Showing 1 words to 3000 words out of 17980 words

Chapter 1 - MAKIRAR MACE COMPLETE BY Yellow .pdf

Yellow   

28 Jul 2025

1074

MAKIRAR MACE
1.Ranar biyun sallan Azumi, akan hanyar Suhaima ta zuwa ziyarar 'yan Uwa na sallah, chan tacikaro da
wani matashi mai tallen Zuma, yana tafiya yana cewa, "Pure Honey! Pure Honey"!! Har bayan mai tallen
ya gifta, Suhaima ta waiga ta ce, "mai Zuma"! A take ya tsaya ya juyo, Suhaima ta ce "barka dai, ya
kasuwa"? Mai tallen yace "mungode Allah". Suhaima ta ce, "amma ka tabbata zuman nan pure ce"? Mai
tallen yace "ai ko shakka banayi" Suhaima ta ce, "to gashi kuma ni yanzu na fito ne, zanje unguwa, amma
bari na kwatanta maka wani gida da zaka kayi sunaso zasu siya", mai tallen yace "to"! Suhaima ta ce,
"idan ka fita kan babban layin nan, zakaga wani gida mai Jan fenti yana da baƙin gate, sannan kuma
akwai nau'ikan flower sosai a gaban gidan", lokaci guda kuwa akayi dace, mai zuman yace "eh nagane
gidan". Suhaima ta ce, "to idan kaje kayi knocking, idan mai gadin ya buɗe, sai kace masa Suhaima ce
taturoka, sai kabuƙaci yayi maka magana da cikin gidan ko"? Sannan Suhaima taƙara dacewa, "shi sunan
mai gadin gidan Goje", mai tallen yace "to nagode fa". Suhaima ta ce, "bakomai" suna masu shauƙi suka
rabu. Suhaima tawuce ziyarar da zata, shima mai tallen zuma yatafi gidan, da isarsa yayi Knocking gate
kamar yanda Suhaima ta faɗamasa, bugawa ɗaya yayi a ƙofar gate ɗin kuwa, sai ga mai gadi yana cewa
"waye ne"? Mai tallen zuma yace, "mai tallen zuma ne", sannan yaƙara da cewa, "Suhaima ce taturoni",
atake sai mai gadin ya buɗe. Shigar da mai tallen zuman zayyi sai yaga Goje da hular ƙauraye sanye a
kansa ya karkatata, mai tallen Zuman yayi sauri ya sauke ƙwaryayen zuman da suke kansa, sai kuwa
yamiƙa hannu ya damƙo hular kayin Goje yace dashi "Kai ƙauran mata", cikin ɓacin rai shima Goje ya
kayi damƙa a hular datake kayin mai tallen Zuma, Goje yana taɓata sai yaji hannunsa kamar anchokamar
allurai, da sauri ya sake yakama hannunsa yana mai cewa "wayyyo" Goje har ƙasa ya kwanta yana rike da
hannu, daga bisani mai tallen zuman yamiƙa hannu yaɗan riƙo hannun Goje yajijjiga, sannan yajanyoshi
yamiƙe, mai zuman yace da Goje "ya to"? Goje yace "bari kawai, dama cikin gidan sun san da zuwan
kane"? Mai tallen zuma yace "a'a", Goje yace "to bari na shiga na sanar dasu", mai tallen zuma yace
"Chau"! Goje ya shiga ya fito ya tarar da mai zuma na zaune akan bencinsa, ganin fitowar Goje yasa mai
zuma yaɗan zakuɗa yace "ga guri fa", sam Goje yaƙi yarda ya zauna, ya ɗan tsaya daga gefe chan, yace
"Alhaji yana fitowa". Bayan wasu 'yan daƙiku sai ga Alhaji yafito daga cikin gida, da Alhaji yaƙariso, ranar
yaga kayin Goje babu hula sai uban malu da yaketa yalƙi a kayin Goje, cikin mamaki Alhaji yace "Goje yau
kuma ina hular ƙaurayen, ya akayi yau kuma naga babu ita"? Goje yace "rankaidaɗe akwai wani tsumin
dana keyi a kayin ne, hula bazata zauna akaina ba yanzu". Alhaji sai yayi dariya yace "SA'A dai". Daga nan
ya buƙaci "abuɗe masa zumar yaga irinta"? Mai tallen zuma yaɗaga faifayin da yake kan kwaryar zuman
yace "ga irinta". Alhaji ya gani yaduba sosai, har aka kaiga ya taɓa yaji babu mix. Wannan yasa Alhaji
yabuƙaci siyan ƙoren zuman duka, mai zuman yace "to, yanzu dai ƙwarya biyu ne, suka rage", Alhaji yace
dashi "aiko da sunfi ƙwarya biyu ma zan siyesu, domin naga zuman Pure ne, don haka kawai nawa zaka
siyarmin"? Mai Tallen yace "ko wace kwarya kabayar dubu goma"? Alhaji cikin mamaki yace "amma ya
akayi zuma mai kyau irin wannan tayi sauƙi sosai haka"? Mai tallen yace "sabida Allah yana son masu
sassauci". Alhaji yace "wannan hakane magananka", Alhaji yaƙara da cewa, "amma kai mutumin inane"?
