Showing 51001 words to 54000 words out of 124968 words

Chapter 18 - MUTUM DA DUNIYARSA Book Complete by Billyn Abdull.doc

07 Aug 2025

5489

Tun Jiddah Na d'ari-d'ari da y'ammatan kusa da ita har suka janye ra'ayinta tafara tanka musu, dukda larabcinta baikai nasu kwarewaba tana k'ok'ari itama. tuni hirar ilimi ta 6arke tsakainta dasu Ummusulaim. Sai hotuna suke musu, Jiddah bata ta6a damuwa da rashin???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? wayaba sai yau, saitaji inama itama tanada ita ta d'auki hotunan domin tarihi........
Tunanintane ya katse jin an Kira sunanta, d'ago kanta tayi ta kalli Aunty Siyama, Aunty siyama ta mik'a Mata wayarta.
 Aunty miya faru? Ajiye miki zanyi? .
 A'a kema ki d'auki hotunan kodan tarihi .
Godiya Jiddah taimata sosai, yayinda tuni Aunty Siyama ta juya ta fita wajen da suma aka tanadar musu kusada su Jiddah.
Suna tsaka da hotunansu wata sassanyar murya data fara jan k'ira'ar Al-Quran ta daki kunnuwansu. Kusan duk a tare suka kalli wajen, dan da hankalinsu duk baya wajen, shiyyasa basusan hidimar da akeba.
Mamaki al'ajabi mai girma ya Kama Jiddah, ganin mamalakkin wannan murya ya fitone cikin jinsin bak'ak'e irinta, sosai ta shagala da kallonsa karatunsa Na ratsata da k'ara Mata nutsuwa, batama San sanda tafara masa video recording ba kamar yanda sauran mutane ketayi, ga wajen yayi tsit bakajin sautin komai saina fitar muryar *Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina*, abin birgewa da alfaharin duk wani Mai alak'a da wannan *TAURARO*.
Saida ya kai har k'arshen Suratul Al-Ahazab sannan ya dakata yana share kwallar data cika idonsa saboda yana karantawa zuciyarsa Na fassara abinda Surar ta kunsa, hakama masana aduniyar ilimi suna saurarensa da fashin bak'i a zukatansu.
Saida yaja doguwar Addu'a kafin yakoma ma zauninsa, Mutane dayawa ya birgesu dajin k'aunarsa, mahaifinsa kam shikad'ai yasan yanda yakejin d'unbin k'aunar Aliyu a ransa, dukkannin burinsa akan ilimin y'ay'ansa Aliyu ya cika masashi.
Taro yacigaba da gudana bisa bigiren abinda ya tara mutane, dan anfara gudanar da gasa cikin nutsuwa. Wajen tsit yake bakajin komai sai sautun karatu dakuma gyara dasu Aliyu keyima yaran dan sune alk'alan Musabaqar.
Lokacin da aka ambaci Nigeria sosai cikin Jiddah ya juya, dak'yar ta iya janyo numfashi da karanto addu'a sannan tasamu mik'ewa zuwa inda kowa ke zuwa ya zauna.
Tunda ta fito ya kafeta da kallo ta k'asan ido, tashin farko yabata maki d'ari bisa d'ari a 6angaren tafiyar Nutsuwa, harta k'araso wajen yana kallonta, amma bazaka ta6a fahimtar hakanba saishi da yakeyi.
