Showing 30001 words to 33000 words out of 124968 words

Chapter 11 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5500

musu gaisuwarsu babu yabo babu fallasa, ko tambayar ya yaransu baiyiba, amma su da suka tambayi yasu kalifa saiya hau washe baki da fad'in duk sun a lafiya.
Takaici ya cika zuciyarsu aunty Sauda da Umma, basubi takansaba sukai masa sallama suka fito.
Umma ma sama-sama taimasa sallama ta fito tabarsu, dan anan zasu kwana sai gobe zasu wuce. Aiko bata sake bi takansuba saida daddare data kawo musu abinci, anan ta iskesu da y'an Uwanta maza, haka kawai tasha jinin jikinta da zaman hirar tasu, saidai batace dasu komaiba ta juya tana fatan ALLAH yasa alkairine.

Washe gari Abba yasamu gaisawa da Inna hajia, itama yaymata dukkan bayanin da yama y'an uwan Umma, ta jinjina wannan lamari sosai, saidai batada hurumin hanashi yin yanda yaso da y'ay'ansa, dan haka tabishi da addu'ar ALLAH ya za6a abinda yafi alkairi.
A ransa yace,  ai yama za6a, dan auren Jiddah da Alhaji Garba babu fashi .
A ranar suka koma shida Alhaji garban bayan angama nunasa cikin dangin Umma da sunan Mijin da Jiddah zata aura.
Kowa dai wannan za6i bai masaba, amma basuda hurumin hanawa saboda dai shikeda iko da y'arsa. Umma da Jiddah da su Aunty Sauda dai basusan abinda ke faruwaba, duk da sunji anad'an maganar sama-sama, saidai basu fahimci wacce Jiddarba.

Kammala biki da kwana biyu suma sukayi azamar tafiya, dama tun jiya aunty Sauda da mama Amina da aunty Hannatu sun koma da sauran dangin Abba.

Abba dai daga Barno Ashe Adamawa ya wuce da Alhaji garba, inda yasanar dasu shine zai auri Jiddah, babu mai hurumin hanashi iko da d'iyarsa, amma wasu sun nuna masa illar hakan, dan Alhaji garba yayma Jiddah Tsufa sosai. Amma ganin ya dage sai suka bishi da fatan alkairi kawai, dan kowa yasan halinsa na kafiyar tsiya.

Da daddare Inna hajia ta kira Umma gefe, cikin tausasa harshe taimata dukkan bayani akan auren Jiddah da Alhaji Garba da Abba ya sanar musu. Take hankalin Umma ya tashe, tace wlhy Sam bazata aminceba, sai dai a wannan karonkam su rabu dashi.
Murmishi Inna Hajia tayi tana jinjina kai, kafin ta nisa cikin dattako tace,  Uhm-uhm Yagana karmu soma haka dake, wannan baikai abinda za'a tashi hankaliba, ALLAH dai shine maiyi, sannan komai da kowa a hannunsa yake, karnaji karna gani ance daga 6angarenki matsala take, kibarshi yayi yanda yaso da d'iyarsa, ALLAH dai maijine kuma Mai ganine, sannan yana tare da masu hak'uri .
 Hakane Inna, amma ita yarinyar lamarinta za'a duba, wlhy koshi kansa Alhaji ya girmesa, manyanfa y'ay'ane dashi zagada-zagada, dan ko autansa saidai suyi sa'anni da Jiddar, amma dan zalunci irina zakari shine zai had'ata aure dashi? Lallai yanzu nakuma aminta da baya k'aunar yarannan da gaske........
 Koma dai Miye yagana nidai nace kiyi hak'uri ki saka masa ido, itako mucigaba da Mata addu'a, kokun koma karnaji wani tashin hankali tsakaninki dashi .
 Shikenan Inna .  Umma tafad'a wasu hawaye masu rad'ad'i Na kwararo mata .
Washe Gari haka suka baro barno ranta a 6ace, su Jiddah duksun damu da halin da sukaga ta shiga daga daren jiya zuwa yau, amma sunyi tambayar duniya tace babu komai.
Haka dai suka iso kano.
Tamkar Jira Abba yake dama da dawowar tasu saigashi a gidan bayan magriba, aunty Zulai da aunty Nafisa duk suna gidan, Maman Sadiq ce kawai suka wuce gida itada yaranta.
Babu wani 6oye-6oye ko lallashi cikin gadara ya sanarma Umma zancen Auren Alhaji Garba da Jiddah, harma da jadada mata zancen kawo kud'i da zaiyi gobe idan ALLAH ya kaimu.
Uffan batace dashiba harya k'araci hargowarsa ya fice.
Yayida tuni tashin hankali ya dabaibaye su Aunty Nafisa wad'anda Jiddah ta sume musu saboda abinda sukaji daga bakin Abba.
Wannan dare dai yazo musu cikeda k'unci da damuwa.
Washe gari Aunty Nafisa takoma gidanta cikin damuwa da tausayin Y'ar uwar tasu.
Itama aunty zulai kwanata hud'u tak'ara ta koma gidan mijinta.