Mai tallen yace "ni a Dokaddaji nake", batare da Alhaji ya fahimci inane Dokaddaji ba, yaƙara dacewa,
"amma ya sunanka"? Mai tallen yace "sunana, Affan". Alhaji yace "to inaso kana kawomin zuma akai
akai". Affan yace "duk sati ne nake shigowa cikin gari". Alhaji yace "to inaso duk sati idan ka shigo kana
kawomin". Daga nan Alhaji yace da Goje "ya ɗauki zuman yakayi cikin gida ya bayarwa Hajiya tajuye ya
kawo a Affan ƙorensa". Goje yamiƙe ya ɗauka, shima Alhaji yabi bayan Goje suka shiga, Alhaji yawuce

parlorn sa ya shiga ya ɗauko kuɗin zuman Affan, da yazo ya mikawa Affan naira dubu hamsin 50,000,
cikin mamaki Affan yace "Alhaji wannan fa, na miyene"? Alhaji yace "na kane", Affan ya sauƙa a benchin
da yake zaune yafara godiya, Alhaji yace "karkadamu domin Allah yanason masu Kyautatawa, kasa a
ranka sassaucin da kakeyiwa mutanene yajawo maka, kuma indai zaka ɗaure akan haka, to tabbas
watarana kanatare da nasara insha Allah. Sabida haka kagodewa Allah". Daga ƙarshe Alhaji yace da Goje
"miƙamasa ƙorensa", Affan yakarɓa sukayi sallama da yarjejeniyar wani sati zaidawo yakawo musu zuma. By Sagiryellow ✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
2.Bayan Affan ya fita a gidan, akan hanyarsa ta komawa gida, sai murna yakeyi ya samu babban
customer. Wannan yasa daya koma gida, batare da ɓata lokaci ba, ya ajiye ƙorensa ya shiga chancikin
Dokaddaji domin duba taburman da suke naɗawa domin tara zuma. Affan yadage sosai a cikin wannan
satin, domin yana buƙatar ya tara zuma mai yawa sosai sabida samu ƙarin babban customer, cikin iKon
Allah kuwa Affan ya dace ya samu zuma sosai. Wayewar garin ranar talata tunda wuri Affan ya gama
haɗa kayansa yatattara, ya kama hanyar garin Dambuwa dake Jihar Borno. Kamar yanda ya kasance
tanacin kasuwa duk ranar talata, amma kasancewar irin yanayin kayan nauyi da Affan yaɗauko ya
banbanta dana kullum, wannan yasa baisamu isowa cikin gari a lokacin daya dace ba, har sai ana azahar.
Da isaarsa kuwa, ya fara zuwa ta gidan da Goje yake aiki, yaje yayi Knocking batare da ɓata lokaci ba,
Goje yazo shi yabuɗe, ya tarbi Affan hannu bibbiyu, sannan yace "bari na shiga nayi maka magana da
Suhaima". Affan yace "to"! Goje ya shiga cikin gidan suka fito tare da Suhaima, da taga Affan ta ce, "Kash!