Cikin hashen larabci balaraben malamin yafara Mata tambayoyi kafin yabata izinin tsunduma ga abinda ya ajiyesu.
Sura kawai ya za6omata a cikin Al-Qurani tunda tace ta sauke a hadda ma sai abinda ba'a rasaba.
Aliyu daya d'auke kansa kamar bashine kemata kallon k'asan idoba d'azun yana saurarensu, jin Surar da Sheikh Mohammed Ali ya cafko mata saida yad'an d'ago kai ya kallesu, aransa kuwa yana ayyana shikenan sun fad'i, danshifa bai tabbatar da yarinyarnan zata iya wani abun kwarai ba, dan sanyinta yayi yawa..........
Tunaninsa ya katse lokacin da nutsatstsiyar muryarta mai zak'i da sanyi tafara karatu cikin Suratul Al-Furqan kamar yanda aka bata Umarni.
Wani irin sanyi da nutsuwa suka ratsa zuciyar Aliyu, ya lumshe idanunsa yana mai fassara Ayoyin daki-daki.
Gurin yay tsit ita kawai ake saurare.
Itadai Jiddah kanta na a k'asa bata kallon kowa a cikinsu, karatunta kawai take idanunta na zurarar da hawaye. Bata tsayaba sai da aka dakatar da ita, aka kuma d'akko mata wata surar.
Hawayenta ta share jikinta Na cigaba da tsuma tafara karanto suratul Al-Hujurat, nanma tayi nisa sosai aka kuma tsaidata takoma Suratul Al-Mutaffifin, aka sake maida Suratul Al-Ma'arij, ayanzukam sosai Jiddah take kuka a wannan sura ta al-ma'arij, saboda abinda take magana akai Na azaba ga wad'anda suka bijirema gaskiya da Ni'ima ga masu ruk'o da gaskiya, tsoratarwa da ranar hisabi da sakamakon kowa, saida takai har k'arshenta sannan aka maidata suratul Al-Zumar, nanma tayi nisa aka tsaidata aka dawo da ita Suratul Al-Ibrahim, tanayidai tana shartar kwallanta aka kuma maidata Suratul Al-'Imran.
Daganan aka tsaidata, Handkerchief d'in gabansa ya mik'a Mata ta Y'ar k'ofar gilas d'in data raba tsakaninsu, ta kar6a yayinda idonsu ya shiga cikin Na juna, cikin fad'uwar gaba tai saurin janye nata tana jawo numfashi dak'yar, wani k'amshi mai dad'i yadaki hancinta lokacin datakai handkerchief d'in kusada fuskarta, idanu ta lumshe ahankali ta furta  Masha ALLAH . saida ta goge fuskarta fes dukda hawayen nacigaba da zubowa kafin ta mik'a masa. Kansa ya girgiza mata yana d'auke kansa, a kan la66anta ta furta  Jazakallahu khairan , ya amsa da  Amin shima a saman la66ansa, dan yana kallonta ta gefen idonsa.
Anfara Mata tambayoyin daduk suka kamata, harma acikin wasu littatafan daban, cikin amincin ALLAH tana bada amsa yanda ya kamata. Duk sanda Sheikh Aliyu zaima Jiddah tambaya sai idonsu yashiga na juna, saidai kowanne yay saurin janyewa.

