Showing 1 words to 3000 words out of 26600 words

Chapter 1 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf

WANKA DA GARI...


©FATIMA SUNUSI RABI'U
Ummu Affan


*Fatan alkhairi ga ƙanwata ta gaban goshi Dr Maryamah Ibrahim Sokoto, ina miki fatan alkhairi
a ko da yaushe, Ubangiji Allah ya baki miji na gari ya albarkaci rayuwarki.*

_Gargaɗi da babban murya, ban amince a ɗaura mini littafi a ko wacce kafa ba, musamman
masu youtube channel kar a fara ba tare da izinina ba, duk mai buƙata ya mini magana a
dukkan littafina ina ajiye lamba, don Allah kar a fara domin bazan lamunta ba._


*Book 1 Page 1-2*


_Unguwar Rimi Kaduna State._
_2015_

Zaune ta ke a gefen makeken gadonta hawaye ne wasu ke bin wasu a kan kyakkyawar
fuskarta, ta ra sa dalilin me yasa Abban Yusra ke mata wulaƙanci, rabon da ta gan shi yau
kimanin wata biyu kenan. Me ya ke nufi da irin wannan wulaƙancin na rashin kwana gida?
Wayarta da ke gefen gado ta ɗauko, lambarsa ta danna wa kira, ringing ta ke amma har ta
ƙarati ɓurarinta ta gama ba alamun za'a ba ta agajin gaggawa, kira na biyu ma haka tayi sai a
na uku ya ɗauka. Tun kafin ta maganantu ya riga ta cewa, "Waike wacce irin mayya ce? Na ce
ki daina kirana amma kin ƙi! K so ki ke sai na saɓa miki?" Cikin sanyin murya ta ce, "Haba Abban Yusra me ya sa ka ke mini haka? Kar fa ka mante da
Sakinarka ka ke magana."
"Sakinaa ki kiyaye ni tun kafin ranki ya ɓaci." Ya furta a ƙufule.
"Tun yaushe kuma? ai raina tuni ya ɓaci, ka tausayi mini Habibi."
Dogon tsaki ya ja tare da yanke kiran.
Miƙewa Sakina tayi cike da ɓacin rai, A fili ta furta "Me ke shirin faruwa da ni? Me na maka ka
ke son ramawa ta wannan hanyar, wanne irin zunibi ke bibiyar rayuwata har haka?"
Mayafinta da key ta zara tayi waje da sauri, moto ta ɗauka tayi mata key ta fita a sittin har Baba
Maigadi na cewa,
"Yau me ke damun uwar ɗakina? Duk inda zaki Allah ya kai ki lafiya."
Kai tsaye gidan Hajiyar Abban Yusra ta nufa, tana zuwa tayi hurn me gadi ya buɗe mata
katafaran gate ɗin gidan ta tura hancin motarta. Guri ta samu tayi parking sannan ta fito, ƙofar
da zata sada ta da parlourn gidan ta nufa, tana shiga ta iske Hajiyar Hamshaƙe kan ɗaya daga
cikin kujerun alfarma da sukawa parloun ƙawanya. Ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana wani
jujjuya su alamar ji da kai da kasaita irin ta jinin sarakuna.