Gashi kazo kuma Alhaji bayanan". Affan yace "badamuwa ai zaku iya ɗauka ku ajiye masa kafinnan zanje
nadawo". Suhaima ta ce, "to badamuwa taɗauki ƙwaryan zuman ta ce, dashi "to sai kajuyo". Affan ya
tashi ya fita, daga bisani sai Goje ya tashi ya buɗe ƙofa ya leƙa yaga lallai Affan baya kusa, sai yajuyo yace,
"Suhaima kinsan miye"? Suhaima ta ce "a'a sai kafaɗa Goje". Goje cikin tattausan murya yace "a gaskiya
ina kyautata zaton wannan mutumin ba mutum bane". Cikin gaggawa Suhaima ta ce, "subhanallah! Goje
ya dai? Miyasa kace haka"? Goje yace "to inko mutum ne, tabbas! Matsafi ne". Suhaima tace "wai miyake
damunkane Goje? Sai sarbaɗe kawai kakeyi". Goje yace "ba sarbaɗe bane, kinga dai duk irin yanda na
shirya kaina, kina da sanin raina in yaɓaci hatta kayan jikina wani lokaci har dagadaga sukeyi su yayyage
ko"? Suhaima ta ce, "eh! Hakane". Goje yaƙara da cewa "inba kimanta ba, Alhaji yataɓa siyamin Keke
watarana Iyalina taɓatamin rai na ɗauko Keken zan dawo nan Keken, takakkarye a hanya, ballentana
kuma mutum yace zai taɓa hular saƙi na, ke kinsani ranar babu zaman lafiya". Suhaima ta ce, "nikam dan
Allah Goje kafaɗamin dalili kawai kabar duk wannan dogon maganan". Goje yace "to wachan satin da
mai tallen zuman nan yazo, kai tsaye yasa hannu ya ciremin hular saƙi na akaina, sannan kuma ya
yamutsata ya sata a aljihu, kuma yakirani da ƙauran mata. Duk jarumta irin nawa a lokacin da nakai
hannu zancire masa hular saƙinsa shima, sai naji wasu allurai sun chokeni ajikin hular tasa, wanda ƙarshe
sai dana faɗi harƙasa. Bugu da ƙari, a yayinda Alhaji ya fito, bayan ya yaba da kyawun zuman sa, ya
buƙaci yaji shi mutumin inane? Sai yace da Alhaji shi mutumin Dokaddaji ne. A iya sanina shine, a
karkarar nan bamu da wani ƙauye mai suna Dokaddaji, sannan kuma bayyi kama da mutanen ƙauye
ba.Tunda aikin ganshi, ko kaɗan sam babu alaman duhun kai a tattare dashi, a waye yake sosai. Nifa tun
daga ranar da yatafi zuwa yau babu irin tsubbe tsubben da banyi ba, akan mutumin nan, domin ya gane
nima ba tayar baya bane, amma kin gashi rass dashi yadawo yau". Jin hakan yasa Suhaima ta ɗanja

dogon numfashi, sannan ta ce, "to yanzu dai abinda za'ayi akwai buƙatar idan yadawo muyi masa
cikakken bincike, domin musan koshi waye ne, inko bahaka ba, to ko nima zai iya jawomin matsala akan
aikina a gidan nan. Tunda kaga sanadiyata yafara zuwa gidan nan". Goje yabuɗi baki yace "kedai zaki
bincike shi, keda kikasan inda kikasamo shi, amma ni Goje to babu ruwana chan muku". Suhaima ta ce,
"haba Goje ya kana abu kamar ba namiji ba"? Goje yace "malama tsoro fa ya halal ne kinji ko"? Suhaima
ta ce "naji". Ana cikin haka sai ga Affan yadawo yana knocking gate. By Sagiryellow ✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
3.Take sai Goje yace "mai tallen zuma ne yadawo, ni nashige ɗakina kije kibuɗe masa". Suhaima ta mike
taje tabuɗe ƙofar, da taga Affan ta ce, "au mai pure honey ne"? Yace "eh!" Affan ya shiga, sannan