Dad'i sosai yacika wakilan Nageria irinsu Malam Abdul-ra'uff da manyan malamai, Sarkin Musulmai da sauransu, saboda jin yanda Jiddah ke amsa komai daki-daki, kurakuran da ake samu daga gareta k'alilanne wad'anda ba'a rasaba.
Bayan an gama da Jiddah aka cigaba da kiran d'alibai.
Saida kowa yayi sannan aka tashi saikuma an tantance wad'anda suka tsallake.


&&&&

Washe Gari Jiddah tasamu nasarar shiga cikin k'asashe bakwai wad'anda suka tsallake, a ranarma Jiddah tasha kuka wajen yin nata.
Washe gari again nanma aka kuma fafatawa da k'asashe uku da suka tsallake, ciki harda Jiddah mai wakiltar Najeriya.
Randa akai Na k'arshe ba k'aramar cika wajen yayiba, dan harda Sarkin Saudia da wasu manya-manyan mutane da duniyar Musulinci ke ji dasu, wad'anda mukeji sunayensu a bakunan malamanmu da litatafai Na Addini da suka riskemu.
A yau kam bak'aramin rud'u Jiddah ta shigaba, saboda tambayoyi su Aliyu ke zak'ulo musu masu wahala da tsunduma kwakwalwa cikin dogon nazari. Kasancewar an Fara da wuri kuma kasashe Uku ne kawai suka fafata sai aka gama da wuri, Nageria ita kad'aice takai wannan mataki a yankin Africa.
Bayan kammalawar su Jiddah manyan malamai suka koma bayan fage domin tantancewa, yayinda a wajen taro aka cigaba da gudanar da lectures masu ratsa jikkuna da duniya gaba d'aya.
Ba'a samu nutsuwar sanar da sakamako ba sai bayan salar zuhur.
Kowa dai kunnensa a bud'e yake da fatan k'asarsa tazo Na farko.
Wajen yay tsit an zubama Manyan wajen idanu dake Magana k'asa-k'asa.
An Kira *Azra Asen* Mai wakiltar k'asar *Turkiyya* wadda itace tazo Na uku.
Gaba d'aya wajen yad'auki kabbara, Azra ta fita inda ake buk'atar ganinta, bayan jinjina da yaba Mata da addu'ar fatan alkairi agareta aka bata k'yautar data samu da k'yautar Nasarar datasamoma k'asarta.
Gaban Jiddah nata fad'uwa da wasiwasin ta farkoce ita kota biyu....
Tunanintane ya katse lokacin da ake shelanta kiran sunan *Arwa Saiyyad* Mai wakiltar k'asar Saudiyya, wadda itace ta biyu. Itama dai tasamu k'aututtukan dasukafi Na Azra tareda fatan alkairi, inda y'an saudia sukai murna, dukda sunyi burin zuwa Na d'aya suma.
Jikin Jiddah duk yay sanyi, azatonta ko ancire sunantane, sai tajiyo Ana kwala kiran sunan *Jiddah Zakari Yaro* *Najeriya* sosai jikinta yahau rawa, saida taimakon Ummusulaim dasuka zama k'awaye ta iya mik'ewa, tafiya take tamkar zata fad'i saboda sassarfa da idanun mutane, ga lalurarta ta tsoron kasancewa muhali d'aya da maza, danma Ubangiji ya sauk'ak'a lamarin..
Dak'yar ta iya k'arasawa garesu. Doguwar Addu'a da jinjina ga Jiddah da iyayenta da malamanta da k'asarta sosai akayi, kafin a damk'a Mata k'autar nasararta dakuma k'yaututtuka da malamai daban-daban wad'an suka fito a k'asashe daban-daban, da manyan attajiran da suka halarci wannan gagarumar Mubabaqa. Kuka kawai Jiddah ta sakamusu harda sheshsheka, inda mutane dayawa suke tayata musamman ma mu y'an Najeriya damuke cikin farinciki.
Aliyu dake murmushi yasaka handkerchief ya d'auke hawayen da suka cika masa idanu, hakama Uncle yahya, su malam mustafa malam Abdul-ra'uff, Sarkin musulmai da sauran malamai dasuka halarci taron y'an Nigeriya duk suna tare da tsantsar farinciki, Aunty Siyama jitake tamkar k'anwarta ciki d'aya, dad'i dukya lullu6eta.
Abubuwa sunciga da gudana kafin taro ya tashi lafiya, masu murna nayi masu kuka nayi.
A ranar su Jiddah suka baro birnin Riyadh zuwa Makkah.
Kowa saiji yake da Jiddah, sai nan-nan su malam Abdul-ra'uff sukeyo da Jiddah, yayinda dad'i ya cikata, gata ga Sarkin musulmai da manyan malamai Na k'asarta da takejin labarinsu kojin wa'azinsu a redio ko TV.
Saidai abinda yabata mamaki bataga malam Aliyu ba tun barowarsu Riyadh, dan badashi suka taho Makkah ba, batadai tambayi kowaba tayi shiru da bakinta, amma haka kawai taji tana kwad'ayin ganinsa kodan tamasa godiyar Handky daya bata ranar, dan dataji d'an Najeriya ne kuma d'an mutumin da zuciyarta take kauna da girmamawa sai dad'i ya kamata, ashema tana sauraren tafseer nasa sosai batasan shi baneba sai yanzu.
Uncle yahya kam fad'a muku irin farin cikin daya tsinci kansa ai 6ata lokacine ma.
Labari kuwa yakai Najeriya tuni, sai hotunan Jiddah ke yawo a jaridu da televisions.
Lokacin da zance yakai kunnen su Umma ai kuka kawai ta sanya Na dad'i, tuni labari yagama zagaye dangi, kowa burinsa Jiddah tadawo ya k'ara ganinta. (Saikace sun manta fuskarta>?#?), sundake sai sayen jarida suke suk'ara ganinta, su Zarah ma har Umma suka sayomawa, aiko tasaka k'asan gado ta 6oye bayan sungama Karantawa, wai zata adana tarihi=??>?-?. Zumud'in dawowar Jiddah garesu dukya cikasu.
Lokacin da aka nuna Jiddah a labarai Abba da Hajia Hindu suka gani Hajia Hindu rud'ewa tayi, shikansa Abba yau saiyaji wani iri, yarinyarsace a tsakkiyar manyan mut?ne da duniyar musulinci ke ji dasu, duk surutan da Hajia Hindu kemasa baibi takantaba yatashi yashige d'akinsa saboda wani jiri dayakeji yana Neman kwasarsa.

