Showing 1 words to 3000 words out of 3030 words

Chapter 1 - KUNDIN TSATSUBA 6 Book Littafin Yaki by Madakin Gini .pdf

KUNDIN TSATSUBA
BOOK 6
Na Abdulaziz Sani Madakin Gini
07032707179


Ba tare da bata wani lokaci ba, Sima ta wuce gaba Kuddaru na biye da ita a baya yana tafiya
dugul-dugul kai ka ce aljani ne ba mutum ba, saboda tsabar gajartarsa.

A bangaren su Yelisa kuwa, sai Jafar ya ce "Kai ya kamata mu tashi mu dan kewaya dajin nan,
kin san an ce zama waje daya tsautsayi ne."

Yelisa ta ce "Haka ne amma kuma ai karambanin akuya ke kai ta ramin kura. Ba ka son zama
waje guda, garin

yawace-yawacenka zaka sa mu fada mugun hannu. RAWN "Ke dai matsoraciya ce, in ba za ki
ba, ni ki kyale ni na tafi."

"A dawo lafiya, ni kam ina nan tare da su Nargaz, shawarar da zan baka kawai in ka ga hallaka
ka kwalla ihu mu kawo maka dauki.

LAJafar yayi murmushi ya ce "Haba, ni fa namiji ne, ai ba a san maza da ragwanci ba, ba na
gudu don wuya, sai dai idan ku ka ji shiru kuna iya bin baya."

Jafar na gama fadın haka yai gaba ya nausa cikin jejin, ba tare da sanin inda ya nufa ba.

Gibiya Sima da waziri Kuddaru kuwa, ba su dade suna tafiya ba a cikin jejin kawai sai suka ga
wani kerarren gida guda daya tal a gefe guda. Al'amarin da ya matukar ba su mamaki, suka
tsaya cak suna kallon gidan. Suka dubi junansu Sima ta ce "Dubi wannan abin al'ajabi, wane ne
kuma ya zo ya dandasa kyakkawan gida haka a tsakiyar jeji? Lallai sai mu je ga wannan gida,
ko don na ga mamallakinsa."

Cikin alamun tsoro Kuddaru ya ce "A'a sarauniyar duniya, kar mu je wajen can, babu mamaki
tarko ne na
mugayen aljanu. Inda kamar ma muna tare da aljani Durfa ne babu matsala, na san zai iya kare
mu daga sharrinsu,"

"Ni kuwa dadi na da kai ka cika tsoro, wai shin an gaya maka cewa ni kyalle ce? Ina tabbatar
maka da cewa ina da cikakken shiri, ba karamin aljani ba ne zai iya cutar da ni."

"Haka ne ranki ya dade ba musu na ke da ke ba amma daj kin san an ce hayar lafiya a bi ta da
kwana."

Ko da jin haka sai Gimbiya Sima ta dakawa Kuddaru tsawa ta ce "Na umarce ka da ka bi ni
izuwa ciki gidan can, idan kuwa ka ki na rantse da darajar sarautata, sa na sa an yi maka azaba
ma radadi."

"Tuba nake ranki ya dade, tabbas zan biki ko d kuwa zan rasa rayuwata. Bin umarninki shi ne
ibadata."

Kai tsaye Gimbiya Sima da Kuddaru suka durfal kofar wannan gida. Da zuwansu suka iske
kofar shiga kulle garam, suka yi suka yi su bude ta abu ya gagara. Ha sun hakura sun juya da
baya da nufin komawa inda suk baro, sai kofar ta bude da kanta. Cikin sauri suka waigo amma
ba su ga kowa a bakin kofar ba. Ba tare da jin tsoro komai ba, Sinta ta juya ta nufi shiga gidan,
Kuddaru na biy da ita a baya cikin tsananin tsoro, sai waige-waige yak kamar a ce kyat ya tsere.
Har suka kunna kai cikin gida jikin Kuddaru bai daina karkarwa ba. A ko yaushe yan waigen
wanna tofar ta shiga, don ya na tsammani za ta iy rufe kanta. Wani abin mamaki babu komai a
cikin gidan fa tarin dukiya ta tsubin zinare, lu'u-lu'u, jauhar da sauransu. cikin wadansu irin
manyan tukwane na kasa. Saboo dadewa ajiya duk yana ta lullube su.
DIAND

Ko da ganin wannan dukiya, sai idanun Kuddaru suka zazzaro farin ciki ya lullube shi ya ce
"Ranki ya dade ai ni ko daga nan na tsaya da wannan tafiyar na gama rabauta, na tabbata
jikokina da tattaba kunnena ma ba za su yi talauci ba a doron kasa."

