
mikewa tsaye koda halittar taga
ta sami wannan nasara sai ta bushe da dariya tare da bude fuka fukanta tayi sama tana mai
cewa ya kai wannan sarki hakika ka cika wahalalle kuma asararre domin girman kanka da
rashin kunyar ba zasu taba kaika ga samun nasara akan abinda ka sa a gabanka ba ina yi
maka bushara da cewa kayi babbar asarar damar da ba zaka kara samun kamarta ba kafin
sarki shardas ya daga kansa sama domin yaga bangaren da halittar tayi a sama tuni halittar ta
bace bat a cikin gajimare tamkar bata taba wanzuwa ba.......
.
SHIN WANNAN WACCE IRIN HALITTA CE
.
SHIN WACCE IRIN DAMA SARKI SHARDAS YAYI ASARA WADDA BA ZAI SAKE SAMUN
KAMARTABA?
.
YAUSHE YARIMA HULKAS ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR HULAR LAMSARA HAR YA GA
BAYAN MAKIYINSA DA YA DAUKA A MATSAYIN MASOYINSA WATO SARKI SHARDAS ?
.
INA LABARIN SU SARKI HULBASU DA HAILUR DA SABUWAR AMARYARSA SHADILA DA
AKA SAKE DAURA MUSU AURE A BIRNIN SARKI HULBASU ?
.
SHIN SU SARKI HULBASU SUNA SAMUN NASARAR HALLAKAR DA DAKARUN DA SUKA
YOWA SHADILA RAKIYA BA TARE DA SUN BAR KODA DAYANSU YA TSIRA BA BALLE
YAJE YA SANAR DA SARKI SHARDAS ?
.
WANNE IRIN AZABABBEN YAKI ZA AYI A GABA ?
.
SHIN YARIMA HULKAS YANA FADAWA TARKON SOYAYYA WADDA HAR ZATA ZAMO
SANADIN RASA RAYUWARSA ?
.
TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI SAMI NASARAR MALLAKAR
HULAR LAMSARA ?
.
SHIN ABUBAKAR SALEH ALQUYRAEMEY ZAI SAMU DAMAR KAMMALA MUKU POSTING
DIN WANNAN LITTATTAFIN KUWA ?
.
Marubucin Yace Mu Hadu A Littafi Na Gaba Wato Littafi Na 8 Don Jin Cigaban Wannan
Kayataccen Kasaitaccen Labari wanda ni AlQuyramey nake muku posting ɗinsa kuma mai son
ganin Farin cikinku nake cewa sai
Allah Ya kaimu Gobe A littafi na Gaba.