Sallama tayi Hajiyar ta amsa kamar me ciwon baki.
Har ƙasa ta duƙa ta na ƙoƙarin gaisheta, hankali ta amsa.
Cikin sauri Fatima ta ɗago ta kalleta da ta tuna yadda Hajiyar ke ƙaunarta, idan kuwa tazo gidan
tayi ta nan-nan da ita kamar ta goyata don so, ai kuwa dole ta sha mamaki ganin yadda yau
Hajiyar ta tarbeta.
"Daman Hajiya wajenki nazo."
"Ai gani kin ganni, ko namujiyarki sun fara makancewa ne?"
Hajiyar ta furta cike da gatse.
Sakina ta ɗaura da cewa, "Kiyi haƙuri daman nazo ne don Allah ki tambayi Abban Yusra ko
wani laifin na masa ni na tambayesa yaƙi sanar da ni ga shi sai wulaƙanta ni ya ke."
"Ai daman ke abin wulaƙantawa ce, to mene ne a ciki domin ya wulaƙanta ki? Nifa ban cika son
yawan kawo ƙara ba, sannan kin fi kowa sanin farin cikin ɗana shi nake so fiye da komi a
duniyar nan."
Sakina ta kalli Hajiyar cike da mamakin jin furucinta, zata iya rantsuwa akan tunda ta ke ba ta
taɓa kawo wa Hajiya ƙarar Abban Yusra ba amma ta ce haka.
"Allah ya huci zuciyarki idan na ɓata miki rai." Sakina ta furta cikin sanyin jiki, tabbas da walaki
goro a miya, domin dai ta san ruwa ba ya tsami haka banza.
Cike da masifa ƙufula ta ji muryar Hajiyar a massarafar sautinta.
"To idan mafarki ki ke ya kamata ki farka Sakina kuma idan baki sani ba ma yau ki sani, wannan
yaron dai aure ya ƙara yau kwana biyar suna ɗayan gidan shi.
Da sauri Sakina ta miƙe, tabbas a rina kafin a kiɗime ta furta,
"Aure! Aure!! kuma?"
"I aure, ni ce na ce karya sanar miki da kaina zan sanar da ke, saboda mugun ɓakin halinki da
zafin kishinki. Yanzu dai tunda an ɗaura kin ga ba yadda kika iya da shi, shekara har nawa ku
ke tare ai ya miki adalci."
Zaman 'yan bori Sakina ta tsinci kanta da yi kafin ta ƙaƙalo murmushin yaƙe,
"To ni a suwa? Wai ɗan wake da gatsine, ban da abin ku mane ne na ta da hankali ko da an
sanar da ni?"
Tsaki Hajiya ta ja 'Mtsuuuww!' Tare da furta, "Idan ma zaki da mu, ke ki ka sani don nasan
shegen baƙin kishinki na tsiya da gado."
Miƙewa Sakinaa tayi domin muddin tana ci gaba da sauraran waɗannan muyagun kalaman na
Hajiya, to za a iya haihuwar guzuma, uwa a kwance 'ya a kwance.
"Ni zan wuce saboda su Yusra sun kusan dawo
makaranta."
Taɓe baki tayi tare da kau da kai.
"Umma ta gaida assha."
Sakinaa ta fita da sauri ta shiga mota, kai tsaye ɗayan gidan Abban Yusra ta nufa, tana zuwa
tayi parking a bakin gate ɗin gidan ta fito tare da ƙwanƙwasa gate ɗin gidan.
Maigadi ya leƙo yana cewa,
"Wane ne?"
Ganin matar Oga ce ya yi saurin zubewa yana kwasar gaisuwa, kasancewar ya santa sosai, a
baya suna zuwa gidan kafin su fara samun matsala da shi. Ta amsa tana ƙoƙarin shiga ciki.
Sosa ƙeya ya yi, "Am...am..ma Hajiya kamar ya fita." Ya faɗa muryarsa na ɗan rawa,