Gaba d'aya gidan Umma ya canja daga yanda kuka sanshi, babu wani farin ciki ko walwala tartare da ahalin gidan a yanzu, komai ya canja musu, kwata-kwata Jiddah tabar zuwa makaranta saboda damuwa.
Tuni Alhaji garba yakawo kud'i, Wanda Uncle yahaya yayta zabga masifa akan hakan. amma sai Abba ya yayyanka masa magana wadda tai masifar 6ata ransa ya janye hannunsa daga maganar Auren Jiddah.
Kwata-kwata sati hud'u aka saka bikin, koma tunanin Yaya batun karatunta baiyiba.
Su Zarah Kansu duksun fita hayyacinsu tamkar sune Jiddahn.
Ahaka aka cinye sati biyu, ana saura kwanaki 10 cif lefe ya iso, saboda Abba yabama Umma haushi saiyasa y'an kawo lefe suka Kai gidansa da Hindu ke ciki, Aunty Nafisa da Maman Sadiq ne kawai sukaje, sauran kam duk k'awayen hajia Hindu ne. Sai shak'iyanci sukeyi wai tsoho ya iya had'o kayan lefe.
Sosai lefen kam aka kashe kud'i dan komai yaji d'am, kaikace na saurayi d'an shekara 26 ne=??.............
'

https://youtu.be/eOU-ju4f6KY

*_Zaku iya samun RAINA KAMA a audio ta wancan link d'in Na sama, Abban dausayi YouTube channel tv=??>??


Yau babu magana>?+?>??




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? [11/28/2019, 5:14 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[12.....]_*


..............Malam Mustafa yadamu kwarai da rashin ganin Jiddah a makaranta, dan da wahala kaga tayi fashi, inhar kuwa tayi washe gari sai kaga k'annenta sunzo sun fad'i dalili, kokuma idan itace tazo tafad'i abinda ya hanata zuwa.
Madina ma ta damu da rashin zuwan Jiddah, gashi ko gidansu bata saniba, dan duk iyakar shakuwarsu k'awancen iya makaranta ya tsaya, sai a yaumane takejin takaicin hakan.
Da aka tashi Malam mustafa yaso zuwa gidansu Jiddah, amma sai wani uziri ya rik'eshi, dole ya hak'ura akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
Saikuma da yamma malam yay kiranshi a waya akan yazo yana nemansa.
Bai samu ganin malam ba sai bayan sallar isha'i, dan ya iskeshi yana da bak'i. Bayan tafiyarsu yasamu gaisawa da malam.
 Mustafa dama akan yarinyarnanne, inaso asamo mana inda mahaifinta yake, dan inason ganawa dashi kafin musan abinyi .
 To malam, insha ALLAH zuwa gobe zanzo na sanar maka .
 To ALLAH ya kaimu da rai .

Washe garima malam mustafa bai samu zuwa wajen Jiddah ba, sai dai binciko Alhaji Zakari dayayi, gidansa da wajen kasuwancinsa.
Duk yanda akai malam mustafa yazo ya sanarma malam.


('('('('('('('('('('('

Jiddah dukta fige a tsaye, da kaganta kasan tana tare da damuwa, Umma takan danne tata damuwar tayita lallashinta da nuna Mata muhimmancin yadda da k'addara Mai k'yau ko sa6anin hakan, tareda tunatar da ita amfanin biyayya ga iyaye.
Da wannan shawawar warin ne Na Umma take d'an rage nauyin damuwarta, har yau take d'an ta6a aikin gyaran gidan saboda su Zarah suna makaranta.
Gaba d'aya bikin saura kwana shidda ne ya rage, amma bazaka ta6a cewa za'ayi wani biki bane agidan, dama Abba yace Umma karta sai komai, dan Alhaji Garba yace amarya kawai yake buk'ata, komai ya tanadar mata.
Wannan dalilinne yakuma saka Umma banzatar da zancen auren, tacigaba da yima d'iyarta addu'ar nema za6in ALLAH.

&&&&&

Biki ya rage saura kwana hud'u dangin Umma suka fara isowa, hakama su Aunty Sauda da aunty Zulai, kowa dai kagani babu wani d'okin auren a tattare dashi. Kowa dandai babu yanda zaiyine da lamarin Abba kawai.


('('('('('('.

