Showing 1 words to 3000 words out of 13980 words

Chapter 1 - ZUCIYA DA KWANJI Book 4 End Complete Writing by MAIMUNA IDRIS SANI BELI .pdf

Zuciya d kwanji 4
1
Su kawu basu can dade da fita ba laila ta
shigo
falon nata, lokacin tana tare da maryam
kanwar
Abdullahi wadda ta gayyato da kanta bayan
su
safiyya sun koma gida domin ta dinga debe
mata
kewa tana kuma taya ta da ayyuka. Tun da
laila
ta shiga falon fatim ta dora mata ido babu
ko
kiftawa, kallonta take da fatar ido,
zuciyarta kuma
na tattaro dukkan mukaman zalinci da
ta'addanci
tana nada mata. A hankali kuma sai ta fara
kumbura kamar mai shirin fashewa, sai kila
idon
maryam ba zai barta ta fashe din ba. Laila
ta
zauna suka gaisa babu yabo babu fallasa
laila da

maryam, domin fadima ta dinke bakinta dif
sai
huci kawai take. Hakan yasa laila duk ta
diririce
ta ce. "Tun satin da ya wuce na sami labarin
fatima, ina ta kokarin in zo Allah bai nufe ni
ba".
Fatima ta ci gaba da binta da kallo kawai ba
tare
da ta tanka mata ba. Tsammanin maryam
duk
cikin ragowar kukan da ta gama gurza ne
dan
haka ta kasa tankawa laila. Maryam da ta ji
nauyin din shirun da fatima ta yi sai ta shiga
zancen, amma kafin ta yi sai ta shiga
zancen,amma kafin kalamanta su fito sai na
lailan suka riga nata fitowa da wani batun.
"Na yi
tsammanin ma kina gidanku,da har zan je
can
ashe kina nan". Fatima ta kara fakar idon
maryam ta bugawa laila harara. Maryam din
kuma sai ta sami gabar da za ta yi maganar
da

za ta hado da fatima. "Haba yaushe za su
tafi
gida su ba kananan yara ba, ko Aunty?" Dole
fatima ta yi murmushi da ya fi kama da
yake,kuma ta kawar da kai ta kara barin
maganar
ta bi ruwa. Can ma sai ta mike ba tare da ta
dubi
kowa ba ta doshi dakin kwanan ta turo kofa.
Ta
bar laila da sake saken hanyar da za ta bi ta
shawo kanta, ta fi kowa sanin wace ce
fadima da
shegen taurin kanta mai zafafa kiyayya
idan ta ki
kuma mara saurin yarda bare a gane abin
da ta
so. Daga karshe sai ta zabi mikewa ta bi ta
duk
kuwa da ba ta tanadi abin fada ba. Ta sami
fatima kishingide kan sofa bed,kuma
shigowar
lailan ta sanyata ta dago,kuma ta tashi
zaune
cikin fushi har ma ta riga ta magana. "Ina

tsammanin ba karuwancin kare kawai kika
gado
ba laila har da rashin zuciyarsa,ina kashedin
da
maigidan nan ya yi miki? Ni ina wulakancin
da na
yi miki? Ai ina tsammanin ko mutuwarsa kika
sami labari babu rawar kafar da za ta kawo
ki
gaisuwa ballantana da izinin Allah yana
raye....."
Laila ta yi saurin zama kusa da ita jiki a
sanyaye
ta dafa kafadarta. "Idan labari na samu
fatima da
kyar zan gasgata cewa ke ce kika zama
haka, ke
ce kike daga muryoyinki suke kare Abduullahi
maimakon Alh. Ke ce kike ihun fada min
bakan
maganganun duk tsawon shekarun da muka
dauka tare kin zubar da su...." Fadima ta
bige
hannunta ta mike tsaye tana huci. "Oh! Dan
kin

suffanta muryoyin nawa fili ne a gidan
radion da
mutum ke zuge jaka ya siye sai a sarrafa shi
yadda ya so? Takaici na kullum kara hawa
yake,musamman idan na fado irin wannan
shafukan da rainin wayo da son wawantar
dani.
Takaici na kullum kara hawa yake,
musamman
idan na fado irin wannan shafukan da
rainin wayo
da son wawantar da ni. Kar ki manta fa da
radin
kaina na amince hawa turbar da zan kuma
rayuwa da alh,babu wanda ya sami ko ya yi
min
jan ido. Idan dai da dalilai nake jin ya
kamata na
komawa Alh ya wajaba ne a yi min uzuri a
duba
dalilan ne idan na nemi janyewa. Kuma cikin
masu duba dalilan nawa ma bai kamata a
same
ki ba laila,dan na san in na janyewa
komawa

