Showing 3001 words to 6000 words out of 12964 words

Chapter 2 - TSATSUBA BOOK 8&9 By Abdulaziz Sani .pdf

taga ya
suma, bayan ta gama dinke raunikan sai ta shafa masa magani sannan ta koma gefe daya
nesa kadan da kan gadon da ta shimfideshi ta zauna akan wata kujera ta kura masa idanu nan
take taga ashe yarima hulkas kyakkyawane na gaske, abin kwatance kuma yana da kira sosai
irin ta manyan sadaukai kawai sai taji zuciyarta tana mai ayyana mata cewa wannan shine irin
namijin da yakamata ta aura nan gaba idan ta girma ta cika cikakkiyar ya mace, wata zuciyar
kuma sai ta kwabeta ta ce da ita baki da hankaline? Ashe har kin manta da kashedin da Aljani
Arwasul masadul yayi
miki cewar kada ki kuskura kiyi soyayya da wani da namiji a lokacin yarintarki face kin isa aure?
.
Koda gama aiyana hakan sai rulaiya ta mike tsaye da sauri ta fice daga cikin dakin, domin ta
daina kallon fuskar yarima hulkas kada zuciyarta ta kamu da sonsa, yarima hulkas bai farka
daga dogon suman da yayi ba sai kashe gari da sassafe. A firgice ya farka yana yin arba da
rulaiya zaune a gabansa tana kalaci sai ya dubeta cikin tsananin farin ciki yace A wanne lokaci
muke a yanzu Dare ne ko Safiya?
Shin mun makara wajen zuwa birnin sarki hulbasu domin ganin gasar karshe ta yar uwata.
.
Koda jin wannan tambaya sai rulaiya tayi tsaki tace ai idan ma muka makara kaine ka janyo
ashe kunnenka na kashi ne ban sani ba me yasaka ka ki bin umarnina alhali na gargadeka
akan ka tsaya a inda na barka kuma na gaya maka cewa kada ka taba komai a cikin gidan nan
in ba don nayi gaggawar kawo maka dauki ba da tuni yanzu ka zama gawa koda rulaiya tazo
nan a jawabinta sai yarima hulkas ya Yunkura da kyar cikin matukar karfin hali ya tashi zaune