Yayinda shirin biki keta kankama a gidan su Jiddah ga malam Abdul-ra'uff kam shirin zuwa Neman auren Jiddah suke ga Alhaji Zakari. Alhmdllhi sun sami isowa yana gida bisa jagorancin malam Mustafa.
Dukda Alhaji Zakari baisan mike tafe dasuba yaymusu tarba ta mutuntawa saboda ganin manyan malamai a gabansa, dukda gefen zuciyarsa Na zargin Jiddah ce takai k'ararsa garesu, shiko ya k'udiri aniyar mutuwar Jiddah ce kawai zata Hana ya aura mata Alhaji Garba. Amma duk saiya danne wannan zancen zucin nasa ya fuskanci su malam.
A nutse malam Salis yayma Abba bayanin abinda ke tafe dasu.
Abba dake masifa a zuciyarsa hace,  Ahaf zargina yazama gaskiya, to lallai dagaku har ita zanyi maganinku ne .
Kwantar da murya yayi a fili tamkar mutumin kwarai yafara magana,  ALLAH sarki malam gaskiya banji dad'in zuwan wannan magana Mai dad'i a k'uarraren lokaciba, dan abin farin cikine ga kowanne Uba yahad'a jini da malam, danasan da wannan kudiri naku daban amshi za6in Jiddah ba, yanzu haka maganar danake muku ranar asabar d'innance d'aurin aurenta wlhy .
Gaba d'aya jikinsu malam yayi sanyi, amma babu yanda suka iya, dan Neman aure akan nema bashida kyau, balle wannanma da aski yazo Gaban goshi.
Sallama sukaima Abba suka tafi, saidai gefen zuciyar malam mustafa bata aminta da maganar Abba ba. Shima Abban kuma ya tsargu da kallon da malam mustafa ke masa.
Dan haka suna tafiya yanufi gidan Umma, kiran Jiddah yay ya Kora Mata gargad'i akan wlhy idan wani malami a makarantarsu ya aiko koda kiranta taje saiya matuk'ar 6ata ranta sosai.
Da to ta amsa, takoma cikin gida tana hawaye. Umma kallo d'aya taimata ta d'auke kanta, bakuma ta tambayeta miya faruba.
Ana saura kwana biyu hajia Hindu ta maido lefen Jiddah gidan Umma, duk da ta kwashi abinda take so aciki babu Wanda ya gane sai aunty Nafisa da maman Sadiq da sukaga lefen. Amma koda sukai magana sai Umma tace subar zancen, ita ta sani, inma dai dai tayi inma sa6anin hakan kanta taimawa.
Aranar y'an Adamawa suka Iso, hakama y'an Barno, tuni gidan ya kacame da yaren Fulatanci da Hausa da kanuri, dolema sai kusan rabuwa akayi, dan gidan yamusu kad'an, wasu suna gidan Uncle yahaya wasu gidan Umma.
Gaba d'aya Uncle yahya ya kauda idonsa akan bikin dukda takaicin auren da tausayin Jiddah Na damunsa ainun.
Wannan biki dai ana yinsane kawai, amarya ma da k'yar tayarda akai mata k'unshi da kitso, gyaran jiki kam komai akace xa'ayi saita saka musu kuka tace bataso.
Tausayinta ke sakasu barinta. Duk wani shagali irinsu kamu babu Wanda akayi, dama ita bawasu k'awayene da itaba, y'an u??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wanta sune k'awayrnta da Ummanta.
Ranar d'aurin aure gida yagama d'inkewa tab, Amarya kam nacan karshen d'aki kudundune babu lafiya itadasu walida, kowanne zazza6i yamasa rijib, ko wanka basuyiba balle ai batun kwalliya.
Karfe 12 aka d'aura auren Alhaji Garba da Hauwa'u Jiddah akan sadaki naira dubu d'ari biyu.
Abin mamaki saiga Malam Abdul-ra'uff dasu malam mustafa sunzo d'aurin auren suma, saboda koba komai dai d'alibarsu ce, wadda sukeji da ita da alfahari da ita.
Tunda zancen d'aurin auren ya shigo cikin gida jikin Jiddah yakuma rikicewa, dole aka fita da ita zuwa asibiti.
Amma Kiri da muzu Abba yace wlhy ko suma take yau saita kwana gidan mijinta, shi yagaji da wannan iskancin.
Umma duk tana jinsa amma uffan bata ceba, dan itama tunda aka fara hidimar bikinnan cikin ciwon k'irji take, dannewa kawai take tana daurewa.

A asibiti sai da Jiddah tasha ledar ruwa uku, barcin data samune yasaka sauran y'an uwanta zabga tagumi sukai jigum-jigum, kowa shikad'ai yasan minene damuwarsa.
Anayin Sallar magriba Abba yazo asibitin yace a sallami Jiddah, dukda bayani da likita kemasa nason abarta tasami hutu yace Sam yanzunan yakeso, dan gidan miji za'a kaita.
Badan likita yasoba aka basu sallama suka dawo gida akahauma Jiddah shiri.
Koda akazo batun yimata fad'a Umma ficewartama tayi daga d'akin tana hawaye, amma bata bari kowa ya gantaba.
Dangi dai sun tofa albarkacin bakinsu nayima Jiddah nasiha akan abokiyar xamanta da mijinta harma da y'ay'ansa da danginsa.
Tuni Jiddah tabar kuka masu hawaye sai dai kukan zuci, a haka aka fiddota wajen motocin d'aukar amarya da akalla sunkai 25, dan haka kowa yasamu waje aka shilla da amarya.
Y'an anguwa wasu Na sambarka wasu Na tausayin Jiddah.