Kawai sai ya kai hanmunsa cikin tukunya guda da nufin ya kwashi dukiyar. Sima ta daka masa
tsawa, ya janye hannunsa da sauri. Ta ce "Na hore ka da kada ka kuskura ka taba komai a cikin
gidan nan, ka sani cewa ba mu baro kasarmu don wannan bukata ba. Wannan dukiyar tamkar
kura ce daga cikin irin dukiyata. Ka yi hakuri in dai muka koma Laharim cikin biyan bukata ta,
zan baka linkin ba linkin din ta."

Sima na gama fadin haka, ta hango wani karamin allon karfe na zinare ajiye bisa wani tebur.
Cikin sauri ta isa wajen ta dubi rubutun da ke jikinsa cikin nutsuwa, ta ga bayani kamar haka:
sind babi shosoba

Ya kai bakon wannan gida, ka yi duba izuwa bangon arewa za ka ga madubin shiga ainihin
taskar gidan nan. Ka bude ka shiga, duk abin da kake nema a rayuwarka zaka samu a ciki.

Ko da Gimgiya Sima ta gama wannan karatu, sai ta juya ta dubi bangon arewa, ai kuwa sai ta yi
arba da wani zagayayyen karfe makale a jikin bango wanda da gani ka san wana shi a ke yi
yana zagayawa tamkar dutsen nikan tsaba wanda dawaki ko shanu ke sarrafawa. Kai tsaye
Sima ta je ga wannan madubi, ta fara kokarin wana shi, amma sai ta ji shi da tauri sosai. Kawai
sai ta kwalawa Kuddaru kira, ya ruga gare ta, suka hada karfi suka wana shi ya rinka juyawa

a hankali. Ba zato sai suka ga wata kofa na budewa a kasan gida. Yayin da suka kure mawanin,
sai kofar ta bude daidai yadda mutum zai iya shiga. Ko da suka leka sai suka ga ashe wani gida

ne a karkashin kasa. Ba tare da bata lokaci ba, Sima ta kama hannun Kuddaru suka shiga cikin
wannan kofa, suna masu bin wata matattakala har suka kule ciki.

A daidai wannan lokaci ne Jafar ya shigo cikin wannan gida, inda aka zube wannan dukiya ta
farko wadda su Sima suka fara gani. Sa'adda Jafar ya ga wannan tulin dukiya, sai shi ma ya
cika da mamaki. Bai taba komai ba har ya hango wannan kofa ta karkashin kasa, kawai sai ya
kunna kai ciki, kamar yadda su gimbiya Sima suka yi.
Bayan Sima da Kuddaru sun yi 'yar doguwar tafiya kadan, sai suka tsinci kansu a tsakiyar wata
katuwar fada mai dauke da dukkanin kayan alatu na duniya, a gefe guda kuma ga tarin
kyawawan samari da 'yan mata nan cikin kayataccen ado wanda idanu bai taba ganin irin su ba.
Wani irin kanshi mai dadin gaske na tashi a wurin. Dangane da abinci da abin sha kuwa, babu
irin nau'in da babu a wannan wuri. Sima ta tsaya ta karewa samarin wajen kallo tsaf, sai ta kasa
gane wanda ya fi wani kyawu. Tabbas duk wanda ta samu daga cikinsu a matsayin mijin aure,
ta gama morewa. Nan fa ta tsaya tana duru-duru da tunanin wanda ya kamata ta zaba. Shi
kuwa waziri Kudduru ko da ya ga wadannan kyawawan 'yan mata, sai ya rude ya dimauce ya
fara aiyanawa a ransa cewa, shi kam sai dai ya tafi da su gaba