Suhaima ta koma ta zauna a benci, shima Affan tayimasa tayin wurin zama, ya amsa da cewa, "to!" Ya
zauna kuwa, sai Suhaima ta ce, "gashi kadawo kuma Alhaji baidawo ba", yace "bakomai", yaƙara da cewa
"ina ƙauran mata"? Suhaima ta ce, "Alhaji ya aikeshi". Daga nan ta ce, "nikam ranar muka haɗu, har
muka rabu Allah baisa na tambayi sunanka ba"? Yace "ayya ni sunana Affan". Suhaima ta ce, "Allah sarki,
amma kai mutumin inane"? Affan yace "ni daga Dokaddaji nake zuwa". Cikin hikima sai Suhaima ta ce,
"ayya kasan ni mace ce, bako ina nasani ba, Dokaddaji wata Jiha ce kenan"? Affan yace "nan ne cikin
Dajin Dambuwa muke", take zuciyar Suhaima ta tsinke, amma tayi ƙarfin hali tace "ƙauyen ku yana kusa
da ina kenan"? Affan yace "bawai ƙauye bane damu, kawai dai ni da Iyayena ne muke zaune a wurin".
Suhaima ta ce, "amma kuma ai bakayi kama da mutanen jeji ba". Affan yace "eh tabbas! Ni bawai anan
na tashi ba, asalin mu, mutaen ƙasar Sudan ne, Kakana wanda ya haifi Babana shi asalinsa mutumin
ƙasar Sudan ne, ana kiransa da Mai Dawa Sudani. Sakamakon ya ɓata shekara yakai hamsin yana aiki a
gidan Tarihi na ƙasar Sudan, wuri ne wanda ya shafe shekaru aru aru, wannan yasa wurin na ƙunshe da
tarihi kala daban daban, na abinda ya shafi dabbobi da mutane. A nan ƙasar Nigeria, zan iya misalta miki
wanchan wurin da Yankari Game Reserve, dake jihar Bauchi. A wanchan lokacin Kakana ya kasance shine
Vigilante Commander, na ɓangaren abinda shafi Dabbobin Daji, Kakana mai Dawa Sudani mutum ne
wanda yake da tsari sosai acikin lamuransa. Sannan kuma mutum ne mai tsayuwa akan gaskiya, dalilin
wannan yasa jama'a da dama suna yabonsa, ana cikin haka watarana sai aka kawo sabon In charge, a
Museum ɗin. In charge ɗin bayan ya shafe wasu watanni yana aiki, sai ya buƙaci suhaɗa baki da Kakana
Mai Dawa Sudani, akan ya naso zai sayar da wata Zakanya a wasu mutanen ƙasar Morocco, domin
Kakana ya basu haɗin kai wajen fita da Zakanyar acikin Meseum ɗin.A fita da Zakanyar da haɗin bakin
Mai Dawa Sudani, sam Kakana yaƙi amincewa, wannan yasa, In charge ɗin nan yafara yiwa Kakana wasu
irin halaye, irin wanda suka shafi raini. Sakamakon Mai Dawa Sudani ya kasance mutum ne, wanda
bayason raini, wannan dalilin yasa kawai rana ɗaya yace shiya ajiye aikin da yakeyi a Meseum na ƙasar
Sudan, a matsayin Vigillante Commander daga wanchan lokacin. Jin hakan yaɗagawa ma'aikata da dama
hankali, tare da sauran manyan mutane da suke faɗa aji, domin sunsan irin hidiman da mai Dawa Sudani
yayi. Wannan yasa sukayi iya ƙoƙarinsu akan ganin mai Dawa Sudani yadawo aiki, amma sam yaƙi
amincewa. Domin ran Mai Dawa Sudani yayi matuƙar ɓaci. Faruwar hakan shi yajawo hatta bishiyar, da
mai Dawa Sudani ya zauna a ƙarƙashinta a yayin shawo kansa da jama'a sukaita ƙoƙarinyi, daga bisani
bayan yatashi a wurin itama bishiyar ta bushe ƙaƙarau. Shine yasa yana dawowa gida kafin suje suƙara
haɗo masa mutane kawai yace dani da Gwaggona mushirya zamu ƙaura a wanchan yankin, sabida ga

abinda yafaru,wannan yasa muka kintsa bashiri mukafito bamu tsaya a ko ina ba, sai a Dajin Dambuwa