('('('('('('('('('('('

*Gidan Alhaji Garba mai tabarma* babban gidane sosai Wanda kallo d'aya zakai masa ka tabbatar da maishi ya tara.
Bayan an wangale musu k'aton gate d'in gidan kusan motoci goma suka sami wajen shigewa ciki harda ta amarya.
Tarba suka samu mai k'yau daga dangin Alhaji Garba, wad'anda suketa fatan ALLAH yasa wannan karon an dace Jiddah tazo kenan.
6angaren Jiddah aka kaita, Wanda ya k'awatu da kayan alatu tamkar suyi magana, komai yaji zam, duk had'uwar gidan Alhaji Garba da dukiyar cikinta hakan baisa dangin Jiddah jin zasu tayata murnaba.
Basu wani jimaba suka juya, akabar Jiddah ita kad'ai kudundune cikin hijjabi daboda zazza6i Mai tsanani daya sake rufeta.
Kusan mintuna ashirin da tafiyar y'an kawo amarya Jiddah tafara jin hayaniya sama-sama, abinda ya dameta shine matsalarta, dan haka bata damu kanta dasonjin mike faruwaba. Zuwa wani lokacima sai taji gidan tsitt tamkar babu kowa a cikinsa.
Tun tana sauraren k'arar AC har barci 6arawo ya saceta a haka, dama Allurar bata gama sakintaba.


*Ango*

Kusan k'arfe sha biyu da rabi ango yashigo gidan, lokacin gidan yay tsit kowa yakama gabansa, Daga y'ay'ansa sai matarsa hajiya deluwa.
Fakin motar yay yafito hannunsa d'auke da k'atuwar leda, Kai tsaye sashen Uwargida ya nufa Wanda yafi kowanne sashe girma a gidan.
Tsit babu motsin kowa sai AC da TV daketa faman aiki, ko ina tsaf tamkar ba taron biki akayiba, koda yake yasan babu wani Wanda ya Isa taka mata sashe da sunan zuwa biki. Ledar hannunsa ya ajiye yanufi corridor d'in dazai sadashi da d'akunan barcinta.
Na farko yafara lek'awa babu kowa, Na biyu ma haka, sai a Na uku ya hangota zaune a saman gado, hamshak'iyar macece wadda ta amsa sunanta Hajia, daka ganta kasan tagama jik'uwa cikin nera, ta girma sosai sanan tanada k'iba dai-dai gwargwado, dan bawata k'atuwa baceba can, Ammafa babu k'arya Y'ar gayuce, dan ko shirin barcin Nata kad'ai ya Isa tabbaatar maka hakan, gata Fara tas masha ALLAH.
Manyan idanunta ta sauke akansa, kafin tasaki wani murmushi cikin kissa tafara fad'in  Kaga ango Mijin Amarya Hauwa'u .
'Dan Murmushin yak'e Alhaji garba yayi, ya zauna kusa da ita k'asan zuciyarsa Na mamakin canjawarta akan wannan auren nasa, Ada inhar zaiyi aure zata d'aga hankalinta, randama aka kawo amarya bata Barin kowa yayi barci Mai dad'i a gidan, amma tunda yafara maganar auren Jiddah ko kad'an bata ta6a nuna damuwartaba, hasalima lefen Jiddah itace ta had'oshi matsayin gudun mawarta.
Fuskarsa d'auke da murmushi yad'an shafa kumatunta.
 Uwargida ran gida! .
Fari tayi masa da fararen idanunta, kafin ta furta  Fad'I kanka tsaye alhajina .
Yad'an dara,  Kinyi k'yau gimbiya ta, sai nakejima tamkar ked'in aka kawomin a yau .
Wani shegen murmushi ta Saki,  Alhajina rufamin asiri, kaga tashi katafi wajen matarka, kar zumud'in son ganinta yasaka juyemin kalaman daka tanada dominta anan wajen .
 Haba gimbiyata, aike kin wuce aimiki jirwaye da zancen wani, duk abinda yafito zuciyar Abubakar a kanki to lallai nakine, babu Mai kamanceceniya dake balle kamoki .
Murmushi takuma Saki tana kamo hannunsa ta sumbaci tsakkiya, kafin yagama dai-daita da shiga sak'on Nata ta haye saman gadon sosai taja bargo da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login