kasancewar ya ba shi umarnin kar ya bar kowa ya shiga gidan. Ko kula shi bata tsaya yi ba tayi
gaba.
Shigarta ke da wuya ta iske su kwance kan doguwar kujera, sallama ta masu gaba ɗaya suka
juyo. Sakinaa ba ƙaramin furgita tayi ba, ganin wacece Amaryar, wacce ke kwance kafaɗar
Abban Yusra, hakan ne ya ƙara tabbatar mata ita ce amaryar da ya yi.
Ba kowa ba ce Amaryar fa ce Aminiyarta ƙawarta ta ƙut-da-ƙut Zaliha. Nunata ta rinƙayi da
hannu bakinta na rawa, cikin rawar murya ta ke cewa,
"Zal...Zali...ha daman ke ce Amaryar Abban Yusra?"
Zaliha ta tashi cike da taƙama da gadara, "Ni ce sai me? Ko haramun ne aurena da shi domin
kina ƙwata?"
Sakinaa ta ce, "Tabbas buri yana kama da mutum, amma Zaliha kin yi kuskure. To bari kiji baki
isa ba kuma kin yi ƙarya ki ce za ki yi kishi da ni, ni nafi ƙarfinki wallahi sai kin ga ne
kuskuranki."
Wani farr da ido Zaliha tayi kafin ta ce, "Sakinaa ke ce zaki ga ne kuskurenki ba ni ba, domin
ke ce ki ka yi kuskure a rayuwa ni nan da kike gani da yar dar iyayena na auri Abban Yusra ke
kuwa fa? Kin ga ke kin zaɓi farin cikin zuciyarki a kan faranta ran iyayenki, kin ƙi bin umarninsu
daga ƙarshe ki ka guje su, ke kina tunanin za ki ga farin ciki a rayuwarki?" Wasu zafafan hawaye suka gangaro kan fuskar Sakinaa, ta kalli Abban Yusra.
"Ka na jin irin munanan kalaman da take bina da su ko. Amma kayi shuru?"
Shi ma miƙewa ya yi ya furta.
"To me zan ce? Me ma ya kawo ki gidan nan? Ke wacce irin natacciyar mace ce haba abin naki
wallahi ya fara isa ta haba!" Ya ƙarashe da ƙaraji.
Da sauri ta kalle shi na mujiyarta jawul kamar jan gauta.
"Ni ka ke furtawa irin waɗan nan munanan kalaman? Babban Yusra Sakinaa ce fa?" Ta ƙarashe
da shassheƙar kuka.
Dariyar ƙeta ya yi, "To abin da yaci doma, ai ba zai bar awai ba. ko kin wuce a furta miki haka
ne? Wallahi gab nake da furta mummunar kalma ki a kan ki." Ya kama hannun Zaliha.
"Mu wuce ciki ko na san idan kina kallonta ranki ɓaci zai yi."
Ta langwaɓar da kai "My ni fa nafi son mu koma can gidan da Sakinaa take yafi mini, ga shi da
girma kuma."
"Duk yadda ki ka ce haka za a yi tawan, ki bari anjima sai mu wuce ko?"
Sakinaa ko saboda tsabar baƙin ciki da takaici fita tayi a fusace ta shiga motarta tayi gida,
Allah ne ya kai ta lafiya amma tuƙi kawai take idanuwanta na rufewa, tana zuwa ta faɗa kan
kujera ta saki wani rikitaccen kuka tana faɗin..
"Na tuba Abba da Umma ku taimaka ku yafe mini, nasan haƙƙinku ne ke bibiyata ga shi wanda
na zaɓa a kan ku yana wulaƙan ta ni ya guje ni.
Ta ƙara fashewa da kuka, na tsantsar baƙinciki da takaici ga kuma damuwa.
Tana cikin wannan halin sai jin muryar Hajiya tayi da ƙarfi tana cewa,
"Ɗiyar matsiyata wacce ubanta ke yawo kullum cikin rana sai ka ce a kan shi talauci ya ƙare."
Sakinaa tayi saurin miƙewa tsaye, cike da jin zafin kalaman Hajiya ta ce,
"Duk abin da zaku mini daga ke har ɗan ki kar ku kuskura ku sake cin zarafin iyayena, domin ba
zan taɓa yadda da hakan ba."
Hajiya ta riƙe ba ki, "To fa, tabbas da sauran rina a kaba. Rashin kunya zaki mini mara mutunci,