daga kwancen da yake ya zuro kafafunsa daga kan gadon da nufin ya takesu amma sai ya ji ya
kasa saboda raunikan dake kan cinyoyinsa nan take takaici ya kamashi har kwallah ta ciko a
idanunsa ya dubi rulaiya cikin alamun karayar zuciya yace ina rokonki da ki gafarta mini bisa
rashin bin umarninki kuma ina kara rokonki daki daukeni a haka cikin halin da nake ciki ki kaini
birnin sarki hulbasu akan lokaci domin naga gasar nan ta karshe tsakanin yar uwata jaruma
siyama da sadauki Darkus.
.
Koda jin wannan batu sai Rulaiya tayi tsaki tace amma dai kai wawa ne wato kai bama ka damu
da lafiyarka ba kawai so kake na kaika kaje kayi kallon gumurzun wasa to ka sani cewa kai rago
ne ba jarumi ba kuma baka iya komai ba a yaki. Ba zaka iya tsinana abin arziki ba a cikin
gagarumar tafiyar dake gabanmu dole sai na baka horo mazaka dauko dan jagoranmu ka
rikeshi a hannunka yanzu nan zamu tafi birnin sarki hulbasu kafin a fara wannan gasa ga
jagoran namu can a bayanka, koda gama fadin haka sai rulaiya ta bude wata akwatu dake kusa
da ita ta debo kayan yaki ta shiga yin damara, shi kuwa yarima hulkas sai ya waiga bayansa da
sauri nan take yayi arba da Wannan tsuntsun sihiri wanda aljani Arwasul masdul ya bashi kawai
sai ya bude tafin hannunsa shi kuwa tsuntsun sai ya taso a sama yana mai kada fuka fukansa
ya dira akan hannunsa yana mai kura masa idanu cikin murna, cikin kankanin lokaci rulaiya ta
gama yin gagarumin shigar yaki ta rataya tagwayen masu a gadon bayanta bayan ta sanya
wani bakin sulke da bakaken takalmi dogaye iya kwaurinta sannan ta lullube kanta da fuskarta
da bakin mayafi ya zamana cewa idanunta kadai ake gani a fili, koda gama wannan kimtsawa
sai ta suri yarima hulkas daga kan gadon da yake kwance tamkar ta dauki buhun auduga ta
goyashi a bayanta suka fice daga cikin gidan gaba daya, shi kuwa yarima hulkas sai ya damke
tsuntsun sihirin a cikin tafin hannunsa guda yana mai matukar farin ciki bisa ganin cewa zasu
tafi izuwa birnin sarki hulbasu wajan iyayensa da yar uwarsa, da fitowarsu kofar gidan sai
yarima hulkas ya ga wani farin ingarman doki a tsaye shi kadai yana harbin iska tamkar aikoshi
akayi garesu ba tare da jiran komai ba kuma ba tare da rulaiya ta dorawa dokin sirdi ba sai ta
kama dokin ta haye bayansa tana goye da yarima hulkas din sannan tace dashi maza ka saki
wannan tsuntsu dake hannunka shine zai nuna mana hanyar da zamu isa can inda kake so
muje, koda jin haka
sai yarima hulkas yai sauri ya bude tafin hannunsa nan take wannan farin tsuntsu ya tashi sama
ya bi gabas ai kuwa sai rulaiya ta zaburi dokin da gudu suka bi inda tsuntsun ya nufa nan fa
yarima yaga dokin nasu yana yin wani irin matsanancin gudu na ban al ajabi tamkar tashi sama
yayi domin karfin gudunsa yafi gaban kwatance, abin da yarima hulkas ya ayyana a ransa
kawai shine wannan ba doki ba ne irin sauran dawakai kuma tabbas yayi imani shi wannan
sihirtaccen dokine domin gani yake kamar dokin zai iya zagaye duniya gaba dayanta a cikin
rabin sa a wannan shine abinda ya faru ga yarima hulkas bayan barci ya daukeshi a turakar
yarima barmas kuma ya farka ya tsinci kansa a wani wuri daban mai ban Al'ajabi..

'' '' ''

Al amarin sarki shardas da bokansa labarusa kuwa sai da suka kara shafe kwanaki tara cif a
cikin daji suna farautar Aljani Arwasul masadul amma duk tsawon wadannan kwanaki basu
sake haduwa da shi ba kuma ko duriyarsa basu gani ba. Al amarin da yai matukar fusata sarki