auren Alh ke tuni kin tattare hannun zani za
ki
shiga....." Laila ma ta mike suka jeru suna
kallon
juna kai tsaye, amma fuskarta cike da
damuwa,ko
dai ta karya ce, to za ta zauna daram a
fuskar
tata ta debo rawar baki ta ce. "Haba..... Don
Allah fatima...ki kori shaidanun da ke son
giftawa
tsakaninmu,ki tuna matsayina a wajenki ta
zarce
a iya kore duk wani abun alkairin baya,
kaunar da
na nuna miki duk tsiya da yadda sabanin ya
shiga
tsakaninmu ta wuce a ce kin debe min.
Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4
p2
Dukkan kauna.... Ni mai kaunar ki ce ki
dinga
tuna haka....." Yanzu hawaye fadima ta ke

sosai
kuma murya a raunane ta hau nuna ta tana
cewa.
"Wallahi laila tun da nake ban taba ganin
maci
amana irinki ba. A ina. Kika kaunace ni? A
kan
wa Alh dangin Alh dangina da Abdullahi
maganar
cikina kika nuna min kaunar ko a wannan
service
din da kika zamewa Alh?. Kar ki wawantar
dani
kin ji? Ba fa daga kauye aka lalubo ni ba. A
mafarki aka nuna min kina cikin masu
kaunata
sai na rsantse miki da Allah idan na farka
sai na
yi tofin korar shaidan da na tabbatar shi
yake
zuga ni amincewa da ke ki kuma cutata". Ta
kara
rushewa da kuka,sannan ta ci gaba magana.
Tsinanne ma irinki na taba gani a duniyata
laila,in

ta so da iyaye na shekaru aru aru basu taba
tir
dani ba sai da na hada sirri da ke, kika
mayar
dani suke min kallon hatsabibiya kuma
makaryaciya. To amma albishirinki, iyayena
ba
irin naki da na Haj. Sa'a ba ne,sun isa da
ni,
kuma na tarbiyantu da tarbiyarsu, ba. Sai
kin
dogara da na zubar da ciki ba, ba sai haj
sa'a ta
yi kurarin biyana kudi duk zan bar muku Alh
ba.
Cikin ruwan sanyi da umarnin iyayena zan
bar
Alh.haj sa'a ta aure shi ko ta aura miki shi
idan
ta so,dan na ga kun fini bukatarsa,dama
can ni
bai taba dada ni da kasa ba, ki je ki
tambaye shi
ki ji ba shi da abin da zai rude ni
wallahi....." A

dan rikice laila ta debo rauni za ta yi
magana,fatima ta tare ta cikin tsawa.
"Wallahi ba
zan ji komai daga gare ki ba laila, in kuma
kin
matsa sai na ji zan iya yi miki rashin kirkin
da zai
sa kila ki canja min suna, in je kawai na
yarda kin
yi nasara a kaina tunda kin hadani da
iyayen da
ban taba karbar ko harara daga gare su ba
sai ta
dalilin aminci da ke. Suka yi min birki daga
burina
na sake zama da Alh kuma na barku sannan
ki
aurenki ya yiwa haj sa'a kyau ko da bai yiwa
alh
ba,nima bai min ba. Sai dai ban taba saka
rai zan
bambamta daga jerin diyan mutunci ba kaf.
Alhamdulillahi cikina bai zube ba, watakila
daga
yanzu zan fara rayuwar da kika zaba mini".