ke kin san mutuncin iyayen naki ne zaki ƙi bin umarninsu ki ƙi musu biyayya akan abinda suka
zo miki da shi?"
Sakinaa wucewa ta yi domin bazata iya sauraron waɗannan munanan kalaman na Hajiya ba.
Ita kuwa Hajiya taci gaba da sababinta, sai zagin Sakinaa take da iyayenta, daga ƙarshe ganin
taƙi biye mata sai ta kira wayar Abban Yusra ta saki kuka, "To wannan yaron kazo gidanka
yanzu ga Sakinaa nan sai zagina ta ke kamar zata rufe ni da bugu." Sakinaa na daga ɗaki tana
jin ta sai dai girgiza kai kawai tayi tana matsar hawaye. Hajiyar zama tayi a parlour tana jiran ƙarasowarsu, domin Zaliha ce ta kirata cewa Sakinaa taje
gidansu, tare da faɗa mata ƙarya da gaskiya, shi ne dalilinta na zuwa gidan. Ko minti ashirin ba
ta cika ba sai ga su. Hajiyar sai kukan ƙarya ta ke suka isketa, kai tsaye bedroom ɗin Sakinaa
ya nufa, yana zuwa ya fara bugun ƙofar kamar zai ɓallata, da ya ke ta saka key. Faɗa ya ke, "Ba za ki zo ki buɗe ba sai na ɓallata?"
A hankali ta tashi taje ta cire key ɗin da ta saka. Aikuwa tana cirewa ya turo ƙofar ya rufeta da
bugu daman da belt hannunsa, kuka take da ihu amma bugunta yake su Hajiya na gani sai ma
zuga shi da take, sai da ya mata ligi-ligi sannan ya barta kwance.
Da ƙyar Sakinaa ta iya jan jikinta ta shiga toilet ta gasa jikinta tana kuka, bayan ta gama ta
ɗauro alwala ta fito ta canza kaya, tayi sallar azhar da ake kira sannan ta kwanta nan ta ke
barcin wahala ya kwasheta.
Wajen ƙarfe biyu na rana ta fara jiyo hayaniyar su Yusra alamar sun dawo makaranta, ta tashi
da sauri. Fahat ne ta ga ya shugo yana kuka.
"Babana me yasa me ka." Ta tambaye shi a rikice.
"Yunwa na ke ji Mami"
Tayi saurin miƙewa domin ta man ta sam bata ɗaura musu abinci ba, ta nufi kitchen domin
ɗaura musu girkin, bayan ta gama duk abinda zata yi ta tsayar da ruwa, ta fito taje tayi musu
wanka ta canza musu kananun kaya, ta rungume Fahat da har yanzu yake kukan yunwa, domin
ba shi da juriyar yunwa, sai rarrashin shi ta ke. Suna haka Abbansu ya shugo ya iske su. Yusra ta ruga da gudu ya caɓata sama ya rungume yana dariya.
"Oyoyo Abba."
Shima Fahat ya taho yana ƙunƙunai, ya ce"Me ke damun Fahat ɗin Abba?"
"Yunwa na ke ji Abba kuma Mami ba ta gama girki ba."
Miƙewa ya yi tsaye ya kama hannun yaran sannan ya gallata mata wata muguwar harara.
"Ku tashi muje gidan Hajiya muci abinci ko."
Yusra ta ce, "Abba Mami ta shirya muje da ita?" Kasancewar ada tasan idan har zasu fita to
dukansu suke fita.
Ya ce, "A'a Mamana kin ga Mami na aiki."
Fahat ya ce, "Amma zamu yo bata take-way ko Abba?"
"I."
Kawai ya amsa musu suka wuce.
Hawaye kawai Sakinaa taji suna kwarara a fuskarta, lallai ɗan adam butulu ne domin yau ga shi
Abban Yusra ya yi mata butulci haka ƙawarta mafi kusanci da ita Zaliha, me yasa taƙi bin
umarnin iyayenta? Sai yau ta tabbatar lallai tayi gudun gara ne, ta faɗawa gidan zago.
Tashi tayi ta nufi kitchen domin duba abinda ta ɗaura, me zata iske? Zaliha ta gani ta sauke
mata girki tana yin nata a wajen bayan kuma gas ɗin ba ɗaya ba ne.

"Zaliha me yasa baki neman zaman lafiya?" Zaliha tayi shewa tare da buga cinya ta ce"Lallai
Sakinaa ke zaman lafiya ki ke so ayi a gidan nan? Ai ba ke ba zaman lafiya a gidan nan, nayi
alƙawarin sai na ƙuntata rayuwarki."
"Ke ba ki isa ki ƙuntata mini ba kuma ina son ki sani, ai wanka da gari ba shi maganin yunwa sai
an sha kuma na san duk wani hali da zan shiga daga Allah ne.."
Tana kammala faɗar hakan.......
08104335144



#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina_Gawurtattu uku 2024_


WANKA DA GARI...