shardas kenan ainun bai san sa adda ya cakumi kwalar boka labarusa ba ya daka masa tsawa
yace kai labarusa ! Nifa na gaji da wannan farauta ta jaki mai kaho ya zama dole a gareka ka
gaggauta yin bincike a cikin hallarar tsafinka ka gano mana wata hanyar daban da zamu bi mu
iya zuwa inda hular lamsara take cikin gaggawa. .
Koda jin wannan batu sai boka labarusa ya fisge kwalar rigarsa daga hannun sarki shardas ya
dubeshi yace ka kwantar da hankalinka ya shugabana idan ba don ance tsafi kogi bane da sai
ince dakai bamu da wata mafita ko hanya da za a samu wadda zata kaimu ga mallakar hular
lamsara cikin sauki da gaggawa to amma ba a koda yaushe kuma a kowanne irin yanayi a
ko'ina komai na iya sauyawa lokacin da ba a zata ba, ba zan ki ta taka ba bari na duba mana na
gani ko akwai wata mafitar bayan wannan gama fadin hakan keda wuya sai boka labarusa ya
zauna a kas dirshan cikin rairayi sannan ya fiddo madubinsa na tsafi ya shiga karanta wadansu
dalasimai na tsafi irin wadanda sarki shardas bai ma taba jin su ba, sai da boka labarusa ya
dauki lokaci mai tsawo yana shafa madubin tsafin nasa idanunsa a rufe sannan ya tsaya cak,
boka labarusa yace ya dodon sarakai ka yi sani cewa a cikin binciken nawa na gano mana wata
hanya mafi sauki wacce zata kaimu ga isa kogon da aka ajiye hular lamsara cikin sauki da
gaggawa amma sai dai akwai wata matsala babba data bullo a cikin wannan lamari ka sani
cewa yanzu a halin da ake ciki Aljanin da muke farauta ruwa a jallo aljani Arwasul masadul sun
hadu da yarima hulkas harma ya bashi tsuntsun tsafi wanda zaiyi masa jagora izuwa inda hular
lamsara take sannan kuma sai abu na biyu yarima hulkas ya hadu da wata babbar sabuwar
abokiyar gabar taka mai suna Rulaiya wadda take da burin daukar fansa akanka kuma a yanzu
haka ta goya yarima hulkas akan wani dokin sihirin tsafi da Aljani arwasul masadul ya hadasu
dashi sun tafi izuwa birnin sarki hulbasu inda matarka shadila take bisa jagorancin wannan
tsuntsun sihiri da Arwasul masadul ya bashi, na gano cewa akwai wani mugun shiri da ake yi
maka a can birnin sarki hulbasu don haka lallai ina tabbatar maka da cewa sarki hulbasu yaci
amanarka kuma yana son ya rabaka da matarka shadila a yaune za ayi gasar karshe ta
jarumtaka a birnin nasa kuma a yau dinne ya shirya kashe gaba dayan dakarunka dake tsaron
lafiyar gimbiya shadila, idan bamu je birnin ba akan lokaci zamu iske tuni ya gama dasu kuma
yabi su yarima hulkas izuwa dauko hular lamsara.
.
Koda boka labarusa yazo dai dai nan a jawabinsa sai kan sarki shardas ya daure ya cika da
tsananin mamaki da fargaba da kuma takaici, ya dubi boka labarusa cikin damuwa yace akan
wanne dalili sarki hulbasu zaici amanata alhalin yana tsananin sona?
Shin wacece wannan sabuwar abokiyar gaba tawa wacce naji ka ambashi sunanta rulaiya
wacce suke tare da yarima hulkas? .
.
Koda jin wadannan tambayoyi sai boka labarusa yace wannan sabuwar abokiyar gaba taka ba
wata bace face Yar attajiri Amsar wanda ka kashe shi a cikin gidan darul daulat bayan yaci
gasar da kukai ta siyen gida a karshe ka gaje dukiyarsa babban burin wannan yarinya rulaiya a
duniya shine ta dauki fansar ran mahaifinta akanka kuma ta mallaki gidan darul daulat tunda
mallakin mahaifinta ne Attajiri Amsar, haka shima a yanzu yarima hulkas bashi da wani buri
wanda ya wuce ya hallaka ka don daukar fansar abinda ka yiwa ubansa hailur da dukkan
zuriarsu ina mai sanar dakai cewa a halin yanzu tuni hailur da matarka gimbiya shadila sun

mayar da auransu a cikin birnin sarki hulbasu har sun tare a cikin wani kasaitaccen gida da
sarki hulbasu ya basu.
.
Koda boka labarusa yazo dai dai nan a zancensa sai sarki shardas ya takarkare ya kwarara
uban ihu irin wanda ke tarwatsa mazaje a filin fama komai jarumtakarsu da rashin tsoronsu. Kai
inda ace akwai mace mai ciki a wajen da tuni ta kama nakudar dole saboda firgita da za tayi na
jin wannan ihu na sarki shardas kananun jarumai da dakarun yaki kuwa firgicewa zasuyi su
dimauta su kama sakin fitsari a wando, shi kansa boka labarusa wannan ihu na sarki shardas
ya razanashi yasa zuciyarsa ta buga tsuntsaye da dabbobin dake cikin dajin kuwa gaba
dayansu sai da suka kama guje guje da iface iface suna sauya sheka da shigewa cikin ramuka
cikin matsanancin fishi sarki shardas ya dubi boka labarusa yace maza ka hanzarta kaini birnin
sarki hulbasu kafin su yarima hulkas su isa can, cikin rawar jiki boka labarusa yayi tsafi wani
katon Aljani ya bayyana tsulum a gabansa suka haye bayansa ya tashi dasu sama ya luluka
izuwa cikin gajimare yana mai tsala azababben gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya, Abinda
sarki shardas bai sani ba shine shi kansa boka labarusan bashi da tabbacin zasu iya isa can
birnin Na sarki hulbasu akan lokaci kafin komai ya gudana.