Yanzu
laila ta fara yanke kauna da cewa fatima za
ta
saurare ta, amma duk da haka haka ta kasa
hakuri ta cire rai, a tausashe ta ce. "Ya
kamata ki
saurare ni fatima, ba ki san abin da ya kawo
ni
ba, amma kin zauna kishi zai hana ki
saurare ni,
ban da abinki fadima ina ni ina ajin Alh?
Ki....."
Fatima na tuno yadda ta ga laila da Alh a
bayan
mota sai ranta ya kara mugun baci,hakan ne
kuma ya sa ta nunawa laila kofa. "Na ce ba
zan
ji ki ba,in kuma akwai dole cikin jin naki sai
in
gani.... Malama ki bace min da gani". Laila
ta yi
saroro tana kalon ta, akwai alamar
hakurinta ya
kare don fuskarta ta baci sosai. Ta jima
tana

kallon fatima kallon na kamar ta rufe ta da
duka,amma babu hali. Kawai sai ta yi kwafa
ta
kada kai ta wuce ta bar fatima da bin ta da
dogon tsaki. ***************
***************
************ Tun a mota laila ta kira Alh a
waya
cikin zafin zuciya. "Alh ina muradin ajiye
wannan
aikin da ka ba ni". A dan rikice Alh ya ce.
"Ban
gane ba,domin me?" Ta shaki numfashi hade
da
takaici da ya cika makogwaro ta ja hanci ta
ce.
"Dan in tsira daga dabi'antuwa da halayyar
karnuka,ya kyauta ka dinga tunawa yadda
fatima
ta makanta ka ba lallai ni a ce na makantu
haka
ba, maganata gaskiya na gama shakar
iyakar
abin da zan iya...." A dan kufule da
sarkewar

numfashi ya tare ta. "Ki takaita
maganganun
bana son dogon surutu don Allah.... Sai
neman
kike ki fada min abin da ranki ke so..... Kar
ki
jagula min lissafi kin ji." Laila ta hadiye
ciwon
tsawa da na mayar da ita ba a bakin komai
ba da
Alh ya yi, ta tattare dukkan abin da za ta
iya na
jin zai fahimtar da shi ya kuma kawo
karshen
hannunta cikin lamarinsa da fatima ta ce.
"Idan
magana ta gaskiya zan fada maka ita ce,
fatima
ba ta ra'ayinka a yanzu na san fatima farin
sani
saboda haka ban taba daukar yada take
bijirewa
da wasa ba. Na san tana nufin abin da take
fada
har cikin ranta tsakani ta da Allah,ba zan

iya ci
gaba da wahalar da kaina ba,idan kana da
abin yi
kawai ka yi ni dai na zare hannuna....iyakar
abin
da zan iya ce maka kawai..." Alh ya sauke
wani
gwauron numfashi wanda ke cike da alhinin
tserewar fatima a bajad din rayuwarsa. Sai
dai
karfin hali na kwatanta masa fatima ta
shirya yin
biyu babu kawai, abdullahi kuma ya yi
alwalar yin
badi babu rai, matukar shi yana numfasawa.
Ya
jinjina kai cikin bacin rai ya ce . "Shi ke
nan,ban
taba tunanin yanke wa Abdullahi danyen
hukunci
ba, sai dai kamar ya zama dole tunda shi ya
zabi
hakan". A dan tsorace laila ta ce. "Me za ka
yi?"
Ya hura iska a baki ya fesar sannan ya ce.

"Zan
wanke kafa na bar kasar nan a yau ko
gobe,ma'aikatan da suka sakaya abdullahi
ma'abota biyayya ne, in na shekara goma
ban
dawo ba za su ci gaba da tsare min shi
shekaru
goma" Laila ta sauke numfashi kawai ba tare
da
ta tanka ba.
1 · Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4
pg3
******************************
************ Sai da
Abdullahi ya sami watanni biyu a tsare
sannan da
taimakon sagiru da irin zazzafan shige da
ficen
da yake sannan ya samu aka basu izinin
ganawa
da Abdullahi,shi da yayyen abdullahi biyu,
abdullahi da abdu wahab. Abdullahi ya fita
kamanninsa matuka,duk da cewa babu

mahalukin
da ke taba lafiyarsa da fatar jikinsa amma
yunwa
da takura na yara masa irin nasu harshen
sai ko
tsananin fargabar laifin da ake tuhumarsa
da shi
wanda har yau bai san shi ba. Tsoronsa Allah
tsoronsa kar q zarge shi cikin manyan yara.
To
shi ba dan kasuwa ba, shi kuma ba dilan
kwaya
ba, wanne laifin ya yi da za a masa wannan
kamun na rashin mutunci? Wuya ta sa
abdullahi
kallon yayyensa da sagiru kawai,ya kasa
amsa ko
sannun da gaisuwar su balle tambayoyin
neman
ba'asi da suke jero masa wanda shi ma bai
san
dasu ba. "Me ka yi abdullahi? Ka yi rigima
da
wani ne? Kudin wani ka ci bashi.....? Kalar
tambayoyin da yayyen nasa ke faman yi