hakance takuma kasancewa a gidan Alhaji Garba, dan gaddama suka kwaso suka dire akan ba Jiddah data zauna a gidan baceba, yayinda Ashir keta rantsuwa da ALLAH itace. Alhaji garba yace bai yardaba saiya bincika.

Yayinda wancan cakwakiyar ke faruwa a Najeriya Su Jiddah suna can suna gudar da Umrah a Makkah, tareda zagayen guraren tarihi domin k'arin ilimi, yayin da daga baya kuma suka tattarasukak nufi Birnin Madina.
Kwanansu bakwai a Madina Gari Mai tarin Ni'ima da dad'in zama, Wanda duk muminin daya shiga baya fatan yaga ya fita, kuka dai Jiddah ta shashi yayinda taganta gaban kabarin MANZON ALLAH (S.A.W) da ahalin gidansa.
Ranar jinta take wata iri daban tamkar ba itaba.
Duk inda yakamata suje wajen tarihi malam Abdul-ra'uff shine jagoransu, itadai Jiddah tana k'ara mamaki Ina Aliyu ya shiga?.
Gaba d'aya kwanakin su Jiddah ashirin Cif da tafiya suka juyo k'asarsu ta haihuwa Najeriya cikeda farin cikin d'umbin nasaarorin da suka k'unso.............
'



*_Barkanmu da Juma'a sweet sister's=??=??>???p?_*












*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=?-?=?O? [12/7/2019, 2:43 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_
[12/7/2019, 11:57 PM] =؞?Noorunnisa=؞?: *_Typing=???_*



*_=ء?HASKE WRITER'S ASSO...._*



*_=ا?MUTUM DA DUNIYARSA....!!=ا?_*
_(ya dace ya gyara kansa)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_[25?'26]_*


............Saukar dare su Jiddah sukayi, hakanne yasaka masu tarbarsu suka kasance k'alilan, tana farin cikin dawowa ga ahalinta gefe kuma na zuciyarta na kewar k'asa mai tsarki, jin hawaye kawai tai suna gangarowa a kumatunta, wanda harga ALLAH batasan yaushene suka fara saukaba. Muryarsa Mai sanyin nan ta daki kunnenta.
 Yakamata a nad'aki sarauniyar kuka ta k'asarnan .
Gabantane ya fad'i, har abadan bazata mance wannan sassanyar muryarba, da sauri ta d'ago idanunta ta saukesu a kansa.
Janye idonsa yayi daga gareta tareda d'ora Mata handky d'in hannunsa saman trolley d'in gabanta ya wuce.
Da kallo kawai ta bisa tana sauke wani kasalallen numfashi a hankali, sanye yake cikin shadda ruwan gwaiduwar kwai, yazuba dukkan hanayensa a aljihu, dukda darene hakan bai hanata shaida k'yawun haibarsa ba, mamaki take dama ashe ya dawo Najeriya shiyyasa bata sake ganinsaba a can.........
 ALLAH ya tabbatar .  Muryar aunty Siyama ta katsema Jiddah tunaninta .
Janye idanunta tayi daga kan Sheikh Aliyu daya k'arasa suna gaisawa da Uncle yahya.
Jiddah ta share hawayenta tana murmushin yak'e,  Aunty addu'ar mi kikeyi? .
 Ta abin alkairin danaga yana Neman k'ulluwa mana Jiddah .
Jiddah bata fahimci inda Aunty Siyama ta dosaba, dan haka sai tai shiru. Itama Aunty Siyamar bata ja zancenba daga nan, saima haramar tafiya da sukeyi, dan dama sun tsaya jiran Malam ne dake gaisawa da mutane.
Har gida sukaima su Jiddah rakiya.