daya ya zuba su a gidansa na Laharim, ko kallonsu kadai ya ke yi, ba zai kara bakin ciki a
rayuwarsa ba. Sima ta nufi inda kyawawan samarin suke, tana mai kallonsu daya bayan

daya, kowannensu nayi mata murmushi gami da mika mata hannu da nufin ta zaße shi. Shi ma
Kuddaru sai ya nufi wadannan zika-zikan 'yan mata, suka rinka yi masa yadda samarin suka
yiwa Sima. Ko da Sima ta kama hannun daya daga cikinsu, sai dukkaninsu suka rikide suka
zama wadansu iri dodanni masu mummunar kama, suka yi mata kama-kama, tana ihu suka
daddaure ta a jikin wai dogon karfe, sannan suka ja da baya su kai cirko-cirko kowannensu na
mande harshe.

Kamar yadda abin ya faru ga Gimbiya Sima, haka ya faru ga waziri Kuddaru, tuni shi ma
wadannan kyawawan yan mata sun rikide sun zama dodanni, kuma sun faure shi amau a jikin
dogon karfe, sun tsaya cak kamar masu jiran umarni. Ba zato sai suka farajin wani irin gurnani
mai ban soro wanda ba su taba jin irin sa ba. Gurnanin ya ci gaba da Karuwa har ya gauraye
fadar gaba daya, sai ga wani jibgegen Hodo irin wadannan amıma girmansa ya ninka na su sau
zoma. Baya iya ganin komai da ke wajen sai ya sunkuyo da Kansa kas. Yayin da Gimbiya Sima
da Kuddaru suka yi arba la wannan dodo, sai suka kwalla ihu don tsananin razana. Shi kuwa
dodon sai ya bushe da dariya wadda ta haifar da agarumar iska. Iskar ta tashi hankalin su
kansu sauran Jodannin, har sai da katon dodon ya rufe bakinsa sannan Kowa ya dawo cikin
hayyacinsa. Nan fa Sima ta fara kokarin eton kansu da karfin tsafi, amma sai abu ya gagara,
domin safin ya ki yayi tasiri akan dodannin. Kai tsaye dodannin uka yi ca a kan Sima da
Kuddaru don su yagalgala su.

Ba zato sai aka ji wani ihu ya ratso cikin fadar da Eudu. Dodannin suka bar su Sima suka waigo
baya, sai suka

yi arba da Jafar. Ko da suka ga wannan 'yar karamar halitta ta nufo su a guje, sai gaba dayansu
suka juyo kansa su ma suka ruga gare shi tamkar an bude garken shanu. Yayin da Jafar ya ga
wadannan dodoni sun yi ca kansa, sai ya razana ya juya da baya ya kara runtumawa da gudu.
Gudu ya ke iya karfinsa don ya fitace daga cikin gidan, amma sai ya ga kamar a waje daya
yake a tsaye. Al'amarin da ya kara razana shi kenan, kuma da zarar ya waiga baya sai ya ga
tsakaninsa da dodannin bai wuce kamu daya ba, a ko yaushe dayansu na iya cafko shi. Karar
sawayensu da gurnaninsu ya cika masa kunne, ya addabe shi. Ba zato sai far ya ji an danko
rigarsa ta baya an yi sama da shi. Da yake yana makale da Kundin Tsatsuba a hammatarsa, sai
ya juyo cikin zafin nama yayi nuni da Kundin Tsatsuba ga wadannan dodanni. Bisa mamaki sai
ya ga wani haske ya fito daga cikin Kundin Tsatsuba ya buge su. Nan take suka rinka kamawa
da wuta suna kumbura suna farfashewa, tamkar mushen da yai kwana da kwanaki ba a binne
ba. Nan fa na baya baya suka juya a guje don kada wannan haske ya riske su, ko da ganin
haka sai Jafar ya tasa su a guje, ya yi ta karar da su da wannan haske. Shi kansa shugaban
nasu sai da ya take da kafarsa yana neman maboya, amma wannan haske bai bari ya tsira ba,
dukkaninsu sai da suka zama gawa dayansu bai kubuta ba.