dake jihar Borno Nigeria. Sakamakon dama chan yace tun yana matashi suna zuwa farauta, wannan
dalilin yasa mukayi sansani a wurin, Bukkokin mu guda uku ɗaya nawa, ɗaya na Kakana, ɗaya na
Gwaggona, mukafara rayuwa a wurin, Idan lokacin damina ne, Mai Dawa Sudani yana zuwa yaciro Kaba
ya saƙa Malafa/Taburman Kaba/Igiya, duk ranar kasuwar Dambuwa sai muna kakowa muna sayarwa,
daga nan kuma sai muyi chefanen sati mukoma gida. Idan kuma lokacin rani ne, to sai mukoma sana'ar
sai da zuma. Ana cikin haka har tsufa tasa Mai Dawa Sudani yadaina zuwa cikin gari, sai nine kaɗai nake
duk wata ɗawainiya yanzu". Jin hakan yasa Suhaima taja dogon numfashi, sannan ta ce, "gaskiya kai ɗan
baiwa ne Affan, kuma kagaji jarumta". Affan yayi murmushi yace "to nikam dai inaso zantafi". Suhaima ta
ce, "to yanzu abinda za'ayi kabarmin sallahun zuman a wurina, in Alhaji yadawo zan bashi, sai nakarɓa
ma kuɗin ko zuwa gobe ma sai kadawo ka karɓa ko ya kagani"? Affan yace "to badamuwa Allah yakaimu
goben". Affan ya tashi yabuɗe ƙofa yafita, sai ga Goje yabuɗe ƙofar ɗaki ya fito, Suhaima ta ce, "ƙauran
mata ka fito"?
By Sagiryellow ✍️08060616515.
MAKIRAR MACE
4.Goje yabuɗi baki yace da Suhaima "zanci mutuncinki, kul! Wannan sunan ya fita a bakinki". Suhaima
tayi dariya ta ce, "da kenan, a yanzu babu wani cika baki da zaka ƙarayimin, dan hakama ni yanzu da
asalin sunanka zafara kiranka". Goje yace "ina rabaki fa", Suhaima ta ce, "Yakura dan Allah karkafasa
mutum sai shegen kurin banza". Goje kawai sai yajuya ɗaki, a take ya ɗauko bindigarsa barudu ya fara
koƙarin ɗurin harsashi, Suhaima dai tana tsaye tana ganin ikon Allah, ana cikin haka kenan, sai sukaji
horn ɗin motar Alhaji yadawo. Daga nan Suhaima tawuce cikin gida, bashiri tafara haɗo kan kwanikan da
aka karya kumallo, bayan ta wanke su tsaff, ta ɗaura dayin mopping ɗin duk wani wurin da yakamata
acikin gidan, batare da ɓata lokaci ba, Suhaima ta tsaftace komai yanda yadayace. Bayan nan ne,
Suhaima ta ɗauki sallahun zuman da Affan ya barmata ta nufi parlorn Alhaji kai tsaye, da isarta bakin
ƙofan falon, ta ɗan tsaya tayi sallama, sannan ta ƙwanƙwasa. Daga ciki, taji muryar Alhaji na cewa
"wa'alaikumussalam, waye ne"? Suhaima ta ce dashi "nice, Suhaima". Alhaji yace "to bismillah kishigo
mana". Suhaima buɗe ƙofar falon ta shiga, tana mai ɗan ɗari ɗari, taƙarisa gaban Alhaji ta ajiye masa
saƙon zuman da Affan yabar mata, sannan ta koma daga gefensa chan, ta ɗan durƙusa, ta ce dashi
"rankaidaɗe, wannan saƙone daga mai kawo maka zuma, sakamakon ɗazu yazo kuma bakanan, shine
yabarmin sallahu, akan inkadawo nabaka". Alhaji ya amsa dacewa "ba komai". Daga nan yamike ya shiga
asalin tirakarsa ya ɗauko kuɗin zuman yamiƙawa Suhaima, takarɓa tana mai godiya, tamike ta koma cikin
gida, tacigaba da sauran al'amuranta. Washagari kuwa bayan rana taɗaga sai ga Affan yazo karbar kudin
zuman sa kamar yanda sukayi alkawari, daya zoshi, ya tarar da Goje yanata ɗibar bacci akwance a benci.