Su Umma suna zaune jiran isowar su Jiddah, dan Uncle yahya ya sanar musu ta waya, dan haka sunajin tsayuwar motoci suka fito cikeda d'oki.
Tuni farincikin ganin juna yasa sun manta da kowa, murmushi Aliyu yayi yana lumshe idonsa, ba k'aramin birgeshi wannan family sukaiba, hakama Malam sun matuk'ar birgeshi, Aunty Siyama kam tuni taji kewar mahaifiyarsu ta mamayeta.
Sai Uncle yahaya ne ya tsaya sukayi sallama da mutane, amma su Jiddah tuni sunyi ciki.

&&&&

Barci dai yau sai 6arawone ya d'auki wannan ahali, washe garima da wannan farin ciki suka tashi, kafin kace mi gida ya d'inke da y'an taya murna, aunty Nafisa kam ai tunda farar safiya ta iso.
Haka wannan yini Yakuma kasance musu cikin kar6ar bak'i, ita Jiddah ma sai kunya takeji.
Dangin Umma ma sunata kiran waya, kawu Bunami (yayan Umma) yace Jiddah tafad'i komi take so indai baifi k'arfintaba zai Mata, dan d'ansa Banu da autar su Umman Balu suna nan zuwa Kano.
Rasama abinda Jiddah zata za6a tayi, dan haka tabashi za6in ya saya Mata komi yaga yamasa. Albarka dai tashata wajen wajen kakarsu.
Rana ta uku da dawowar su Jiddah saiga Abbah suna tsakar gida suna hira da innarsu Balu ya shigo, duk shiru sukai sai Balu d'ince dake murmushi. Shima saiya Saki fuskarsa yana fad'in  Ah ah yau Balu ce a kanonmu haka? .
 Aiko nice yayanmu, ai tunda nazo nake cigiyarka akace kayi tafiyane .
Cikin in ina yake fad'in  E...eh...eh ta..fiya nayi wlhy, jiya na dawo da daddare shiyyasa .
Su Zarah dake zaune kawunansu a k'asa duk saida suka d'ago suka d'an kallesa saboda jin k'aryar da ya sharo babba dashi.
Yayinda shikuma yad'an hararesu yacigaba da gaisawa da Balu.
Duk abinnan dake faruwa Umma na cikin kicin tana jinsu, amma ko tarima batayiba, saida taji shigarsa d'aki sannan ta fito tabi bayansa da ruwa d'auke a hannunta.
Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta gefe tana gaisheshi, jin a yanda ya amsa saita kuma kallonsa, harma ta kasa hak'uri saida tace,  Lafiya kuwa? .
 Lafiya lau, mi kika gani ne? .
 Babu komai .  Umma ta fad'a tana mik'a masa ruwan .
Soyake yay Mata murnar nasarar da Jiddah ta samu amma ya kasa, sai mulmula maganar yake a zuciyarsa. Tsaf Umma na lura dashi, amma sai tayi tamkar bata ganshiba. Daga k'arshe daya rasa ta inda zai kamo zance saiya maida akalar maganar kan zuwan Balu. Itadai Umma eh a'a shine amsarta dashi, harya k'araci zamansa yay mata sallama ya tafi.
Sosai hakan yayma Umma da Jiddah ciwo a zuciya, koba komai yakamata ya nuna murnarsa ga nasarar data samo, kodan ma darajar Addininta data samo nasarar a dalilinsa, amma saiyay k'ememe.


('('('('('('('('('('('

 Aliyu kasan miyasa na kiraka kuwa? .
 A'a baba .
Zama malam ya gyara sosai yana murmushi,  Wato Aliyu abari ya wuce shike kawo da rabon wani Na hango maka .
Kallon malam, Aliyu yayi dan bai fahimci inda zancen ya dosaba.
Malam yakumayin murmushi  Zancen yarinya Jiddah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login