Bayan Jafar ya ganta da wadannan dodanni, sai ya sake duban Kundin Tsatsuba da kyau ya
rungume shi a kirjinsa cikin tsananin farin ciki ya ce a ransa 'Ashe ma ni ina tare da maganin
mugaye ban sani ba?' Yana gama fadin haka ne, ya daga kai ya dubi inda Gimbiya Sima da
Kuddaru
ke daure. Kawai sai ya ruga gare su ya fara kokarin kwance igiyar da a ka daure Sima da ita.
Nan fa abu ya gagara, domin ba shi da karfin da zai iya kwance murtukekiyar igiyar. Jafar ya
tsaya ya duba kowace kusurwa a wajen ya ga babu wani makami da zai iya amfani da shi ya
yanke igiyar, kawai sai yai nuni ga igiyar da Kundin Tsatuba. Take wani jan siririn haske ya fito
ya tsintsinka igiyoyin, Sima ta fado kasa. Sannan ya sake nuna igiyar da ta daure Kuddaru, ita
ma ta tsintsinke.

Gimbiya Sima na mikewa tsaye suka dubi juna ita da Jafar. Koya ga tsananin kyawunta, sai ya
rude, idanunsa suka kafe ko kiftawa ba sa yi, bakinsa ya kulle, har sai da ta dafa kafadunsa ta
girgiza shi, tana murmushi ta ce "Godiya a gareka ya kai Jafar bin Ruziyal. Lallai kam ka ceci
rayuwata, ba zan taba mancewa da kai ba."
Cikin tsananin mamaki Jafar ya ce "Wace ce ke? Ya a kai kika san ni? Kuma mene ne dalilin
zuwanki nan?"

Gimbiya Sima ta yi murmushi ta ce "Ni ce Gimbiya Sima mai mulkin kasar Laharim, na san ka
ne ta hanyar ganin ka a cikin allon tsafin Boka Sulbaini. Dangane da abin da ya kawo ni nan
wurin kuwa, ba zan iya baka amsa ba a halin yanzu, sai dai nan gaba idan damar hakan ta
sama."
Kafin Jafar ya kara fadin wani abu, tuni Sima ta dafa Kuddaru wanda ke kwance a kasa, sun
face gaba daya. Jafar yayi ta dube-dube amma ko duriyarsu bai ji ba. Al'amarin da ya kara jefa

shi cikin mamaki kenan. Kawai sai ya kama hanya ya fita daga cikin gidan ya koma inda ya baro
Yelisa da su aljani Nargaz.

Da zuwa ya dubi Yelisa ya ce "Tashi mu tafi."
Ko gardama ba ta yi ba ta dane bayan Gulzum shi ma haka. Gulzum yai sama da su, Nargaz na
take musu baya Abin da ba su sani ba shi ne aljani Durfas na biye da su dauke da Gimbiya
Sima da kuma waziri Kaddaru, wadanda suka kusan rasa rayukansu a gidan dodanni.

Tafiya ta ci gaba, ya zamana ba a kara yada zango ba, sai bayan kwana hudu sannan Yelisa ta
bukaci da a sauko kasa ta huta.

Ko da jin haka, sai Jafar ya bushe da dariya ya ce "Ina zata za ki iya hakuri har tsawon cikon
kwanaki taran, don kin san jiya da shekaran jiya aljani Nargaz ne ya dauke mu gaba daya, na
tabbata yanzu muna mu daf da riskar jejin Kalkim."

Yelisa tayi murmushi ta ce "Amma dai ka sani cewa na yi karfın hali, tunda na jure zaman
kwana hudu a kan wannan aljanin wanda ko'ina a jikinsa tauri ne kamar dutse In ba don ma
mun sha magunguna ba da tuni mun kamu da mugun ciwon basir."