FATIMA SUNUSI RABIU
Ummu Affan


*Book 1 Page 3-4*

Tana kammala faɗar hakan tayi wucewarta, daman saboda yaranta za tayi girkin kuma sun fita
da Abbansu faƙat.
Zaliha kuwa taji haushin kalaman Sakinaa don haka ta ɗau alƙawarin sai ta yi wa Sakinaa
sharrin da sai tayi da na sanin abinda ta faɗa mata.
Ko da su Abban Yusra suka dawo Sakinaa ko leƙowa ba tayi ba, yaranta suna shugowa tayi
sauri ta musu shirin islamiyya ganin lokaci ya kusan ƙurewa sannan ta rakasu har gurin Direban
da ke kai su makaranta.
Tana dawowa daga rakasu ta iske Abban Yusra da Zaliha a farlour, za ta wuce bedroom taji
yana kiranta. Tsayawa tayi ba tare da ta juyo ba, bai damu da yadda tayin ba ya ce,
"Tun da kin hana Zaliha ta dun ga shigar miki kitchen sai ka ce ke ki ka gina sa? To daga yau ke
zaki din ga mata girki duk abinda take so za ki dafa.
Da sauri ta juyo ta kalli Zaliha cike da mamakin jin irin sharrin da ta mata.
"Haba Abban Yusra yan zun ni ce zan zama mai girkin Zaliha sai ka ce wata 'yar aiki, ai ba abin
da ka ɗauke ni kenan ba."
"To da me ki ka dace? Ai wallahi yafi kyau ma a ki raki da 'yar aikin don matsayinku guda ne
yanzu a wajena." Ya faɗa yana wani hura hanci.
"Shi ke nan." Tana faɗa ta wuce ba tare da ta kuma cewa komai ba.
Tun daga ranar Sakinaa ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta zamo ita ke yin komai na gidan duk Zaliha

tasa ya kori 'yan aikin gidan Baba Maigadi kawai aka bari sai Direbansu Yusra, hatta wanki da
guga ita ce. Daman tana wanki idan ta so, haka ba ko wanne kaya take bayarwa ba, guga kam
tana ci mata rai.
Yaranta Yusra da Fahat Zaliha ta ɗau ɗawainiyarsu sosai take kula da yaran, shirinsu zuwa
School da islamiyya haka fannin abincinsu ba ta wasa, ko a da can Zaliha me ƙaunar yaran ce.
Hajiya kuwa kusan kullum sai tazo gidan tayi tawa Fatima tujara da habaice-habaice, tayi ta
tsine mata ita da iyayenta, wani sa'in ma su ukun suke haɗuwa suyi ta mata rashin mutumci da
tujara, maƙaƙen maganganu kuwa tana shan su da gori.
Fatima ba ta da kwanciyar hankali wuni kuka, tayi duhi ta jeme tayi baƙi sosai ta rame kullum
cikin kuka take saboda tsabar wahala da baƙin ciki.
Wata rana tana zaune a kitchen tana aiki ta jiyo muryar Hajiya na kiranta, tashi tayi da sauri har
tana tuntuɓe ta zube a gabanta.
"Hajiya ashe kin zo barka da zuwa."
Hajiya ta daka mata tsawa, "Ya isa haka, yau dai zamanki yazo ƙarshe a gidan nan." Sakinaa ta
kalli Hajiyar da sauri ta ce, "Me nayi kuma Hajiya? Ki rufa mini asiri na mutu maza su kai ni, don
Allah kar ki tozarta ni, idan ba ki kalle ni ki duba su Fahat."
Zaliha ta taɓe baki, "Ƙwarƙwasa raka kishiya biki, yau dai ƙarya ta ƙare sai a koma gida aci
gaba da cin tuwon dawa miyar kuka daman da shi aka raine ki."
Hajiya ta ce, "Hakkun kuwa sai a gaida me dattin hula, da mai baƙin ɗanƙwali." Zaliha ta saka
dariyar mugunta tare da buga cinya, "A koma can idan ma ya amsheki idan kuma ya ce abi
duniya ne to ai gaki gata maraba take da waɗanda ma suka fiki, ke duniya wanda bai zo ba ma
jiransa take." Tuni ruwan hawaye suka tsinke a fuskar Sakinaa Hajiya ta ce, "Wannan yaron inaso ka sallame
ta, idan kuma zaka ci gaba da zama da ita to, ni dai naga rabuwarku tafi."
"Hajiya duk abin da ki ke so haka za a yi." Numfasawa tayi "A'a kar ka ce na shiga haƙƙinka."
Takarda da biro ya ɗauko ya yi rubutu ya cillawa Sakinaa yana faɗin, "Ko ɗaya Hajiya ai na
yadda ƙwallon mangwaro ne na huta da ƙuda." Ɗauka Sakunaa tayi ta buɗe a hankali saki ɗaya
ta gani.
Hawaye ne suka wanke fuskarta kallonsu tayi, sai kuma ta miƙe tsaye ta wuce.
Beedroom ɗinta ta shiga, ta faɗa toilet wanka tayi sannan ta fito, ta shirya cikin wasu riga da
siket na atamfa sannan ta sauke ƙaton akwatinta ta zuba kayanta da duk wani abu mai
muhimmanci nata, ta zuba takardun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login