+i ++ ++

Acan birnin sarki hulbasu kuwa gari na wayewa aka tashi da tsananin tashin hankali a gidan
sarautar saboda an nemi yarima
hulkas sama da kasa an rasa babu inda ba a duba ba acikin birnin ba har da cikin dazuzzuka
amma kamar maye yaci shirwa ga shi kuma a can filin gasa jama a sun taru makil ana ta shewa
da ihu ana jiran isowar sarki hulbasu da su jaruma siyama babu wanda yafi kowa tashin hankali
sama da shadila domin tunda akace yarima hulkas ya bata take ta faman rusa kuka saboda
gani take kamar ya fada hannun sarki shardas ne.
.
Da kyar hailu ya shawo kanta ya rarrasheta don kada ta tarwatsa musu dukkan shirinsu na
ranar inda ya tabbatar mata da cewa yayi bincike a hallarar tsafinsa ya gano cewa yarima
hulkas na nan a raye kuma zai dawo kafin a gama wannan gasa nan dai ya lallabata suka shiga
cikin ayarin sarki hulbasu aka tafi filin gasa koda jama a suka jiyo bushin Algaita da bugun
tambura alamar cewa sarki ya iso filin gasar sai filin ya sake rudewa da shewa gami da tafi nan
fa aka bude kofar filin gasar sarki da mukarrabansa suka shigo bisa dawakai dakaru na take
musu baya, amma abin da ya daurewa kowa kai shine sarki hulbasu yayi gagarumar shigar yaki
tamkar yana cikin jaruman gasar haka ma dakarunsa na musamman masu tsaron lafiyarsa
kuma a cikinsu har da wadansu bakin dakaru wadanda suka rufe fuskokinsu ba wasu bane
wadannan bakin dakarun da ke bayan sarki hulbasu ba face su jarumi hailur.
.
Lokacin da dakarun sarki shardas masu tsaron lafiyar gimbiya shadila sukaga sarki hulbasu ya
fito da wannan shiri sai suka sha jinin jikinsu suka fara zargin cewa lallai akwai wani abu dake
shirin yi musu don haka sai suka fara yin kus kus a tsakaninsu, Abinda basu sani ba shine
wanda duk ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi kuma maso abinka yafika dabara, jaruma
siyama na daga cikin tsakiyar dakarun sarki tayi gagarumar shigar yaki tare da mahaifiyarta bisa

doki guda,
.
Koda yan kallo suka ga siyama sai suka rude da ihu aka kama yi mata jinjina, ita dai kawai
jaruma siyama tana yin murmushin karfin haline amma hankalinta a wannan rana a tashe yake
saboda rashin ganin dan uwanta yarima hulkas.
.
Bayan sarki hulbasu da tawagarsa sun gama shigowa filin gasar kuma sun zauna a inda aka
tanadar musu sai mai gabatarwa ya fara da kirawo sunan sadauki darkus nan fa magoya bayan
darkus suka rude da shewa gami da tafi suka shiga yi masa kirari gami da jinjina koda aka bude
wata kofa sadauki darkus ya fito yana tafiya kamar wani toron giwa a cikin gagarumar shigar yaki sai filin gasar ya yi tsit tamkar mutuwa ta gifta saboda kwarjininsu da karar sautin takun
sawayensa har sai da sadauki darkus ya iso tsakiyar filin gasar ya tsaya mai gabatarwa ya
kirawo sunan jaruma siyama sannan filin gasar ya sake kaurewa da shewa gami da yafi, cikin
nutsuwa jaruma siyama ta fito daga cikin tawagar sarki hulbasu ta shiga filin gasar, har sai da ta
isa.
.
Daf da sadauki darkus sannan ta ja ta tsaya a lokacin da tazarar dake tsakaninta da sadauki
darkus bata wuce taku uku ba, ba tare da bata wani lokaci ba alkalan gasar suka bada umarnin
a fara gasa nan take, aka buga tambarin fara gumurzu kamar hadin baki sai duk su biyun a
lokaci guda kowannansu ya juya da baya yayi taku bakwai sannan suka tsaya suka juyo suna
masu zare takubbansu, kawai sai suka ruga da masifaffen gudun tsiya tamkar zasu tashi sama
suna masu kwallah ihu mai firgitarwa suna jijjiga makamansu a sararin samaniya kafin su hadu
sai kowannansu ya daka tsalle sama yakaiwa dan uwansa mummunan sara..
Kai nima AlQuyraemey ganin wannan saran ne yasa na tsaya a nan nace sai wani lokacin cewa
sai Allah ya kaimu gobe.