masa ke
nan har da kwalla a idanuwansu. In ka
dauke
sagiru da bai tambaye shi komai ba tunda shi
dai
tuni ya san daga inda siyasar ta bullo. A
karshe
har lokacin su ya cika, sai a sannan jarumi
abdullahi ya motsa kwanjinsa dan tafiyar da
abin
da ke zuciyarsa cikin magana da hutawa.
"Yaya
don Allah a kular min da fatima,a sanar da
ita
ban laminci ta taka ko kofar gida ba, idan
lalurar
rashin lafiya ta riske ta a je da ita kar a
barta ta
ji da kanta.... Duk suka zubo masa ido da
duban
mamaki. Yayansa Abdulwahab ya gaji ya ce
"Wace ce haka? Abdullahi ya amsa cikin
kawar da
kai. "Amaryarsa da yayi baka gari". Sannan
matan naka a barsu su fita barkatai,kuma

in
larura ta kama su a barsu su ji da kawunan
su?
Babu kuruciya cikin maganar nan taka?"
Suka ci
gaba da dubansa su duka da alamun jiran
amsa,
shi kuma kai tsaye ya amsa. "Ta fisu
rauni,kuma
ta fisu hatsari". Duk suka kara tsira masa
ido,sai
dai babu wanda ya nemi karin bayani duk da
kuwa maganar tasa na bukatar fashin baki.
Suka
yi masa sallama bayan sun cika shi da
nasihar
tawakkali da mayar da lamari ga Allah,tare
da
ambatonsa cikin ko wanne hali.
***************
*************************** Bayan sallar
ishar
ranar abdulwahab ya kai ziyara gidan
abdullahi
cikin rakiyar babban dan wansa sahabi.

Hindatu
da sadiya tare da shi a falon Abdullahi yana
musu
bayanin da ke akwai game da Abdullahi,tare
da
jawabin kwantar da hankali. Har wani lokaci
bai
ga fatima ba, kasancewar kannen hindatu
sun zo
sun gaishe da shi, ya tambaya wace ce
amaryar
abu turab a ciki aka ce babu. Dan haka
yanzu da
kansa bayan ya duba agogo ya bukaci a kira
masa ita. Hindatu ta je ta sanar da ita
sannan ta
dawo. Can jimawa sai gata ta shiga a
nutse,tana
sanye da hijabi wanda bai iya boye cikinta
ba,
wanda a yanzu yake da watanni kusan
bakwai.
Sai dai babu abin da ya ragu cikin shan
kamshi
da kasaitar ta. Ba karamar kaduwa

Abdulwahab
ya yi da ganin fatima ba, dan sai da ya ya
maimaita sunanta a zuci lokacin da abdullahi
ya
ce........ A kular min da fadima. Sannan ma
ya
fara tantamar ce matar Abdullahi ko kuwa?
Cikin
wannan rudin ya dinga satar kallon ta har ta
rusuna ta gaishe shi. Ya amsa cike da alamun
mamakin sannan ya kama sunanta. "Fatima
ce?"
Ita ma muryarsa ce ta ja hankalinta ta
daga kai
sosai ta kalle shi,sai ta tarar da aminin Alh.
Ya
sha zuwa gidanta. Lokacin da take auren
Alh, Alh
ya rakito ta da kyar tana zuwa gaishe shi ba
tare
da fuskarta ta boye masa dole ta zo gaishe
shi
ba. Ta dade da sanin yanda Alh ke ji da shi
saboda yawan ambatonsa da ya ke. Ta amsa
ambaton sunanta da ya yi cikin hadiye