Ko da jin wannan batu, sai Jafar da aljani Gulzum suka bushe da dariya, shi kuwa Nargaz sau
ya murtuke fuska, zuciyarsa tai bakikkirin ya ce a ransa 'Ku yi mini jafa'i son ranku, da sannu
zan kuntata muku abin bakin cikin da ba za ku taba mancewa ba. Ni na san wahalar banza za
ku sha, kura da shan bugu gardi da kwashe kudi.
Gaba daya wannan hira ta wakana ne yayin da suke kokarin saukowa kasa. Suna dira bisa
turba, sai Yelisa ta sauka daga kan aljani Gulzum ta dubi Jafar ta ce "Ni zan dan mike kafa sai
na dawo.
Cikin hanzari shi ma Jafar ya sauko kasa ya ce "Dakata Yelisa bari na zo na yi miki rakiya."

Ko da jin haka sai ta waigo ta dube shi cikin mamaki a lokacin da tuni ya iso gabanta. "A
wancan karon da muka yada zango, kai kadai ka tafi yawon mike kafa ban yi maka rakiya ba,
saboda me yanzu kai za kai mini rakiyar?"

Jafar ya ce "Saboda a wancan lokaci ni ma da kyar na kwaci rayuwata, ina tsoron kada abin da
ya faru gare ni, ke ma ya same ki."

ba?" "Ashe wani abu ya same ka amma ba ka ba ni labari

"Haka ne, kin san komai sai da hali, halin hakan ne ban samu ba, amma yanzu mu je gaba zan
sanar da ke labarin abubuwan al'ajabin da na gain, da kuma hadarin da na shiga."

Ba tare da wata gardama ba Yelisa ta amince, suka jera suka nufi cikin jeji inda suka bar aljani
Gulzum da aljani Nargaz su ma suka bude na su shafin hirar.

Nargaz ya fara da cewa "Kai amma fa aikin da ke gabanmu ba karami ba ne, yanzu fa ka ga ba
lallai ba ne gaba dayanmu mu tsira da rayukanmu yayin da muka shiga jejin Kalkim. Kafin mu
sami nasarar dauko takobin Sarjis ma sai mun sha bakar wahala, daga nan kuma sai mu wuce
fadar sarki Lu'umanu mu shiga kurkukunsa da ke karkashin kasa mu sato aljani Markahul
Sabus. Ko ka san cewa bakaken aljanun da ke gadin wannan kurkuku duk duniya babu wasu
aljanu masu karfi-da taurin kai kamarsu? Ni kam ban ga hanyar da za mu bi ba mu kubuta daga
sharrinsu."

18 in a Yayın da aljani Gulzum ya ji wannari bayani, sai yai ajiyar zuciya ya ce "A gaskiya mu
aljanu girmanmu da karfinmu duk ya zama na banza, tunda ga shi har kullum bayi mu ke ga
bil'adama. Ka dubi duk irin hadarih da mu ke shiga don kawai mu biy mu "Biya hrusu
bukatunsuwanda koyaushe za mu iva rasa rayukaniu, amma a Rarshe sakamakonmu bava
wuce a shayar da mu jini. Na sha tunanin hanyar da zan bi na iya sarrafa bökayen duniya ya
zamana ni zan bayar da umarni ba dai a ba if ba amma na kasa samun nasara." в ова вy uda
inew ad

eb

UC BW Ko da jin wannan batu, sai aljani Nargaz ya kyalkyale da dariya ya ce Va de Animata ka
bahi mamaki, to yaushe aka haife ka ma har da za ka ył Kukan gajiya da bauta wa bil'adama?
Dududu shekarunka ba za sú haurà dubu daya da dari hudu ba, ni fa yau shekarata dubu
ashirin da aku a doron kasa. Tun ina shekara tara nake bauta ga bil'adama, sar musaya ta ake
kamar yadda ke musayar rigar sawa. Idan aka auna ni waccan nahiyar, sai a maida ni wata
nahiyar ta duniya. Kaf kasashen duniya babu inda ban je na yi bauta ba, na zauna da bokaye a
kalla guda dubu dari shida da saba in da bakwai. A kwai wani gidan sarauta da na zauna
tsawon shekara dubu biyu îna yi masu bauta, run iyayel da kakanninsu har sai da tattaba
kummensu suka gaje ni. A Karshe dai zamani ne yasa dole na guje su dornin wadansu
kangararrun mutane ne suka ci kasar da

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login