Akwai littattafai guda Uku da nake aiki akansu nan bada jimawaba zan gama sune kamar haka:
1- Jarumin Jarumai
2- Gwarzon Sadauki
3- Jarumi Dan Baiwa wanda dukkansu Abdulaziz Sani Madakin Gini ne ya rubutasu ga mai so
zai iya yi mani magana ta WhatsApp 08138873799


TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part C.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Abubakar Saleh AlQuyraemey
.
Kafin su hadu sai kowannan su ya daka tsalle sama ya kaiwa dan uwansa mummunan sara,
duka su biyun a tare suka duro kasa lokacin suna masu juyawa junansu baya, bisa mamaki sai
aka ga kowannansu ya tsaya cak a inda yake ba tare da ya juyo ya cigaba da yaki ba, Al amarin

da ya baiwa kowa mamaki kenan a filin Gasar. Aka sake yin tsit a karo na biyu daga can kuma
sai aka ga jaruma siyama da sadauki darkus sun waigo sun fuskanci juna shi yana mai dafe
saman kirjinsa jini na zuba ita kuma tana mai dafa hakarkarinta Na hagu jini na zuba.
.
A sannan ne yan kallo suka gane cewa ashe kowannansu ya samu nasarar yiwa dan uwansa
mugun rauni Cikin matukar juriya da jarumtaka sadauki darkus ya yagi rigarsa ya daure kirjin
nasa tamau don tsaida jini itama jaruma siyama sai tayi sauri ta cire mayafin dake zagaye a
wuyanta ta daure hakarkarin nata ba tare da jiran komai ba sai suka rugo izuwa kan juna suka
kacame da masifaffen yaki mai matukar ban tsoro da ban al ajabi a wannan lokaci mahaifiyar
siyama na zaune daf da hailur kuma tuni ta fara kuka bisa ganin yadda aka yiwa yarta rauni tun
a farkon fara wannan gasa shikuwa hailur sai ya dubeta yace kwantar da hankalinki yake
matata ni na san ko wacece yata ina mai tabbatar miki da cewa ba zata mutu ba kuma ita ce
zata lashe wannan gasa sai da aka shafe sa auku cur ana wannan mummunan BAKIN
ARTABU tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama ya zamana cewa sun galabaitar da juna
domin kowannan ya sami rauni kimanin guda biyu a jikinsa jiri ne ke dibarsu tamkar zasu sake
yin RAGAS saboda karfi yazo daya ana cikin haka ne sadauki darkus ya shammaci jaruma
siyama ya dankara mata wani karkarfan naushi a ciki saboda karfin naushin sai da jaruma
siyama tayi sama da baya bayanta yaje ya gwaru da katangar filin gasar ta fado kasa da rub da
ciki a matukar galabaice tana aman jini.
.
Koda sadauki darkus yaga ya sami wannan nasara sai ya bushe da dariyar mugunta ya daga
takobinsa sama ya ruga izuwa inda
take ya daka tsalle sama da nufin ya duro kanta ya soke gadon bayanta tuni a wannan lokaci
kowa ya gama sallamawa cewa jaruma siyama ta mutu ba zato ba tsammani sai aka ga jaruma
siyama ta mirgina can gefe guda takobin sadauki darkus ta lume a cikin kasa kafin sadauki
darkus ya zaro takobin tuni siyama ta doki kasa da tafin hannayanta biyu kawai sai gani akayi
tayi sama kuma tayi katantanwa sannan ta doki kirjin sadauki darkus da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login