Cikin hikima Affan yatashi Goje a nitse, har bayan Goje ya zauna, Affan yace "Goje yau lafiyarka kuwa
kaketa ɗimar bacci da hantsin nan"? Goje yabuɗi baki yace "wato kabari kawai Affan, yau na kwashe
aƙalla shekaru sunkai arba'in, bantaɓayin bacci na sama da minti arba'in ba". Jin hakan yasa Affan yaɗan
jijjiga kai, sannan yace "am Goje kaga ina kunyarka, don haka dan Allah mubar wannan maganan", daga
ƙarshe Affan ya buƙaci Goje yaɗan shiga cikin gida yayi masa magana da Suhaima mana. Goje yaki sam,
yace da Affan, "ni nadaina shiga harkar Suhaima", cikin mamaki Affan yace "mikuma yafaru, yasa kace
haka"? Goje yace "nafahimci Suhaima tana da rainin tsiya ne, nikuma a rayuwata natsani raini". Ana cikin

haka sai ga Suhaima taleko, da ta hangi Affan, ta koma ta ɗauki mayafinta ta yafa, sannan ɗauko kwaryar
da saƙon kuɗin zuman. Da ta fito, taƙariso tayimusu sallama. Goje ya haɗa rai yaƙi amsawa, Affan ne
kaɗai ya amsa, bayan Affan ya amsa suka gaisa da Suhaima, daga nan Affan ya buƙaci yaji abinda ya
haɗasu da Goje? Suhaima ta ce, "wai kawai dan nace shiba jarumi bane, sai dai ya zaɓa ko Ina cemasa
ƙauran mata ko kuma ina kiransa da Yakura? Tunda sunansa kenan". Jin hakan yasa Affan yayi dariya,
sannan yajuya yace "wai haka akayi ƙauran mata"? Goje yace "uhmm"! Affan yace "to aike kuma
Suhaima ba a haka, ko dan albarkacin hular saƙin da take kansa yakamata ki girmama hular ki kirashi da
Goje kamar yanda yakeso". Suhaima ta ce "to naji", tajuya taga Goje tace "dama kaci albarkacin hular
kankan nan ne da bazan ƙaracewa Goje ba". Shidai Goje yayi shiru kawai tamkar bayawurin, daga nan
Suhaima ta miƙawa Affan saƙon sa ta ce, dashi "ga alkawarin ka". Affan yasa hannu yakarɓa, yayi godiya
yasa a aljihunsa. Suhaima ganin Affan bai ƙirga kuɗin ba, kai tsaye yasa a aljihunsa, yasa tabuƙaci yaciro
kuɗin yaƙirga domin yin hakan yana da kyau ya lissafasu kafin yasaka a aljihunsa. Affan sam yaƙi, ƙarshe
ma kawai yace dasu "ni natafi sai wani sati", yafita yatafi. Bayan Affan ya koma gida, yaje yatarar da Mai
Dawa Sudani da Goggonsa suna zaune acikin bukkar Goggonsa, shima Affan ya shiga yasamu wuri daga
gefen Goggonsa ya zauna, Mai Dawa Sudani yafara da tambayar Affan "kai daga ina ne yanzun"? Affan
yace "ni daga Dambuwa ne". Mai Dawa Sudani yace "yau kuma ranar fashi, mi kajekayi a cikin gari"?
Anan ne Affan ya zayyane musu duk yanda akayi yahaɗu da Alhaji tun daga farko har zuwa yanzu, jin
hakan yasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login