mamki ko
sanayyar dai cikin 'yan sakanni,ta girgije
ranarta
ta mike sosai ta zauna kan kujera. Amma shi
sai
ya kasa hadiye nasa mamakin ya ce. "Ya yi
aka
yi haka? Ke ce amaryar kanina Abdullahi?"
Ta
dan yi murnmushin mai kama da na dole,ta
kuma
kawar da kai ta bar tambayar ta sha ruwa.
Mamaki ya kara kashe shi, dan shirunta ya
tabbatar masa da cewa amsar ke nan,
lamarin ya
yi kama da almara. Ya jinjina ya kara
jinjinawa,
ita kuma ta girgije ta ki taya shi mamakin
har dai
ya sauke numfashi ya fara ba ta bayani.
"Mun
sami abdullahi dazu,kuma alhamdulillahi
mun
same shi da koshin lafiya,illa iyaka abin da
ba a

rasa ba. Sai dai shima bamu sami jin ta
bakinsa
ba na masaniya a kan kamun da aka yi
masa.sai
dai ba zamu kosa da yiwa Allah godiya ba,
komai
ma zai zo cikin sauki tunda dai an san inda
ya
ke". Fadima ta yi ajiyar zuciya kawai tana
kurawa
faratan yatsunta ido,har yanzu ba ta tanka
ba,
kuma babu alamu na za ta tanka din. Yaya
abdulwahab bai damu ba,dan ba tun yau ya
san
halinta na shariya ba ya kuma ce mata
Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4
pg4
"Ya bayar da sallahu a fada muku,duk wata
take
da bukatar fita idan ta taso ta tambayi
daya daga
cikinmu ko a waya ne.Amma ke ki yi hakuri

kar ki
fitar masa ko ina,idan yana da dalili mu dai
bai
fada mana ba. To sai ki yi hakuri ki kiyaye".
Ko
motsi ba ta yi ba bare alamun za ta
tanka,sai dai
fa ta cika taf! Da mamaki,wato duk halin
kuncin
da abdullahi ya shiga ba zai fasa motsa
kwanjinsa a kanta ba, ko da kuwa motsawar
kawai zai tsira ba tare da sun tasirantar ba.
Duk
da za ta iya karyata kanta cewa ba sa
tasirin
wanda su suka kawo ta matsayin da ta tsinci
kanta a yanzu,na yana ja tana ja.
Abdulwahab da
ya gaji da jiran cewar ta yana kuma so ya ji
ta
bakinta sai ya kuma kalato ta. "Sannan ya
ce ayi
miki sannu da jiki". Ta kokarta da kyar da
tarin
kwalla a idonta ta ce. "Na gode". Ta ci gaba

da
sharar kwallar wadda ta faru sakamakon
tuna.
Maraicinta da ta yi ta kowanne
bangare,kamar jin
jiki tare da rashn mai tattali da tausasan
kalamai.
Sannan ga jin jiki na rashin mataimaki a
ayyukan
gida, wanda take fama jar da na Allah ya
tsine,kuma duk a lokacin da ta fi bukatar
mai
caring din da kuma mai taimako da aikin.
Ta
dinga share kwallarta tana kuma
sharewa,abin da
kuma ya kara daure kan Abdulwahab ke
nan,Ya
shiga sassanyan nazarin da ya ke a kanta.
Da ya
kasa canka kawai ya cika su da kudi masu
kauri
ya yi sallama dasu ya fita. Ya tafi da
tsananin
mamakin yadda aka yi abdullahi ya samu

nasarar
auren wannan 'yar darun ta Alh wadda
kuma Alh
ya dauki dakkan so da fatan duniyar nan ya
dora
mata,har bayan Allah ya kaddari rabuwarsu.
A
lokacin ya halarci aikin hajji daga sudan
inda
yake karati,kullum sai Alh ya yi masa waya
yana
rokon ya yi masa addu'a Allah ya dawo masa
da
fatima. Sai dai gaskiyar maganar ya yi
matukar
murnar aurenta da kaninsa abdullahi,dan
tuni ya
tsufa da sanin tarangahuma abdullahi a
kwarewa
da gudunar da mulki,wadda yake yi da
karfin
zuciya da na kwanjinsa, wadannan ne kuma
za
su ba shi damar iya shugabantar
kasaitacciyar

mace kamar fatima. Wannan gabar ce kuma
ta
ankarar da shi tantamar anya babu sanya
hannun
Alh cikin sakacewar da aka yiwa abdullahi?
Lallai
biri ya so kama da mutum,dan haka ya yi
alkwarin binciko gaskiyar al'amari. Ya fara
da
neman wayar Alh tun a daren ranar,amma
duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login